Showing 108001 words to 111000 words out of 157423 words
ki gudu ki bar ni ko kuma ki sakani yin abun kunya a gidan sarakai". Aunty Nidrah tayi dariya tare da karɓar ledar tana cewa, "Allah ni ba ruwana kawai dai kai ne.." tun kafin ta ƙarasa Ya Jameel da idanuwansa ke kanta ya ce "Ni ne me Madam? Banda fa sharri". Ya ƙare zancen yana nunata da key ɗin mota, cike da shagwaɓa Nidrah ta turo baki tana faɗin, "Ni dai Allah karka tafi ban gama ganin ka ba". Har zai shiga motar sai kuma ya fasa ya jingina ajiki yana kallon ta, murmushi ta saki itama shi ɗin take kallo irin kallon nan mai shiga jiki ya riƙa yawo a cikin jini da ɓargon ƙashi, kallo ne dake cike da so da kauna da kuma yarda da juna, sun fi mintuna uku a haka kafin Nidrah ta fara janye idanuwanta a hankali tana sauke ajiyar zuciya "Har kin gama ganin nawa?" Ya Jameel ya faɗa a kasalance yana jin jikinsa duka ya mutu, bata iya amsa masa ba sai dai tayi ƙasa da kai, ita kanta ita kadai tasan yanayin da take jin kanta akan ƙaunarsa, bata ƙi jinin su kwana su tashi su sake kwana a haka ba domin kallonsa kaɗai na jefawa zuciyarta natsuwa tare da bata farinciki marar misaltuwa, murmushi ya saki don kuwa abun da take ji akan sa shima shi yake ji a kanta "Kin ga Nidrah shiga ki turo mini Janaam mu wuce gaba-daya kallon nan naki ya kashe mini jiki ba zan iya ƙara ko da minti biyu bane anan don gaskiya da matsala". Aunty Nidrah bata san lokacin da saka masa dariya ba tan cewa, "Tuna nake yi to a sauka lafiya Allah ya tsare, wato kam har ka manta Janaam anan zata kwana har da wani cewa na shiga na turo maka ita". Ta ƙare zancen tana ɗan hararar sa da wasa, kansa ya shafa haɗe da cewa, "To ai duk kece kika shagaltar Dani, amma ba komai daga yau sai gobe zakiyi bayani ne". Yana kaiwa nan ya juya ya buɗe motar ya shiga ya tayar, kunya ce ta kama Ni na rufe fuskanta har sai da nake yana faɗin sai da safe sannan na shiga ɗaga masa hannu har sai da ya fice sannan na juya na koma cikin gida ina jin wani farin ciki na mamaye dukkanin ƙofofin zuciyata, Ya Jameel namiji ne har da ƙari indai wajen iya kula da mace ne, tarairaya tare da bata lokacin sa, na tabbata samun sa baban alkhairi ne aguna kuma bazan taɓa yin dana sani ba ko nadamar hakan.
