Showing 60001 words to 63000 words out of 157423 words
wurin nan ba har sai kin faɗa mun ko waye shi da har kike ɗaga masa hannu". Dariya abun ya bani amma bana so yaga damata, don haka na kallesa sama da ƙasa ina nuna sa da hannu kafin nace, "A matsayinka nawa? Tukuna ma ina ruwanka da rayuwata? Hanyar jirgi daban data mota saboda haka ka matsa na wuce bana buƙatar daga dawowar mu mufara saida". Ina gama fadar hakan na raɓa ta gefensa zan wuce ya sake tare ni yana yimini kallon kin renani ko, hannuna na rumƙe ina tausar zuciyata dake tunzurani dana ɗaukesa mari na duƙar da kaina ƙasa ina addu'ar neman tsari da kariya daga sharrinsa, cikin wani ƙaraji na ji ya ce, "idan baki faɗamun ko waye shi ba na rantse komai zai iya faruwa dashi domin shiga rayuwarki yanzu ne nafara yi ko kina so ko baya so". "To bazan faɗa maka ɗin ba ka je kayi duk abinda zaka yi kaga shi ɗin sa'ar ka ne ko kuma zai kyaleka". Na faɗa kai tsaye ina zare masa idanuwa nima ta cikin nikab don ya fara kai ni bango, hannu Umar Farouk ya sa ya dafe kansa cikin tsanin ɓacin rai yana murza sumar kansa tamkar wani zautacce kafin ya nuna ni da yatsa yana cewa, "Idan nace zan aikata abu to tabbas zan aikata, just tell me waye shi tun kafin ɓacin rai na yafi haka?" Ya faɗa da wani irin ƙaraji tamkar zai dake ni, da sauri Nu'aymah ta shiga tsakiyar mu tace, "Wai meye haka friendy shi ɗin fa yayanta ne, Ya Jamil ne same father same mother suke dashi, akan me daga dawowar mu zaka tayar da fitina tsakanin ku sam hakan baya yimini daɗi". Ta faɗa a ɗan hasale tana kallonsa, "Me yasa zaki faɗa masa ko waye shi besty? Ai da ki kyale sa sai naga idan yana da iko da rayuwata da zai sa dole sai na faɗa masa". Na ƙare maganar cikin ɓacin rai nima haɗe da raɓawa ta gefe na wuce ina yi masa tsaki araina ina cewa, 'Wannan bazai taɓa sauyawa ba'. Umar Farouk kuwa duk da ya ji ko meye alaƙar dake tsakanin Janaam da Ya Jamil hakan bai sa ya ji wani sassaucin abinda yake ji cikin zuciyarsa ba, Saleem ne da shigowarsa kenan makarantar ya iske abin da ke faruwa ya tsaya yana kallon ikon Allah, ya ƙara so wajen ya dafa kafaɗar Umar Farouk yana cewa, "Wai meke faruwa ne Umar Farouk? Janaam ce fa!" Umar Farouk bai tsaya saurarar sa ba ya fizge jikinsa ya bar wajen, can bayan department ɗin su ya nufa ya samu ɗaya daga cikin kujerun dake wajen ya zauna haɗe dasa hannayensa duka ya dafe kansa, me ke faruwa da nine? Me na aikata hakan? Janaam ce fa, ya faɗa yana tuno kalmar Saleem ta ƙarshe, ji yai komai baya yi masa daɗi ga wani irin abu yai masa tsaye a zuciya, gaba-daya ya kasa tantancewa shin dai-dai ya aikata ko ba daidai ba, abu ɗaya ya sani bai taɓa jin irin abinda ya ji aransa ba akan Janaam sai yau, ke nan hakan na nufin tabbas son ta yake yi? Hakan na nufin so ne haɗe da kishin ta lokaci ɗaya yake yi?
