Showing 75001 words to 78000 words out of 157423 words

Chapter 26 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

506

LAMBAR

07040402435

09079274454

Masu son Vip ku bibiyi Arewabook @billysfari https://www.arewabooks.com/chapter?id=68926e51a9466b1b79a0206f

                            42.

Kasa ƙarasowa daga ciki Dady ya yi yana bin tun daga tsakar ɗakin har zuwa yan matan da kallo, idanuwansa ya sauke akan cake ɗin dake saman gadon tare da flower ɗin dake hannun Umar Farouk sannan ya ɗago yana kallonsa, gefe Umar Farouk ya ajiye flower ɗin yana shan jinin jikinsa ganin yadda Dady ya ɗaure fuska, Dady bai iya cewa komai ba ya janye daga bakin ƙofar yana cewa abokan nasa "Bismillah ku ƙaraso daga ciki Alhamdulillah yaron naku ma ya samu sauki". Ya kare zancen tare da ƙarasowa cikin dakin ba tare daya sake kallon gefen da su Billy ke tsaye ba, kusan hada baki duk su duka suka yi hadda Nu'aymah suna gaishe dasu Dady cikin girmamawa, Dady bai iya amsa masu ba sai su Alhaji Ibrahim ne abokan nasa suka amsa, hannu suka miƙawa Umar Farouk dake gaishesu suna yi masa ya jiki Alhaji Ibrahim yace, "Ah jiki kam da sauki Umar Farouk tunda gashi har kuna celebrating ne na birthday ɗin ka ko?" Umar Farouk ya ɗaga kai yana yin ƙasa da kansa cikin girmamawa, shi dai Dady kasa cewa komai yai don lamarin Umar Farouk ya fara bashi tsoro, Alhaji Ibrahim yai murmushi haɗe da cewa "Masha Allah to Allah ya yiwa rayuwa albarka kuma ya baka lafiya". Umar Farouk ya amsa da amin ba tare daya ɗago ba ganin irin kallon da Dady keyi masa kafin ya maida kallon gasu Nu'aymah ɗaya bayan ɗaya, "Kai daga ina kuke? Su waye ku?". Ita ce tambayar dasu Nu'aymah suka ji Dady ya jefo masu data sa Nu'aymah cikinta murɗawa, cikin sake girmamawa tunda sun san ko waye Dady da matsayin da yake da shi a cikin garin felicia tace, "mu abokan karatunsa ne Dady mun zo duba sa ne?" "Ok what of this? Tarbiyar da iyayen ku suka baku kenan?" Ya faɗa yana nuna cake da kyalkyalin spray daya zuba a ƙasa da kuma kan gado da jikin Umar Farouk ɗin, Alhaji Ibrahim ne yai saurin amshe maganar cikin dariya yana mayar masa da amsa yake cewa, "Banda abunka ranka shi daɗe ai wannan is normal tunda colleague ɗin sa ne a school, is not bad su zo su tayasa murnar ƙara shekara sannan suyi wishing ɗinsa". Saleem ne yai sallama tare da shigowa, ganin su Dady da abinda ke faruwa cikin ɗakin yasa gabansa faduwa amma sai ya dake ya ƙarasa ciki yana gaishe su cikin girmamawa, Dady ne ya dago kai a ɗan fusace yana cewa, "Saleem shashancin da kukeyi kenan har a anan?". "No Dady duka yan class ɗin mu ne muka zo dubasa tare da yi masa murnar ƙara shekara, mazan mun je masallaci ne muyi sallah shiyasa". Saleem ya tsinci kansa da kirƙiro wannan ƙaryar ba tare daya shirya ba "Abun da nake faɗa maka kenan ai irin wannan ɗin ba wani by bane ga student tunda ana tare". Alhaji Ibrahim ya faɗa kafin su Billy da