Showing 48001 words to 51000 words out of 157423 words

Chapter 17 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

513

ƙawarta ya shigo paloun ransa a ɓace, kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai haɗe dayin sallama da ƙawar tata, "Sannu da zuwa Alhaji". Ta faɗa tana kallonsa, sai daya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce, "ina makullan gidan gona ta suke dana baki ajiya? Dauko mun zan sauki baƙi aciki ne". Ya faɗa yana danne ɓacin ran dake sake taso masa, kai tsaye Momy ta ce, "Suna hannun Umar Farouk, shi naba ya zauna aciki kafin ka sauko ya dawo gida". "What? Kenan na yiwa yarona hukunci kin canza saboda kin fini son sa ko? A wane dalili zaki bashi makullan gidana bayan ni na koresa da kaina?" "Saboda kai ka haifesa kuma idan ya bar nan ɗin bai da wajen zuwa dole sai can." Rasa ma abun da zai cemata Dady yayi sai kallonta da yake yi cike da mamaki, sosai ya yi kokarin danne fushinsa kafin yace, "Shikennan kici gaba da ɗora ɗanki a rayuwar duk da kike so, kin ɗauki makullan gidana ba da izinina ba kin bashi gashi can ya maida gidan tamkar hotel yana tara yan mata aciki, duk ranar daya jawo miki abun kunya kece da bakinciki ba ni ba, a ranar zakiyi dana sanin duk wudan nan abubuwan da kike yi, sannan ki tabbata gobe kin karbo mini makullan gidana ko idan har na fita gidan nan na samesa aciki zan sa yan sanda su fitar mini dashi ne bayan nasa sun hukunta sa". Yana gama fadar hakan ya bar wajen, Momy kuwa wayarta ta dauka ta shiga kiran Umar Farouk, yana zaune har lokacin sai tunane-tunane yake yi kiran nata ya shigo a cikin wayarsa dake gefe, har zai share kiran sai kuma ya jawo wayar don ganin ko waye, My world, da ya gani jikin screen ɗin a rubuce ya sashi ɗaga kiran da sauri yana kai wayar a kunne sa haɗe da cewa, "Hello Momy". "Na'am Umar Farouk ya kake ya karfin jikin naka?" "Alhamdulillah Momy duk yau sau biyu kaɗai muka yi waya, hope lafiya kike ko?" "Lafiya ƙalau Umar Farouk, kawata ce barrister Lubnah ke handling wani case a kotu, shine fa duk ta uzzura mini da waya ban samu na sake kiran ka ba sai yanzu, Ni ko nace kai da waye a gidan nan yanzu? Saleem na nan ko ya tafi?" "No, yana nan Momy akwai wani abu ne?" "A'a ina so na ji kai ko shi kun yi baƙi ne?" Murza goshi Umar Farouk yai don jikinsa ya bashi an kaiwa Dady wata gulmar ne, sai da ya furzar da iska sosai a bakinsa sannan ya ce, "Ni ne nayi baƙuwa Momy, Nu'aymah ce kawata classmate ɗina kuma, ta zo duba ni da jiki ne, sannan ban san zata zo ba kawai Saleem ne ya bata address sai cemun ya yi zata zo duba ni". Ƙarfaffar ajiyar zuciya Momy ta sauke haɗe da cewa, "Alhamdulillah! Shikennan gobe ka tattara ka dawo gida, zan yi waya da Saleem shi kuma". "But menene Momy". Ya faɗa yana son yasan dalilin da yasa Momy faɗar hakan, "Kai dai kawai kayi abinda na faɗa, sai da safe ka kula da kan ka kaji ko?" "Oh k, bye Mom". Umar Farouk ya faɗa shima ba tare daya ja zancen ba yana ajiye wayar...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRA N1000 KI KARANTA HANKALI KWANCE.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

09079274454

                            28.