Bayan gama waya ta da ya Nu'aym ina ganin shigowar kiran Umar Farouk nai banza dashi, daga ƙarshe da naga zai takura mini na kashe wayar gaba-daya, wayar Aunty Nidrah na ji ta dau ƙara data saka chargy ta fita ta barta, tsaki na saki don kuwa na san bazai wuce shi ɗin ne ba ina gyara kwanciyata, haka yai ta kira ko gajiya baya yi har sai da na ji Aunty Nidrah ta shigo ta dauki wayar, ban san me aka ce ba sai ji nai tana kiran sunana ban amsa ba na ƙyaleta ina yi kamar nayi bacci, can na ji tana cewa, "Ya Umar tayi bacci". Ashe ko shi dinne kamar yadda nayi tsammani, na sauke ajiyar zuciya a hankali yadda baza ta iya jiyo ni ba, ina so na gyara kwanciyata amma na kasa har sai da na ji ta gama wayar, kallo ta bi ni dashi kafin tace, "Sis yanzu dama bakiyi bacci ba shine kina ji na ina kiran ki ka mun shiru? Ai Shikenan kin kyauta". Ta faɗa tana hawowa kan gadon, idanuwana na a rufe ba tare dana buɗe ba na ce "Allah bacci nake yi Aunty Nidrah, kuma ma me zai ce mun bayan ya gama jefani a cakwakiya, na sani Ya Jameel daƙyar idan bai saka hukuma a zancen nan ba, kuma da zaran ya gano gaskiya na kaɗe sai buzu na". Dariya na ji Aunty Nidrah ta yi wanda hakan ya sani buɗe idanuwa ina kallonta kafin tace, "Matsoraciya ki kwantar da hankalin ki Baby ya ce an sallamo Salis ba abin da ya same sa, sai dai fa da zancen ki don Baby ya ce zai saka hukuma a maganar a binciko su waye sukai aikin". Ban san lokacin da na mike zaune a tsakiyar gadon ba ina zaro idanuwa, take na ji idanuwana sun kawo kwalla, juyawa Aunty Nidrah ta yi daga kwanciyar rigingine da take fuskarta na kallon saman dakin tana cewa, "Salis ya ce Abar zancen amma yana da kyau kiyi tunani sosai, barin kashi ciki Janaam baya taɓa maganin yunwa, ki ba Umar Farouk dama ko kuma ki kai karshen matsalar ki sanar da yayanki komai akan shi wanda kike so ɗin, ina ganin hakan zai magance wannan matsalar cikin sauƙi ba tare da wata damuwa ba, duk da dai ya Umar Farouk na sonki ba kaɗan ba, na sani sai anyi da gaske in har an ci Sa'a zai iya hakura dake". Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na koma na kwanta ina juya mata baya nima kamar yadda tayi ina cewa, "Da kin san irin soyayyar da Ya Nu'aym ke yi mini Aunty Nidrah da ko kadan baza ki ga soyayyar da kike cewa yana yi mini ba, a kaso dubu Umar Farouk bai kwashi ko da kaso ɗaya ba a soyayyar da ya Nu'aym ke yi mini". "Shikennan Sis Allah ya tabbatar da Alkhairi". Na ji Aunty Nidrah ta faɗa tare da kashe mana hasken ɗakin da makunnin sa ke jikin gadon gefen da take....
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[8/20, 6:08 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
49.
Washe gari tun da nayi sallar asuba na koma ban farka ba sai kusan ƙarfe goma da rabi, ɗakin a gyare yake tsaf ba kowa ciki don haka ina saukowa daga kan gadon shi nafara gyarawa sannan na wuce toilet, brush na fara yi kafin nayi wanka na fito, sai dana fara shiryawa sannan na ɗauko wayata na kunna, message ɗin Umar Farouk na fara cin karo dashi har guda biyu na goge su duka ba tare dana ɓata lokaci na ba wajen karantawa, Ya Nu'aym na turawa Morning message kafin na buɗe Data na shiga WatsApp, kamar dai kullum contact