Showing 24001 words to 27000 words out of 157423 words

Chapter 9 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

532

inda Allah ya taimaketa kayan jikinta baƙaƙe ne ta yarfe hijabinta sannan ta ƙarasa cikin makarantar, idan tace wannan abun bai ɓata mata rai ba to tabbas tayi ƙarya, sai dai ta sani munduwa ɗaya bata amo ita kaɗai, so yake yi ta biye masa amma ta ɗauki alkawarin duk abinda zai yi mata bazata taɓa kulasa ɗin ba har ya gaji ya bari, kamar yadda bazata taɓa daina jin tsanarsa a zuciyarta ba in dai zai ci gaba da tozarta mutane haka.

Ko data iso bakin department ɗin su har malamin ya shiga, tana zuwa ya dakatar da ita waje ya hanata shiga, kamar za tayi kuka ta ciro wayarta ta turawa Nu'aymah sako akan tayi mata attendance, lokacin wayar na a hannun Umar Farouk don seat ɗaya suka zauna da Nu'aymah. Yana ganin sakon ya yi deleting ya kuma hana Nu'aymah da tayi yunkurin yi mata attendance ɗin bayan an tashi tayi mata.

Ransa fes suka fito hall ɗin da sukayi lecture suna tafe shi da Nu'aymah suna fira suna dariya, Nu'aymah na hango ni da sauri ta nufo wajena tana faɗin "Am sorry Besty nasan ni mai laifi ce agunki, wlh Umar Farouk ne yace na shigo da wuri akwai maganar da yake so muyi, kinga ma ko dana shigo ɗin bamu samu yin maganar ba, amma bari naje mu gama yanzun nan zan dawo". Nayi sauri ina ƙoƙarin danne zuciyata na ce. "Karki damu ba komai ni zan wuce ma yanzu, Please na tura maki sako ki yimin attendance kin samu yi mini ɗin kuwa?" Nu'aymah ta ciro wayarta ta shiga dubawa da alama bata ga sakon ba ta nuna mani wayar tana cewa. "Kinga wallahi bai shigo ba, amma kin san ko baki turo mini ba ai dole zanyi maki ko?" "A da kenan Besty kafin ki sauya banda yanzu". Na faɗa ina kokarin barin wajen, ko kadan bana so na faɗawa Nu'aymah magana marar daɗi akan alaƙarta da Umar Farouk don bamu samu zuwa tare ba kamar yadda muka saba, nasan laifin ba nata bane duka set up ɗin Umar Farouk ne, ya yi ne don ya ƙuntata mani, Nu'aymah naji ta riƙo hannuna tana cewa. "Meye haka besty, ya naga kayanki a jiƙe kuma kamar kina cikin ɓacin rai, lafiya dai ko?" "Ba komai". Na faɗa ina ƙoƙarin haɗiye takaicin dake raina, "To ki jirani naje yanzun nan na dawo sai mu tafi". "No jeki kawai, ni zan hau adai-daita." Na fada ina cire hannunta daga riƙon data jimun, "Haba besty ba dai fushi kika yi ba ko?" Nu'aymah ta faɗa fuskarta ɗauke da damuwa, ganin haka yasa na ɗan sassauta yanayin nawa haɗe da cewa, "ba wani fushi, bana so n takuraki Kinga bansani lokacin da zaku gama ba, kibari kawai na tafi". "Ni gaskiya a'a Besty don Allah ki jirani ba komawa sanyi ba indai ba fushi kika yi ba". Bana so ta dauki wani abu a ranta kawai sai nace ta tafi zan jira ta ɗin amma kada ta jima taga an kusa kiran sallar magrib, da sauri ta bar wajen na bita da kallo cike da tausayinta, na rasa me ta gani a jikin Umar Farouk da har take sonsa haka don ko maza zasu ƙare bana jin ni zan iya yi masa ko da kallon mutunci ne balle kuma na wata alaƙa, alaƙar ma wai ta soyayya..

Call/WatsApp

07040402435

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            15.

