Showing 15001 words to 18000 words out of 157423 words

Chapter 6 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

533

yanzu Umar Farouk ya furta mata kalmar so, da babu abinda zai hanata gabatar dashi ga iyayenta, ni dai sai binta nakeyi da kallo don abun nata ya soma bani tsoro, eh tsoro mana ace mutum ya wulakanta ki a tsakiyar mutane sannan ya zaga gefe yace zai baki haƙuri, don sakarci kuma irin na Nu'aymah tace zata haƙura, ko da yake an ce mai so wawa ne.

A ɓangaren Umar Farouk ko har ya manta da abinda ya faru tsakaninsa da Nu'aymah jiya, yau ya shigo makaranta ne da zimmar nunawa Janaam kuskurenta tare da yimata abinda har ta mutu bazata taɓa mantawa ba, tun ƙarfe bakwai ya shigo ya kasa ya tsare a bakin kofar shiga department ɗin nasu yana jiran shigowarta, zaune yake cikin motarsa daya buɗe gefen driver ya fiddo ƙafarsa ɗaya a waje, 'yan matansa kuma na gefensa tsaye wasu sun jingina a jikin motar ita kuma Felicia saman motar ta haye tana yan hare-hare hango Nu'aymah da Janaam dake tafe daga can nesa, yau abakin gate driver ya ajiyesu don zai wuce da Nihla makaranta ya ajiyeta shiyasa suka tako ƙasa, tunda Nu'aymah ta hango Umar Farouk ta faɗaɗa fara'arta tana murmushin jin daɗin ganinsa. Janaam kuwa sai harara take aika masa da ita daga shi har yan matan nasa ta cikin niƙab, Felicia na ganin sun kusa karasowa ta diro daga kan mota tana cewa, "Zan koyawa yaran can hankali yau". Ba tare da Umar Farouk ya ɗago ba ya ce, "waya aike ki ne? Wannan aiki na ne ba na ɗaya daga cikin ku ba". Yana gama faɗar hakan ya fito cikin motar ya tunkaro inda su Janaam ke nufowa, yana kawowa ya tare gabansu fuskar nan tasa a haɗe ba ɗigon annuri ko ɗaya akai, cikin daburcewa da farin ciki Nu'aymah ta fara ƙoƙarin yi masa magana yai saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga masa hannu idanuwansa na akaina, cikin dakewa na sake haɗe rai duk da ina cikin niƙab, "faɗamun ke yar gidan uban waye? Me kike taƙama dashi da har kike jin kanki ke wata ce? Kin san hatsarin da ke cikin shiga sabgata ba tare da nine na so hakan ba?" Umar Farouk ya faɗa yana sake matso ni, ƙin matsawa nayi baya don babu alamun jin tsoro atattare dani nace, "And so?" ina jefa masa wani mugun kallo a lalace mai cike da tsana da kuma reni, ran Umar Farouk ne ya sake ɓaci ya juya gefe yana shafa kansa, ban an kara ba kawai na ji ya ɗage mani niƙaf ya fizge tare da wurgi dashi gefe, tashin hankali! Abinda na faɗa kenan cikin zuciyata idanuwana na canja kala saboda tsananin ɓacin rai, ina ɗagowa ban tsaya wata-wata ba na ɗaukesa da wani zazzafan mari, shekarata uku kenan a makarantar yanzu muna shekarar ƙarshe semester ta farko, tunda nake ban taɓa cire niƙaf ɗina ba, nasan da yawa a makarantar kai a class ɗin mu ma ko za'a kashesu basu san yadda fuskata take ba, shine yau saboda jakanci na Umar Farouk zai kware mani fuska a tsakiyar makaranta saboda yana jin shi wani ne, nunasa na shiga yi da yatsa cikin matsanancin ɓacin rai ina cewa, "Ni ba karya bace kamar wuɗancan karnukan dake bibiyarka Umar Farouk, ba kuma wulakantacciya bace da zaka yi tunanin zan iya zuba idanuwa ka wulakanta ni, idan kana tunanin zaka iya tozartani a cikin makarantar nan to a shirye nake dana tozartaka fiye da haka kaima saboda kai ba ubana bane, ba kuma kai ka halicceni ba balle naji tsoronka kamar yadda sauran mutane ke ji, ina tunanin kuɗi ubanka ya biya maka ya kawoka makarantar nan ai ko?, to haka nima kuɗi ubana ya biya ya kawo ni don haka banga dalilin da zai sa in dauki reni ga kowa ba, hmmm! Wai da kake ɗaukar kanka wani kana tunanin duk mai hankali zai ji tsoronka ne bayan kai da yan daudu ba kuda maraba! kana namiji amma kana ɓuya a bayan mata har kake tunanin zan ji tsoronka? Never walh". Na kare maganar cikin zare idanuwa kafin naja hijab ɗina na rufe fuskarta dashi sannan na bar wajen na nufi class ina jin zuciyata na mun ƙuna, Nu'aymah da gaba-daya ta ruɗe sai kawai ta dauki nikaf ɗinta ta bita a baya.

