Showing 42001 words to 45000 words out of 157423 words

Chapter 15 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

504

kwanta, idan baka son sanar dani shikenan ka tashi kaci abinci, kayi sallah magrib?" Ya girgiza mata kai tamkar wani ƙaramin yaro Momy ta miƙe tsaye Sannan ta riƙo shi tana tayar dashi ta taimaka masa ya shiga toilet,  sai data duba ɗakin ta hango carpet shimfide wacce ya yi sallah ɗazu sannan ta koma palour, abincin data zo dashi ta ɗauka ta shigar masa dashi ta zauna a bakin gefen gado tana jin gabaɗaya zuciyarta ba daɗi, tana zaune ya yi sallah ya gama ta taso ta zuba masa abincin a plate, pounded yam ce sai stew ɗin kayan miya data sha naman rago da crayfish, Umar Farouk nason irin girkin sosai shiyasa a kullum ba tada zaɓin kanta wajen girka abinda za'a ci sai abinda tasan yana so, da kanta ta ɗebo abincin ga spoon ta kai masa abaki, kauda kai ya yi ta sake kai masa abincin tana cewa, "Farouk so kake yi nima ka jefani cikin damuwa? Kasan a wane yanayi nike tun ɗazu akan wanan halin da kake ciki?" Bai iya cewa komai ba sai dai kawai ya juyo ya soma karɓar abincin yana ci, Allah ya sani baya jin son cin abincin a ransa kawai ya karɓa ne saboda baya son damuwarta, bai wani ci sosai ba don ko rabin ƙullin ɗayar data aza masa bai canye ba ya kauda kai gefe, bata son takura masa sai kawai ta ajiye abincin tasa wani plate ɗin ta rufe, wayarta ta ciro cikin jaka ta kira Dr. Mahmoud family doctor ɗin su, kusan missed call biyar tayi masa bai ɗaga ba cike da jin haushi ta ciro wayar a kunnenta tana tsaki, "Ina Dr. Mahmoud kuma ya shig haka ne anata kira bai ɗaga ba?" Ta tambayi kanta tana juya akalar kiranta ga Saleem idanuwanta na akan Umar Farouk daya jingina da jikin gado ya ɗora kansa tare da lumshe idanuwansa ya rufesu tamkar mai bacci, ringing biyu Saleem ya ɗaga wayar yana faɗin, "Momy Barka da dare, ina wuni?" "Yawwa Saleem lafiya ƙalau, kana gari ka dawo kuwa?" "Eh Momy, lafiya dai ko?" Ya faɗa jin muryarta cike da damuwa, "Eh to kazo gidan gonar Dadyn Farouk ka sameni, ina ka san wajen ko?" "Eh". "To kayi sauri ina jiran ka". Ta faɗa tare da katse kiran, wayar Umar Farouk dake cikin jakarta ce ta hau ruri, ta miƙa hannu ta ɗauko jakar ta ciro wayar, kiran ya tsinke don haka sai kawai ta miƙawa Umar Farouk, yana karɓa kiran ya sake shigowa, sunan Billy ya gani ya kafa tsaki yana jin ƙirjinsa nayi masa wani irin nauyi, faɗuwa gabansa ya soma yi tunowa da fuskar dake cikin yi masa barazana aduk lokacin daya tuna da ita, da sauri ya kashe wayar gaba-daya ya ajiye a gefe yana sauke wata irin ajiyar zuciya tare da maida idanuwansa ya rufe kamar yadda suke ɗazu, Momy ta ɗora hannu saman sumar kansa tana shafawa a hankali, wayarta ta yi ƙara tayi saurin ɗagawa, ganin number Dr. Mahmoud tayi saurin kai wayar a kunne, gaisawa suka fara yi kafin ya shiga bata hakuri na rashin ɗaga kiran nata, ya shaida mata cewa an kawo masu wata patient ce emergency shine suka shiga tiyata da ita amma yanzu ya fito sallar magrib zai yi, "ok to Shikennan, idan ka gama Please Farouk ne bai da lafiya don Allah kazo ka duba shi, mun nan gidan gonar Dadynsa". Mommy ta faɗa tana riƙo hannun Farouk ɗin tana matsawa a hankali, Dr Mahmoud ya amsa mata da "to" sannan sukayi sallama.

