Showing 9001 words to 12000 words out of 157423 words
wurin dining ta jeresu, juyawar da zatayi ta hango Umar Farouk sai cika yake yi, da sauri ta ƙarasa wajensa ganin gefen bakinsa da jini tayi saurin zaunawa kusa dashi tana shafo wajen cike da kulawa ta ce, "Na shiga uku Faruk me ya sameka haka ne?" Har lokacin zuciya bata sake sa ba ya kasa cewa komai sai ma cire hannunta da ya yi yana juyar dakai gefe, "Ya Salam! Kamun bayani Umar meya sameka ne". ta faɗa cikin sigar lallashi tare da bayyanar da damuwa ƙarara akan fuskarta, nan ma yafi minti biyar bai tanka mata ba gaba-daya duk tabi ta ruɗe sai faman lallashinsa takeyi tamkar wani ƙaramin yaro, iska ya furzar da iska ta baki kafin yace. "Mom wai kamar ni za'a tare wa hanya? Ni za'a ce a daka Mom saboda an gama renani". "Wait Umar Farouk duka kuma? kamar ya a dake ka? Ko ni dana haifeka tun kana ƙarami ban taɓa sa hannu na dake ka ba balle yanzu daka girma, waye yai wannan gangancin halama bai san kai ko ɗan gidan waye ba? Bai san waye ubanka bane hala?" Momy ta faɗa cikin ɓacin rai tana kallonsa, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace, "Zan sanar dashi in dai a makarantar yake, kuma ko yanzu nayi masa abinda gobe akace ya sake tsare mani hanya bazai yi ba, zan kuma cigaba da yi masa matukar yana a cikin makarantar nan sai nasa ya barta da ƙafafuwansa, "No kar kayi haka Umar Farouk, kasan halin mahaifinka bazai taɓa goya maka baya ba idan ka aikata hakan har wani abu ya taso daga baya, kayi hakuri ka ƙyalesa ina ai ka ja masa kunne ko?" "Mom ki dubi abinda yayi mun fa?" Ya shafa gefen bakinsa inda ya fashe kaɗan, Mom ta kallesa tace, "Na gani, amma garin ya hakan ta faru Umar Farouk? Ko faɗa kukayi dashi ne?" "Kusan haka Mom ". "To kayi hakuri na tabbata kayi masa abinda yafi wanda yayi maka, don haka ka ƙyalesa, ka tashi kaje ka watsa ruwa kafito ga abinci na shirya maka kaci, ta shi muje na haɗa maka ruwan wankan amma don Allah wannan magana ta mutu anan na kashe ta kaji ko yarona?" Ta faɗa tana shafa kansa cike da son lallashinsa, ba yadda Umar Faruk ya iya don duk zuciyarsa yana matuƙar son mahaifiyarsa, duk abinda zata hanasa ko yana sonsa ya hakura kenan, ya ɗago kai ya yi ya kalli mom tare da riƙo hannunta yace, "Shikenan Mom na hakura wake amma, ba don haka ba da ya yabawa aya zaƙi". "Aikin kenan, Indai kaine nasan zaka iya fiye da haka tunda ba gudun abun magana kakeyi ba, yanzu kuma kai da waye Farouk?" Dady da fitowarsa kenan daga ɓangaren Hajiya Hussaina uwar gidansa ya faɗa yana ƙarasowa cikin paloun riƙe da hannun Fauzah, ɗago kai Umar Farouk ya yi ya gaishesa sannan ya miƙe zai fita, "Ina zaka je? Koma ka zauna". Dady ya faɗa yana nuna masa wajen zaman daya tashi ba alamun wasa a fuskarsa, komawa ya yi ya zauna Dady ya ce, "Tambayarka nakeyi kai da waye kayi faɗa?" "Ban san shi ba Dady". Umar Farouk ya faɗa yana haɗe rai, "Ai tun a office an kirani an faɗa mani komai, yanzu kai abinda kayi dai-dai ne? Ka fasa masa glass ɗin mota sannan kayi faɗa dashi saboda ɗai ya tare maka hanyar fita sai kace gate ɗin na gidanku ne, to shi kuma fa daka tare masa hanya kaki bashi waje ya wuce sannan kuma ka fasa masa glass ɗin mota me zai ce Farouk? Baka fa san shi ba yanzu ta ina kake tunani zaka gyara wannan laifin daka aikata". "Dady shima fa yayi mani laifi, akan me zai tare mani hanya?" Umar Farouk ya faɗa cikin ɗan fushi tare da miƙewa yabar paloun, Momy dake gefe tsaye tace, "Ka