*LAST FREE PAGE*

Sai da nayi minti goma sha biyar a tsaye ina jiran dawowar Nu'aymah, jin shiru gashi har magrib ta kawo jiki ya sa na ɗauki waya na kirata, ringing ta yi tayi bata ɗaga ba har sai da rai na ya soma ɓaci sannan na ji can ta ɗaga. "Haba Nu'aymah idan baki tashi tafiya ba sai na wuce abina, magrib ke neman yi fa amma ace har yanzu muna cikin school bamu koma gida ba". Na faɗa raina a ɗan ɓace ina kashe wayata ba tare dana jira me zata ce ba, can sai gata tare da Umar Farouk na hango tafe, hararar ta nayi lokacin da suka ƙaraso ba tare dana damu da Umar Farouk dake wajen ba nace, "Allah da kin ƙara minti ɗaya sai dai ki isko nayi tafiyata". Nu'aymah tayi dariya tana bani haƙuri sannan ta zura key ɗin motar ta buɗe ta shiga ta zauna nima na zagaya na buɗe ɗaya gefen na shiga na zauna. "Good night Aymah". Na ji Umar Farouk daya leƙo ta jikin glass ɗin gefen ta ya faɗa yana barin wajen, na taɓe baki ina kauda kaina gefe har ta tayar da motar muka fara tafiya, wata ƙara motar ta fara yi da yasa Nu'aymah ta tsaya tana faɗin, "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un". "Me yafaru ne?" Na faɗa ina kallonta, sai data daki steering motar sannan tace, "Wallahi tayar motar mu tayi faci Janaam, gashi ba masu ƙara iska anan kusa, ya zamuyi kenan?" Ban kai ga bata amsa ba tana rufe baki Umar Farouk na kawowa saiti damu cikin tashi motar, tsayawa yai haɗe da cewa, "Aymah lafiya?" Ta amsa masa tana cewa, "Tayar motar nan ta gaba ta yi faci". Umar Farouk ya kalli ƙasan motar ta ɓangaren da yasa Felicia ta sace masa tayar Nu'aymah ɗin ya saki murmushi sannan ya ɗago kai yana cewa, "To yanzu ya za'a yi friendy? Zan rage maku hanya ne ko kuma na jaku acikin motar?" Nu'aymah tayi dariya haɗe da cewa, "Wane ka jamu aciki friendy? Bari kawai muzo kayi dropping ɗin mu gida in yaso zan Turo driven Abba ya dauki motar". "Yadai yi dropping naki gida ke kaɗai". Na faɗa ina buɗe gefen da nike na fita, cikin ɗan ɗaga murya na ji Umar Farouk yace, "Ungo na mashin ki bata Aymah dama nima banyi niyar ɗaukarta a motata ba". Ban san me Nu'aymah tace masa ba don tuni nayi gaba abina, ina fitowa bakin gate na tsaya ina jiran abun hawa duk da nasan zai ɗanyi wahala na samu saboda marece ya yi sosai, ina tsaye suka fito Umar Farouk ya yi parking yana sauke glass ɗin gefen Nu'aymah, na ɗauke kaina gefe duk da ina jin Nu'aymah na yimin magiya na shigo mu tafi amma nayi banza da ita, saboda dana shiga motarsa nafi so na koma gida a ƙafa, ina kallo ya tada motar sukayi tafiyarsu yana faman yi mini dariya, na ji wasu hawaye masu zafi sun cika mini ido don na ji ajikina shi ne yasa aka sace tayar motar Nu'aymah don kawai ya ƙuntata mini, saurin haɗiye hawayena nayi don bana so na zubar dasu a banza ga wanda bai san mutuncin kansa ba ma balle na wani. Ganin bazan samu abun hawa ba yasa na fara takawa da ƙafa zuwa gida, haka kuwa