Momy na gama waya da Umar Farouk ta kira Saleem, sai daya gaishe da ita cikin girmamawa ta amsa kafin shima ta tambayesa wace yarinya ce ta zo wajen Farouk, ya shaida mata course mate ɗin su ce kamar dai yadda Farouk ya yi mata bayani, sheda masa tayi gobe Farouk zai dawo gida saboda haka zai iya wuce shima, Saleem ya amsa mata da to kafin sukayi sallama, shiru Momy tayi bayan kammala wayar sannan ta miƙe ta shiga toilet ta watso ruwa ta fito tayi shirin kwanciya.

A ɓangaren Nu'aymah kuwa kasa bacci tayi cikin daren sai faman juyi takeyi, ganin Umar Farouk ya sake jefata a wani hali na soyayyarsa mai zafi don ji tai kamar bata taɓa ganinsa ba sai yau, ya ƙara mata kyau da kwarjini fiye da kullum duk da yadda taga ya ɗan yi rama kaɗan, da alama ya ɗan jiki, wayarta ta ciro ta kamo lambarsa, kamar zata kira sai kuma ta kasa ta shiga jujjuya wayar, wayar ce tayi ƙara tana dubawa tamkar a mafarki taga my dream na yawo a jikin screen ɗin wayar, tsabar rudewa  hannunta ya shiga rawa ta kasa daukar har sai da ta kusa tsinkewa, tayi saurin kai wayar a kunne cikin rawar murya tana cewa, "H..he.hello Umar Farouk". A ta ɓangaren sa cikin wata dasasshiyar murya yana shafa kansa ya ce, "Aymah ya kike?". "Lafiya ƙalau ya jikin naka". "Am fine, wuɗannan kayan fa?" Ya faɗa yana sauke idanuwansa akan katam katam ɗin maltina da ruwan da tazo dasu, sai data sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Menene aciki idan aboki ya yiwa abokinsa hidima? Ko ka manta we're friends?" "Is ok". Ya faɗa kafin ya kashe wayar, ji Nu'aymah tayi tamkar ta saka kuka saboda taso su dan taɓa hira da shi ko zata rage raɗaɗin da take ji a zuciyarta, daƙyar ta samu bacci ya iya ɗaukarta, baccin da ko awa ɗaya ba'a yi ba aka kira Sallah asuba.

Ƙarfe bakwai dai-dai suka fito suka nufi airport ita da iyayenta da kuma ƙanwarta Nihla, takwas da rabi jirgin su ya tashi zuwa ƙasar cairo, kwanan su ɗaya anan sannan suka wuce u.k Nu'aym da kansa ya zo ɗaukarsu, Abba da Ummi da kuma Nihla sune a baya, Nu'aymah kuma itace a seat ɗin mai zaman banza Nu'aym na gefe yana driven, sassauta murya yai tare da matso da kunnensa kusa ga Nu'aymah yana faɗin, ""Aymah ya kika baro mun matata?" Murmushi ta saki tare da cewa, "Kai ya Aym kabari mufara isa gida tukuna, hadda sako ta bani na baka". Nu'aym daya juyo yana kallon Nu'aymah jin Janaam ta bada sako a  bashi sai gashi yana ƙoƙarin sauka akan titi. Da sauri Abba da yaga zai daki motar ya ce.

"Kalli gabanka mana Nu'aym wai me kuke tattaunawa haka da baza ku bari har mu isa gida ba". Nu'aym yai saurin kaucewa motar yana shafa kai tare da maida hankalinsa ga tuƙin yana jin tamkar yakai gudun motar ƙarshe don su isa gida da wuri Aymah ta bashi saƙon masoyiyar tasa. A dai-dai bakin wani ƙayataccen gida yai parking haɗe dayin horn mai gadi ya buɗe sannan ya danna hancin motar ciki, wani irin ƙayataccen mension ne da ba zaka taɓa cewa bahaushe ne ya mallakesa ba saboda kayatuwarsa, masu aiki ne suka fito suka kwashi kayan bayan sun fito sun nufi cikin mension ɗin suka biyo bayan su dasu. Suna shiga komai tsaf don Nu'aym yasa an gyara ko ina tun kafin su iso, kai tsaya Abba ya nufi bangaren daya kasance nashi aduk lokacin daya zo hutun karshen shekara ko suka zo Hutu shi da iyalansa, haka ma Ummi nata sashen ta wuce don su samu damar watsa ruwa su huta, Nu'aymah da Nihla na ƙoƙarin barin wajen Saleem yai saurin riko Nu'aymah yana cewa.