gani ko? Yanzu fisabilillahi daga faruwar abu har ansamu yan gulma an kiraka an faɗa maka, kai kum kazo ka zauna akai ka yarda? Wlh ni narasa me yaron nan ya tare wa mutane, duka duka Farouk guda nawa ne da za'a tasa shi agaba haka, kazo ba bincike kuma ka rufesu da faɗa". "Yau kika haifesa Maryam, nace yau kika haifesa! Wannan wace irin tarbiyya ce kike ɗora yaronki akai? Shikenan yayi laifi baza'a yi masa faɗa ba? A gabanki ina yimasa magana ya tashi ya tafiyarsa. gaba-daya kin ɓata yaro da sunan soyayya sai abinda yaga dama yake? To baku isa ba daga ke har shi wallahi, bazai yiwu ya riƙa dauko mani magana ba a gari, kina kallo baya da abokanai sai mata amma kullum faɗa kikeyi ai ƙawayensa ne abokan karatunsa, to na gaji idan bazai yi karatun ba aure yake so ya fitar da mata nayi masa auren na huta.." Yadda Mom taga ran Dady ya ɓaci yana ta faman faɗa ya sata yin shiru har ya gama sannan tace, "Kayi haƙuri, amma don Allah kana bincike idan aka faɗa maka abu akansa, gabaɗaya abun nan na tambayesa ya faɗamun ba haka ya faru ba, shi wancan ɗin shiya fara shiga harkar sa..." Wani dogon tsaki Dady ya ja jin abinda take faɗa haɗe da miƙewa yabar paloun, bai san har sai yaushe zata fara yarda da kuskuren Umar Farouk ba, ko sau dubu ya yi laifi itama sai ta karesa sau dubu, sashen sa ya nufa ita kuma Momy ta nufi na Umar Faruk da abincinsa data jere masa akan tray, ko data shiga yana wanka bai fito ba, ta sauke ajiyar zuciya tare da ɗauke masa kayan daya cire daya watsar anan paloun ta gyara sannan ta fice daga ɗakin, tasan tunda har ya shiga wanka to ya hakura, hakan ya sama mata natsuwa a zuciya tare da bata tabbacin ya sauko daga dokin fushin daya hau.
*****
A can ɓangaren Ya Nu'aym kuma suna isa gida sashensa ya nufa ya shiga toilet ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya, yunwa yake ji sosai don haka yana gama feshe jikinsa da turare ya nufi palour, kana kallonsa kasan babu walwala a tattare dashi, a gefe ɗaya kuma bakinsa ya ɗan kumbura inda ya fashe, fuskarsa ma da tayi ja har yanzu bata koma normal ba saboda hasken da yake dashi, Iyayensa ya tadda zaune a saman dining tare da Nu'aymah da itama har ta watsa ruwa ta fito shi kadai ake jira, wajen ya ƙarasa ya jawo kujera ya zauna ba tare daya kalli ɗaya daga cikinsu ba yace. "Ummi barka da marece, Abba ina wuni?" Tare suka amsa masa da lafiya ƙalau kafin Abban nasa da tunda ya doso wajensu yake kallonsa yace, "Nu'aym me ya jimaka a baki ne? Me ya samu fuskar ka haka?" Ba tare da Nu'aym ya ɗago ba yace "Ba komai Abba". Ummi ce tasa hannu ta ɗago fuskarsa idanuwanta suka sauka agefen da bakinsa ya ɗan taso tace, "Karya kakeyi Nu'aym akwai abinda kake ɓoye mana, me ya fasa maka baki haka?" Ya Nu'aym da har ya zuba abincinsa ya samo ci yace, "Ummi ba komai nace". "Idan haka ne ya akayi naga fuskarta haka? Kafara ɓoye muna abu ko?" "Abba mun ɗan yi faɗa ne da wani yaro, shine har ya fasa glass ɗin motar Nu'aymah". "What!?" Daga Ummi har Abba suka faɗa tare, Abba har yana miƙewa tare da dukan dining table ɗin dake gabansa kafin yaci gaba da cewa, "Kaga matsalar ƙasar nan ko? Shi yasa bana son zamanka anan kana mingling da yaran talakawa da basa martaba komai balle daraja sa, ya fasa mata glass ɗin mota sannan kai ma ya fasa maka fuska, to kai me kayi masa ne?" Nu'ayma yayi shiru bai ce komai ba yaci gaba da cin abincinsa, Nu'aymah ce ta da gaba-daya ta tattara hankalinta ga abincin da take ci tace.