Gorar ruwa ya ga an miƙo masa, ba tare daya damu da wanda ya miƙo masa ruwan ba ya karba ya kafa a baki har sai daya shanye ruwan tas sannan yai jifa da gorar gefe yana goge bakinsa, Saleem dake tsaye a gabansa ya je ya zauna ta gefensa yana kallon sa. Sai bayan sakon goma sannan Umar Farouk ya iya cewa, "Saleem son Janaam nake yi, son ta nake irin son da na rantse zan iya rasa raina a kanta, ni kaɗai nasan irin azabar da na ji acikin zuciyata lokacin dana ganta da wani, na ji duniyar gaba-daya tayi mini wani irin duhu, ina son ta Saleem ya zan yi?". Wata irin dariya Saleem ya fashe da ita har yana rike ciki, Umar Farouk ya tamke fuska haɗe da miƙewa zai bar wajen Saleem yai saurin dakatar dashi ta hanyar tsaida dariyar yana cewa. "Lallai ka ɗebo ruwan dafa kanka Umar Farouk don bana tunanin Janaam zata saurareka balle har ta so...". Kafin ya rufe baki har Umar Farouk ya juyo ya shaƙo wuyansa da ƙarfi yana watsa masa wani mugun kallo yake cewa. "Idan ka sake bakinka ya ƙarasa fadar wannan kalmar sai na ajiye abotar dake tsakanina da kai na datse maka harshe, dole ne Janaam ta so ni kamar yadda nake son ta ko tana so ko bata so, ita ɗin tawa ce ni kaɗai". Ya ƙare maganar tare da turesa gefe Saleem sai tari yake yana saauke numfashi daya bayan ɗaya, amma duk da haka bai iya yin shiru ba sai daya sake cewa. "Nu'aymah fa dake son ka ya zaka yi da ita?" "Aura mata kai zan yi". Umar Farouk ya faɗa ba tare daya juyo ba ya bar wajen. A ɓangaren Nu'aymah kuwa koda ta iske Janaam a class kasa cewa komai tayi, sai dai kawai ta nemi waje ta zauna zuciyarta da kwakwalwar ta sai faman juya abinda Umar Farouk ya aikata take yi tana tunanin meye dalilin sa na aikata hakan, da zaran zuciyarta ta ɗebo mata wani tunanin daban sai tayi saurin ƙaryatawa saboda tasan har duniya ta naɗe hakan bazai taɓa yiwuwa ba saboda irin tsama da tsanar dake tsakanin su, ta san ko da wasa Umar Farouk bazai taɓa son Janaam ba kamar yadda itama bazata taɓa son sa ba, don haka sai ta watsar da zancen ta kalli Janaam ta ce, "Besty kin yi kyau ina ma zaki cire wannan niƙab ɗin da kika sa kuma ya Nu'aym zai gane ki?" "Hmm da kin sha duka a hannunsa kuwa bisa laifin cewa na cire niƙab ɗina, duk da ba don shi nake sakawa ba amma yanzu ya fini ƙaunar na saka ɗin". Na faɗa ina dariya haɗe da kallon Nu'aymah, murmushi ta saki sannan tace, "Na lura ya Nu'aym yasan duk wani abun daya dace dake kuma zai yi miki kyau, ga kishi har ba'a magana da alama nan gaba kaɗan ma kwace mini ke zai yi". "Sai dai kuma kar a ƙara besty, ai kema kin san duk wani abu da zai yi mini kyau, shi yasa ba karamin son zoben nan nakeyi ba." Na faɗa ina ɗago mata hannun da zoben yake. Haka muka ci gaba da firar mu tamkar wani abun bai faru ba har ɗaya daga cikin lecturers ɗin mu ya shigo, ba karatu ya yi mana ba kawai yan shawarwari ya bamu akan mu maida hankali semester ɗin nan kada muyi wasa, daga nan ya koma bamu labaran jajirtaccin ɗalibban da aka taɓa yi a school ɗin da a yanzu su ke akan wani babban matsayi a cikin jahar dama ƙasar baki ɗaya. Shigowar Umar Farouk tayi dai-dai da fitar malamin, don haka kai tsaye wajen seat ɗina ya nufo, akan taɓle ɗin kujerar da nike akai ya zauna a gabana ya tsare ni da idanuwa, har zan tashi na bar masa seat ɗin sai wata zuciya ta hanni saboda idan nayi hakan zai ɗauka ina jin tsoronsa ne, ni kuma a yanzu babu hakan a zuciyata a shirye nake da duk abinda ya zo dashi, don haka sai nai masa banza ina ci gaba da sabgar gabana, Nu'aymah da seat ɗinta ke gefena ta miƙe tana kallo da ta ce. "Friendy ina son magana dakai". "Just two minute ina zuwa". Umar Farouk ya faɗa har lokacin idanuwansa na kaina, Nu'aymah tayi gaba tana cewa. "Besty sai kin fito". tare da ficewa class ɗin miƙewa nai nima da niyar bin bayanta, ina yin step ɗaya a na biyu na ji muryar Umar Farouk cikin irin Muryar da ban taɓa jinsa yai ba yana cewa..."