"Sis wai meye haka kike ta faman ja mini rai? Don Allah fadamun wane saƙo kyakkyawata ta baki ki bani". Rolling din idanuwa Nu'aymah tayi kafin ta zuba masa su haɗe da cewa. "Ya Nu'aym kabari nayi wanka na sauko tukuna tunda ba guduwa zanyi ba.." tun kafin ta rufe baki ya balla mata harara yana cewa. "Aymah kin renani ko? Yaushe nafara wasa dake haka? Allah kika sake na sake maimaita miki tambayar nan sai na ɓallaki". Nu'aymah ta turo baki haɗe da cewa. "Kai Ya Aym bafa wani saƙo bane, kawai cewa tayi na faɗa maka kai kaɗai ne aduniyarta da.." bata ƙarasa ba ya ɗan ture ta yana ciro wayar sa daga cikin aljihu, vedio call ya kira Janaam tana zaune ita da Mamah tana latsar wayarta tayi saurin barin wajen ta shige ɗakinta tana ɗaga call ɗin. Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke haɗe da ɗaga mata hannu yana cewa. "Hi". Janaam ta yi dariya tana ɗaga masa hannu itama ta ce. "Hi masoyi". "Ya kike?" "Fine ya ƙawata da su Abba sun iso lafiya?" "Lafiya ƙalau yanzu nan ban daɗe da ɗauko su daga airport ba, Aymah ta faɗa mini saƙon ki, but ba shi nai expecting ji daga wajenki ba, just feel like you're not rily care with me". "How masoyi?" Na faɗa ina ɗan zaro idanuwa, yadda nayi da idanuwan ya bashi dariya don haka ya murmusa sosai har haƙoran sa na bayyana haɗe da cewa. "Yeah, nayi zaton zaki sanar da ita how much you missed me ta faɗa mini, kuma kice mata ta faɗa mini cewa na turo a nema mini aurenki ta yadda zan samu kwarin guiwa na dawo kasata naci gaba da zama kusa dake like 5&6?" "Kai masoyi, ko yanzun menene banbancin? Kullum fa muna nane da juna a waya, "Duk da haka dai ai distance ya shiga tsakanin mu, a gaskiya bana jin zan iya ci gaba da jurewa kawai zan sanar da Abba alaƙar mu idan ya dawo kawai yaje ya nema mani aurenki saboda na tabbatar cewa ni kaɗai ne a duniyar ki". "Masoyi kenan! Na rasa sai yaushe zaka gamsu da soyayyar da nake yi maka.." tun kafin na ƙarasa ya ce, "Sai ranar da naga mun zama abu ɗaya ni dake, ranar da kika zamo ni na zama ke, to ranar ne zan samu cikakkiyar gamsuwa akan soyayyar ki, kullum da fargabar shigowar wani acikin rayuwar mu nake kwana da kuma da ita nake tashi, saboda nasan duniyarki tafi ƙarfin rayuwata ni kaɗai". Na langaɓe kai ina ƙoƙarin isar masa da wani saƙo acikin ƙwayar idanuwana haɗe da cewa, "Ka yarda da zancena, ka kuma karɓi saƙon dana aiko maka shi tafiyayye daga ƙasata zuwa inda kake cewa kai kaɗai ne aduniyata kuma babu wani na biyun ka, wannan alƙawarina ne masoyi daga kai ba ƙari". Ina kallon yadda fuskarsa ta cika da annuri har yana neman hannun kujerar da yake kusa da ita ya zauna, iska ya fitar ta baki yana ƙara kafeni da mayataccin idanuwansa dake haifar mini da gajiya kafin yace, "I love you and no matter how dull my days go, your presence makes everything in my life colorful". Nayi murmushi cike da jin kunya ina rufe fuskata, jin ƙarar kiss daya turo baki yana jefo mini da hannu ta jikin glass ɗin wayar yasa nayi saurin katse vedio call ɗin ina dariya, Allah ya sani ina tsananin kaunar ya Nu'aym, zuciyata, gangar jikina haɗi da rouhina sun gama amincewa da shi ɗari bisa ɗari, lokaci kaɗan nake jira na miƙa masa duka ragamar rayuwata yai duk yadda yake so da ita, na faɗa ina faɗawa kan ƙatuwar katifata haɗe da rungume wayar ina jin tamkar shi ɗinne a jikina.