Ba tare da Umar Farouk ya buɗe idanuwansa ba ya ce, "Why Momy?" Hannunta ɗaya ta sake ɗorawa a saman hannunsa da take riƙe dashi tana cewa, "Ya za'a yi na zuba maka idanuwa haka Farouk? Akwai fa zazzaɓi ajikin ka sosai kawai ka fiye kafiya ne?" jin abinda ta ce ya sa bai sake cewa komai ba daga haka ya yi shiru, ba'a jima ba Saleem ya iso yai knocking a bakin kofa, wayarsa Momy ta kira ya ɗaga ya ce mata gashi bakin ƙofa, dama tayi tsammanin shine don haka tace ya shigo ciki, bayan ta gama wayar dashi ta kalli Umar Farouk tace, "Saleem ne zaka iya mu koma palour?" Umar Farouk ya miƙe cikin wani calmness na shi kamar ba shi ba ya nufi palour Momy ta rufa masa baya, zaune suka samu Saleem har ya shigo ya yiwa kansa wajen zama, yana ganin Momy ya miƙe yana gaisheta shi kuma Umar Farouk ya je kusa dashi a saman doguwar kujera ya kwanta yana ɗora hannunsa a saman goshin sa ya ɗan rufe fuskar dashi, "zauna Saleem". Mommy ta faɗa tana nuna masa kujera bayan ta zauna, kallon Umar Farouk tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya tana maido kallonta ga Saleem da shima idanuwansa ke kan Umar Farouk ɗin ta ce, "Saleem kada ka ɓoye mun gaskiya, ina so ka faɗa mun me yake damun abokin ka, yau tun da ya dawo makaranta yake cikin wannan yanayin da ka gansa, abinci ma daƙyar na samu ya ci kaɗan, me yake faruwa dashi ne?" Sai da saleem ya kalli Umar Farouk da yaga har ya ɗan yi wata irin faɗawa sannan ya ce, "Momy ban san abinda ke damunsa ba gaskiya, amma dai..." A hankali Umar Farouk ya buɗe idanuwa yana kallonsa, bai san me yasa ba ya ji baya son ya sanar da Momy abinda ke faruwa ba, Saleem yaci gaba da cewa, "Akwai wata yarinya da suke samun yar tsama da shi basa jituwa ko kaɗan da ita, shine yau...." Saleemya kwashe duka abinda ya faru yau wajen exam har zuwa marin da tayi masa ya sanar da Momy, runtse ido Momy tayi tana jin tamkar a fuskarta yarinyar tayi marin, shi kuma Umar Farouk a hankali ya lumshe idanuwa ya mayar ya rufe, shi ba marin ne ya tuno ba, hoton fuskar Janaam dake saka zuciyarsa kaduwa idan ya tuna da ita shi ya dawo masa a fuska, jikinsa ya ji ya amsa duka yana jin zuciyarsa na wani kumbura tamkar ana hura mata iska, sai daya sauke wata irin karfaffar ajiyar zuciya sannan ya ji ta rage masa nauyayyen yanayin daya ji ya tsinci kansa a ciki, Momy ce da ranta ya gama ɓaci ta cewa Saleem, "'yar gidan waye wannan yarinyar? Wane irin courage ne take dashi da zata iya sa hannunta akan fuskar ɗana? Ta san ko waye shi da kuma matsayinsa? Waye ita kuma yar gidan uban waye?" Saleem yace, "Kiyi haƙuri Momy, shima yana yi mata..." Kafin ya ƙarasa maganar Momy da ranta ya gama ɓaci ta katsesa tana faɗin, "She deserved it Saleem koma meye yake yi mata, meye haɗin ta dashi da ta shiga rayuwarsa? Matsayinsu ɗaya ne da zata ce duk abinda ya yi mata sai ta rama?" Sake da baki Saleem ke kallon Momy kafin ya yi ƙasa da kansa yace, "Am sorry Momy". Tana wata irin cika ta kalli Umar Farouk ranta a ɓace tace, "Me yasa ka kyaleta yarona? Me yasa baka gaggaura mata maroran da har ta mutu tabon shacin yatsun hannayenka bai fita a fuskarta ba? Me yasa baka bar mata tarihin da ko gobe aka ce ta mari wani baza ta koma ba? Ka bani kunya wlh, to bari ka ji, daga yau bana so ka sake ɗaga mata ƙafa har kubar makarantar, ina so ka nuna mata babban kuskure data aikata ka ji ko? Stupid girl na tsane ta". Ji Umar Farouk yai surutun Momy na sake haifar masa da ciwon kai, don haka ba tare daya ce komai ba ya miƙe ya koma cikin ɗaki ya haye kan gado abunsa ya kwanta, shi da zata tafi tabar shi shi kaɗai ma da zai fi jin daɗi akan wuɗannan suruttan mara amfani da suka zo suna yi masa, don ba ƙaramin sake jefasa a wani yanayin suke sake yi ba..