"Abba shima ya fasa masa baki amma laifin ya Nu'aym ne, sai da nace ya ƙyalesa kada ya biye masa amma yaƙi.." "Ke dallah rufe mun baki shashashar yarinya". Ummi tayi saurin katse Nu'aymah tana ci gaba da cewa, "So kike yi ya zama sakarai kamar ke?". Abba da takaici ya gama rufewa yace. "Fadamun wane yaro ne shi? Na rantse idan na ganowa ko waye ubansa sai ya biya kudin wancan glass ɗin motar daya fasa, kai kuma ka haɗa kayanka gobe ka koma wajen aikinka don banga ma amfanin zuwan nan naka ba". "Abba sai zuwa jibi zan wuce". Ya Nu'aym ya faɗa yana ci gaba da cin abincinsa hankali kwance. Ummi ta ɗago ta kallesa tace, "Ai da gobe da jibi ɗin duka ɗaya ne kawai ka koma hankalinmu zai fi kwanciya, upper month muna nan zuwa idan su Nu'aym sun kammala exam". "Amma Ummi ban gama abinda nake son yi ba, shikennan don ɗan wannan abun ya faru duk sai kubi ku tayar da hankalinku? Gaskiyar Nu'aymah ne laifina ne, da ban biye masa ba da duk hakan bata faru ba, Please Ummi, Abba don Allah kubar wannan zancen, zuwa jibi zan koma kamar yadda na tsara". Yana gama maganar ya ture abincin gabansa ya miƙe ya bar wajen. Da kallo duka suka bisa cike da mamaki kafin Abba ya kalli Nu'aymah yace, "Ke ɗan gidan waye suka yi fadan dashi?". "Ban sani ba Abba". Nu'aymah ta faɗa don ita kam bazata iya faɗar ko waye ba, Ummi ta maka mata harara haɗe da cewa, "Baki sani ba halama ba ɗan makarantar ku bane?" Nu'aymah ta langaɓe kai tare da kallon Ummi sannan tace, "Yanzu Ummi Shikennan duk wanda ke cikin makarantar dole sai na sanshi? Please kubar maganar mana kamar yadda yace". "Anki abari shashasha da bata san ciwon kanta ba, wallahi kika kuskura na ga hannunki ga key ɗin motata sai na saɓa maki". ta ƙare zancen aɗan hasale tare da miƙewa yanar wajen itama ta koma palour, Abba ma bai iya cin abincin ba ya tashi ya fice daga gidan saboda dama cikin shiri yake zai fita...
ALLAH KA JIKAN IYAYENMU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
7.