Umar Farouk kuwa tamkar an dasa shi a wajen haka ya kasa motsawa kuma ya kasa ɗago kai, ya rasa me yafi yi masa zafi tsakanin marin da Janaam ta sauke masa da kuma kalaman data faffaɗa masa, dariya ya soma yi yana imagining wai kamar shi za'a yiwa haka, wata dariyàr ya sake yi sannan ya juya ya nufi wajen motarsa da yan matansa ke gun sake da baki ganin abinda ya faru, wanda yàna juyowa gaba-daya suka sha jinin jikinsu don sun san tsaf zai juye akansu, book ɗinsa kawai ya ciro cikin motar ya rufe sannan ya nufi class, yan matan na ƙoƙarin rufa masa baya yai saurin dakatar dasu yai tafiyarsa abunsa.

Lecture ake yi amma gaba-daya hankalinsa baya wajen sai kallon Nu'aymah data mayar da niƙaf ɗin ta yake yi da wani irin mugun mamakin abinda tayi masa, ana gamawa ya fito ya ja motar sa ya fice daga makarantar ba tare daya damu dayin lecture ɗin dake gaba ba.

Ni kuwa ina kalle da Nu'aymah dake son yi mani magana akan abinda ya faru amma nayi mata banza, ganin bata ga fuska ba yasa ta sha jinin jikinta har muka gama lecture ɗin wunin ranar ba tare data cemun uffan ba, bayan mun tashi muna tafe na kalli yadda duk tayi wani sanyi nayi murmushi haɗe da cewa. "Wai Aymah lafiya naga duk kin yi wani sanyi sai kace marar lafiya?" Nu'aymah ta ɗago kai ta kalleni na ɗaga mata gira haɗe da cewa, "Meye?" Ta sauke ajiyar zuciya ta kalleni sannan tace. "Besty kin bani tsoro, anya kece kuwa?" Na haɗe girar sama da ƙasa kafin na bata amsa nace, "Me kika gani? Wani abun ne ya faru?" Tana kokarin bani amsa muka ga motar Nu'aymah ta tsaya agabanmu, Ya Nu'aym ne na gani bayan ya zuge glass fuskarsa ɗauke da murmushi, bansan dalili ba ganinsa kawai yasa naji ɓacin ran da nake ciki ya gushe, "Sannunku yan mata, ina zuwa?" Ya faɗa yana ɗaga mana gira cikin sigar zolaya, dariya duk muka sa kafin Nu'aymah ta buɗe gaba ta shiga ni kuma na buɗe baya na shige...

ALLAH KA JIƘAN IYAYEN MU👏

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            10.

