Showing 135001 words to 138000 words out of 157423 words
kafin yace, "Nu'aym kana nan kana lafiya? Ya jikin naka ina fatar dai babu wata matsala?" "Babu Abba kai kaɗai nake sauraro na samu baki zuciya ta tayi sanyi" ya faɗa yana wani lumshe idanuwa saboda yadda yarinyar dake jikinsa ke wani shasshafa masa kirji cikin wani irin salo, hannunta dake akan nipples dinsa ya riƙe ya kai akan big p ɗinsa yana runtse idanuwa saboda wani irin yanayi daya shiga haɗe da cewa, "I'm fine Abba zan kiraka amma ina so ta ko wace hanya a tabbatar da an kauda yaron nan saboda na tsanesa, itama abu daya yasa bana so a kauda ita yanzu amma Abba..." "Mtsss.. ba sai ka faɗa ba yarona, so nake yi nafara gamawa dashi yaron da ubansa tukuna shiyasa ban bi takan yarinyar ba don kar su gano shiri na, ina gamawa dasu zan dawo kanta zan kuma sa akawo maka ita har inda kake, sai na nuna mata daga ita har iyayenta ruwa ba sa'an kwando bane kuma sunyi kuskuren shiga gonar ɗana su yaudaresa". Nishin da ya ji ɗan nasa yana saukewa da ƙarfi ta cikin kunnuwan sa yasa Abba saurin katse kiran yana jan tsaki, matsalarsa kenan da yaron nasa ya rasa ina ya samo wannan halin, idan yana shashancin sa baya daukar komai da muhimmanci balle ya sauraresa, knocking ya ji anyi a bakin ƙofa da sauri ya juyo yana faɗin, "waye?" Nu'aymah da taji komai ta ce, "Abba nice" tai maganar cikin rawar murya tare dasa hannu ta buɗe kofar ta shigo bayan yai mata izini "Ke lafiya?" Abba ya faɗa yana yi mata wani kallo ganin yadda tabi ta ruɗe jikinta na wani kyarma "Abba dama ya Nu'aym na raye bai mutu ba?" Gabansa ne yai wata irin faɗuwa amma ya dake cikin basarwa ya ce, "Waye ya faɗa miki hakan?" "Abba da kunnuwana naji kana waya dashi, why Abba? Me yasa zakuyi ƙaryan mutuwa? Ni na dauka cewa ya Nu'aym mutumen kirki ne ya dace da rayuwar Janaam shi yasa nayi amfani dashi ya dawo kasar nan don cimma buri na, a tunanina hakan zai sa Janaam ta fita batun Umar Farouk ya dawo gareni idan ya Nu'aym na kusa ashe ban sani ba babban kuskure na aikata, menene amfanin cewa ya mutu bayan daga kai har shi kun san bai mutu b.." kafin ta rufe baki Abba ya ɗauketa da wani irin zazzafan mari yana nunata da yatsa yace, "Ba kida hurumin tambaya akan wannan maganar, sannan babu ruwan ki acikin domin ba kece zaki shirya mana yadda kike son abubuwa su tafi ba mu ne zamu shiryawa kanmu hakan, ke atunaninki ke kika dawo da Nu'aym ƙasar nan? To ba ke bace nine na shirya hakan don cimma buri na na aura masa waccan yarinyar don lalata rayuwar yaron, tun a waccan ranar da sukayi faɗa da Nu'ayma a school ɗin ku na binciko ko waye shi, ashe ɗan abokin hamayyata ne dana dade ina neman hanyar ɗaukar fansa akansa, duk wani abu dake faruwa tsakanin ke da shi ina sane ina kuma bibiyar ku, na so nayi amfani dake wajen lalata rayuwarsa gaba-daya amma sai ya wargaza mini shiri ta hanyar komawa ga ƙawarki, a yadda na tsani Justice Ibrahim kuma na kuma san zafin kan da ɗansa ke dashi na kulla abubuwa da dama da zasu taimaka mini wajen cimma buri na akan su, sai dai kash abubuwa basu tafi yadda naso ba, kwatsam kuma sai gashi cikin sauƙi na kama fatsa har cikin gidana, sai kawai nayi amfani da wannan damar a karo na biyu don cimma buri na, ya rage naki yanzu ki koma gefe ki ja bakinki kiyi shiru ko kuma ki saka kanki aciki ki jefa mahaifiyar ki a damuwa don komai zan iya aikatawa idan har kika yarda naji wannan maganar ta fita". Wani irin kuka ne ya zo wa Nu'aymah tayi saurin toshe baki tare da rugawa da gudu