Showing 132001 words to 135000 words out of 157423 words
saye cikin hijabin ta har ƙasa, gabaɗaya ilahirin jikinta rawa yakeyi tana jan ƙafafuwanta daƙyar da take ji tamkar basu iya ɗaukar gangar jikinta, wani tashin hankali take ji da faduwar gaba tunda ta shigo cikin kotun da idanuwan mutane sukayi casa kanta har aka iso da ita jikin akwatin da zata tsayawa aciki, ji tayi kamar zata iya faɗuwa hakan yasa tayi saurin riƙe akwatin tana lumshe idanuwa ta kasa ɗagowa ta kalli kowa, Umar Farouk yai wata irin zabura yana miƙo hannu ganin kamar faɗuwa z a tayi do tunda aka shigo da ita idanuwansa ke akanta, haushin kansa yake ji matuƙa na ganin shine silar shigar ta wannan yanayin da yake kallonta aciki da baya da ikon hanata shigarsa acikin domin sosai ya hango sauyawar da tayi cikin wata daya da kwanaki, so yake yi ta ɗago idanuwanta su haɗa ido ko sau daya ne amma taki bari hakan ta faru, rumƙe bakin akwatin yai da karfi tamkar zai karya wanda Justice Ibrahim na kalle dashi saboda tunda aka shigo da ita da yaga ya maida hankalinsa a kanta shima idanuwansa ke kan ɗan nasa daya hango zallar soyayyar yarinyar mai ƙarfi ta cikin idanuwansa, a hankali ya ja ajiyar zuciya ya sauke yana dauke kansa wajen Umar Farouk ɗin sakamakon maganar da ya ji Barrister Aysha data tsayu agabanta ta so ma yi, "Malam Janaam kece wacce komai ya faru agabanta sannan ke ce kadai zaki iya warware mana komai kikawo ƙarshen wannan shari'ar, don haka kotu zata so taji menene alakar ki da Umar Farouk da kuma shi wanda aka kashe, sannan kotu na buƙatar ki faɗa mata gaskiyar abinda ya faru a gabanki dangane da wannan kisan, amma kafin nan ki sake gabatarwa da kotu kan ki". Daƙyar Janaam ta iya buɗe baki cikin rawar murya tace, "Sunana Amatul-Alim Isma'il wadda akafi sani da Janaam". Sai a lokacin Justice Ibrahim ya maido hankalinsa akanta yana kallon ta ya ce, "Amatul-Alim shin kinsan dalilin tsayuwar ki a gaban kotu?" Janaam ta ɗaga kai ba tare data ɗago ba ta amsa masa da "Eh ya mai Shari'a" "Kin san wancan da ake tuhuma da aikata kisan?" Janaam ta ɗago kai ta kalli gefen da alƙali ke nuna mata inda Umar Farouk ke tsaye ta ce, "Eh na sanshi ya mai girma mai shari'a". Jinjina kai Justice Ibrahim yai ya yi rubutu sannan ya sake dawowa yana kallon Umar Farouk ya ce, "Umar Farouk shin kasan Amatul-Alim?" Justice Ibrahim ya ƙare yana kallon dan nasa da har lokacin ya kasa ɗauke idanuwansa akan Janaam yana jin wata irin ƙaunarta mai ƙarfi na sake shiga zuciyarsa, halin da yake kallonta acikin yafi yi masa zafi sau dubu fiye da halin da yake ciki, baya tunanin a duniya akwai abinda yake jima raɗaɗi a zuciyarsa irin ya ganta cikin damuwa, ya rasa me yasa ta shiga ƙunci saboda wancan guy ɗin da babinsa ya riga ya rufe sai kace ya fishi da zata saka damuwar rashinsa atare da ita bayan shine yafi dacewa da ita sama da shi kuma ba dawowa zai yi ba, maganar alƙali ta maido dashi hayyaccinsa daya sake maimaita masa tambayar da yake masa a karo na biyu, kai kawai ya iya ɗaga masa yana jin wani zafi a ƙasan zuciyarsa ba tare daya ce uffan ba, sake kallon Janaam Justice Ibrahim yai yace, "Amatul-Alim kinyi alkawari zaki fadawa kotu iya gaskiyar abinda kika sani akan wannan kisan da aka gabatar dake a matsayin shedun gani da ido?". Nan ma dago kai Janaam tayi ta ɗaga wa alkali kai, karaf idanuwnta suka sarke dana Umar Farouk, take jikinta ya soma rawa, wani irin tsoro haɗe da tashin hankali ya shigeta lokaci ɗaya, yayin data fara ja da baya idanuwanta cike da kwalla tana