Showing 99001 words to 102000 words out of 157423 words

Chapter 34 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

540

yaron da aka ce Umar Farouk ya kashe, kuma ya dauki shari'ar ya kaita a kotun mu". Ɗago kai ta yi zuciyarta na wani ɗaci take kallonsa kafin tace, "ka gyara zancenka, ake tuhumar Umar Farouk ya kashe bawai ya kashe kai tsaye ba, ɗana kuma Allah zai yi masa mafita ko a wace kotun ce aka kai shi don nasan haka ba wai zai dameka bane". "Wace irin magana ce wannan Hajiya Maryam, ɗana fa ne kuma nake faɗa maki a kotuna aka shigar da ƙararsa, idan abun bai dameni ba zan sanar dake ne?" "Zan dai sani ko da baka sanar dani ba ko awace kotun ce tunda ɗana ne". "Mtss.." Dady yai tsaki tare da yaye duvet ɗin ya sauko da ƙafafuwansa kasa ya mike ya bar ɗakin, wani irin kuka Momy ta fashe dashi tasan tabbas Indai a kotun mahaifin nasa aka shigar da shari'ar babu ta yadda Umar Farouk zai iya kubuta a hannunsa matukar yana da laifi ba tare daya hukunta sa ba, balle ga abun ya haɗa da adawa da kuma son daukar fansa daga wajen mahaifin yaron, sai data sha kukanta mai isarta da ya zame mata tamkar jiki tunda abun ya faruwa sannan ta share hawayenta ta dauko wayarta, Barrister Nazir ta kira dake matsayin yaya a wajen ta suka yi magana, sun jima akan waya kafin suyi sallama ta mike ta shiga toilet, wanka ta yi ta ɗauro arwala ta fito sallar isha'i ta gabatar tayi shafa'i da wuturi sannan tayi shigar baccinta ta haye akan gado ta jawo system ɗinta ta cigaba da abinda take yi.

Dady kuwa yana fitowa ɓangarensa ya koma ya shiga kai da komowa cikin ɗaki yana tunanin ta ina zai fara, sosai damuwa ta rufesa har yana jin cewa daƙyar zai iya gabatar da shari'ar saboda ba abu bane mai sauki danka ya tsayu a gabanka ka yanke masa hukunci bisa babban laifi irin wannan da kowa yasan hukuncin da doka ta tanada akai shine duk wanda ya kashe a kashesa. Tabbas wannan ya san jarabashi ne ubangijinsa yai yaga zai iya tsaida gaskiya akan kansa kamar yadda yake yiwa sauran al'umma ko bazai iya ba. Ganin bai da mafita al'amarin yasa ya ɗauro arwala ya tada sallah, sallolin dare ya yi sosai yana rokon Allah ya bashi kwarin guiwar wanzar da adalci a tsakanin dansa da kuma Dr Abdullahi ga duk wanda ke da gaskiya ya hana shi yin son kai, karo na farko daya ji hawaye sun sauko masa don Allah ya fishi sanin irin soyayyar da yakewa Umar Farouk, duk wannan abubuwan da yake yi yana yine don saita shi akan hanya tare da nuna masa kura-kuransa daga shi har Momy bawai don baya son sa ba, ji yai tamkar ace mafarki ne yake yi a tashesa, da ya ji daɗi da salama a zuciyarsa, a ranar kasa kwana yai yana addu'ar Allah ya karfafesa ya bashi damar yin wannan shari'ar bisa adalci kamar yadda itama Momy ta kwana zaune saman system ɗinta don ko kadan bata bari ta runtsa ba.