ɗin Nu'aymah na fara dubawa ko zanci karo da sakonta kamar yadda nake saka ran ganin haka ako da yau she amma tsit babu wani saƙo data bar mun, jikina ne ya sake yin sanyi ban tsaya bin takan ko wane saƙo ba na fito na kira wayarta amma har wayar tai ringing ta gama bata ɗaga ba, haka na yi mata kusan 3miseed call amma taki ɗagawa a dole na hakura ina jin ba daɗi a raina, tun tashi na ba nida wata ƙawa idan ba Nu'aymah ba sai kuma abokan karatuna tun na primary da secondary, a jami'a kuma ba ni da wasu abokan ko da na karatu ne sama da ita, taya zan iya jurewa fuskantar shariya daga wajen ta? Na sani wannan abu ne mai wahala aguna da zuciyata baza ta iya ɗauka ba balle har ta iya jurewa, ina wannan tunanin na ji anyi sallama a bakin ƙofar ɗakin an shigo, ɗago kan da zan yi muka yi ido biyu da Mamie, murmushi na saki ina sadda kaina ƙasa har ta ƙara so ciki ta zauna a bakin gadon tana cewa, "Ashe har kin tashi baccin?" Kaina har lokacin na a ƙasa na amsa mata da "Eh Mamie ina kwana?" "Lafiya ƙalau Janaam, yanzu nagama faɗa da Nidrah ashe ba tare kuka fita ba sai yanzu take kirana wai kina daki ta bari kina bacci aje aduba ki idan kin tashi nasa driver ya kai ki shagon da suka je wankin kai". Murmushi kawai na yi don nasan ta yi hakan ne don kar ta tada ni daga baccin da nake ta takura ni, miƙewa Mamie ta yi haɗe da cewa, "To sauko kifara karyawa kafin nan driver ya dawo daga inda na aikesa ya karbo mini sako sai ya ajiye ki wajen su". Ba musu na miƙe na bi bayanta muka sauka ƙasa, wajen dining ta nufa tana cewa na ƙaraso wajen nima, da kanta ta ja mun kujera na zauna ta zuba mini toasted bread da omelet egg, sai soyayyen arish da Peppe soup na cowtail a gefe, sai data haɗa mini ruwan tea sannan ta bar wajen tana kwalawa mai aikin su Indo kira, sallama akayi a plourn ta amsa tana faɗin, "A'a Umar Farouk kai ne?" Gabana yai wata irin faɗuwa lokaci ɗaya jin muryarsa da sunansa da aka faɗa, ban iya ɗago kai na kallesa ba sai ma tuttura abincin dana soma yi saboda nayi sauri na tashi nabar wajen, ina jinsa tamkar ba shi ba suna gaisawa da Mamie tana tambayarsa mutanen gidan su cikin girmamawa yana amsa mata da kowa lafiya kalau, na taɓe baki araina ina faɗin kamar da gaske.
Umar Farouk kuwa tunda ya shigo cikin palourn idanuwansa suka sauka akan Janaam ya ji ya kasa controlling kansa sai kallonta yake yi, bayan sun gama gaisawa da Mamie ya shafa kansa yana cewa, "Mamie yunwa nake ji akwai wani abun taɓawa?" Mamie bata kawo komai a ranta ba don bata ma kula da irin kallon da yake yiwa Janaam ɗin ba ta ce, "Eh akwai Indo jeki ki haɗo masa abun karyawa idan kin dawo sai ki shiga ki gyaro mani palorn can yara sun sake ɓatawa". Har Indo ta miƙe zata tafi Umar Farouk yai saurin dakatar da ita yana faɗin, "Mamie babu shi akan dining?" Mamie ta kalli gefen dining sannan ta ce akwai shi amma bakuwa mukai a wajen, na san halinka ba lallai ne idan nace kaje can na zuba maka kaci ka amince ba, kuma kamar ma kaɗan ya rage tunda gidan cike yake da baƙi shi yasa nace Indo ta haɗo maka wani". "Ba komai zai ishe ni Mamie ai ba da yawa zan ci ba, Indo jeki wajen aikin ki na gode". Umar Farouk ya faɗa tare da miƙewa ya nufi wajen