Showing 150001 words to 153000 words out of 157423 words
masa ya kauda kai haɗe da cewa, "zan samu aron wayarka?" Sai da inspector Ashir ya kalli bakin kofar ɗan sandan dake tsare da ita na gefe sannan ya maido da kallonsa ga Umar Farouk ya ce, "hakan ya saɓawa doka". "Zaka iya tafiya domin wannan taimakon kaɗai nake buƙata a yanzu". "Zanyi maka amma kaima akwai abinda zaka mun, mahaifiyarka tace baka ci abinci ba, na kuma yi mata alkawarin zan sa kaci, idan ka tabbatar zakayi hakan bisimillah". Ya faɗa yana miko masa wayasa, Umar Farouk bai ce komai ba jikinsa na rawa ya karɓa ya fara kokarin saka lambar Janaam, inspector Ashir ya mike yabar wajen tare da ba dan sandan dake jikin kofa umarnin ya biyo shi ya dauko masa abincin da aka kawowa Umar Farouk, ba musu ya bi bayansa, shi kuma Umar Farouk ya kai wayar a kunnensa. Dai-dai lokacin Janaam ta fito wanka ta gama shiryawa zata kwanta taga kira ya shigo a wayarta, jiki a sanyaye duk da taga sabuwar lamba ce ta ɗaga ba tare da wani tunanin ba, Umar Farouk na ji ta daga ya nufi jikin karafunan cell ɗin ya riƙe sosai yana lumshe idanuwansa jin yadda zazzaƙar muryarta tana sallama ta sauka a kunnuwansa, a hankali ya buɗe idanuwan cikin karyayyar murya yace, "Janaam!" Cak numfashin Janaam ya tsaya jin Muryar Umar Farouk a cikin wayar, dube-dube ta shiga yi cike da tsoro shin da gaske muryarsa ce take ji ko kuwa shi ɗin ne acikin ɗakin ta? "me yasa kikai hakan Janam kin san me kika aikata yanzu?" Ya faɗa cikin tashin hankali tare da dafe kansa da yai wata irin sarawa, wata irin zabura Janaam tayi tana miƙewa daga bakin katifar tata data zauna tare da ja baya wani irin tsoro na sake mamayeta, shikenan ta shiga uku dama tasan Umar Farouk zai iya aikata abinda ya faɗa kasheta zai yi, bakinta ta shiga motsawa amma maganar da take son yi ta kasa fitowa, murayarsa ta sake ji a hankali wannan karon yana cewa, "Amaah idan na rasa ki na rasa rayuwata gabaɗaya, idan kika bari wannan hukuncin ya hau kanki rayuwata ta ƙare, ya zama komai da nake yi babu ma’ana idan babu ke a duniyar nan. zuciyata zatana kuna idan baki tare da ni, ke ce mafarkina da gaskiya, ke ce abinda ya sa nake ganin dalilin ci gaba da rayuwa. Without you Janaam duniya ta zama kamar kabari a gare ni. Don Allah ki fahimci cewa rayuwata gaba-daya taki ce kuma idan na rasa ki na rasa kaina, ki bari mu kasance a tare halin rayuwa ko mutuwa domin ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba". Gaban Janaam ne ya sake faduwa jin kalmarsa ta mu kasance a tare a halin rayuwa ko mutuwa, shikenan hakan na nufin tabbas zai kasheta ya kuma kashe kansa kamar yadda ya faɗa, da sauri ta katse kiran tare da fashewa da kuka tana rufe bakinta, a halin yanzu babu tsarin soyayya a rayuwarta domin duk wani sinadarin so ya mutu a zuciyarta kuma bai bar komai ba sai dafi da mikin da har ta mutu bazata manta ba, amma taya Umar Farouk ya fito? Ina ya samu wayar kiranta kar dai ace guduwa yai daga police station ɗin don ya kasheta? Ta tambayi kanta hawaye naci gaba da sauka a kuncinta, ya kamata tayi wani abun kafin yakaraso inda take da sauri ta shiga neman number Barrister Maryam, tunawa tayi da ba ta da ita, Aunty Nidrah ta fado mata arai