girgiza kai tana nuna sa, magana take son yi amma ta kasa sai hawaye ke saukar mata a fuska tana girgiza kai, can sai gani kawai akai tayi luuu ta faɗi ƙasa, nan take alkali yayi umurni da a ɗauketa a fita da ita kotu kuma ta karaɗe da surutu kowa da abinda yake fada, Mamah da su Ya Jamil ne suka taso da wata cikin jami'an tsaro aka ɗauki Janaam aka fice da ita, bayan mintuna biyar alƙali ya bubbuga tabur yana umurtar da ayi shiru don ci gaba da sauraron ƙarar, Umar Farouk kuwa tamkar zai karya akwatin haka ya sake yi masa wani irin riko yana jijjigasa ganin halin da Janaam ta shiga ciki idanuwansa sunyi jijir, sai da akayi shiru kotu tayi tsit Umar Farouk ya ɗago kai idanuwansa cike da kwalla yana cewa, "Ya mai girma mai Shari'a ya kamata kotu ta kawo karshen wannan zaman tunda har nai ikirarin cewa ni na aikata wannan kisan da kaina, Yakamata kotu ta fahimci babu bukatar aci gaba da kawo mutanen da basu ji basu gani ba ana jefasu a wani hali saboda tashin hankali tunda na amsa laifinta da kaina, kowa ya san Janaam kimtsattsiyar yarinya ce kuma kamilalliya bai kamata ace ta tsaya a gaban kotu ba". Wani irin tsaki Momy da bata san lokacin daya zo mata ba taja haɗe da mikewa tana cewa, "Ina da ja akan maganganunnan nasa ya mai girma mai Shari'a, shi kansa baya cikin hayyaccinsa yana buƙatar ganin likita a daidai wannan gaɓar domin bai san abinda yake faɗa, tun ɗazu kotu ta zauna tana faman sauraren labaran da babu hujjoji aciin su daga wasu tsirarun mutane a matsayin shedu, idan har Umar Farouk zai iya aikata kisa ya mai girma mai Shari'a baya buƙatar don ya yiwa mutum duka yasa a ɗaukesa a kaisa asibiti ayi masa magani kamar yadda suka bada bayani domin hakan nuna tausaya wa ce, shi kuma mai tausayi bazai taɓa iya aikata kisa ba, idan har Umar Farouk zai iya yi masu duka sannan ya bisu har asibiti yaja masu kunne a kan kada su kuskura su fadi shine ya aikata masu hakan to lallai shi ɗin matsoraci ne kuma yana tsoron hukuma, shi kuma makashi baya da tsoro idan zai aikata kisa, ya mai Shari'a ina so kotu tayi duba da wuɗannan bayanan nawa kada tayi gaggawar yanke hukunci har sai an samu ƙwararan hujjoji da zasu tabbatar da lallai shi ya aikata kisannan" "Ina da ja ya mai Shari'a, dukkanin hujjojin mu masu karfi ne kuma sun tabbatar da abinda Umar Farouk ya aikata domin idan ba haka bane bazai ci gaba da amsa cewa shi ya aikata kisan ba, ruwa sun riga da sun karewa ɗan kada ne yaga baya da wata hanyar da zata fiddashi tun farko shi yasa ya amsa laifinsa don hutar da Shari'a, shedun gani da ido da muka gabatar kuma ya mai Shari'a da ba shi ne ya aikata kisan ba da bazata firgita ta shiga tashin hankali ba, muna rokon wannan kotu mai adalci data duba tarin hujjojin mu da karfin da suke dasu ta yankewa Umar Farouk hukuncin kisa shima daidai da laifinsa". Dr Abdullahi gwaram ya jinjina kai yana cije baki cike da son tabbatar da abinda Barrister Aysha ɗin ta faɗa, murmushin yaƙe Barrister Maryam tayi tana jin wani abuna taso mata a wuya, Umar Farouk ya gama da ita ace kan soyayya ya jefa kansa a wannan yanayin soyayyar ma ta yarinyar da kwata-kwata data ganta bata dace da shi ba, wannan wane kalar abun fadi ne ya barwa kansa da ita kanta, ganin yadda Shari'ar ta ɗauki zafi yasa Justice Ibrahim cewa aje hutun minti talatin don shi kansa gaba-daya yama daure, zai iya cewa wannan shari'ar na cikin shari'un daya taɓa yi da suka caza masa kai da ƙwaƙwalwa ba kaɗan ba, don haka yana bukatar hutu da kuma yin tunani sosai kafin yanke hukunci.
