Showing 30001 words to 33000 words out of 157423 words
yadda Umar Farouk ya tuttule mani ruwa a jiki, wannan karon kasa riƙe kaina nayi sai da nayi kuka sosai akan wannan wulakancin daya yai mini, na ɗauka idan mace ba ta kama kanta ne ko tana shigar banza take haduwa da irin wuɗan nan yan iskan mazan, na ɗauka idan na killace jikina da kuma kama kaina bazan hadu da irin wannan kaluben da namiji ke wulakanta mace ba, ashe ba haka bane akwai mazan da duk iya kamun kanki zasu iya wulakanta ki ko tozarta ki, wata zuciyar ce ta gargaɗe ni akan cewa abinda nakeyi shine dai-dai kuma shi ya dace ga 'ya mace, abinda ya faru dani kuma kawai kalubalen rayuwa ne da dole sai ana haɗuwa da shi sannan rayuwa zata ci gaba da wanzuwa, kamewa ta da killace kaina ya matuƙar yin tasiri sosai akan abinda ya faru dani, ba don haka ba wataƙil kalubalen sai ya lunka haka, da wannan na ji zuciyata tayi sanyi na kuma ɗauki alwashin bazan sake nunawa Umar Farouk abinda yake yimini na ɓata mini rai ba har mubar makarantar, duk da nadan hakan abune mai wahala a wajena....
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE
070404042435, GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUƁEMU A WANNN LAMBAR DON YA MALLAKI NASA.
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
18.
Ganin wannan tunane-tunanen da nake yi bazai amfaneni ba tunda mai faruwa ta riga ta faru yasa na miƙe na nufi dakin Mamah, tana tsaye a jikin wardrobe tana kwaso kaya tana zubawa kan gado da alama gyaran su zatayi, na ƙarasa ciki bakina ɗauke da sallama ina cewa, "Mamah Barka da rana". Ta amsa mini fuskarta ɗauke da murmushi tana cewa, "Lafiya ƙalau Janaam, ya makaranta?". "Alhamdulillah Mamah". Na faɗa ina karɓar gyaran kayan ita kuma ta zauna bakin gado tana linke wasu, take cewa. "Amm..Janaam ya akayi kika dawo gida da wuri haka? Ina cewa kika yi yau kuna da lecturer ɗin marece sai kusan six zaki dawo, ko wani abun ya faru ne?" Ta ƙare maganar tana kallon fuskata don ina da tabbacin sauyawar da taga nayi yasa ta faɗi haka, murmushin yaƙe nayi don har lokacin bana jin zuciyata dai-dai kafin nace, "Kaina yake ɗan mun ciwo shiyasa na dawo gida may be stress ne yai mun yawa". "Assha to kin sha magani ko nakira yayanki ya biyo maki dashi?" "No Mamah na Sha ba sai an wahalar dashi ba". "Shikennan Allah yaƙara sauki amma ki rika samun time kina ba kwakwalwar ki jutu tunda dai karatun nan ba dashi za'a je lahira ba, ina ganinki yadda kike hana kanki bacci kina karatu har sai dare ya miƙa, Kinga ko ai dole kai yai miki ciwo tunda akwai bashin bacci a tattare dake". Ban iya cewa komai ba a wannan karon nayi murmushi kawai ina ci gaba da gyaran tare da ɗauko mata wata firar daban har muka kammala, duk yau ban ji ya Nu'aym ba don tun jiya da mukayi waya ban sake jinsa ba, takan yiwu ma ya kira lokacin dana kashe wayar bai sameni bane. Don haka na ɗauki wayata na kirasa, line busy naji alamun yana waya, sai ban sake kiransa ba don na tabbata zai biyo kiran nawa idan ya kammala, bayan kusan awa ɗaya da kiransa sai gashi ya kirani, murmushi na saki haɗe da ɗaga kiran ina kai wayar a kunnena, saukar numfarfashinsa da naji tamkar wanda yai wasar tsere cikin kunnena