Nu'aymah ma miƙewa tayi ta nufi ɗakinta, tana shiga ta tadda wayarta na ƙara da sauri ta ƙarasa inda take ajiye agefen bedside ta ɗauka ta ɗaga tana zaunawa bakin gado. "Hello Besty ykk?" Ta faɗa bayan takai wayar a kunnenta, Janaam dake kwance saman katifar ɗakinta irin ƙatuwar nan da inches ɗinta zai kai girman gado ta sauke ajiyar zuciya tana cewa. "Alhamdulillah, ina kika shige Aymah inata kiranki baki ɗaga ba, wallahi na dauka wani abun ne ya faru da naji shiru baki ɗaga ba, ya jikin Ya Nu'aym?". "Yaji sauki ina sa ran ma ya fita don yanzu su Abbah suka gama faɗa dashi wai ya koma gobe". "Injin ba saboda abinda ya faru bane?" "Kusan haka dai Besty, kin san shi Abbah yafi son zaman ya Nu'aym can ƙasar UK, shine fa da ya ji abinda ya faru shi da Ummi suka ce lallai sai ya koma gobe, amma dai naji kamar yace bazai koma gobe ba sai jibi". "Allah ya kyauta Besty, ai abunne baiyi daɗi ba, shiyasa kika ga bana shiga sha'anin Umar Farouk, infact ma ni na tsanesa wallahi". "Tofah! Da yai maki me? Ni fa mamaki kike bani Janaam, ban taɓa ganin Umar Farouk ya shiga harkar wani ba tunda muke makarantar nan, kawai dai idan mutum ya shiga harkar sane bazai sha da daɗi ba, kuma banga laifinsa ba saboda ko kece bazaki lumunci ariƙa shiga gonar ki ba haka kurum dole ki dauki mataki". Na taɓe baki don tuni na kwana da sanin ƙawar tawa ta fada a soyayyarsa, cikin rashin gamsuwa da kalamanta nace, "Wannan duka bazai zamo hujjar wulaƙanta ɗan adam ba, ai abun nasa ne idan kika lura Besty yai yawa wallahi, kai kenan baƙin rai da cin zarafin jama'a, ga baƙar zuciya da muguwar ɗabiar zama cikin yan mata sai kace ɗa.." "Kinga ya isa haka, wannan rayuwarsa ce fa duka! Inaga kawai mubar zancen nan, bana son yi da mutum?" Nu'aymah ta ƙare zancen kamar ta ɗan ji haushi, na saki dariya haɗe da cewa, "Ba wani yi da mutum kawai dai kice bakya son gaskiya". "Na ji ɗin, ya Mamah take?" "Tana lafiya ina Nihla mutuniyar?" Nu'aymah ta amsa mani da "Tunda muka dawo ban sakata a idanuwana ba, "Taya zaki sakata kina cin zalunta, gobe karfe nawa zamu fita?" "Karfe bakwai" Nu'aymah ta faɗa, zaro idanuwa nayi haɗe da cewa. "Lokacin ko bacci ban tashi ba, 8 fa zamuyi lecture?" "Idan bance maki haka ba bazaki fito da wuri ba har sai kinsa mun makara, yau ma ba don Allah ya taimaka malamin bai shigo kan lokaci ba da tsaf kin ja ya hana mu shiga". "A'a fa, yau ba laifi na kaɗai bane hadda na Ya Nu'aym". Na faɗa ina dariya don dama nasan zata yi wannan korafin, "Ehmm to shikenan zan faɗa masa ko me kika ce".
Fira sosai mukayi da ita kafin muka yi sallama jin ankira sallah magrib. Tashi nayi na shiga toilet na ɗauro arwala nayi sallah sannan na fita zuwa ɗakin Mamah, samu nayi tana kitchen tana aiki na karɓar mata ina cewa. "Sannu Mamah, tun ɗazu nake son zuwa na riƙa maki aiki na tsaya yin waya da Nu'aymah". "In jin dai tana lafiya?" "Lafiya klw, gobe 8 muke da lecture Mamah in Sha Allahu tun bakwai da rabi zan fita". "Ba laifi, sai ki samu wani abunda zaki haɗa sai ki tafi dashi tunda nasan ba tsayawa zakiyi nagama breakfast ba, akwai wrap ɗin samosa acikin fridge dana haɗawa yayanki ɗazu, ki ɗauka ki haɗa gobe idan kika tashi warming ɗinta kaɗai zakiyi". Na amsa wa Mamah da to ina ƙarasa kwashe tuwon dana isko tana tuƙa wa, bayan na kammala na kwashi kayan abincin na kai akan dining na jere sannan na koma kitchen na soma haɗin samosa ɗin don akwai komai a kasa, Mamah kuma