Kiran Ya Jameel ne ya maidoni a duniyar dana lula ta tunanin masoyin nawa da yadda nake son tsara mana rayuwar mu idan muka yi aure, ajiye wayar nayi saman katifar kafin na fice zuwa wajen kiran da yake mun, zaune na samesa shi da abokinsa Anish, tare sukayi secondary da ya Jameel babu wanda bai san shi ba a gidan mu haka ma a gidan su babu wanda bai san Ya Jameel, a takaice dai mun zama tamkar yan uwa mu da shi". Gaishe su nayi cikin girmamawa haɗe da cewa. "Ya Jameel ga ni". "Kawo mana abinci a gajiye muke". Na amsa da to sannan na shiga kitchen na haɗo masu abincin a ƙaton tray na ɗora a saman center table na jawo shi zuwa agaban su, har zan tafi Ya Jameel ya dakatar dani yana cewa". "Ƙarasa ladar ki ki zuba muna mana". Duk da yadda na tsargu da irin kallon da Ya Anish ke mun haka na dawo na zuba masu abincin na miƙa masu sannan na koma ɗakina don Mamah ta fita bata gida. Ban san lokacin da suka gama suka fita ba ko dana fito falon kayan da suka gama cin abincin kaɗai na tarar, tattare kayan nayi nakai kitchen na wanke na tsane na ajiye ko wane a inda yake sannan na fito na zauna falo na kunna kallo ina ci gaba da yi.

********

Umar Farouk kuwa washe gari ya dawo gida bayan ya sauke Saleem a gidan su, a palour ya tadda Momy zaune tana kallo yayi sallama yana ƙarasowa daga ciki, Tauheeda dake fitowa daga ɗakinta tana yin ido biyu da yayan nata da gudu ta rugo ta rungumesa, cikin madaukakin sauti Momy data taso ta nufo wajensa itama a ɗan tsawace ta ce, "Menene haka Tauheeda? Wane irin shashanci ne wannan zaki kada shi". Tauheeda ta turo baki tana ƙoƙarin cire jikinta daga rungumar data yi masa zata bar wajen yasa hannu ya riƙo hannunta, cikin paloun ya ƙarasa shigowa har lokacin yana rike da hannunta ya samu kujera ya zauna itama ya zaunar da ita gefensa, fuskarsa ba yabo ba fallasa yake kallon Tauheeda haɗe da cewa, "Tauheeda me kike ci haka naga kwana biyu kacal amma kin ƙara girma, anya kina karatu kuwa?" Tauheeda ta saki murmushi tana noce kai ƙasa tare da wasa da yatsun hannunta, shafa kanta Umar Farouk yai kafin yace, "To jeki kawo mun wani abu naci yunwa nake ji sosai". Ba tare da Tauheeda ta bari sun haɗa idanuwa da Momy ba da tun ɗazu sai faman harararta take yi ta nufi kitchen, ɗago kai Umar Farouk yai yana kallon Mommy ya ce, "Momy Barka da safiya, ina kwana?" Fuskarta dauke da murmushi tace, "Lafiya ƙalau Umar Farouk, ya jikin naka?" "Alhamdulillah na samu sauki". "Masha Allah haka ake so, ina shi Saleem ɗin yake?" Umar Farouk ya amsa mata da , "Yanzu na ajiyesa gidan su, ga key ɗin" ya kare zancen yana miƙa ma Momy makullan gidan gonar na Dady, dai-dai lokacin Tauheeda ta iso da ƙaton tray a hannunta, a saman center table ta ajiye ta jawosa zuwa gabansa tana faɗin. "Ya Umar wanne zan fara zuba maka?, peppe soup ko sandwich da omelet egg?" Murmushi ya sakar mata haɗe da cewa, "na hutar dake Tauheeda, bari zan haɗa da kaina". Murmushi ta sakar masa sannan ta mike ta fice daga palourn, da kansa ya soma haɗa tea yana kurɓa suna ɗan taɓa fira da Momy har ya kammala, miƙewa yai da niyar zuwa sashen sa sai ga Daddy ya shigo, da mamaki ya bishi da kallo shi kuma Umar Farouk ya sadda kai ƙasa haɗe da cewa...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9.