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA, KI BIYA NAIRA N1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

                            25.

"Saleem, wlh Allah ya isa tsakani na da yarinyar nan data jefa mun yaro acikin wannan halin, da nasan gidansu sai na je itama na ɗauketa marin da sai iyayenta sun yi jinyarta don na nuna mata irin gagarumin kuskure data tabka, shashashar banza da wofi". Mommy ta faɗa tana fitar da wani iska a baki, a dai-dai lokacin Dr. Mahmoud ya ƙaraso ya kirata ga waya ya sanar mata gashi ƙofar gidan, ta kalli Saleem ta ce, "Je ka shigo dashi."

Dubasa Dr Mahmoud ya yi ya ga zazzaɓi ne kawai ke damunsa, allurai ya yi masa bayan ya tambaya ko yaci abinci Momy ta ce eh sannan ya rubuta magunguna ya ce a siyo a bashi ya sha, Momy tayi masa godiya sannan ya yi masu sallama ya tafi, bayan mintuna goma itama ta miƙe ta isa wajen Umar Farouk da har bacci ya soma ɗaukar sa saboda hadda alluran bacci akayi masa, dafa kansa tayi tana shafawa a hankali kafin tayi masa addu'a ta tofa masa ta gyara masa rufar da yai da duvet, palour ta fito ɗauke da jakarta tana cewa Saleem dake zaune yana latsar waya. "Muje Saleem a siyo magani sai ka dawo ka kwana tare dashi, ina fatan hakan ba damuwa ko?" "Eh Momy". Saleem ya faɗa haɗe da miƙewa ya bi bayanta, sai da suka shiga motar ta ja ta fice daga gidan ta hau titi sannan tace, "Saleem akwai abinci dana zo dashi, kayi ƙoƙari da daddare idan ya farka ka bashi yaci sannan yasha maganinsa, haka ma wannan yarinyar ka ja mata layi akan shiga rayuwar ɗana, zan kyaleta ne a wannan karon saboda shima ɗin ya yi kuskure a ta wata fuskar, amma next time idan ta sake aikata abinda tayi masa har gidansu zan je in wulakantata". "In Sha Allahu Momy hakan ma bazai sake faruwa ba, kawai dai sai in shi Farouk ɗin ne ya ji bazai iya barin abun ya wuce ya maido sa ba.." juyowar da Momy tayi tana kallonsa yasa ya kasa ƙarasa faɗar abinda yai niya. A wani ƙaton chemest suka tsaya Momy ta bashi kuɗaɗe masu yawa tace ya shiga ya siyo maganin, ba wasu kudi aka kashe ba don magungunan ba suda yawa, daya dawo ya miƙa mata sauran can jin ta ce ya je ya hau abun hawa dasu,  idan akwai kuma abinda suke buƙata sai ya tsaya ya siya masu ko da fruit ne, "To Momy sai da safe". "Allah ya tashe mu lafiya". Ta faɗa tana tada motar ta nufi gida, shi kuma Saleem ya tari abun hawa ya haye yana faɗa masa inda zai kai shi.