ALLAH KA JIKAN IYAYENMU 👏
[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRA N1000 KI KARANTA HANKALI KWANCE
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435
09079274454
35.
"Am Ja...". juyowar da nayi ina yi masa wani kallo sama da ƙasa ya sa bai ƙarasa abinda yake son faɗa ba sai kallona kawai da yake yi, tsaki nai sannan na juya nabar wajen ba tare da nace uffan ba, Umar Farouk yai saurin runtse idanuwa jin tsakin dana yi masa saboda a duniya babu abinda ya tsana kamar shi, tsoron wulakancin sa yasa kowa ya kama bakinsa daga dariyar da suka so yi don ba ƙaramin yarfasa Janaam tayi ba.
A can waje Nu'aymah na tsaye tare da Saleem ta fidda wata leda a motarta ta miƙa masa haɗe da cewa yaba Umar Farouk, kallo ɗaya tayi mini lokacin dana fito ta ɗauke kai tana cewa Saleem sai sun yi waya sannan ta juyo ta ce dani, "Besty mu je ko?" Waya ta na ciri na yi saurin kaiwa a kunne ina cewa, "No ki je Ya Jamil zai zo ya ɗauke ni". Haɗe da juyawa nabar wajen.
Isowar Umar Farouk a wajen yasa ta kasa cewa komai kawi ta birni da kallo, a gefe suka koma da shi suna magana, duk da irin abun da yai mata dazu haka na hangota tana faman yi masa dariya da alama wata maganar ya faɗa mata, na girgiza kai haɗe da yi mata addu'a Allah ya yaye mata wahala ya rabata da son sa ko zuciyarta ta huta ina ci gaba da kiran Ya Jamil. Bayan minti waya da shi sheda mini yai yana zuwa yanzu na bashi minti goma zai ƙaraso, don haka na koma can gefe da baza su iya hango ni ba na zauna zaman jiran sa, ko da Nu'aymah suka gama magana da Umar Farouk ta kirani wai ina ina? Na sheda mata tayi tafiyarta na riga na wuce, don haka daga ita har Umar Farouk ina kallon lokacin da suka tada motocin su suka tafi na sauke ajiyar zuciya ina godewa Allah daya sa basu ganeni ba.