akayi tamkar hadin baki ban samu abun hawa ba har na iso gida a gajiye, sosai nake jin kaina tamkar ba ni ba saboda tsananin wahala, na samu daƙyar na fara yin sallah sannan nayi wanka na kwanta, ina ganin kiran Nu'aym amma na kasa ɗaga wa har ya tsinke, sake shigowa wani kiran yai amma saboda baccin yai mun yawa ina kallo na kasa ɗagaw har bacci ya yi awon gaba dani, bani na farka ba sai zuwa ƙarfe goma na dare, na wuce kitchen na ɗibo abinci Mamah na zaune a falo tayi mini sannu don tunda na shigo zata fara yi mini faɗa na faɗa mata ban samu abun hawa ba yau a ƙasa na dawo gida. Murmushi nayi kawai na soma cin abinci na ina kallon wata drama da Mamah ke yawan kallo da ake yi a Zee word, ina cin abincin Ya Jameel ya shigo, da alama shima a gajiye yake yadda naga ya faɗa kan kujera, gaida Mamah ya yi na gaishe sa nima sannan yace, "Mamah yau nasha wahala sosai, amma alhamdulillah an samu abinda ake buƙata, zuwa wani sati ina sa ran zan buɗe shagona in sha Allah". Mamah ta amsa mashi da cewa, "Kai ma sha Allah, Nasrun Minallah Allah ya sanya maka albarka a ciki kuma yasa abuɗe cikin nasara da alkhairi, yau kam anko kuka yi kai da ƙanwar ka". Sai daya kalleni sannan ya cewa Mamah, "Anko muka yi? Na me kenan Mamah?" "Na wahala da kace ka sha, itama yau tun daga school ɗinsu ta dawo gida ƙasa wai ba abun hawa, ka ganta nan sai kusan ƙarfe takwas ta dawo gidan nan". "Subhanallahi me yasa kika ƙi kirana, ai da duk abinda nake yi na aje naje na ɗaukoki, halan ina ita ƙawar taki ne ko bata shiga ba ne yau?" Ina tsiyaya ruwa a cup zan sha na ce, "Tayar motar tace tayi faci". "Ok tare kuka dawo ƙasa kenan? Next time idan haka ta sake faruwa ki kirani sai naje na ɗauko ku". Shiru nayi nabar zancen a yadda ya fahimcesa don idan yasan gaskiya ba ƙaramin faɗa zan sha ba ya kuma datse taren tamu kamar yadda ya so yi tun farko, Mamah tayi tsammanin zai fara shiga ya watso ruwa ne sannan yaci abinci, amma sai taji yace na fara kawo masa abinci yaci idan ya gama sai yayi wankan ya kwanta ya huta gaba-daya, na je na haɗo masa abincin na kawo masa sannan na koma inda nake zaune ɗazu na zauna, yana cin abincin muna fira har ya kammala na kwashe kayan na kai kitchen na wanke, daga can ɗakina na wuce na kwaso littafaina na soma bitar abinda akayi mana, kiran Nu'aymah ne ya shigo a wayata da sai a lokacin na bi ta kanta, tambayata tayi ya na iso gida na amsa mata da lafiya ƙalau, muka ɗanyi magana a tsaitsaye sannan ta kashe wayar, tarin messages ɗin ya Nu'aym na gani da missed call ba adadi, duka yana tambayata ne akan ya nike, ina lafiya, "I'm fine". Na rubuta na tura masa a taƙaice sannan na kashe wayar don har ga Allah yau bana jin yin hirar karatu nake so nayi sosai kafin na sake komawa na kwanta. Bani na kwanta ba sai zuwa kusan ƙarfe ɗaya na dare bayan na kammala karatun na shiga toilet na yo arwalar bacci sannan na kwanta.