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRA N1000 KI KARANTA HANKALI KWANCE.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435.

                            29.

"Dady Barka da safiya". Daga haka bai tsaya jin abunda zai cewa ba ya raɓa ta gefensa ya wuce, sai daya ɓace wa ganinsa kafin Dady ya maido kallonsa ga Momy yace, "You see? Kin ga irin tarbiyar yaron naki ko? Na rasa sai yaushe zai san daraja ta a matsayina na mahaifinsa". "Don Allah kadena irin wuɗannan maganganun tunda ya gaisheka, hakan bai kamata ba ko kaɗan wallahi". Ta ƙare zancen tana miƙo masa makullan gidan gonar, "Allah ya kyauta". Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya tare da karɓar makullan ya wuce sashen sa, Momy ta sauke ajiyar zuciya don bata yi tsammanin zai bar zancen ba sannan tabi bayansa.

Umar Farouk kuwa ko daya shiga ɗakinsa a gyare ya samesa tsaf kamar kullum don Momy na kula da hakan ko da yaushe ta hanyar sa Tauheeda ta gyara masa, bakin gado ya zauna yana sauke ajiyar zuciya haɗe da bin ɗakin da kallo, babu abinda yake tunani sai rai ɗaya daya hana masa natsuwar zuciya da kwanciyar hankali wato Janaam, kwanaki biyar kenan ya kasa mantawa da wannan fuskar da gabaɗaya ganinta ya hargitsa masa lissafi, ya kasa tantance me yasa duk bayan daƙiƙu sai tunaninta ya bijoro masa a ƙwaƙwalwa, "Ya Allah!" Ya furta haɗe da ciro wayarsa daga aljihu, group ɗin su na makaranta ya shiga ya yi viewing contacts ɗin dake ciki, a hankali ya shiga duba jerin numbobin yana karanta contact names ɗin dake jiki har ya iso kan na Janaam data saka Amatul-Alim Isma'il, saurin shiga contact ɗin yai yana tuna cewa tabbas wannan sunan shi ya ji ta ambata a waccan ranar tare da viewing hoton data saka a DP dake ɗauke da harafin *'N'* da aka ƙawata da wasu flowers da beautiful sparks, shiru yai na mintuna yana tunanin meye haɗin ta da wannan harafin don daga sunanta har na mahaifin ta babu wanda yafara da shi, tsintar kansa yai da saving number da *'Amaah'* ba wai don ya ƙawata sunan ba sai don kawai bazai iya rubuta sa a Amatul-Alim ɗin ba saboda yai masa tsawo, bayan ya gama ya ajiye wayar a saman gado ya miƙe ya rage kayan jikinsa ya rage daga shi sai ves da boxer sannn ya shiga toilet, mintuna biyar ya ɗaukesa ya fito ya cimma wayar tasa na ƙara, bai bi ta kanta ba ya shiga kallon kansa ta madubi yana ɗan ya mutsa sumar kansa har kiran ya tsinke wani ya sake shigowa, sai da akayi masa kusan 3miseed call ana huɗu kafin ya nufi inda wayar take ajiye saman gado, Number ƙasar waje ya gani lokacin daya ɗauko wayar ya ɗaga ya kai a kunnensa, "Hello Umar Farouk". Ya ji an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login