Mintuna goma na kwashe a wajen zaune kafin Ya Jameel ya zo ya ɗauke ni, tafe muke muna fira dashi na ce, "Ya Jamil wai sai yaushe zaka kaini gun Aunty Nidrah? Allah na matsu na gane ta". Na faɗa ina turo baki haɗe da kallonsa, bai tanka ni ba har muka kusa isowa gida, sai gani nayi ya ɗauke ta ɗayan titin da zai kaimu gidan kawu yayan Mamah da akayi auren 'yarsa last month, juyowa nayi ina kallonsa kafin nace, "Ya Jamil gidan su Aunty Nidrah fa nake tambayarka yaushe zaka kai ni ba gidan Kawu ba". "Janaam kina da matsala wani lokacin, kisa idanuwa mana kiga inda zan kaiki". Ɗan muskutawa nayi ina sake turo baki haɗe da cewa, "Kayi hakuri naga anguwar su kawo muka nufa shi yasa". "Sai akace miji kuma Kawun shi kaɗai ne a anguwar ba". Ya faɗa yana kallona hakan yasa na kama bakina nayi shiru, ba'a jima ba muka iso bakin wani tafkeken gida daya gama haɗuwa Ya Jamil ya yi parking abakin gate haɗe da ciro wayarsa. "Ranki shi daɗe gamu mun iso muna waje". Na ji ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi yana lumshe idanuwa haɗe da buɗewa. Yana ajiye waya ko minti uku ba'a ƙara ba naga wata kyakkyawar budurwa da baza mu wuce sa'anni da ita ba don ko zata girme ni sai kaɗan ta fito daga cikin gidan saye cikin doguwar riga atamfa ɗinkin ya ɗan kama mata jiki tayi matukar kyau sosai ta yane jikinta da mayafi mai ɗan yalwa daya wuce ƙirjinta kaɗan tana tafiya cike da natsuwa idanuwanta na a kanmu sai murmushi take yi, juyowa nai na kalli ya Jameel alamar tambaya ko ita ce Aunty Nidrah, ya amsa mini yana kallon ta yake cewa "Nidrah, Auntynki". Murmushi na saki ina buɗe marfin motar da sauri tare da fitowa kafin taƙaraso, cike da natsuwa ta ƙaraso wajen tana isowa na ji ta rungume ni tana faɗin, "You're highly welcome Sister, yau Allah ya yi kenan?" Rungumeta nayi nima cikin jin daɗi haɗe da cewa, "Thanks Aunty Nidrah, ina kwana". Ta amsa mini da lafiya ƙalau kafin muka saki juna murmushi kwance akan fuskar kowanen mu, a zuciyata kuwa mamaki nake yadda ta ganeni daga haɗuwar farko duk da dai ba abun mamaki bane kasancewar muna ɗan yanayi da Ya Jamil, muryar shi ta katse ni da na ji yana ce mata. "Eh na cika alƙawari da yau ma sai da akai min gori, ga Janaam nan na kawo miki kafin na tashi wajen aiki zan dawo na ɗauketa, nasan ban taɓa haɗa kuba ko a waya da nace haɗin baki kuka yi keda ita ko wace yau ta dame ni da zancen na kawota, itama daga School ta aza rigimar yaushe zan kawo ta wajenki shine nace bari na sauke alkawarin nan kawai ko nima na huta". Dariya Aunty Nidrah ta yi da tun dazu ita nake kallo ina yaba natsuwarta kafin naji cikin muryata mai daɗi tace, "Mun ji yallaɓai kuma muna godiya ni da Sis, a sauka lafiya Allah ya kiyaye". "Au! Korata ma kike yi? Tom Shikennan na tafi". Ya Jamil ya faɗa tare da tada motarsa ya ɗaga mata hannu itama ta ɗaga masa tana dariya ta ce, "A dawo lafiya", bata iya baro wajen ba har sai da taga ta dena ganin motarsa sannan ta juyo tana cewa. "Sis mu shiga daga ciki ko?". Ta riƙo hannuna ina biye da ita baya muka shiga cikin gidan ta karamar kofar dake jikin gate ɗin, mamaki ne ya kama ni lokacin da muka shigo ciki ganin kamar mota Umar Farouk anyi parking a gefe, wani ɓangare na zuciyata ne ya faɗa mini me zai kawo Umar Farouk anan kuma, taɓe baki nayi muka ci gaba da tafiya har muka iso a babban palour cikin gidan, wata babbar mace muka tadda a ciki tana gaisawa da wani