*********

Sosai hankalin Nu'aym ya tashi ganin irin reply ɗin da Janaam ta mai do masa dashi, take zuciyarsa ta fara yi masa yan saƙe-saƙe tana hakaito masa wasu abubuwa, gashi ya yita kiranta lambarta a kashe, kamar zai yi kuka ya juya akalar kiran nasa ga Nu'aymah, tana ɗagawa ko gaisawa basuyi ba yace. "Aymah lafiya, me ke faruwa da Janaam ne?" "Ban gane ba Ya Aym, wani abunne aka ce maka ya faru da ita?" "Oh my God! Stop this ki faɗa mini gaskiya, lafiya take saboda na kikkira wayarta bata ɗaga ba na tura mata saƙonni masu yawa sai dai ta maido mini da amsar daba ita nayi tsammani daga wajen ta ba, daga ƙarshe ma ko dana sake trying number nata it's switch up, what's going on?" "Calm down Ya Nu'aym, Janaam tana lafiya, amma wai yaushe har kuka yi irin wannan shaƙuwar da gabaɗaya duk kabi ka ruɗe hakan?" "Aymah make damunki ne ina tambayarki kina tambayata?" "Kayi haƙuri Ya Aym, mun haɗu da ita school lafiya ƙalau take, yanzu haka bamu daɗe da gama waya da ita ba, ina ga dai akwai sabgar da take yi ko kuma wani abun daban, amma dai na tabbata lafiya take". Nu'aymah ya sauke wata ƙarfaffiyar ajiyar zuciya haɗe da cewa, "Alhamdulillah, Shikenan Aymah sai da safe." "Ok Ya Aym take care bye". Ta faɗa tana kashe kiran cike da mamaki, duk data jima da sanin soyayyar dake tsakanin su amma batayi tsammanin shakuwar dake tsakaninsu tayi karfin da zai iya shiga irin wannan damuwar ba don bai ji daga gareta ba, murmushi ta saki tana hango tsananin dacewar yayan nata da ƙawarta kamar yadda itama take ganin ta dace da Umar Farouk ɗinta.