tayi saurin lalubo Number ta kirata, ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin da take ciki tayi haɗe da cewa, "Aunty Nidrah turo min lambar Barrister Maryam ina nufin Momy?" Ta ƙare zancen tana share hawayen fuskarta "Lafiya Janaam?" Aunty Nidrah dake kwance ta faɗa haɗe da miƙewa zaune kan gadon, cikin muryar kuka Janaam ta ce, "Kawai ki turo mun Aunty akwai matsala". Dai-dai lokacin Ya Jameel ya fito wanka yana daure da towel, kallonsa Aunty Nidrah tayi ta ce, "Janaam ce ke kuka wai na turo mata lambar Momyn Farouk akwai matsala". Karɓar wayar yai ya kai a kunnensa yana cewa, "Janaam meke faruwa". Kasa cewa komai tayi kawa ta fashe masa da kuka, mikawa Aunty Nidrah wayar yai ya zura jalabiyarsa ya dauki key ɗin motarsa yace, "taso ki rufe gidan bari naje naga meke faruwa". "Beb dare yayi fa?" "Baki ji kukan da take yi ba ina tsoron wani abu ya sameta kin san gobe za'a koma kotu fa, ki kwanta yanzu zan dawowa in Sha Allah". Ya kare zancen yana yi gaba ba tare daya jira me zata ce ba. Yana isa gidan ya yi horn mai gadi ya ce waye yace masa shi ne ya buɗe masa, jiki na rawa mai gadi ya buɗe masa gate ya shiga, yana shiga Mamah na fitowa daga dakinta jin shigowar motarsa ta kallesa hankalinta a tashe tace, "kai lafiya?" "Ina Janaam?" Ya tambaya ta ce "Tana ɗakinta wai meke faruwa ka baro gidanka cikin daren nan?" Ya Jamil bai iya cewa komai ba kai tsaye ya nufi dakin Janaam ya kwankwasa kofa, sake firgicewa Janaam tayi tai baya ba tare data bari tayi wani motsi mai ƙarfi ba don duk a zaton ta Umar Farouk ɗin ne, sai da taji ya buga kofar da ɗan ƙarfi yana faɗin, "Janaam ki buɗe ƙofar ni ne". Da gudu ta karaso jikin kofar hannunta na rawa ta cire key ɗin, tana budewa jikinta na wani irin kyarma ta faɗa jikin Ya Jameel tana kuka, "kai wai lafiya?" Mamah ta faɗa rai aɓace ganin babu wanda yai mata bayanin abinda ke faruwa, lallashin Janaam Umar Farouk yai kafin ya jata su koma cikin falo ya zaunar da ita saman kujera sannan ya shiga yiwa Mamah bayanin abinda ke faruwa, sallallami ta shiga yi ta soma yi mata faɗa ya ce, "A'a Mamah, bari muji wace irin matsala ce, dubi fa yadda duk ta fita hayyacinta". Nan ya juya ga Janaam ya tambaye ta meke faruwa, bata ɓoye masa komai ba ta sanar dasu wanda gabaɗaya su kansu hankalinsu ya tashi, musamman jin wai Nu'aym na raye, kallon Mamah Ya Jameel yai haɗe da cewa, "Ina ga Mamah ku tashi mu tafi can gidana don maganar Janaam ba abinda Farouk bazai iya aikatawa ba". "Ba inda zan je ta Allah ba tashi ba, ku ku tafi can gobe ma hadu a kotun Allah ya kareta da sharrin su". Ya Jameel zai sake magana akan lallai sai sun tafi tare ta dakatar dashi tana cewa, "ka tashi ku tafi kasan kabaro yar mutane kuma kasan halin da take ciki bawai lafiya ta isheta ba, koma ma meye Allah ya kawo mana karshensa". Ba yadda Ya Jameel ya iya ya ɗaukowa Janaam hijab dinta ya bata ta saka suka yiwa Mamah sallama Janaam na nanike dashi suka tafi, Mamh ta sauke ajiyar zuciya kanta na sake daurewa akan lamarin data rasa ta ina za'a gano bakin zaren, kasa kwanciya tayi don haka ta ɗauro arwala ta kabbarta sallah tana mai addu'a Allah ya yaye masu wannan jarabawar ya bayyana gaskiya gobe ko hankalinsu na kwantawa.