tabar ɗakin, tana zuwa ta faɗa kan gado ta fashe da kuka, ya zatayi da wannan tsaka mai wuya data shiga, me yasa mahaifinta ya zama haka ko dama tun can halayyar sa da dabi'unsa kenan bata sani ba? Ya zatayi ta kubutar da Umar Farouk tunda yayanta na raye? Me zai faru da mahaifiyarta da Abba yayi iƙirarin ita zata jefa cikin damuwa? A take ta ji wani irin zazzaɓi mai ƙarfi ya rufeta, a yanzu tana bukatar taimako wannan lokacin kuma tasan mutum daya ce zata iya yi mata hakan wato Janaam, amma taya hakan zai faru tunda itama tana asibiti a kwance? Sake ƙudundunewa tayi cikin bargo hawaye naci gaba da zubar mata a fuska cike da rashin sanin me zata yi..
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/4, 3:54 PM] Queen Qee's💎: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
64.
Duk da yadda zuciyar Momy tayi nauyi cike da damuwa hakan bai sarar mata da guiwa ba a matsayinta na uwa kuma lauyan dake kare ɗanta, sai ma ji tayi ta samu wani irin karsashi atattare da ita wajen sake tsananta bincike musamman data ga irin dukan da aka yiwa ɗanta gaban idanuwanta, wanda ba don shine yafara karya doka ba daya saka hannu ya daki yan sandan da sai ta bi masa kadin wannan duka da sukayi masa a gaban kotu, a palour ta zauna ta ajiye jakarta a gefe ta cire mayafinta tana jingina a jikin kujerar da take zaune kafin a hankali ta lumshe idanuwanta ta rufe ta shiga duniyar tunanin nemawa ɗanta mafita, cikin sanyin murya Tauheeda data fito daga ɗakinta jin shigowar mahaifiyar tata da kuma yanayin da take ciki ta ce, "Momy sannu da zuwa?" Kamar baza ta kulata ba sai kuma ta miƙo mata hannu har lokacin idanuwanta na a rufe, a ɗaɗɗare Tauheeda ta ƙarasa gunta ta kama hannunta Momyn ta jata zuwa kusa da ita ta zaunar da ita, "Tauheeda taya zan kubutar da yayanki daga kisan da ake zargin ya aikata? Ina ji ajikina ba shine yai wannan kisan ba". Karo na farko kenan da Momy ta taɓa zaunawa haka da Tauheeda tayi mata magana mai taushi cikin sanyin murya, Tauheeda ta ɗago kai ta kalli mahaifiyar tata da har lokacin idanuwanta ke a rufe haɗe da cewa. "You should pray first Momy, sai kiyi bincike sosai, hardworking nasa a cimma nasara inji wani malamin mu, Momy nima ban yarda Ya Umar zai iya kashe mutum ba idan kuma da gaske ya kashe Momy to ina gawar wanda ya kashe?" Da sauri Momy ta buɗe idanuwa haɗe da yashi zaune tana kallon Tauheeda, ta ce "Me kika ce?" "Ina gawar wanda ya Umar ɗin ya kashe idan da gaske ne?" Take wani tunani ya zowa Momy cikin kai nan take ta jawo handbag dinta ta ciro wayar ta tare da wasu takardun bayanan da suka rubuta na shaidu da aka gabatar a kotu don maganar Tauheeda ta hasko mata wani abun, ba tare data bi takan Tauheeda ba ta miƙe ta wuce bedroom dinta ta dauko bayanan data karbo a police station da wayoyin Umar Farouk ta dawo parlour ta zubesu a gabanta, daya bayan ɗaya ta shiga duba bayanan da kuma hujjojin da suka haɗa a bangaren su tana tunano shedun da lauyoyin mai ƙara suka gabatar, lokaci ɗaya tana sake nazari akansu tare da ɗaukar wayoyin n kumar Farouk ta shiga yin binciken wasu abubuwa da take son ganowa musamman akan Janaam, ganin haka yasa Tauheeda ta je ta hado mata abinci da ruwa ta kawo mata, sai data tsiyaya ruwan a cup ta miƙawa Momy tana cewa, "Momy ga ruwa". Ta karɓa sannan ta zuba mata abincin ta jiye mata a gefenta, bayan Momy ta shanye ruwan ta ajiye cup ɗin ta miƙa hannu ta jawo wata takarda ta zana wasu lambobi akai sannan ta sake jawo wata ta kura mata idanuwa, murmushi ta saki