*Bayan minti 30*
Sai da justice Ibrahim ya buƙaci lauyan mai ƙara dasu sake gabatar da shedar su ta karshe kafin aci gaba da gudanar da shari'ar don jin ta bakinta, sai dai tuni aka wuce da Janaam asibiti saboda ta sake shiga cikin wani matsanancin halin, Barrister Aysha ta mike tana cewa, "ya mai Shari'a shedar mu ta gani da ido kamar yadda aka gani firgici, tashin hankali da dimaucewa ya sake jefata a yanayin rashin lafiyar da dama bata jima da tasowa akan gado ba, saboda haka muna ba kotu hakuri na rashin sake bayyanarta anan". Jinjina kai yai kafin ya ce, "Lauyan wanda ake ƙara ko kuna da wata hujja da zaku kare wanda ake kara?" Barrister Nazir ya mike ya ce yana rokon kotu ta bashi damar ya gabatar da maigadin gidan Dr Abdullahi gwaram, alƙali ya bashi dama aka shigo da Malam Shehu sai faman zare idanuwa yake yi yana jin tamkar ya saki fitsari, bayan ya gabatar da kansa gaban kotu Barrister Nazir yace, "Malam Shehu kai ne maigadin gidan Dr Abdullahi wanda ke da alhakin shige da ficen duk wanda ke cikin gidan dama wasu na waje masu shigowa?" "Eh nine yallaɓai". "Ko zaka sanar da kotu dawa-dawa suka shiga gidan a ranar da kuma suwa suka fita?" "Eh to a gaskiya Alhaji da Hajiya da kuma yaransu su kaɗai suka fita cikin gidan kafin abun ya faru kuma su kaɗai suka shigo". "Kenan bayan su babu wanda ya shiga ko ya fita". "Haka ne yallaɓai" "Ka tabbata?" "Eh". maigadin ya faɗa iya gaskiyarsa don har ga Allah bai ga shigar kowa ba kuma bai ga fitar kowa ba. Murmushi Barrister Nazir yai haɗe da cewa, "Ya mai girma mai Shari'a, mai gadi shike da alhakin sa ido wajen shiga da fitar kowa na cikin gidan dana waje, yarda da kuma amincewa tasa Dr Abdullahi gwaram ya ɗaukesa aiki don bawa iyalansa da gidansa kariya, idan har zamu iya gabatar da maigadinsa a matsayin sheda da a gaban kotu ya tabbatar da bai ga shigar Umar Farouk acikin gidansa ba to hakan na tabbatar da cewa ba Umar Farouk ne ya aikata kisan ba tunda ba'a ga shigarsa cikin gidan ba, mai yiyuwa ne makashin na cikin gidan suka fita suka rufe dashi basu sani ba ko kuma akwai lauje cikin naɗi a wannan al'amarin, saboda haka kotu tayi watsi da wannan shari'ar kuma ta wanke Umar Farouk tas daga wannan zargi da ake yi masa". "Ina da ja ya mai Shari'a". Barrister Aysha ta faɗa tare da miƙewa, "Ya mai Shari'a Umar Farouk zai iya shiga cikin gidan ba dole sai ta kofa ba, zai kuma iya shiga ta kofa saboda wasu uzurukka dakan iya gittama mai gadi na yin sallah ko kuma zagayawa, idan kuma akace ba haka ba shin Umar Farouk aljanine? Taya akayi aka isko shi cikin gidan har ba cikin dayan biyun can yai ba? mu ɗauka ba shi ya aikata kisan ba, me yake yi aciki bayan babu wata alaƙa ko kusanci ko kuma dangantaka tsakaninsa da su da zata kai shi gidan? Na shiga ban ɗauka ba fa baza ta taɓa fidda ɓarawo ba". Jinjina kai Justice Ibrahim yai da alama ya gamsu da bayanin ta, sai da Barrister Aysha tayi taku uku zuwa inda Umar Farouk ke tsaye Sannan tace, "Umar Farouk ya kamata ka hutar da masu kareka ka yiwa kotu bayanin yadda akai ka shiga cikin gidan ka aikata kisan da ake ikirarin ka aikata". Gaba-daya idanuwan kowa komawa sukai akan Umar Farouk daya dago kai ya kalli Momy wato Barrister Maryam da itama shi take kallo gabanta na wani irin faɗuwa sannan ya juya ya maida kallonsa ga alkalin wato mahaifinsa Justice Ibrahim da bai san lokacin daya hadiyi wasu yawu masu karfi ba. Ajiyar zuciya Umar Farouk ya sauke yana kallon Barrister Aysha kafin ya ce...