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/4, 3:54 PM] Queen Qee's💎: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
72.
Bayan sun isa gida Ya Jameel yaiwa Aunty Nidrah bayanin abinda ke faruwa ta ji gaba-daya jikinta yai sanyi, komai lalacewar naka dai ai naka ne baza kaji daɗi ba idan kaga abubuwa marasa daɗi na faruwa saboda shi, da kanta ta karbi wayar Janaam ta saka mata lambar Momy ta kira, Momy na zaune da system a gabanta ta gama sauraren bayanan da Ilyas ya turo mata na tattaunawar da Dr Abdullahi yai da inspector ashir kiran Janaam ya shigo, idonta na akan system ɗin ta daga kiran, "Barrister akwai matsala yanzu Umar Farouk ya kirani" "what? A ina ya samu waya?" Momy ta faɗa haɗe da miƙewa cike da mamaki tana shafa goshinta "ban sani ba". Janaam ta faɗa idanuwanta na lumshewa saboda tsananin ciwon da kanta ke yi mata, "Can't be possible, ki turo mun lambar daya kiraki da ita". Da "Toh". Janaam ta amsa tana katse kiran tare da yin copy ɗin lambar ta tura mata sannan ta ajiye wayar tana kwantawa, ji take gabaɗaya wani irin zazzaɓi na taso mata ta dunƙule waje ɗaya, Aunty Nidrah ta ja duvet ta lullubeta haɗe da gyara kwanciyarta a kusa da ita tana kashe masu fitilar ɗakin tare da karanto masu addu'o'in bacci.
Number na shigowa Ilyas na sake turowa Momy wasu bayanan, number tafara dubawa taga ta Inspector Ashir ce, cike da mamaki ta buɗe voice ɗin da Ilyas ɗin ya turo sai ga Muryar Umar Farouk tangararam tana ji, wani mamakin ne ya sake kamata kenan me hakan ke nufi? Me suke kullawa kuma da suka ba Umar Farouk waya bayan hakan ya sabawa doka, miƙewa ta yi ta shiga kai da komowa a tsakiyar ɗakin, duk wani tunani da zata yi don gano dalilin da yasa sukai hakan tayi amma ta kasa gano komai sai ma zafi da kanta ya sake dauka. Ta zauna bakin gado ta sake nutsa cikin wani tunanin idan ta kamo wannan ta kamo wancan amma har ta gama babu abinda ta iya ganowa..
A police station kuwa Umar Farouk na jin ta kashe wayar ya dafe goshinsa idanuwansa na sake kaɗawa bayin ja, A haka inspector Ashir ya shigo shi da dan sandan ɗauke da kular abincin da aka kawo masa yasa ya ajiye masa gabansa, hannu ya miƙa masa ya ɗora masa wayarsa yana ja da baya ya zauna, Umar Farouk baya magana biyu don haka bai ce komai ba ya jawo kular abincin ya soma ci duk da baya son cin abincin, murmushi inspector Ashir ya saki haɗe da cewa, "Good of you". Sannan ya juya yabar wajen, Dr. Abdullahi ya kira suka yi magana sannan ya kashe wayar ya koma saman kujerarsa ya zauna ya shiga lilo da ita yana sakin murmushin da shi kaɗai yasan ko na meye.