haɗe da zana wata lambar tana komawa kan kujera tana kallon takardun ɗaya bayan ɗaya, a hankali ta ce, "Saleem-Janaam-maigadi-kisan kai-Umar Farouk-Dr abdullahi-'yan sanda-asibiti-gawa, tana ina?" Momy ta ƙare zancen tana tambayar kanta, abinda tun farkon Shari'a yakamata su fara tabbatar da bayanan haka a rubuce, hannu ta miƙawa Tauheeda ta ɗauko abincin ta bata, a hankali take cin abincin tana sake zurfafa tunaninta, tabbas akwai bukatar bayanai daga asibiti ta yadda akai da gawar a rubuce bayan an tabbatar da wanda aka kashe ɗin ya mutu, sai data gama cin abincinta a tsanake sannan ta miƙe haɗe da kallon Tauheeda tace, "Haɗo mini takardun nan waje ɗaya duka ki kawo mini a ɗaki". Tana gama fadar hakan ta ɗauki jakarta da wayoyin Umar Farouk ɗin da tata ta wuce ɗakinta, tana zuwa ta ajiye su akan gado sannan ta rage kayan jikinta ta wuce toilet, bata wani jima ba ta fito ta samu Tauheedah har ta shigo mata da takardun ta ɗora akan gado, ɗauke su tayi ta ajiye inda ya dace tare da wayoyin Umar Farouk ɗin sannan tayi sallar la'asar, tana gamawa ta kira Barrister Nazir tayi masa bayanin abinda ta sake fahimta akan case ɗin, shiru yai yana nazari shima kafin yace, "Barrister Maryam wannan lamarin kawai ɗaure kai aciki, wannan abokin nasa ma Salim abun tuhuma ne kuma ina zarginsa akan yasan wani abu, sannan kamar yadda kika ce yakamata mu samu bayanan tabbatar da mutuwar nan tun farko, amma ko yanzu bata ɓaci ba zamu iya yin haka". "In Sha Allah Barrister Nazir ni ina ji ajikina wannan abun kamar shiri ne, kawai Umar Farouk ya taka sawun ɓarawo ne, idan ba haka ba me yasa mai gadi zai bar aikinsa ya tafi wani wajen bayan yasan masu gidan basa nan, bayan haka taya su da suka je bukin taya yarsu murnar kammala school zasu dawo kafin a ƙare kuma tare da ita? Wannan fa abun dubawa ne saboda a bayanan da muka gani an aikata kisan karfe sha daya da mintuna ashirin kama 'r yadda na gani a rubuce, iyayen yaron sun dawo gida karfe sha biyu dai-dai, sannan an kammala bukin ne karfe ɗaya da rabi, me yasa basu kai wannan lokacin ba suka dawo gida? Abu na biyu Mai gadi ya tabbatar da babu kowa a gidan, ya akai bai san wanda aka kashe na ciki ba? Dole akwai lauje cikin naɗi a case ɗin nan Barrister Nazir don haka mu kanmu muna bukatar wannan yarinyar da suka gabatar a matsayin shedar gani da ido". "Tabbas muna bukatar ta". Barrister Nazir ya faɗa yana nazarin wasu abubuwa shima, sun jima suna tattaunawa kafin sukayi sallama, suna gama wayar takira inspector Ashir, bayan sun gaisa ta ce, "Inspector Ashir su waye da waye suka dauki gawar yaron Dr. Abdullahi zuwa asibiti, wace asibiti ce aka kai gawar kuma wane Dr ne ya karɓi gawar zuwa sashen bincike?" Wani zufa ne ya keto wa inspector Ashir jin tambayoyin da Momy ta jero masa da bai yi tsammanin jinsu daga gareta ba, cikin sarƙewa murya yace, "Eh.eh to in ganin kamar su sajan Bala ne da sajan James, bari zan haɗa ki dasu idan mun dawo don yanzu wani aiki zamu fita da aka kiramu cikin gaggawa". Shiru Momy tayi tana nazarin yadda muryarsa ke fita kafin tace "ok" tare da kashe wayar, lambar wani data sani cikin jami'an c.i.d office ta jawo ta tura masa lambar inspector Ashir sannan ta kirasa, sai da suka gaisawa sannan tace, "Ilyas na turo maka wata lamba ina so ka duba yanzu yanzu afara bibiyar layin akwai binciken da mukeyi akansa". "Ok Barrister Maryam yanzu nan zamuyi hakan". Ya faɗa yana katse kira tare da buɗe akwatin messages dinsa ya ciro number nan take suka fara aiki kanta.