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU
*IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
63.
"Na tafi gidan su Janaam da niyar daukota mu wuce school sai na tadda bata gida ko da na aika akirata aka ce taje gidansu Nu'aymah, hakan yasa na nufi gidansu Nu'aymah saboda babu nisa tsakanin gidansu dana su Janaam, bayan na isa ƙofar gidan nayi parking ɗin motata a can gefe na fiddo wayata da niyar kiranta sai ga wani yaro na gani, hakan yasa na fasa kiranta na tura yaron ya shiga cikin gidan ya kirawota, ba'a jima ba ya dawo yace gidan ba kowa, raina ne ya ɓaci naga tabbas wannan rainin hankali ne Janaam tayi mini sanin da nayi tabbas tunda daga gidansu aka ce tana gidan to tana ciki kawai bata son fitowa ne shiyasa tace a faɗi hakan, cikin ɓacin rai na fito cikin motar na nufi ciki gidan kai tsaye ba tare da wani tunani ba, ban samu mai gadi a kofar gidan ba sai kawai na kutsa kaina ciki, ina shiga na gansu tare...". "Shine kai kuma ka kashe shi?" Barrister Aysha ta faɗa tun kafin ya ƙarasa, "objection my Lord yakamata ta bari ya karasa bayaninsa, a matsayinta na lauya tayi shisshigi wajen dora laifi akan wanda ake zargi ba tare daya gama kare kansa ba". Momy ta faɗa cikin bacin rai don tunda Umar Farouk ya soma bayani ta ji wani takaici da ɓacin rai na lullubeta, Justice Ibrahim yai gyaran murya haɗe da gargadin barrister Aysha, hakuri ta bayar sannan taci gaba da cewa, "muna sauraronka sai me ya faru?" "Kamar yadda kika faɗa ni kuma sai nayi cikinsa daga nan na samu Sa'a na kashe shi." "bisa wane dalili?" "Saboda Janaam tawa ce ni kaɗai" Umar Farouk ya faɗa kai tsaye, Ko rufe baki bai yi ba cikin ƙaraji Dr Abdullahi gwaram ya miƙe yana zage-zage haɗe da cewa "Karya kake yi ɗan iskan yaro wulaƙanta ce, yarona ba abinda zai yi da ita, ita ɗin ƙawa ce ga yar uwarsa kawai, yaron dake zaune a kasar waje da mata kala-kala duka ya rasa wacce zai yi soyayya da ita sai wannan yarinyar? To ni da kaina idan na sani bayan taɓa barinsa ba wannan maganar sharri ne kawai, dama can abokin gabarka ne don har duka ka taɓa yi masa in ban manta ba lokacin daya shigo ƙasar nan don haka ba zan taɓa kyaleka ba koda zan ƙarar da komai nawa har sai naga kaima an kasheka kamar yadda ka kashe mani ɗa". tsawatarwa alkali ya shiga yi ta hanyar bubbuga table da gudumar dake gabansa, amma duk da haka Dr Abdullahi gwaram yaki yin shiru, hakan yasa Justice Ibrahim da gabaɗaya kansa ya sake kullewa ransa ya kuma matukar ɓaci ya sake ɗaga shari'ar har sai bayan wasu sati biyu inda ya tabbatar da a ranar zai yanke hukuncin ƙarshe saboda haka masu kare wanda ake ƙara su ƙarasa tattaro hujjojinsu don karesa, haka kuma lauyoyin wanda ke ƙara ya umurce su dasu gabatar da Janaam a zama na karshe domin jin ta bakinta kafin yanke hukuncin, bayan na ya ɗago kai yana kallon Dr Abdullahi gwaram yace, "Bisa raini ga kotu a fili da Dr Abdullahi gwaram yayi da nuna rashin ɗa'a, wannan kotu ta yanke masa biyan tarar Naira dubu hamsin ko kuma kwana uku a gidan yari bisa tsarin dokar Nigeria Sashe na 133 Penal Code, daga nan ya sallami shari'ar sai bayan sati biyu, sosai momy ta ji dadin wannan damar da aka basu don zai sake taimaka masu wajen sake binciko gaskiya, a yanzu jikinta ya bata cewa koda Umar Farouk yai kisan a yadda yai bayani to tabbas akwai dalili wanda hakan na iya kawo sauyawar hukunci a kansa.