Barrister Nazir kuwa duk wasu hujjoji ta ɓangarensa ya haɗa, inda a cikin bayanan maganar Dr Abdullahi da inspector Ashir suka fahimci cewa Nu'aym na ƙasar UK, kawai mahaifinsa na kokarin wasa da kwakwalwar su ne shiyasa ya kawo zancen India a bayanan sa wanda duka ba gaskiya ba ne a binciken da sukai sun samu hujjoji masu ƙarfin da suke da tabbacin cewa yana ƙasar ta U.k, a daren sun tattauna sosai da Momy inda nan take ta tuntubi wata ƙawarta Ayusher dake U.k ko akwai wanda ta sani dake aiki da immigration na kasar da jami'an ƙasar? nan take ta yiwa mijinta bayani da yake ɗan ƙasar ne shi kuma yana da contact da manyan mutane a kasar ya haɗa ta da abokinsa Locus Henry babban jami'in yan sanda na ƙasar, ba tare da ɓata lokaci ba cikin daren ta neme sa through vedio call tayi masa bayanin case ɗin abinda ke faruwa tare da rokon ya taimaka mata, abunka da komai ya canza yanzu cikin sauki ta internet zaka iya gudanar da duk wasu bincike ka kuma samu bayanan duk da kake buƙata da taimakon Locus Henry bayan ya nemi ta turo masa hoton wanda ake zargin yana kasar a raye suka samu Comfirmation of life don har anguwar da Nu'aym ke zaune sai da suka samu, haka ma sun samu bayanai daga hukumar shige da fice (Immigration Service) da kuma ofishin hukumar jama’a (Civil Registry). Sun kuma samu immigration record nashi na (entry and exist) da yake nuna shigarsa ƙasar da kwanan wata. daga police report ma nan take sun bada rahoton cewa yana raye a kasar bayan sun ga hotunan sa sun kuma yi bincike, suma embassy/consulate wato jami'an jakadancin kasar sun tabbatar da hakan ta hanyar passport stamp dinsa, daga karshe sun yi nasarar samun vedio testimony da aka samu a CCTV cameras ɗin inda yake zaune. A takaice dai wannan daren Momy bata runtsa ba har sai da taga ta haɗa duk wasu legal document da zasu gabatarwa da kotu, bayan ta kammala ta rufe system ɗinta tana jin tamkar kanta zai tsage tasa hannuwa ta rike kan, tafi minti goma a haka kafin ta mike ta shiga toilet tayi arwala ta fito, raka'a biyu tayi ta sallame ta daga hannuwanta sama tayi addu'o'i masu tarin yawa sannan ta tashi tayi raka'atanil fijir don asuba ta kawo jiki, bayan ta gama taci gaba da tasbihi har aka kira sallahr asuba sannan ta mike ta gabatar da ita, anan kan sallaya bayan ta gama bacci mai nauyi ya ɗauketa, ba ita ta tashi ba sai ƙarfe takwas na safe da Tauheeda ta shigo ta tayar da ita, a gurguje ta shiga toilet ta watso ruwa ta soma shiri, tana fitowa Tauheeda ta shigo mata da abun kari a tray, fried yam ce tasha source da soyayyen kwai sai kunun gyaɗa ta ajiye mata a saman gadon tana cewa, "Momy have your break kafin ki tafi, jiya naga bakiyi bacci ba in sha Allah zakuyi nasara, Allah zai fito da Ya Umar". Dago kai Momy tayi ta kalleta, karo na farko da taki wani abu akan yar tata amma sai tayi saurin basarwa, bata ce komai ba ta zauna sama-sama taci doyar don bata jin komai nayi mata daɗi, bayan ta kammala ta mike ta dauki system ɗinta ta saka cikin briefcase tare da wasu takardu sannan ta rufe ta mikawa Tauheedah, wayoyinta ta dauka da key ɗin motarta ta fito Tauheeda ta biyo ta a baya, "Dadyn ku fa?" Ta tambaya tana nufar kofar fita daga falon Tauheedah ta ce, "Bai shigo ba". "ok". Kaɗai Momy tace sannan ta fice, bayan ta buɗe motar ta shiga Tauheedah ta miƙo mata briefcase din ta karɓa ta tayar da motar haɗe dayin reverse tana cewa, "Ki kula, idan ya shigo kice masa na wuce". "Allah ya tsare". Tauheeda ta faɗa haɗe da sauke ajiyar zuciya tana kallon Momyn har motar ta fice sannan ta koma cikin gida ta kwaso kayan da Momy taci abincin ta fito ta zauna falo tana ci, bayan kusan minti talatin da tafiyar Momy tana zaune tana kallo Dady ya shigo ta gaishesa, kanta ya dafa fuskarsa kana kallo kasan ba lallai ne shima ya samu yin baccin ba jiya ya ce, "Mamana kin tashi lafiya?" "Lafiya lau Dady, Momy tace na faɗa maka ta wuce". Kai kawai ya ɗaga sannan ya juya ya fita.