saurayi, cike da fara'a ta tarbe ni tana faɗin, "Lale marhabin da Janaam, yau dai Allah ya yi zuwanki kullum sai zancenki ake mun". A yadda matar tayi magana ya tabbatar mini da tasan da zuwan nawa, murmushi na saki cikin girmamawa ina ƙarasowa cikin palorn kamar yadda Aunty Nidrah ke yi mani umurni, sai dana zauna akan kujera sannan na ɗan rissina kai cikin girmamawa haɗe da ɗan zamowa akan kujerar ina gaisheta, cikin fara'a ta amsa tana tambayata yasu Mamah suke na amsa mata da lafiya ƙalau ina komawa kan kujerar dai-dai haɗe da wasa da yatsun hannuna, aunty Nidrah bata zauna a palorn ba naga ta nufi wani wajen, waya na ji tana ƙara ashe ta matar ce wadda da alama itace matar gidan wato mahaifiyar Aunty Nidrah, bayan ta ɗaga na ji tana cewa, "Ok Alhaji gani nan zuwa, dama Umar Farouk ne ya zo gaishe mu shiyasa ban ƙaraso ba", "To zai ji". Ta faɗa tare da aje wayar, Ni dai kai na na ƙasa na kasa ɗagowa saboda gaba-daya na takura, jin kalmar Umar Farouk yasa na sake shiga kokonto ko dai shi ɗin ne, musamman da nake jin jikina tamkar idanuwa na yawo akai, Muryar matar na ji ta sake cewa, "Umar Farouk bari na shiga daga ciki Uncle ɗin naka na jira tafiya zai yi, yace a gaishe ka ina ga sauri yake yi daƙyar zaku samu gaisawa". Tana gama faɗar hakan ta miƙe tare da kallona ta ce, "Janaam ai kina nan sai dare zaki tafi ko?" Ba tare dana ɗago ba nace, "Eh idan Ya Jamil ya ta so aiki shi zai zo ya daukeni". "To ba matsala bari naje wajen baban naku na fito". Ta ƙare zancen tana barin wajen, ɗago kai nayi da niyar kallon ta karaf idanuwana suka sauka akan nasa, "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" na faɗa cikin zuciyata don tabbas Umar Farouk ɗin ne, dama tunda na shigo jikina ke bani kallona ake yi, tsaki na saki can ƙasa ƙasa ganin irin kallon da yake yi mini tare da jaye idanuwana ina kauda kaina gefe don bana jin ko sama da ƙasa zata hade zan iya yi masa magana ko da nan ɗin gidan su ne.
Umar Farouk kuwa dama tunda suka shigo ya ji an ambaci Janaam zuciyarsa ta kaɗa, ɗago kan da zai yi idanuwansa suka sauka akan ta tamkar waccan ranar daya fara ganin fuskarta don tun acikin mota da zasu zo ta cire niƙab ɗinta, kasa jaye idanuwansa daga kanta yai har ta ƙaraso ciki ta zauna, gaba daya ya shagala da kallonta ya manta a inda yake da kuma wace duniya yake, wani sabon yanayi da sabon al'amari ya sake ji ya saukar masa a zuciya shi yasa har Mamie mahaifiyar Nidrah ta yi masa magana bai samu tankata ba, yana ƙoƙarin buɗe baki yai mata magana Nidrah ta shigo paloun tare da yarinya biye da ita a bayanta dauke da ƙaton tray da aka shake da drinks da kuma kayan motsa baki, a jiyar zuciya ya ja ya sauke yana furzar da iska ta baki haɗe da ja baya yai relaxing akan kujerar da yake zaune yana lumshe idanuwa haɗe da rufesu. Sai da yarinyar ta ɗaura tray ɗin akan table dake gefen kujerar da Janaam ke zaune tana faman haɗe rai ta tsiyaya mata ruwa da lemu ta ajiye mata sannan ta fice, Nidrah dake latsar waya ta ɗago kai ta ce, "Sis bismillah ko?" Sannan ta juya a seat ɗin da Umar Farouk ke zaune ta ci gaba da cewa, "Ya Umar lafiya dai ko? Ina Mamie tayi ta barka zaune kai kaɗai ko da yake ga Sis nan ta taya ka zama". Bai ce komai ba haka kuma bai buɗe idanuwansa ba balle ya tankata, taɓe baki tayi haɗe da maida kallonta ga Janaam ta ce, "Janaam meet my cousin brother Umar Farouk, Momynsa ƙanwar Dady ce and he's very