da yadda yake magana cikin sanyi murya yasa naji jikina ya mutu, a kasalance na buɗe baki nace, "Barka da rana, hop lafiya kake?" Ya amsa mini da, "Barka kyakkyawata andena fushin dani". Ya maganar yana sauke murya daya bayan ɗaya, jin muryarsa da nayi wata iri yasa na sake ciro wayar a kunnena na duba cike da kokonta anya shine kuwa? Tabbas shi ɗin ne, na faɗa a zuciyata ina sake maida wayar a kunnena, cike da kulawa nace, "Ya Nu'aym are you ok". "Yes i'm". Ya faɗa yana ɗan sauke murmushi, "Baki amsan tambaya na ba sai kika jefo mun taki tambayar." "Ehmm..naga kamar tawa ɗin zata fi muhimmanci don in tabbatar kana cikin ƙoshin lafiya, jiya i was so busy shiyasa faruwar hakan but am sorry". "Shikennan ya wuce, ya kike?" "Ina lafiya, kaifa?" "Alhamdulillah ni ma kusan hakan, sai dai yar kewarki da baza'a rasa ba." "Karka damu gani nan kusa dakai maƙale a zuciyarka". "Still am missing you kyakkyawata and bazan Dena ba har sai na ganki a tare dani". "Allah!" Na faɗa ina dariya cike da farinciki a zuciyata, ina son Ya Nu'aym saboda yadda yake so na kuma yake bani kulawa, ina jinsa a zuciyata da bazan taɓa iya cire sa aciki ba, ya amsa mini da cewa, "Ko kina tantamar hakan ne gobe kawai na biyo jirgi na share miki ita". "A'a ni dai ban faɗa ba". Na bashi amsa ina dariya, haka muka ci gaba da firar mu cike da so da ƙaunar juna, don dukkanin mu muna yiwa juna wata kalar soyayya da mutuwa kaɗai ce zata iya raba mu.
Bayan mun gama waya da shi na shiga WhatsApp chart muka ci gaba da chart da shi da kuma wasu ƙawayena dana gani online.
********
Umar Farouk yana komawa gida wani faɗan Dady ya sake rufesa dashi akan abinda ya yi a police station, daga karshe yace tunda bazai dena dauko masa magana ba ya tattara yabar masa gida yaje duk abinda ya zaba ya yi, Umar Farouk dama kamar jira yake yi bai wani tsaya ba mahaifin nasa hakuri ba ya je ya kwaso kayansa a cikin akwati, Momy tayi saurin rike akwatin tana faɗin, "Ina zaka je Umar Farouk, bana so kana yin nesa dani ka sani, ka bari na lallashi mahaifinka ya yafe maka". "Ki kwantar da hankalinki Mommy, ran Dady ya riga ya ɓaci kawai bari nayi masa yadda yake so, daga baya idan ya huce zan bashi haƙuri na dawo". "To Shikenan ka jira ni anan". Ta faɗa tana wucewa ɓangaren Dady, keys ɗin gidan gonarsa ta dauko taba Umar Farouk tana cewa, "Ungo katafi can gidan gonarsa ka zauna, don Allah kada kaje wani wajen ka sake yin wani abinda zai sake hasala dakai, na rasa mutane wudanne irin munafukai ne da basa son ka zauna lafiya da mahaifinka". "Ba komai Momy, ke kaɗai zaki iya fahimtar hakan amma shi Dady baya tsayawa ya fahimta balle har ya saurareni, shin mutum ya taɓa faɗa ba'a takarda ba, kamar ni waccan kurtum banzan zai riƙa zagi". Ya faɗa yana pointing kansa cike da ɓacin rai. "Karka damu zan yi kokarin fahimtar dashi in sha Allah, ka dai fiddo yarinyar mutane ko?" "Eh". Ya bata amsa a takaice ta saka masa makullin gidan gonar agaban aljihunsa sannan ta raka shi har mota tana sake jaddada masa kada ya je ko ina ya zauna a can kuma ya kula da kanshi". Sai da taga ya fita sannan ta dawo gida tana sauke ajiyar zuciya cike da damuwa, ji takeyi gidan ya koma mata tamkar empty