suka yi tsamo-tsamo tamkar wuɗanda ruwa ya doka suka ce, "mu zamu tafi Saleem sai an jima Allah yaƙara sauki". Sannan suka nufi kofar fita gaban kowace na faɗuwa, Dady bai sake cewa komai ba sai kallon Umar Farouk yake yi daya ki bari su haɗa ido kafin ya juyawa rai a ɓace yabar ɗakin abokansa suka rufa masa baya bayan sunyi wa Farouk Allah yaƙara sauki, wata ƙarfaffar ajiyar zuciya Saleem ya sauke tare da ƙarasowa gaban gadon yana dafa Umar Farouk ya ce, "Ya akayi hakan? Yaushe su Billy suka zo". Kai Umar Farouk ya ɗago yana kallon Nu'aymah ya ce, "Tare suka zo da ita". Saleem ya kalli Nu'aymah da tun dazu ta ji tamkar an ɗaure mata ƙafafuwa saboda tsoro wanda hakan yasa ta kasa bin su Felicia da zasu fita ya ce, "Ai naga shigowar motar ki amma ban yi tsammanin tare kike da su ba". Jiki a sanyaye Nu'aymah ta ce, "Tare muka zo dasu amma ban san abinda suka shirya yi kenan ba da ko dauko su ban yi a motata ba, baka ji yadda ƙirjina ke duka ba da su Dady suka shigo, ni kaina ban ji daɗin yadda suka isko mu ba kamar yadda fuskar Dady ta nuna hakan shi ma". "Da akai me?" Umar Farouk ya faɗa yana kallonta, bata ce komai ba ta sauke kai ƙasa ya ɗan ja tsaki haɗe da komawa ya kwanta, shiru ɗakin yai babu wanda ya sake cewa komai a cikin su wanda hakan ya sa Saleem ya shiga gyara wajen kafin Momy ta dawo ta shiga yin nata faɗan itama, kamar daga sama suka ji Umar Farouk ya ce, "Ina Janaam!" Cak Saleem ya tsaya da abinda yake yi jin tambayar da yake da tabbacin Nu'aymah ya yiwa ita ba shi ba, maganar da yake da tabbacin ko shakka babu dole tayi hurting Nu'aymah, jin Nu'aymah bata tanka ba yasa Saleem juyowa ya kalli Umar Farouk yana son nuna masa kada yayi hakan amma ya kauda kansa gefe, hakan yasa Saleem ficewa yabar dakin yana jin ba daɗi don ko yaya ne bai kamata ya yi mata hakan ba. Nu'aymah da maganar ta dakar mata zuciya amma ta yi kokarin ɓoye hakan tana kallonsa ko ƙyafta idanuwa batayi haɗe da cizon ƙasan bakinta na tsawon wasu yan daƙiƙu kafin tace, "me yasa ka damu da son sanin inda wadda bata damu dakai take ba?" "Ba tambayar da nayi maki ba kenan, ki amsa min ina Janaam". Umar Farouk ya faɗa yana zuba mata idanuwansa dake sake narka mata zuciya da soyayyar sa, janye idanuwanta dake kokarin kawo kwalla ta yi haɗe da jin takawa bijirewa amsa masa tambayarsa ta ce, "Tana nan babu yadda bamuyi da ita ba akan tazo muzo dubaka amma taƙi, hakan ya nuna.." bata ƙarasa ba ya ɗaga mata hannu yana cewa, "Ko meye ma ba ruwan ki, haka ta zaɓa kuma ra'ayin ta ne, saboda haka bana buƙatar sharhi akan amsar da kika bani". Ran Nu'aymah ne ya ɓaci bata san lokacin data fara masifa ba tana cewa, "idan ka san ra'ayin ta ne akan me zaka tambaye ni ita? Wallahi friendy kana bani mamaki yadda idanuwan ka suka rufe ka kasa fahimtar cewa Janaam bata sonka, asali ma babu wanda ta tsana sama dakai amma kullum sai kokari kake ka nuna mini tafi muhimmanci a rayuwarka