Momy na isa gida tayi parking a parking lot ta fito ta rufe motar ta nufi ciki, da Dady ta ci karo a bakin kofar shiga sashen nata tsaye saye da jala biya ya zuba hannayensa duka baya, bata bi ta kansa ba ta haɗe rai ta raɓa ta gefensa zata shige, "Daga ina kike?" Ta ji ya faɗa wanda hakan yasa ta tsaya cak ba tare data juyo ba, sai da Dady ya juyo yana kallonta ta bayanta ya sake jefo mata tambayar a karo na biyu sannan tace, "Daga wajen ɗa na". Dama Dady yasan za'a yi hakan amma don ya nuna mata ɓacin ransa ya dawo ta gabanta yana kallon cikin idanuwanta yake cewa, "Da izinin waye kika fita?" "Da izinin Allah mana, ina shi ya bani iko kuma ya bani lafiya da abinda zan hau naje gun ɗana na duba halin da yake ciki? idan har kai ba ka son sa to ni ina sonsa". Ta ƙare zancen tana naɗe hannayenta akan ƙirji tare da zuba masa idanuwa itama, ɗauke kansa Dady yayi yana dafe goshi tare da juyar da kansa na yan mintuna sannan ya juyo yana nunata da yatsa yake cewa, "Idan kika sake fita cikin gidannan kika je wajensa bada izinina ba kada ki kuskura ki dawo mini cikin gida, na lura tubƙa nake yi ako yaushe kina warwarewa akan yaron nan shin har sai yaushe zaki fara ganin kuskure ɗanki kuma ki yadda ya yi kuskure?" Bata ce komai ba shi kuma ya yi tsaki kawai yabar wajen yana jin zafin irin abubuwan da take yi sai kace gareta farau ɗa. Momy kuwa ƙarasawa tayi ciki jiki a sanyaye, Tauheeda na zaune tana kallo ta taso tana ajiye remote ɗin dake hannunta gefe akan kujera ta nufo wajen Momy tana faɗin, "Mommy sannu da dawowa". Sai dai bata kai ga rufe baki ba Mommy tasa hannu ta tureta gefe daga gabanta ba tare data tanka ta ba ta wuce abunta, duk da Tauheeda ta ji ba daɗi haka ta sake binta har ɗaki. Mommy na zaune bakin gado ta riƙe kanta da hannayenta duka tana jin damuwar maganganun Dady acikin kwakwalwar ta, Tauheeda ta turo ƙofa ta shigo, tun kafin tayi magana Momy tace, "Get out from here". Tamkar Tauheeda zata saka kuka tace, "Pls Mommy Ya Umar fa?" Yadda ta ɗago ta watsa mata wani kallo ya sata saurin juyawa zata bar ɗakin, har ta kusa fita ta ji muryar Momy tana faɗin, "Kada ki kuskura ki sake dawowa ɗakin nan and mind you kada kice zaki kirasa a waya ki damesa bayan ya samu yin bacci". Da kai Tauheeda ta amsa hawaye na sauko mata a fuska kafin tabar wajen, palour ta koma ta zauna sai ta ji kallon gaba-daya ya fita ranta, Dady ne ya shigo ta ɗago kai tana kallon sa, "Mamana lafiya?" Ya faɗa yana kallon ta, murmushi ta saki haɗe da cewa, "Dady kaina ne yake ɗan ciwo". "Kin tabbata shi kaɗai ne damuwarki?" "Eh Dady". Ta faɗa tare da miƙewa tana kashe kallon sannan ta nufi ɗakinta, "Ki samu ki sha magani sai ki kwanta kin ji ko?" Dady ya faɗa yana bin ta da idanuwa cike da tausayinta, sai data shige ɗakinta sannan ya maido kallonsa ga ɗakin da Momy ke ciki yana sauke ajiyar zuciya a hankali kafin kuma ya nufi sashen sa, don a yadda yake ji yanzu idan yace zai je gun Momy komai zai iya faruwa.