saboda rashin Umar Farouk aciki, Allah ya sani tana jin wata irin soyayya da ƙaunarsa irin soyayyar da bata taɓa yiwa wani mahaluki ba a doron duniya, tabbas tasan Umar Farouk jarrabawar rayuwarta ne, zai yi nesa da ita a idanuwanta ba don ranta naso ba, amma a son samunta bazai taba bari ta ba yake wani wajen ya zauna, duk da tasan yana kwance a zuciyarta aduk wani bugawar lumfashinta, ta rasa aduniya wace irin soyayya ce takewa yaron nata da sam ba tada abun kwatanta wa da ita, 'Ya Allah ka tsare mini yarona ka kare shi da munanan ɗabi'un dake sa ana haɗa shi da mahaifinsa, Allah kuma ka kula mani da shi a duk inda zai je' abinda ta faɗa kenan a cikin zuciyarta tana wucewa ɗakin sister ɗinsa wato Tauheeda, kwance ta sameta tana bacci ta zubar da kayanta duka a ko ina tsakiyar ɗakin, sai data tsincesu tas ta kai masu datti a cikin washing machine, wankakkin kuma data zubo ƙasa daga cikin wardrobe ta kwashe mata su ta gyara mata ta mayar a cikin wardrobe ɗin sannan ta hau kan gadon ta naɗa mata duka a cinya tana cewa. "Har yaushe zakiyi hankali Tauheeda kidena wannan baccin asarar, ke kenan bazaki iya taɓuka komai ba a cikin gidan nan balle kuma ɗakinki, komai sai ace sai anyi maki? Wace irin rayuwa ce wannan?" Tauheeda ta tashi tana mutsittsika idanuwanta ta ce, "Momy zan gyara fa idan na tashi, Allah bacci nake ji sosai". Ta ƙare zancen tana ƙoƙarin komawa baccin, "Mtsss idan kika koma baccin nan zan saɓa maki wallahi, ki tashi ki gyara ɗakin naki sannan kije ki gyarawa yayanki nasa ki sameni a kitchen". "Momy kin fa san halinsa?" "Koma meye kije ki gyara masa kin sani sarai ya tsani datti, duk lokacin daya dawo ya tadda shi haka kuma kinsan me zai iya yimiki". Tauheeda ta tashi tana turo baki don ba ƙaramin takurata Momy take yi ba akan ya Umar, komai dai shi, kulawarta, soyayyarta, tausayinta, kyautatawarta duka sun tafi akan Umar Farouk ne, sai kace ita ba yarta bace, wasu lokutan tana mamakin yadda Momy ta fifita soyayyar ya Umar a kanta ita da take mace, sau dubu zata siya masa abu amma ita bata siya mata sau ɗaya ba sai dai Dadynta ya siya mata, ita kam ba don Dadyn ta na son ta ba yana kula da ita acikin gidan da Shikenan bata san halin da zata shiga ba don Momy bata ɗaga mata ƙafa ko kaɗan, yunƙurawa ta yi ta sauko daga kan gadon ta fara gyara sa sannan ta fito zuwa ɗakin Umar Farouk ɗin, ba abinda ke bata mamaki dashi sai yadda ɗakinsa yake tsaf-tsaf akoda yaushe amma kullum sai Momy tasa ta gyara wai baya son datti, ita kuma bata ga wata datti ba a ɗakin nasa da za'a riƙa takura mata da gyara da akoda yaushe, duk da haka bi tayi ta gyara ko ina ta fesa masa room freshener da sauran turarukkan daki na ƙamshi sannan ta fito ta samu Momy ɗin a kitchen suka ci gaba da aiki tana yi tana kallonta saboda ganin sauyi mai ɗauke da damuwa akan fuskarta da tayi, tana son ta tambayeta dalilin damuwarta amma rashin samun fuskar da take yi daga wajen ta akoda yaushe yasa ta kasa, amma a kasan zuciyarta ganinta a haka da take yi na jefata acikin wani hali don Allah ya sani babu abinda ta tsana aduniya kamar taga ɓacin ran momynta ko Dadynta, shiyasa duk takura mata ɗin da take yi take jurewa don kar ranta ya ɓaci...