ya jawo kujerar dake facing ɗin wadda Janaam take zaune akai ya zauna shima, har Mamie ta ƙaraso wajen zatayi saving nasa ya ce, "Mamie bar shi zan zuba da kai na". "Zaka iya? Na san fa ba komai ka iya ba tunda Momynka ta riga ta shagwaɓa ka". Bai ce komai ba ya ɗan shafa kai Mamie ta jawo plate ta zuba masa sauran toested bread ɗin daya rage guda biyu ta zuba masa peppe soup a gefe don arish ɗin ya ƙare, wayarta dake riƙe a hannunta tayi ƙara ta ɗaga bayan ta tura masa plate ɗin agabansa tana barin wajen, Umar Farouk daya bita da kallo ganin ta bar palourn ya miƙa hannu ya jawo plate ɗin dake gabana ina ci ya tura mini nashi, idanuwansa na a kaina da duk wani motsina ya soma cin abincin, gaba-daya ji nai na tsargu da zamansa a wajen da ƙyar na iya jawo cup ɗin tea da Mamie ta haɗa mini na soma kurɓa a hankali kafin na ajiye tare da miƙa hannu na ciro tissue na goge hannuna da baki na sannan na miƙe zan bar wajen, "Koma ki zauna". Na ji ya faɗa cike da bani umurni tamkar wani ubana, sai a lokacin na ɗago kai na kallesa ina watsa masa harar da bai san ma ina yi ba don ci gaba da cin abincinsa yai tamkar ba shi yai maganar ba, ina buɗe baki da biyar mayar masa da magana sai ga Mamie ta dawo palourn, a hankali na ɗan yi tsaki in barin wajen, Umar Farouk ya ci gaba da cin abincinsa hankali kwance har lokacin ba tare daya ɗago kai ya kalle ta ba, "Janaam har kin gama? Ga shi har yanzu drivern be dawo ba balle ya sauke ki wajen su, ko yanzu ita ce ta kira wai ke suke jira, Umar Farouk ko zaka sauke ta idan babu inda zaka je". Mamie ta faɗa tana kallon Umar Farouk ɗin, hannunsa ya cire a cikin abincin ya jawo tissue ya goge sannan ya jawo ruwan tea ɗin da yaga Janaam ta ajiye ta kasa sha ya shanye kusan fiye da rabi sannan ya ajiye cup ɗin ya mike yana cewa, "Da zan tafi school ne amma bari sai nafara sauke ta". Ya ƙare zancen yana sauke idanuwansa a kaina, tamkar na fasa ihu haka na ji na kalli Mamie kamar zan yi kuka na ce, "A'a Mamie ni zan tafi da kaina ba sai ya sauke ni ba, zan hau abun hawa sai na kira ta tayi mana kwatancen inda take idan mun je kawai yai tafiyarsa". "A'a ai ba'a yi hakan ba, ga na gida a barki kije titi taron abun hawa, ai wannan bai kyautu ba, ki je ya sauke ki". Mamie ta faɗa tare da ƙare zancen tana yi masa bayanin inda zai sauke ni, ba yanda na iya dama cikin shirina na sauko gabaɗaya, bayan Mamie ta gama magana dashi ya wuce gaba sannan ta juyo ta ce, "Ku je ya sauke ki Janaam cousin brother ɗin Nidrah ne baya da wata matsala". Ban iya na amsa mata ba sai dai kawai na ɗaga kai ina bi bayansa, da Mamie tasan ko wa zata haɗani da shi da bata faɗi hakan ba don a ganina kaf faɗin duniyar nan babu wanda ya kai shi matsala. Ko dana fito yana tsaye yana amsa waya ya juyo ya kalle ni ya ɗauke kai bai ce mun komai ba kuma shi bai buɗe motar ba ya ci gaba da wayarsa, nima ban ce masa uffan ba na ja gefe na tsaya zuciyata sai tafarfasa take yi a wani ɓangare kuma gabana sai faɗuwa yake yi ina ji tamkar na zura da gudu, takai ci ne ya kamani na nufi hanyar fita gate ganin fiye da minti biyar sai wayarsa yake yi hankali kwance yai banza da ni tamkar bai san da wanzuwa ta a wajen ba, dai-dai lokacin