*******

Kwance Abba yake ya lumshe idanuwansa, ji yake yi wutar daukar fansa na ƙara ruruwa a cikin zuciyarsa, baya da wani buri yanzu irin yaga ya raba Chief of judge justice Ibrahim Lawal Shanawa da ɗansa da rayuwarsa na har abada, yadda ya tozarta sa a shekaru biyar da suka wuce shima ya tozarta sa idan ya gagara aiwatar da adalci, yadda ya raba shi da aikinsa shima araba shi da aikinsa don duk yadda zai yi bayan ya yankewa dansa hukuncin kisa da kansa sai kuma yasa an sallamesa a kujerarsa. Nu'aymah ce ta shigo ɗakin jiki a sanyaye tana kallon mahaifinta yadda ya shiga damuwa, da yake idanuwansa a rufe yake sai bai ga shigowarta ba ji kawai yai tana magana, "Abba don Allah kasa asaki Umar Farouk, na tabbata ko menene ya janyo haka dasa hannun waccan munafukar, Abba ita ce tayi sanadiyar duk abinda ya faru ciki har da kauracewar farin cikina, kamata yai itama a kamata". A hankali Abba ya buɗe idanuwansa da suka cika da ɓacin ran kalaman Nu'aymah yana cewa, "Anya kina son dan uwanki Nu'aymah kina kishinsa? kin san wa kike cewa nace a saki bayan ya kashe maki dan uwa? To ki buɗe kunnuwanki da kyau kiji, ko da dukiyata duka zata kare bazan bar wannan shari'ar ba har sai naga an zubar da jinin ɗansa, yadda na tsani yaron haka na tsani ubansa, kuma zuciyata baza ta taɓa yin sanyi ba idan har ba naga sun wulakanta ba, an faɗa masa so hauka ne, me yasa bai kashe yarinyar ba sai ɗana? Me ya kawo shi gidana ma shine abun tambaya". Nu'aymah na hawaye ta ce, "ban sani ba Abba wannan ita kadai ce zata iya amsawa, tasan Umar Farouk farko dashi nake soyayya sai ta kwace mini shi bayan soyayya suke yi da ya Nu'aym, tasan zan iya faɗa masa komai shine ta shirya wannan makircin". "What! Nu'aymah kina nufin wannan yaron shi kike soyayya dashi? Dan makiyan nawa da yai sanadiyar raɓani da aikina a kasata, wanda ba don ina da mutane ba ya yanke mini hukuncin kisa saboda wani abu da bai taka kara ya kawo ba shi kike cewa kina soyayya dashi a gaban idanuwa na? To wallahi ko da hakan bata faru ba ko mutuwa zakiyi bazan taɓa bari ki auresa ba, shashashar banza da bata san inda ke yi mata ciwo ba, zaki fice mun da gani ko sai na saɓa miki". Kuka Nu'aymah ta shiga yi tana bubbuga ƙafafuwa Abba ya taso a fusace ya yo kanta yana masifa wanda hakan ya sata rugawa aguje tabar ɗakin tana ɓare baki, Ummi ce ta shigo ɗakin data haɗu da Nu'aymah tana ƙoƙarin lallashin ta taƙi tsayawa, a bakin kofa ta tsaya ganin yadda ran Abba ɗin yai matukar ɓaci yana faman Safa da marwa a tsakiyar ɗakin tace.

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[8/20, 6:08 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

09079274454

https://www.arewabooks.com/chapter?id=6894e7bd8ebf53d524760d91

                            44.