Inspector Ashir kuwa babu wani aiki da zasu fita yi kawai rashin amsar da zai bawa Barrister Maryam yasa shi yin ƙaryar, yana jin ta kashe kiran ya shiga kai da komowa cikin office ɗin nasa yana tunanin ko meye abun yi, da sauri ya jawo lambar Dr. Abdullahi ya kira, yana ɗagawa yace, "Ranka shi daɗe akwai matsala, da alama Barrister Maryam tafara gano wani abu, yanzu ta kira tana tambayar su waye suka dauki gawar yaronka da asibitin da aka je da kuma Doctor ɗin daya karbi gawar zuwa sashen bincike, kuma kasan.." kafin ya karasa Dr. Abdullahi yace, "Na san zata iya mana, amma ko me zata yi hakan bazai canza ɗanta ya kashe mini ɗa ba kuma dole a kashe shi shima don bazan yafe ba" "Amma ranka shi daɗe.." "is ok inspector Ashir kabarta tayi binciken ta babu abinda zai sauya". "Shikenan ranka shi daɗe ". Inspector Ashir ya faɗa tare da kashe wayar yana sauke ajiyar zuciya don shi kam fa cikinsa ya ɗuri ruwa.
Abba na gama waya da inspector Ashir ya nufi ɗakin Nu'aymah yana kwala mata kira, yana kawowa bakin ɗakin nata tana fitowa "Ina wayarki?" Ya faɗa yana nuna mata hannu, ɗaki ta nuna masa ya wuce ciki kai tsaye ya dauka ya shiga messages dinta da WatsApp yana duddubawa cikin ɓacin rai ko zai ga wata alama da zata nuna ita taje tayi wani shirmen, bai ga komai ba ya dago kai yana watsa mata wani kallo haɗe da cewa, "Kin je kin aikata wani abun ne? fadamun gaskiya ko yanzu ranki ya ɓaci?" Ya faɗa a hasale yana yi kanta ta shiga girgiza kai tana ja da baya hawayen dake maƙale cikin idanuwanta na saukowa akan fuskarta, Ummie ce ta shigo cikin ɗakin da sauri ta shiga tsakaninsu tana faɗin, "wai menene haka Abba me kuma yarinyar nan tayi maka ne? Tun dazu data fito ɗakinka take faman kuka ko abinci taƙi taci nayi tambayarka me ya faru har na gaji taki cewa komai, don Allah idan akan yaron nan ne ka shafa mata lafiya tunda ita kanta tasan hukuncin da zai ƙare akansa dole ta hakura dashi". "Rufamun baki ki fice ki bani waje, ban faɗa miki idan ina yi da ƴaƴana ba bana so kina saka mini baki? Zaki fita ko kuwa sai ranki ya ɓaci?" Ya daka mata tsawa wanda hakan yasa Ummie barin ɗakin cikin bacin rai, sai daya tabbatar da Ummie ta sauka sannan ya kalli Nu'aymah yace, "Na dai faɗa muki abinda zai iya faruwa ga mahaifiyarki idan kika sake kikai kuskuren da har wani ya ji maganar nan ko da kuwa ita ce, ban taɓa sa abu a gabana ba na faɗi saboda haka ke baki isa kisa wannan karon na fadi ba, shashashar yarinya da bata san ciwon kanta ba". Yana ƙare zancen ya jefa wayar tata a gaban aljihunsa sannan yabar ɗakin yana huci, dole ne yasa mata idanuwa da tsaro sosai don bazata sake fita gidan ba sai an gama shari'ar, idan ba haka ba ya fahimci komai zai iya faruwa don ita kadai ce ta san da zancen kuma zata iya bashi matsala.