Umar Farouk kuwa bai tashi ba sai kusan ƙarfe biyu da rabi na dare, Saleem na zaune saman kujerar dake gefe cikin ɗakin yana latsar waya, ganin yana ƙoƙarin saukowa daga kan gadon yasa yai saurin miƙewa ya nufi wajensa yana ƙoƙarin riƙasa ya ɗaga masa hannu haɗe da cewa, "No, zan iya". Saleem ya ɗan ja baya Umar Farouk ya miƙe ya shiga toilet, ruwa ya fara watsawa sannan ya ɗauro arwala ya fito, lokacin har Saleem ya koma palour hakan ya bashi damar kimtsa kansa, wata farar jalabiya ya ciro cikin kayansa yasa sannan ya shimfida abun sallah ya kabbarta ya ranka sallolin dake kansa, yana gamawa Saleem na shigowa da leda a hannunsa, wajen basket ɗin abincin da Momy ta zo dashi ya nufa ya zubo masa abinci ya kawo masa yana faɗin, "Momy ce tace na tabbata ka ci abinci idan ka farka kafin kasha magani". Wani kallo ya yi masa Saleem ya ɗauke kai, tsaki Umar Farouk yai zai tashi Saleem ya ce, "Saƙon fa Momy ne, idan kuma baza kaci ba sai nakira na faɗa mata". Umar Farouk yasan tabbas idan Momy ta ji zata iya baro gidan yanzu ba tare da tayi la'akari da dare ne ba, wani tsakin ya sake ja kafin ya koma ya zauna ya soma cin abincin yana wani yatsine fuska haɗe da ɓata rai tamkar mai cin wani abu marasa daɗi, ɗan kaɗan ya ci kafin ya ajiye abincin don baya yi masa daɗi, Saleem ya miƙo masa gorar ruwa ya amsa yana maka masa harara, bai damu ba don inda sabo ya saba da halinsa, ƙwayoyin maganin ya shiga ɓallo masa yana cire gorar ruwan a baki ya miƙa masa, da idanuwa Umar Farouk ya tsaresa Saleem ya ɗauke kansa yana ƙoƙarin ciro wayar sa, tsaki ya saki a karo na ba adadi kafin ya karɓi maganin ya watsa a baki sannan ya aza gorar ruwan, sai daya shanye su tas sannan ya dire gorar, murmushi Saleem ya saki haɗe da cewa. "Ko kai fa, ya jikin?" Gorar dake gabansa ya ɗauka ya jefe sa da ita Saleem yasa dariya yana faɗin, "Sorry Mr. Man, na so yan matan nan daka matsawa lamba su zo suga yadda ciwo ya wujijjigaki kayi laushi, na tabbata da baza su sake jin shakkunka ba ko kaɗan, musamman dai Janaam". Wani abu Umar Farouk ya ji ya taso masa jin ya ambaci sunan Janaam, a hankali ya jingina da gado yana runtse idanuwa har ya rufesu, tunanin Janaam ya fara yi tun daga ranar data shigo makarantar har zuwa ranar daya ɗage mata niƙaf ta maresa da kuma abubuwan da suka riƙa faruwa tsakaninsu zuwa jiya da ya ji komai ya canza masa a kanta tamkar a zuwan mafarki. Ganin haka yasa Saleem miƙewa ya koma palour don sosai yasan halin Umar Farouk bai fiye son takurawa ba...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN BA KYAUTA BA NE KI BIYA NAIRA N1000 KI KARANTA HANKALI KWANCE.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

                            26.

A ɓangaren Nu'aymah ko kaɗan bata ji daɗin abun daya faru ba ranar kammala exam ɗin su tsakanin Janaam da Umar Farouk, dukkanin su a ganinta basu kyauta ba musamman Umar Farouk data fi ɗora laifin duka akansa, hakan yasa ko data dawo gida dukansu bata nemi kowa ba duk da tana jin hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login