Sai da Momy ta tsaya a office ita da Barrister Nazir suka yi printing out din takardun data haɗa bayanan jiya Barrister Nazir sai jinjina mata yake yi sannan suka wuce kotu.
*KOTU*
Karfe 9:30am (na safe).
Kotu ta cika tayi makil duk an yi shiru bayan shigowar alkali ya zauna a kujerarsa, shaidun masu ƙara suna gefe zaune zukatansu cike da farin ciki domin hango nasara atare dasu, yayin da mutanen dake sauraren ƙararrakin a zauren kotu suka natsu suna jiran abin da zai faru. A wannan rana, bayan sauraren ƙararraki biyu da akayi tare da yanke hukuncin ƙarshe mai gabatar da ƙararraki ya gabatar data su Umar Farouk, Momy dake zaune gefe idanuwanta na akan lauyoyin Dr Abdullahi ta sauke ajiyar zuciya a hankali bayan shigowa da akayi da Umar Farouk da kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai, duk da wahala da raunin data hango tattare dashi ta san lokaci ya yi da za ta fitar da takobin gaskiya ta daddatsa duk wata karya da akayi amfani da ita da karfin Allah ta kubutar da ɗanta.
Bayan yan rubuce rubuce da alkali yai ya dago kai yana kallon lauyoyin kowane ɓangare da jira kawai suke a basu damar yin magana, "kafin bangaren wanda ke ƙara ya gabatar da shedun sa na ƙarshe na gani da ido ko akwai wasu hujjoji da Lauyan wanda ake ƙara suka tanada kafin a yanke hukunci?" Justice Ibrahim Lawal Shanawa ya faɗa yana kallon ɓangaren su Momy. Miƙewa Momy tayi cike da karsashi da kuma yaƙini da ƙwazo irin na uwa tace "Ya mai girma mai Shari'a kafin nace komai kuma kotu taci gaba da saurarar wannan shari’a zan so na fayyace wa kotu cewa gaba ɗaya wannan Shari'a ta ta’allaka ne kan tuhumar wanda nake ƙara ya kashe mutum. Amma yau, a gaban wannan kotu mai adalci zan fito da ainahin gaskiya a fili cike da tabbacin abinda zan faɗa tare da yakinin cewa wanda aka ce an kashe yana raye bai mutu ba amma ba, yana a wata ƙasar an ɓoye shi, an ɓatar da labarinsa, domin a jingina wa wanda ake zargi laifin da bai aikata ba saboda cimma wata manufar". Takawa tayi zuwa gaban alƙali rike da takardun da suka haɗa hujjoji ta ɗaga su tana ci gaba da cewa. "Ya mai girma mai Shari'a wuɗannan sune shaidar da muka hado dake dauke rahotonni daga hukumomin ƙasar da yake ciki da suka bayar kama daga kan Comfirmation of life, immigration record, police report, embassy/consulate da kuma vedio testimony a matsayin notice to the court". Ta ƙare zancen tana mika takardun zuwa ga alkali,
Nan fa zauren kotu ya cika da surutai da mamaki da kuma ta'ajibin wannan sabon al'amari kowa sai faɗar albarkacin bakinsa yake yi, Momy ta ta tsaya daram zuciyarta sai buguwa da sauri take yi amma idonta na nuna ƙarfin uwa wacce ta kawo gaskiya a gaban duniya don karya ƙarya, fuskarta kuwa cike take da ƙarfin gwiwa tana nuna jarumtaka irin ta uwa wacce ta tsaya tsayin daka wajen kare ɗanta tana jiran taji ko shari’a zata ci gaba da wanzuwa ne cikin duhu ko kuma zata dauki hanyar rushewa ne da karfin gaskiya da kuma hujjojin data gabatar, sai da alkali ya gama duba duka takardun data gabatarwa kotu sannan ya ɗaga hannu sama alamun kotu tayi shiru mutane su saurara sannan ya ce "kotu na ci gaba da sauraren ki Barrister maryam". Laptop dinta ta dauko ta kunna ta kamo vedio ɗin Nu'aym acikin swimming