********
Tunda Nu'aymah ta dawo gida ta ji bazata iya jurewa rashin ji daga Umar Farouk ba, bazata iya yin fushi dashi ba ko kaɗan ko da shi zai iyayin hakan da ita, hakan yasa ta dinga kiransa a waya sai dai bai ɗaga ba saboda a lokacin yana bacci, daya tashi kuma baibi takan wayar ba har ya je wajen belin Felicia ya dawo, bayan ya dawo ne yana kallon kiranta ba kakkautawa lokacin daya isa gidan gona amma yaƙi ɗagawa saboda yanayin da yake ciki, daga ƙarshe ma sai ya kashe wayarsa gaba-daya yana kwantawa akan doguwar kujerar dake cikin ƙayataccen palourn haɗe da lumshe idanuwa, a iya tunani da hasashen sa babu wacce ta jawo masa shiga cikin wannan yanayin face waccan munafukar dake saka niƙab, ya ja ajiyar zuciya a hankali ya sauke yana ji a ransa cewa dole itama ta ɗanɗani ƙuncin baƙin ciki kamar yadda yake cikinsa shima.
Nu'aymah kuwa tana jin number Umar Farouk switch up ta saki wani irin kukan takaici dake tasowa daga ƙasan zuciyarta, tana son Umar Farouk gangar jiki, zuciya da kuma Rouhi sai dai shi sam yaƙi fahimtar hakan balle ya martaba soyayyar da take masa, sai ma kokari yake ya dora ta wani matsayi da sam bata marhaba dashi a wajensa saboda ya yi mata kaɗan, sai da tayi kukanta mai isarta ta gama sannan ta miƙe ta shiga tayi wanka, bayan ta fito ta gwada kiran lambarsa bata shiga ba, cike da damuwa ta maida akalar kiran gata Janaam sai dai itama wayarta bata shiga ba, ji tayi gaba-daya duniyar tayi mata kullin goro, ta rasa wani farin ciki a daren sai tarin ƙunci da damuwa. A haka ta kwanta daren ba tare da ta iya cin komai ba tana Allah Allah safiya ta waye su haɗu school idan ma hakuri zata bashi ta bashi ya yafe mata don bazata iya jurar wannan hukuncin nasa ba da take da tabbacin zai iya tsayar mata da bugawar lumfashi matukar ya ci gaba da yi mata shi....
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE
070404042435, GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUƁEMU A WANNAN LAMBAR DON YA MALLAKI NASA.
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
19.
Washe gari cike da ƙwarin guiwa na shirya zuwa makaranta, a raina ina jin cewa duk abinda Umar Farouk zai yi mini a shirye nake dana fuskance shi kuma na shanye shi, sallama na yiwa Mamah sannan na fice daga gida zuwa ainahin babban titi don samun abun hawa, ina fitowa dai-dai bakin layin gidanmu na tsaya anan bakin titi ina jiran abun hawa, ban wani jima tsaye ba na ji anyi horn ta bayana, juyowar da zan yi naga ashe Nu'aymah ce itama ta fito don gidansu shine a farkon layi mu kuma can kusan ƙarshen layi muke don gida huɗu ne tsakanin gidan mu da nasu, parking tayi a gaba na tana sauke glass. "Yau kam ba kida hujjar cewa baza mu tafi tare ba saboda haka buɗe ki shigo mu tafi kada mu makara". Yi nayi kamar ban jita ba ina tunanin na shiga ko kar na shiga, aduk lokacin dana tuno da kalaman da Umar Farouk ya jefe ni dasu akan tafiya da mukeyi tare da Nu'aymah sai na ji ba daɗi araina tare da tsanar sake binta zuwa school duk da ba ita ɗin ce ta yi mini ba, titi na kalla babu alamun ko da ɗan acaɓa ne