*********

Washe gari bayan kammala lecture ɗin mu muka nufi wajen cin abinci, tun akan hanya Nu'aymah ke waya har muka iso wajen, wayar da nake da tabbacin da Umar Farouk ne take yi wanda hakan ya sa nake ji tamkar nayi mata shegen duka, daƙyar na samu ta gama wayar tana faɗin "ok sai ka shigo". Sannan ta katse kiran, girgiza kai kawai nayi ba tare da nace mata uffan ba kafin nakira a kawo mana abinci, indomie da soyayyen kwai mukayi oder sai kuma lemu mai sanyi da ruwa, bayan an kawo mana abincin muna fara ci sai ga Umar Farouk ya shigo, tun dana ganshi na ɗaure fuska ina sake haɗe rai tamkar ban taɓa dariya ba, seat ɗin dake tsakiyar mu ya ja ya zauna yana kallon Nu'aymah yake faɗin. "Wai Aymah meye matsalarki ne? Ina matsayin abokin ki baza ki iya nema na ba muje muci abinci mai kyau da ma'ana ba sai kin zo kin ci irin wannan jagwalgwalon da zai iya taɓa maki ciki? Wane ba kauyen ke baki shawarar yin hakan? Please don Allah tashi muje na kai ki restaurant inda zaki ci tsabtataccen abinci mai kyau da lafiya Kinga nima yunwar nake ji ga su Felicia can a waje tare muke suna jira sai mu tafi gabaɗaya". Ina kallon yadda Nu'aymah ta haɗe rai jin ya ambaci mutanen nashi nayi kamar zanyi dariya amma nayi saurin rufe baki ina tari, cike da kishi Nu'aymah tace. "Ni bazan je tare dasu ba kawai kuje". "Dalili? Ko kin manta tare kika ganmu dasu?" Umar Farouk ya faɗa yana haɗe rai, Nu'aymah na kumbura fuska itama ta ce, "Amma ai nasan matsayina da nasu ba ɗaya ba, taya za'a yi kace zamu fita tare dasu, kawai ka sallamesu sai mu tafi tare da Janaam". Wani kalar kallo Umar Farouk ya yi mata tare da kallona yace, "Ni na faɗa maki cewa kina da wani matsayi ne daya zarta nasu aguna? Kawai ki tashi muje in zaki je amma ni bazan ɗauki masu shigar munafukai a motata ba, kuma kema kin san da haka". Ya ƙare zancen yana miƙewa tare da kafeta da idanuwa, a mamaki na sai naga Nu'aymah ta miƙe, so ya riga da yayi mata illar da bata isa ta iya yi masa musu ba, kallona tayi tace, "Besty bari muje mu dawo". Na kaɗa kaina ta cikin niƙab ina cewa, "A sauka lafiya Besty". Ba tare dana kalli inda suke ba, ni dai burina yabar wajen na samu naci abincina hankali kwance, in da sabo a 'yan kwanakin nan nafara sabawa da irin wulaƙancin da yake yi mini, har sun juya sun tafi sai Umar Farouk ya tsaya, juyowa ya yi sai kawai ganin shi nayi akaina ya dauki plate ɗin abincin da Nu'aymah ta tashi ta bari ya kifa a cikin abincin nawa yana faɗin. "Nasan ba lallai ne ki ƙoshi da naki ba, to ga wannan ki ƙara dashi tunda babu a gidan tsoho". Yana gama fadar hakan ya juya, har yayi step ɗaya sai kuma ya sake dawowa yana cewa, "Oh! na manta ya kamata fa na rage maki aiki yan mata". yana gama faɗar hakan ya ɗauki gorar lemun dake gabana ya buɗe ya tuttulesa duka a cikin abincin yana ƙare mini kallo, nayi folding hannaye na akan ƙirji ina yin relaxing a bayan kujera ina kallons har ya gama tuttule lemun duka acikin indomien dake gabana, gorar ruwa ya sake ɗauka ba tare dana ankare ba kawai naji yana tuttula mini ita a jiki, cikin ɓacin rai na miƙe da niyar zabga masa mari kamar waccan ranar sai kawai na ji kamar an riƙe mini hannu. Murmushi ya saki haɗe da cewa. "Me ya hanaki 'yan mata? Wlh kikayi kuskuren sake ɗora hannunki akan fuskata sai na yimiki wulakancin da baki taɓa tsammani ba a rayuwarki, zaman makarantar nan ma sai yayi maki wahala bagidajiya kawai ai da ki mareni ki gani, ko waccan ranar da kika ga na ƙyaleki akwai tanadin abubuwa da dama dana yimaki da sai kin yi nadamar abinda kika yi mini a rayuwarki, wannan ma kaɗan daga ciki kika gani". Yana ƙare maganar yayi gaba yana cewa Nu'aymah su tafi, tsaye tayi ta kasa motsawa tana kallon irin wulaƙancin da yaiwa Janaam, juyowa yai ransa a ɗan ɓace jin bata biyo shi ba yace. "Muje mana Aymah?". "Kawai kaje ni bazan tafi ba". Ya ɗan zaro idanuwana yana yanke fuska yake cewa, "Saboda me?" Nu'aymah tace, "Haba Umar Farouk Janaam fa ƙawata ce, ko me tayi maka ai ta cancanci kayi mata kara ka ɗaga mata ƙafa ka dena yi mata wuɗannan abubuwan ko don ni?" Wani kallo ya yiwa Nu'aymah yana haɗe girar sama da ƙasa yake cewa, "Nayi mata kara? Wace karar ita tayi mani bayan kina kallo ta ɗaga hannu ta mare ni a gaban mutane? Tukuna ma da kike cewa ko don ki na ɗaga mata ƙafa to a matsayinki na wa a wajena zan yi hakan? Ko kin manta you're just a friend not my sister, cousins ko wani daga cikin family nawa to akan me zan ƙyaleta?". "Haka zaka ce Umar Farouk?" Nu'aymah ta faɗa idanuwanta cike da hawaye, Umar Farouk ya amsa mata da "Eh haka na faɗa, ke daban ita daban ba ɗaya kuke ba a wajena balle kiyi tunanin zata ci albarkacin ki, don haka idan zaki zo mu tafi kizo idan kuma kin fasa zuwa fine". Yana gama faɗar hakan ya fice ya ja motarsa dasu Billy ke ciki suna jiransa suka bar wajen....

ƘARSHEN FREE PAGES KENAN, WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, GA MAI BUƘATA ZAI IYA TURA KUƊINSA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT ₦1000

*ACCOUNT NO*

7040402435 (MONIEPOINT)

*ACCOUNT NAME*

BALKISU SANI KAURA

*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR*

07040402435

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

           

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login