Sai da Umar Farouk ya kwashe sati biyu a asibiti kafin aka sallamo sa, kallo ɗaya zaka yi masa ka tabbatar daga jinya ya taso, jinyar ma bata gangar jiki kadai ba har data zuciya don duk iya ƙoƙarin da zai yi wajen ganin ya shawo kan Janaam ta karɓi soyayyarsa ya yi amma bai yi nasara ba, hakan ya haifar masa dayin wata irin rama duk da irin tarin kulawar da yake samu wajen likitoci da kuma Iyayensa, hatta Dady dake fushi dashi sai daya sauko ganin irin ramar da yai , gaba-daya an ɗauka matsalar ciwon hannunsa daya samu karaya da ƙafa ne ke damunsa don har Dady ya soma shirye-shiryen ko za'a fitar dashi waje saboda yadda Momy tabi duk ta ɗaga hankalinta, gashi anyi masa tambayar duniya akan meke damunsa amma yaki buɗe baki ko da likita yai wa bayani, wanda hakan yasa da likitan ya dudduba sa yaga ya samu sauki ya basu sallama tare da yiwa Momy bayanin cewa su kula da kyau akwai abinda yake tunani wanda shi ya haifar masa da damuwa har ta yi masa yawa har yake wannan ramar, idan kuma bai dena ba to komai zai iya faruwa dashi nan gaba. Hankalin Momy sake tashi yai bayan sun dawo gida ta ci gaba da lallaɓa Umar Farouk tamkar wani ƙaramin yaro don tasan ko meke damun sa amma yaƙi bata damar hakan, daga karshe ta kira Saleem ta tambayesa amma sanin halin Umar Farouk bai iya ya faɗa mata gaskiyar abinda ke faruwa ba saboda rashin sanin ta ina ma zai fara sheda mata cewa yarinyar da a ranar ya hango tsantsar tsanarta a idanuwanta har ta kasa hakuri ma ta furta da bakinta ta tsane ta ita ɗanta Umar Farouk ke so har take wahalar dashi, ya san da kamar wahala idan zata karɓi zancen musamman ma idan ba shi Umar Farouk ɗin ya sanar da ita da kansa ba, yasan komai Momy zata iya yima Janaam musamman yadda taga ɗanta ya shiga wani hali ta dalilin ta, Momy tasan halin Umar Farouk tunda bai yi niyar buɗe baki ya faɗi abinda ke damun sa ba to fa duk abinda za'a yi bazai faɗa ba, don haka ta sashi agaba tana sharar hawaye tana fadar tunda ya fiso ya rasata saboda damuwar sa da bata so to ya je yai duk yadda yaga dama baza ta sake tambayarsa ba. Duk taurin kan Umar Farouk babu abinda ya tsana aduniya sama da ɓacin ran Momy, saboda haka yana ganin ranta ya ɓaci sai ya soma karfafa kansa ya rage tunani da damuwar da yake ciki har ya soma fita tare da Saleem saboda ya nuna mata ba komai kamar yadda yake faɗa mata akoda yaushe, ya yi kokarin canzawa sosai yadda Momy zata cire wa kanta damuwa kuma ba laifi ya yi nasara, sai da yai sati ɗaya da sallamo wa daga asibiti sannan ya koma school.