balle kuma mai adaidaita, na juyo ina kallonta tayi murmushi tana tada motar take cewa, "Ai nasan halinki shigo muje kin san dai bazan iya barin ki awajen nan ba". Ta ƙare zancen tare da miƙo hannu ta can ciki ta buɗe mani ƙofar, sai dana sauke ajiyar zuciya sannan na taka kaɗan na isa wajen motar na buɗe na shiga na zauna haɗe da rufo ƙofar sannan ta ja muka tafi. Har muka kusa isa school babu wanda yace wani abu, sai da muka iso bakin gate sannan na ce, "Kin ga sauke ni anan na ƙara sa da ƙafata". "Bazan yi hakan ba wallahi, wai wannan wane abune Janaam? Ni face Besty ɗinki Allah bai kamata kina yimini hakan ba". "Shikennan na ji". Na faɗa a taƙaice muna ƙarasowa department ɗin namu. Da yake akwai sauran lokaci kafin mu shiga lecture ɗin sai bata buɗe ƙofar na fita ba sai ma ɗora kanta da tayi a jikin kujerar da take zaune haɗe da kallona tace. "Janaam ina cikin damuwa". Na tsura mata idanuwa ina kallo alamar tambaya, ta lumshe idanuwa tayi ta rufe lokaci ɗaya ta buɗe tana murmushin da kana kallo kasan na yaƙe ne don tabbatar mini da zancenta, "ke kuwa me zai dame ki keda ke zaune lafiya acikin school ɗinnan babu wanda ya takura maki, ai ko ni da ake takurawa wallahi bana cikin damuwa balle ke, kin sani this week zamu fara C.A daga nan kuma sai zancen rubuta semi final exam ɗin mu, me zai sa ki bari wani abu ya dame ki har haka?" Na faɗa har lokacin idanuwana na kanta, sai data ɗan sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "To ya zan yi Besty tunda abin da ke damuna ɗin nan tare yake dani? Wlh Ina matukar son Umar Farouk Besty fiye da kaina, jiya gabaɗaya ban samu nayi bacci ba saboda abin da ya faru tsakanina dashi ta sanadiyar ki, don Allah ku daidaita tsakanin ku ku dena wannan faɗan ko na samu cikar buri na". Tunda ta ambaci sunansa na haɗe rai har ta dire zancenta sannan nace, "Kinga Besty buɗe mun ƙofa na fita naga kin saka lock a jiki, ai na rantse da na san wannan maganar zaki mun da ban tsaya ɓata lokaci na ba, hmmm ni Amatul-Alim in daidaita da wancan abun da ban san me kika gani naso a tattare dashi ba?, Allah ya tsare ya kiyashe ni walh, ki kwantar da hankalinki domin a shirye nake dashi yanzu, bazai sake ɓata mini rai a banza ba saboda na fahimci shi kansa bai san ina rayuwa ta fuskanta ba balle yabar wani yai rayuwarsa yadda yake so". "Besty kenan! Ai Umar Farouk yana da abubuwan so a tare dashi yadda kika san ya Nu'aym na da su, kamar yadda ban san kema me kika gani na so ga ya Nu'aym da kuke soyayya dashi tamkar ku haɗiye juna ba to baza ki san nima me na gano ba?" Kallonta nayi sama da ƙasa jin abinda ta faɗa ina taɓe baki kafin nace. "Ai kema kinsan ko goma ta lalace ta fi biyar albarka, Ya Nu'aym ko kusa ba sa'an shi bane tun daga kan shekaru, hankali, ɗabi'u na gari, mu'amalar rayuwa, wayewa da sauransu, don haka kima dena haɗa su don wutsiyar raƙumi ta riga tayi nesa da ƙasa". "Na ji ɗin, ko ma dai meye ina son sa a haka." "Allah ya taimaka." Na faɗa ina buɗe kofar bayan ta cire lock ɗin jiki, itama ta buɗe gefenta ta fita don kusan ma tare muka fito