sama dani, kar fa ka manta itace silar faruwar hakan agare ka, ita ce tai sanadiyar kwanciyar ka anan amma saboda rashin tausayi irin nata ta kasa zuwa ta dubaka saboda bata damu dakai ba kuma a hakan har kake tunanin zuciyarta zata yi laushin da zata iya tausaya maka ta zo dubaka ko kuma ta so ka? Idan kana tunanin hakan to ba dai Janaam ba don idan ta tsani abu ta tsanesa kenan har abada, don haka tun wuri ya kamata idanuwan ka su fito a duhu". Umar Farouk da tunda Nu'aymah ta fara magana ya ya kumshe idanuwan sa ya rufe su saboda yadda zuciyar sa ke wani zafi akan kalaman da take faɗa kan masoyiyar sa, tana rufe baki kai tsaye ya ce, "get out Nu'aymah". Tsaye Nu'aymah tayi tana kallon sa cike da mamaki kafin ta sake jin sa cikin wata kakkausar murya da ƙarfi ya sake cewa, "Get out from here". Tare da buɗe idanuwan sa da suka kaɗa suka yi jajir saboda tsananin ɓacin rai, kasa motsawa Nu'aymah tayi daga inda take saboda yadda mamakinsa ya rufe ta, cikin ɓacin rai ya ce, "who the hell are you da zaki fadi magana marasa daɗi akan Janaam? Ki faɗi duk maganar da kika ga dama akaina i accept that, amma banda Janaam domin ita ɗin tamkar rayuwata ce, ina jinta aduk wani bugawar lumfashi na da kuma rayuwata, ina son Janaam son da ban taɓa yiwa wata mace ba aduniya haka kuma ina girmamata a zuciyata fiye da kowa ciki har da kaina, akan me zaki fadi bakar magana a kanta har kina ƙoƙarin hada kanki da ita? Ke wacece wane matsayi kike dashi aguna da zakiyi tsammanin haɗa kanki da ita? This will be the last da zaki faɗi ko da maganar banza ce a kanta balle kuma baƙar magana be cause it hurts me and now get out from here bana son ganinki". Da gudu Nu'aymah tabar ɗakin tana kuka, Saleem dake zaune saman kujera abakin kofar yana sauraren duk abinda ke faruwa ya yi saurin miƙe wa yana kokarin tsaida ita ya bata hakuri amma taki saurarer sa, da gudu ta fizgi motar ta ta bar asibitin, cikin wani irin speed take tuƙin tana sharar kwalla, bata taɓa tunanin soyayyarta zata yi mata zafi irin haka ba, bata taɓa tsammanin zuciyar da take so baza tayi mata kallon so da tausayi ba, bata zata soyayyata zata zo da akasin ba da bata fara ba tun farko, da ta san Umar Farouk bazai so ta ba Janaam zai so da ta ɓoye sirrin zuciyarta bata bayyana ba, da ta yiwa zuciyarta ƙwaƙƙwaran kashe din da baza ta kamu da son wanda zuciyar sa ƙawarta zai so ba ita ba, wani irin zafi take ji da raɗaɗi a zuciya tana yi tana sharar ƙwalla, kaɗan ya rage ta buge wani dattijo a saman hanya kafin ta isa gida saboda yadda duhu ya mamaye mata zuciya har ya hanata ganin gabanta, tsananin tashin hankali ya sa sarautar Allah kaɗai ta kaita gida lafiya tana isa da gudu ta haye sama ta shige dakinta haɗe da murza wa ƙofa makulli ta faɗa akan gadon ta tana ci gaba da wani irin kuka mai ban tausayi da sai wanda ya taɓa fadawa a ƙangin soyayyar da shi yake so ba'a son sa kaɗai zai iya fahimta.