Misunderstanding ɗin da muka samu da Ya Nu'aym ta sanadiyar Umar Farouk yana da yawa saboda yawan kiran da yake yi mini da akoda yaushe hakan bata faruwa sai lokutan da Ya Nu'aym yake kirana, duk da magana mai daɗi bata taɓa haɗa ni da Umar Farouk ba bai taɓa jin cewa zai daina kirana ba, a yadda yake nuna mini ko zaginsa zan yi indai zan ɗauki wayarsa yaji muryata to zai ji daɗi saboda jin murya ta kaɗai na bashi natsuwar zuciya tare da samun farinciki, hakan daya faɗa shi ya hankaltar dani kuskuren ɗaga wayarsa da nake yi har muna samun matsala da ya Nu'aym sai kawai na rufe duka layoyan sa da yake kirana dasu ta yadda bazai sake samuna ba ko ya kira, bayan na tura masa ƙwaƙƙwaran jan kunne tare da baƙaƙen maganganu, daga lokacin na samu lafiya kuma muka dena samun matsala ni da ya Nu'aym, kyakkyawar alaƙa da kuma shaƙuwa ta sake shiga tsakanina dashi muka sake komawa tamkar sababbin masoya, kullum muna lake dashi a waya ko kuma vedio call, yayin da kwanaki keta shuɗe wa lokacin ƙarewa makarantar mu nata matsawo, da kansa yake kirgar ko kwanaki nawa suka rage mana mufara exam, inda yai mini alkawarin cewa tare dashi za'a yi shagalin bukin graduation ɗin mu don zai shigo kuma bazai koma ba har sai anyi mana baiko an tsayar da ranar bikin mu, ina son ya Nu'aym da duk wasu dabi'u nasa saboda mutumen kirki ne uwa uba ga soyayya da yake nuna mini tamkar zai hadiye ni, shi yasa duk wani abu da zai sa yai fushi ko ransa ya ɓaci ina nisanta kaina dashi musamman wanda zai hada alaƙata da wani namijin saboda tsananin kishinsa akaina yana da yawa, na kuma fahimci ba komai yasa yake yin haka ba sai don yana so na da yawa kuma yana kaunata fiye da kima, ban sani ba ko Nu'aymah ta fahimci Umar Farouk na so na shi yasa tayi baya-baya da alakar mu duk da muna gaisawa idan muka haɗu kuma muna zaunawa muyi fira, sai dai duk wani abu daya shafi sirrin juna da ada muke fadawa junan mu yanzu ta dena, ko firar ya Nu'aym na dauko mata sai dai kawai tayi murmushi tace wannan tsakanin ku ne, tun ina jin ba daɗi har na hakura na dena, duk wanda yasan yadda nake da ita ada ya san yanzu ba haka muke ba, ita kanta na san bawai tana jin daɗin irin zaman da mukeyi yanzu bane saboda tayi wani irin sanyi sannan kuma ta rame, ko da yake ban sani ba ko har da soyayyar Umar Farouk ke damunta data dena gani, don haka na kudurta a raina koma menene zan yi amfani da damata idan Umar Farouk ya dawo school na ajiye tsana da komai a gefe na nuna masa tarin ƙaunar da Nu'aymah keyi masa na kuma tabbatar masa da ina da wanda nake so kuma na tsaida da zan aura, na tabbata hakan zai sa ya hakura dani ya koma gareta.

(Anya Janaam kina ganin zaki iya? Kar fa kije ki ɓallowa kan ki ruwa🧐).

*****

Yau muna zaune ni da wasu yan class ɗin mu ana fira kafin mu shiga C.A da zamuyi don tuni muka fara contentiour assessment ɗin mu, Nu'aymah bata shigo ba shi yasa na ji bazan iya tsabbace kaina a gefe ba na shige cikin su ana tattaunawa akan abinda ya shafi karatu don karawa juna sani, motar Umar Farouk ta shigo ta yi parking adai-dai ƙofar department ɗin mu, wanda hakan yasa tun kafin ma ya ƙaraso mazan da muke zaune tare dasu duk suka tashi suka koma gefe, dariya matan dake wajen suka sa masu ni kuma na haɗe rai ina dafe goshi, don har ga Allah in nace na ji daɗin dawowar sa to nayi ƙarya, ta wani ɓangaren kuma tunanin ko don Nu'aymah da nake son samawa maslaha akan soyayyar ta dashi shigowar tasa zatayi amfani, kai tsaye wajen da muke zaune Umar Farouk ya nufo bayan fitowarsa daga cikin mota, ina wannan tunanin sai ji nayi suna gaishe sa haɗe da yi masa ya jiki?  Ina jin yadda idanuwansa ke yawo akaina amma ban damu da ɗago kaina na kallesa ba balle yasa ran zan gaishe sa, ganin nayi sun miƙe zasu bar wajen don haka nima na miƙe na bi bayan su, cikin sanyin murya na ji Umar Farouk ya kira sunana, "Amaah..." Sunan da shi kaɗai ne ke kirana dashi duk fadin duniya kuma idan ya kira ni da sunan sai na ji gabana yai wata irin faɗuwa, runtsu idanuwana nai ba tare dana tsaya ba na ji ya sake cewa "Don girman Allah da soyayyar da kike wa mahaifin ki ki tsaya". Tare da biyo ni a baya, ba don raina ya so ba na tsaya saboda girman Allah daya haɗa ni dashi da mahaifina daya ambata, zagayowa yai ya tsaya a gabana kaina na ƙasa ina sake haɗe rai, tsawon minti guda muka ɗauka a haka Umar Farouk ya kasa cewa uffan sai kallona kawai da yake yi wanda ina jin haka ajiki na, ganin bai da niyar cewa komai yasa na ɗago kai da niyar faɗa masa magana idanuwana suka sauka cikin nasa, innalillahi wainna ilaihirrajiun, na faɗa acikin raina gabana na faɗuwa ganin yadda ya ɗan rame ya kuma yi duhu tamkar ba shi ba tare da jin wani iri a zuciyata, duk da dama can shi ba fari bane tas amma ya sake yin duhu sosai, duka a cikin yan sakanni nayi masa wannan kallon, take sai naji zuciyata ta karye ina tabbatarwa da kaina cewa ban kyauta ba tunda saboda ni ya shiga wannan halin yai jinya har ta tsawon wata ɗaya amma ko sau daya ban je na duba sa ba  kuma ban yi masa sannu ba balle na tambayesa ya jikinsa, ko ba komai shi ɗin musulmi ne dake da haƙƙi akaina daya kamata idan yai rashin lafiya na duba sa, sake ɗago kai nai muka sake haɗa ido, murmushi ya sakar mini a wannan karon kafin yace...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[8/20, 6:08 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