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/4, 3:54 PM] Queen Qee's💎: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
65.
Yau kwanan Janaam huɗu asibiti don likitoci sunce tana buƙatar hutu sosai da kuma kulawa saboda jinin ta ya ɗan hau da alamu ma depression na neman ya kamata saboda yawan tunani da damuwa da take yi, Mamah ce tare da ita da matar Ya Jameel Aunty Nidrah dan itama jikinta ba laifi yanzu yayi kyau sai dan abinda baka rasa ba na laulayi da masu ciki ke fama dashi, kasancewar Ya Jameel kullum yana wajen aiki kuma baya son barin ta a gida ita kaɗai cikin kaɗaici yasa kullum idan zai tafi wajen aiki da ita yake zuwa asibiti kafin ya wuce sai ta karbi Mamah data kwana ita kuma ta koma gida tayi wanka ta zo masu da abincin rana da zasu ci, breakfast kuma su suke zuwa da ita, haka ma da magrib idan ya taso wajen aiki zai biyo ya ɗauketa su koma gida da daddare idan zai dawo sai yabiyo biyo masu da abincin dare, Janaam ta rame tayi wani irin baƙi tamkar ba ita ba, kullum cikin kuka take abinci ma sai anyi da gaske da ban baki da lallami ake samu taci, kana kallonta kasan ba ciwon gangar jiki kadai ke damunta ba har dana zuciya don shi kadai ne ke saurin raunata mutum kamar yadda ya yi mata, yau suna zaune bayan sallar la'asar tare da Mamah da Aunty Nidrah dake kan sallaya ta kammala sallah, Barrister Nazir ne da Barrister Maryam suka shigo fuskar nan tata a haɗe tana nuna tsantsar tsana da kuma kiyayyarta akan wacce suka tunkaro wajensu, gaban Aunty Nidrah ne yai wani irin faduwa sanin ko waye Momy da sauri ta miƙe cikin sake fuska da girmamawa, suna kawowa Barrister Nazir ya koma gefe ya tsaya Aunty Nidrah tace, "Sannu da zuwa Momy ina wunin ku?" Bata amsa ta ba ta kalli inda Mamah take ta ce "Barka dai Hajiya ya masu jiki?" "Da sauki" Mamah ta faɗa tana kallonta cike da mamakin abinda ya kawo su wajensu don ta gane su sune lauyoyin dake kare Umar Farouk da ta gani a kotu waccan ranar, Aunty Nidrah ta jawowa Momy kujera ta zauna tana cewa, "Mamah wannan itace Momy ƙanwar.." saurin ɗaga mata hannu Momy tayi haɗe da cewa, "Ya isa Nidrah bana buƙatar alaƙa idan ina bakin aikina, saboda haka kija bakinki kiyi shiru ba wajenki nazo ba". "Shikenan" Nidrah ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya tare da addu'ar Allah yasa kada Momy tayi abinda zai jawo zubewar kima da darajar ta a wajen mahaifiyar mijinta da kuma 'yar uwarsa a matsayinta na ƙanwar mahaifinta, kallon Janaam Momy tayi da wani irin takaicinta ke cinta haɗe da cewa, "Sunana Barrister Maryam Hafiz Hakim tare da abokin aiki na Barrister Nazir, na san kin gane mu mune lauyoyin dake kare wanda ake zargin aikata kisan kai a gaban idanuwanki, mun zo ne idan