Umar Farouk ya gama wayar ya juyo, ganin na miƙi hanyar fita ya sashi cewa, "kin san me zai iya faruwa ga duk wanda kika yi gangancin tarewa kika hau abin hawan sa, beside sai na koma ciki na sanar da Mamie baki ji umurnin data baki ba". A hasale na juyo da niyar ce masa halan ita Mamie ɗin uwata ce, sai naga tuni shi har yabar wajen ya nufi wajen motar sa, ina tsaye ya jawo motar yai parking a gabana tare da buɗe mani gefen da zan shiga, ba don kar Mamie taga nayi mata rashin kunya ba da ba abinda zai sa na shiga motar sa wallahi, kwafa nayi sannan na bude gidan baya na shiga ina bugo ƙofar da ƙarfi, murmushi Umar Farouk yai yana kallona ta jikin madubin dake gaba saman motar haɗe da cewa, "Zaki iya komawa gida idan bakya ra'ayin tafiyar don ni ba drivern ki bane, da zaki koma ɗin ki zauna gida ma da zan fi jin daɗi akan fitar da zaki yi ki je a kalle mini ke". buɗe marfin nayi da niyar fita na koma cikin gida, jin yace zai fi jin daɗi idan na fasa tafiyar ya sa ina fitowa na dawo gaba ɗin na zauna cikin dakewa ina ce masa mu tafi don na ɓata masa rai, juyowa yai ya kalleni na sakar masa murmushin nan irin na yake haɗe da ɗaga masa gira ina sake cewa, "Mu je ko". A yadda ya haɗe rai yana kallona ya gama tabbatar mani da cewa ya ji haushin rashin fasa fitar tawa, hakan ya faranta mini zuciya sosai na saki wani murmushin da har cikin zuciyata wannan karon ina dauke kaina gefe, wata irin dariya na ji ya saki bayan ya tada motar tare da juyawa ya danna lock ya ja motar muka fice yana ci gaba da dariyar sa kafin yace, "Gaskiya Janaam kin haɗu shi yasa nake ƙara jin son ki a zuciyata, ba kya taɓa bari nayi failling target ɗina da kanki kike taimako na har sai ya faɗa yadda nake buƙata, thank you my Amaah". Ya kare zancen haɗe da juyowa yana kallona tare ɗaga mini girar shima kamar yadda nayi masa, kau da kai nayi ina jin haushin kaina ta yadda na kasa gano ashe tunzura ni yai amfani ne da ɓacin raina kawai ya cimma burinsa. Haka muka ci gaba da tafiya ya saki disko sai kiɗa ke tashi a motar yana mamin wakar cike da farin ciki, wuɗannan ɗabi'un nasa na ɗaya daga cikin abubuwan da suka sa mini tsanarsa tun farkon ganina dashi a school, a duk lokacin daya shigo School to sautin waƙa da kiɗa a motar sa suke alamta mana shi ɗin ne, ba kya taɓa raba shi dajin kiɗa da waƙa don ko a fili ako yaushe yana laƙe da bluetooth a kunnuwan sa, wataƙil ya fahimci yadda na sake haɗe rai ina faman yin tsaki saboda yadda na tsani kiɗan tare da kauda kai shi yasa na ji ya ce, "Sorry Amaah". Haɗe da kai hannu yana kashe kiɗan gaba-daya kafin yaci gaba da cewa, "Me yasa a school kaɗai kike saka wannan abun da kike rufe fuskar ki da shi? Me yasa baza ki mayar da saka shi ɗabi'ar ki ba gaba-daya don killace kyakkyawar fuskar nan da Allah ya yi miki? Ko kina tunanin a can kaɗai ne ake samun maza ɓata gari banda a cikin gari?" Na ji ya jefo mini tambayoyin a jere haɗe da juyowa yana kallona lokaci ɗaya kuma yana ci gaba da driving ɗin sa, "Haka naga dama kuma haka nake ra'ayi". Na bashi amsa kai tsaye kuma a hasale, murmushi ya sake yi yana cewa, "Ba laifi, amma dai kin san hakan fuska biyu ne ko? Kuma idan munyi aure dole kin san ɗaya