A can asibiti kuwa cikin ɓacin rai Saleem ya faɗa dakin yana yiwa Farouk wani kallo kafin yace "Me ka aikata haka Umar Farouk? Me kake tunanin makomar alaƙar Janaam da Nu'aymah yanzu? me yasa ka zaɓi kabi wannan hanyar da zata yi hurting Nu'aymah wajen nuna mata soyayyar Janaam bayan kasan ita tana son ka, anya hakan da ka yi kana ganin ka yiwa Nu'aymah adalci?". A hankali Umar Farouk ya mai da idanuwansa ya rufe ba tare daya bi takan tambayoyin da Saleem ke jefo masa ba don bai da lokacin amsa masa su, infact ma baya da amsar su, haka Saleem ya ƙara ci maganar sa ya bar ɗakin ransa a ɓace shima, bai san pain ɗin soyayya ba don bai taɓa yi ba, amma sai yake ganin kamar Farouk bai yiwa Nu'aymah adalci ba kuma bai cancanci yayi mata hakan ba duba da irin yadda take bashi kulawa haɗe da nuna mashi so...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

09079274454

Masu son vip ku bibiyemu ta Arewabook @billysfari https://www.arewabooks.com/chapter?id=6894e7bd8ebf53d524760d91



                            43.

Ina zaune bayan sallar magrib ina karatun azkar na ji wayata ta fara ruri, sai da naƙarasa salatin Annabi da nake yi a karshe sannan na miƙa hannuna na dauko wayar fuskata ɗauke da murmushi don na gama tabbatarwa da kaina ya Nu'aym ne ya kira saboda shi kadai ne ke kirana a irin wannan lokacin, ganin number ce ya sa ni sakin tsaki, kamar bazan ɗaga ba sai kuma na canza shawara, kiran na sake shigowa a karo na uku nayi saurin ɗagawa ina kai wayar a kunne na, shiru na yi banyi magana ba haka ma ta ɗaya ɓangaren ba'a ce komai ba, sai da muka kwashi minti ɗaya a haka kafin na ji an sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa, "Amaahh..." Cikin wani irin salo daya sa tsikar jikina tashi lokaci ɗaya kuma gabana na faɗuwa, cikin tsananin tsoro ina hadiye wasu yawu da ƙarfi na ce, "Waye?" Shiru akayi kafin can a sake cewa, "Ni ne wanda zuciyar ki ta tsana shi kuma zuciyar sa ke son ki, ni ne wanda ke son rayuwarki sama da yadda nike son tawa rayuwar, ni ne wanda rayuwar sa bazata taɓa ingantuwa ba har sai da rayuwar ki a tare dashi, ni ne mai baƙin fenti a fuskar ki da zuciyar ki ta kasa sama masa gurbin da zaki iya yafe masa, Amaah ni ne wanda ke neman taimakon ki ido a rufe don samun soyayyar ki, a shirye nake da nayi komai akanki saboda in matuƙar sanki da ƙaunarki Amatul-Alim, na yarda kiyi mini duk wani hukunci dazai goge laifina a fuskar ki ki bani matsugunni a zuciyar ki ko da dai-dai da ƙwarar zara ne, ina son ki Amaah, ina matukar kaunar ki Amaah, na sani izgilanci da son zuciya su suka jawo mini wannan jarabawar akan ki, pls kiyi hakuri ki yafe mini duk abinda nayi miki ki karɓi soyayyata saboda Allah ba saboda halina ba". A yanzu kam na gama fahimtar wanda ke magana amma don na tabbatar masa da cewa baya gabana sai na nuna masa ban gane ko waye ke magana ba na ce, "Bana fahimtar irin wudannan kalaman daga bakunan wuɗan da ban san su ba, saboda haka idan ka gama sai an jima". Saurin taron numfashi na yai kafin na kashe yana cewa, "Na haɗaki da girman Allah kada ki kashe waya zan sanar dake ko ni waye tunda baki gane ba, Janaam ni ne Umar Farouk, nasan jin kalamai na kike yi tamkar almara amma wallahi da gaske ne Amaah ina matukar son ki da ƙaunar ki kamar yadda na faɗa miki waccan ranar duk da tsanani ciwon da nake ciki, ina son ki Janaam kuma shirye nake dana bada rayuwata sau dubu saboda taki