Bayan an fito kotu Momy ta buƙaci ganin Umar Farouk, kallonsa tayi yadda ya koma haɗe dayin murmushi mai cike da takaici ta ce, "Yanzu me ka aikatawa kanka haka? me yasa kaƙi buɗe baki kayi mana bayani tun farko har sai da aka iso wannan gaɓar". "Saboda bana son ɓata miki lokaci Momy don duk abinda na faɗa bazai canja komai ba akan abinda na aikata". "Shikenan kaci gaba dayin shiru ni kuma zanci gaba da bincike sai na gano gaskiyar da kake ɓoyewa ". Shiru yai bai ce komai ba Mommy tayi gaba don takaicinsa take ji sosai, saurin dakatar da ita yai haɗe da cewa, "Momy ina son Janaam, yanayin da take ciki a yanzu yafi mun zafi da raɗadi akan wannan yanayin da nake ciki, yadda nake jin fargabar wani abu ya sameta na ciwo ko damuwa bana fargabar mutuwa haka Momy, ina son Janam so mai tsanani da ko zan rasa rayuwata Indai tana cikin koshin lafiy, farinciki da kuma walwala wallahi bazan damu ba, pls ki taimaka ki dubo halin da take ciki a asibiti ko ki roƙa mini a barni naje na dubata idan ke baza ki je ba" wani kallo Momy tayi masa da tunda yake bai taɓa ganin tayi masa irinsa ba kafin tace, "ba kada hankali". Sannan tabar wajen, bayanta Umar Farouk ya bi yana rokonta kamar zaiyi kuka jami'an tsaro sukai saurin dakatar dashi suna tsare masa gaba, wani kallo yai masu abunka da dama yana cikin ɓacin rai da zafin zuciya kawai ya hau kai masu duka, sai da kusan yan sanda bakwai suka taru a kansa sannan suka iya rirrike sa suka rufesa da duka kafin suka tallabesa suka jefa mota suka bar wajen dashi, ƙwalla Mommy ta share saboda agaban idonta komai ya faru, wata tsanar Janaam taji ta sake shiga zuciyarta, dole tabi duk hanyar da zata bi ta kubutar da ɗanta ta kuma yi nesa da shi ta yadda ko tunaninta bazai sake yi ba.
Abban Nu'aymah kuwa cikin bacin rai ya bayar kotu bayan ya wakilta lauyansa ya biya tarar da kotu ta yanke masa bisa reni da rashin girmamawa da yayi mata, tunda ya isa gida ya shiga kai da kamowa cikin dakinsa yana tunanin menene abinda ya dace yayi yanzu? Dole ya nunawa justice Ibrahim ko shi waye ya kuma nuna masa faɗa da aljani fa sai an shirya, wayarsa ya ciro acikin aljihu ya kira wata Number ta ƙasar waje, bugu ɗaya aka ɗaga ana cewa "hello Abba". Can cikin wata dakusasshiyar murya, ajiyar zuciya ya sauke