09079274454

Masu son Vip sai ku bibiyi Arewabook @billysfari ta wannan link https://www.arewabooks.com/chapter?id=6894e7bd8ebf53d524760d91

                            45.

"Kiyi hakuri Amaahh na tsaida ke, na san na yi miki abubuwan da basu dace ba, amma ki yarda ni ɗan adam ne ina kuskure don Allah ki yafe mini, na sani yanzu haka kina jin ina takura ki sosai shiyasa har kikai blocking ɗin layoyana, na ji ba daɗi na ji zafi a zuciya ta sosai amma ya zan yi? Ni ne na jawa kaina da kaina watakil da baki tsaneni ba kuma baki yimun hakan ba, shi yasa duk abinda zaki yi mini bazan iya fushi dake ba saboda Allah ya riga ya ɗora mini cutar son ki saboda haka dole nayi hakuri, pls Amaahh don Allah ki bani damar gyara kura-kurai na wallahi ina sanki". Ƙasa nai da kaina don yanzu ban san kuma me zan faɗa masa ba, Allah ma muna yiwa laifi ya yafe mana balle mu daya halitta, Allah ya sani har yanzu ina jin zafin abubuwan da yai mun acikin zuciyata idan na kallesa, zan iya hakuri na yafe masa amma bazan iya karɓar soyayyar sa ba, har ga Allah bazan iya soyayya dashi ba don bana sonsa. Ina son na samu damar fahimtar dashi komai akan soyayya ta da shi ba abu bane mai yiyuwa kuma na fahimtar dashi soyayyar da Nu'aymah ke yi masa zai fi dacewa ya koma gareta, na sani idan har ni ban bashi damar saurarar sa ba to shima bazai saurareni ba, don haka na dago kai na ce, "Shikennan ka ɗauka wannan zancen ya wuce na yafe maka, Allah ya ƙara sauki". Wani irin murmushi Umar Farouk ya saki ni kuma na raɓa ta gefensa na wuce wani ɓangare na zuciyata na faɗa mini cewa nayi abinda ya dace yayin da wani ɓangaren kuma ke nuna mini nayi kuskure, koma dai meye yakamata ace na sama ma kaina lafiya agun shi haka itama Nu'aymah na sama mata mafita.

Fuskar Umar Farouk kuwa tamkar an yi masa wahayi mai daɗi saboda farin cikin daya tsinci kansa aciki, dama ita magana mai daɗi sadaka ce, duk da Janaam bata nuna masa ta karɓi soyayyarsa ba hakan kaɗai data faɗa nan take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login