ta shiga wanka, ina kammalawa na sakata cikin fridge na gyara kitchen ɗin tsaf sannan na dawo falo na zauna ina latsar wayata kafin Mamah tafito. Ya Jameel ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Na amsa ina ajiye wayata gefe haɗe da miƙewa na karɓi ledar daya shigo da ita a hannunsa ina yi masa sannu da zuwa, murmushi ya saki yana cewa. "Barka da hutawa auta". Don wata rana haka yake kirana kasancewar daga ni sai shi Allah yaba iyayenmu, mahaifin mu kuma ya rasu bayan na kammala secondary, lokacin kuma ya Jameel na wajen bautar ƙasar sa, mutuwar mahaifin mu ta haifar da abubuwa da dama na kewa da kaɗai ci atare damu, sai dai bata canza kyakkyawar kulawar da muke samu daga wajensa ba lokacin da yana raye kasancewar babu abinda muka nema muka rasa daga wajen Ya Jameel, tsaye yake sosai a kanmu ni da mahaifiyata, duk wani abu na jin daɗi yanayi mana daidai ƙarfinsa, baya taɓa bari mu gani ga wani muyi sha'awa ba tare da muma mun mallaki abun ba, kama daga kan ci, abun sha da kuma suturar sawa don yana gama bautar ƙasarsa a ma'aikatar da aka turasa Allah ya dubi maraicinmu suka ɗaukesa aiki, shi ya sama mani gurbin karatun gaba da secondary mai kyau kuma yake biya mani tare da ɗauke duk wasu lalurorina na makaranta. Sau ɗaya bai taɓa gajiya ba wajen bani kudin transport da sauransu har Allah ya hore masa abun hawa, lokacin ne kuma Besty tafara kaini da ɗauko ni kasancewar ajin mu ɗaya kuma a anguwar mu ɗaya, ko kadan bai son alakar mu da ita kasancewarta yar gidan masu kuɗi, a cewar sa baya so watarana tayi mani gori ko tayi mani wani abun da zai zubar mani da mutunci na don bazai lamunta ba, yaso hanani tafiya school tare da ita a motarta yace shi da kansa zai riƙa kai ni kuma ya ɗauko ni, amma Mamah tace ya ƙyaleni ai kamar rage masa aiki ne tunda shima aiki yayi masa yawa ba zaune yake ba, babu yadda ya iya dole ya haƙura ya barni tare da ja mani kunne akan nadai rage shige masu, ni kuwa a nawa tunanin ba wani abu bane don tun muna ƙanana tare muke da Besty iyayenta sun san gidanmu nima iyaye na sun san gidansu, sai dai ba kamar yanzu ba da shaƙuwar mu tayi yawa.
Turo baki nayi jin abinda ya faɗa ina buɗa ledar dana karɓa a hannunsa haɗe da cewa, "Ni dai Ya Jameel kadena cemun auta, Allah da baba nada rai kasan na isa Mamah ta haifa mun ƙane ko ƙanwa". "To ai dai ba'a haifa maki ɗin ba yanzu sai kiyi hakuri, ko baba nada rai tunda aka zo wannan lokacin ba lallai ne a haifi wani ba, don haka sai ki hakura tunda kece ƙarama ki amshi auta". Mamah ce ta fito tana faɗin. "Kara dai kam, saboda ni da ya'ya yanzu ai sai naka Jameel idan ka haifa ko kuma nata".
Nasan halin Mamah biye masa zatayi suyi ta tsokanata don haka sai kawai na wuce kitchen da ledar dana karɓa hannunsa, fruit ne sai drinks masu sanyi, na cire drinks ɗin na ɗauki fruit ɗin na wanke na gyara sannan na hado da drinks ɗin akan tray na kai saman dining, fira na isko sunayi da Mamah tana yi masa zancen aure yana cewa ta taya shi da addu'a Allah ya bashi ta gari wacce zata kula mashi damu ta kuma yi hakuri zama tare damu don bazai iya barin mu yaje yayi gini wani wurin ba muna nan, Mamah tace, ba komai indai ya dace da mata ta gari da zata kula mata dashi ita Alhamdulillah ta yi zaman ta anan ɗin, ni dama inda rayuwa aure zanyi natafi gidan mijina. Kaina na ɗora a saman kafaɗarta haɗe da cewa, "Nifa Mamah bazanyi aure ba na fiso naci gaba da zama tare dake har ki