rayuwar, wallahi ina son ki Janaam da dukkanin zuciya, gangar jiki da kuma ruhi na.." tun kafin ya rufe baki wani takaici da bakin ciki dake taso mini a ƙasan zuciya suka sani cewa "Ni kuma bana son ka Umar Farouk a zuciyata dama duka rayuwata, don haka tun wuri ka jawa bakinka linzami kadena kira na". Ina gama fadar hakan na katse kiran cikin ɓacin rai ina cewa, "Aikin banza". Tamkar jira ake na katse kiran na sake ganin wani kiran ya shigo, a raina har na shirya kalar rashin mutuncin da zan yiwa Umar Farouk idan har shi ne ya sake kira, sai dai jin ringing na musamman da ganin sunan wanda ya kira ya sa na ɗan sauke ajiyar zuciya ina ɗaga kiran, "hello Ya Aym". Na faɗa cikin sanyin murya ina kokarin danne ɓacin ran da Umar Farouk ya saka mini, Muryar ya Aym ce na ji cikin wani yanayi yana cewa. "Dawa kike waya?" Gabana ne yai wata irin faɗuwa don ko da wasa na san ban isa na faɗa masa ko da waye ba, don haka na yi shiru na kasa magana, cikin tsawa ya sake jefo mini tambayar yana cewa, "dawa kike waya nace Janaam?" Wata irin zabura nai idanuwana na cika da ƙwalla na ce, "Kayi haƙuri da Aymah ce muke yi". Na tsinci kaina da yi masa wannan ƙaryar ƙwalla na sauko mini a idanuwa, wani iska na ji ya furzar haɗe da cewa, "Sama da mintuna ashirin ina kiranki ana sa mun line busy kuma kice mun da Aymah kike waya, why Janaam me yasa zaki mun karya? Me yasa baza ki barni na ji da raɗaɗi ɗaya a zuciyata ba sai kin ƙara da wani laifin? why Janaam ko dai nafara gazawa a soyayyata shi yasa kika fara bawa wasu lokutan da kika san nawa ne a wajen ki?" "No ya Aym ba haka bane.." na faɗa cikin karyewar murya sai dai tun kafin na rufe baki ya sake daka mani wata tsawar dake nuni da ransa a matuƙar bace yake yana ci gaba da zuba mini masifa, tun ina ɓoye kukan dake zo mini har na kasa na saki kukan nima ina yi, duk da haka ya Nu'aym bai dena yimin masifa ba sai ma kashe wayar sa da yai gaba-daya, tun da nake da ya Nu'aym bai taɓa ko da ɗaga mun murya ba balle yai mun tsawa, sai gashi yau ya rufe ni da masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, wata tsanar Umar Farouk ce na ji ta sake shiga zuciya ta don duk ta sanadin sa hakan ta faru, sai dana ci kuka na mai isata kafin na miƙe na shiga toilet na ɗauro arwala, sallar isha'i na fara yi sannan nayi nafila na haɗa da shafi'i da wuturi gaba-daya nayi, bayan na kammala na mike ina jin tamkar kaina zai tsage saboda kukan da nayi na koma kan katifata na kwanta, ji nai bazan iya jure fushin da ya Nu'aym keyi dani ba na ɗauki wayata na kirasa har sau biyu amma bai ɗaga ba, text message na tura masa nan ma ba reply, wayar Nu'aymah na kira bugu ɗaya ta ɗaga,"hello Besty". Na faɗa cikin Muryar kuka, Nu'aymah ta amsa mini itama cikin wata irin Muryar da ban saba jinta a ciki ba wanda hakan ya sani cewa, "besty lafiya dai ko?" "Lafiya ƙalau besty". "Amma ya akayi na ji muryarki haka?" Ji nai ta ɗan ja tsaki kafin tace, "faɗa mun menene Besty?" Ni dai mafita nake nema kuma na san ita kadai ce zata iya sama mini ita adai-dai wannan lokacin, don haka ban ɓoye mata komai ba na sanar da ita abinda ke faruwa tsakanina da ya Nu'aym, shiru na ji tayi kafin tace, "Ki ƙyalesa besty kada ki sake kiransa ko yi masa Tex zai sauko tunda har kin bashi hakuri, kuma nima zan kirasa na nuna masa ba haka bane abinda yake tunani, i trust you Janaam baza ki taɓa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login