Sai da Ya Nu'aym ya tada motar ya hau titi sannan ya juya yana kallon Nu'aymah yace, "Aymah why are you so Cool? Me yafaru ne?" Juyowa Aymah tayi tana kallona na haɗe rai tare da kauda kaina gefe, sai data sauke ajiyar zuciya sannan ta kallesa naji tace. "Ba komai Ya Nu'aym kawai na ɗan gaji ne". "Ehm..wai haka ne Janaam?" Ya tambaya yana kallona ta cikin madubi, murmushi na saki tare da cewa. "Eh tunda haka ta faɗa maka Ya Nu'aym, ina wuni?" "Lafiya kalau, ya lectures?" "Alhamdulillah". Na amsa masa ina kallon waje ta cikin glass ɗin motar dake gefena, daga haka babu wanda ya sake cewa komai har muka iso gidansu, har zan fita yai saurin dakatar dani yana cewa. "No bari na ajiyeki gida". Kasa yi masa musu nayi duk da bana son Ya Jameel ya ganeni saboda yawan ja mini kunne da yake yi akan shige masu da yake ganin kamar ina yawan yi. "Besty sai gobe ko?" Nu'aymah ta faɗa bayan ta fita tana ɗago mani hannu, Nima hannun na ɗaga mata sannan Ya Nu'aym ya ja motar yabar wajen.

Shiru kake ji ba wanda ya sake cewa wani abu tsakanina dashi kafin can ya Nu'aym yace. "Janaam in sha Allah gobe da safe zan bar ƙasar nan, kiyi haƙuri na saɓa alkawarin cewa zan baki kwanaki kiyi tunani akan soyayyata, hakan ya faru ne saboda matsa mini da su Abba keyi akan na koma hankalinsu zaifi kwanciya, bayan haka akwai ayukka masu tarin yawa dana baro daya kamata ace na koma ɗin duk da ba hakan naso ba". Shiru ya ɗanyi yana driven a hankali tamkar wanda baya so ya isa inda zai je kafin yaci gaba da cewa.

"Janaam ina so kifaɗa mini gaskiya idan har kina da ra'ayi akaina". Cikin jin kunya na saukar da kaina ƙasa ina tunanin amsar da zan bashi, idan har nace zuciyata bata son Ya Nu'aym to nayi ƙarya, sai dai ina tunanin ya yi wuri na amshi tayin soyayyarsa cikin kwana biyu har sai na gama fahimtarsa da sanin ko waye shi." "Please Janaam kice wani abu mana". Na ji ya sake faɗa haɗe dayin parking adai-dai lokacin da muka iso ƙofar gidanmu. Tsoron kar Ya Jameel ya rutsani yasa nayi saurin fitowa cikin motar ina cewa, "Na amince ya Nu'aym". Ina gama faɗar hakan cike da jin kunya na shige gida da gudu ina jin zuciyata na wani irin bugawa da sauri da sauri".

Nu'aym kuwa Janaam na faɗin hakan ya rintse idanuwa yana yiwa Allah godiya, tabbas ranar yau na ɗaya daga cikin ranaku masu matukar muhimmanci a tarihin rayuwarsa da bazai iya mantawa da ita ba, kalamai ukun data furta nata amince dashi sun matukar sanyaya masa zuciya, kofar gidansu ya ƙurama idanuwa tamkar wanda ke jiran fitowar ta kafin ya saki murmushi ya ja motarsa yabar wajen.

******

"Umar Farouk wai lafiya tun safe daka dawo school kazo ka shige ɗaki ka rufe ƙofa baka fito ba? Me yake damun ka ne?" Mom dake tsaye bakin kofar ɗakin Umar Farouk tana bubbuga wa ta faɗa cike da damuwa, mayarta ta kusan bakwai kenan tana yi masa knocking amma bai buɗe ba, yanayin da yaji muryarta yasa shi tasowa ya buɗe kofar tare da juyawa ya koma ciki, "Umar Farouk lafiya kake?" Ta faɗa tana shigowa cikin ɗakin, sinne kai ya yi ƙasa don gani yake tamkar idan aka kalli fuskarsa za'a hango marin da Janaam tayi masa, a hankali yace, "Momy kaina ne yake ɗan yi mini ciwo amma is ok now na ji na samu sauƙi". "Are you sure Umar Farouk?"."Yes Momy yunwa dai nake ji bari na watso ruwa sai na fito naci abinci". Ya faɗa tare da barin wajen don baya son ta sake jefo masa wata tambayar, ruwa masu sanyi ya sakarwa kansa sosai har na tsawon minti biyar kafin yayi wankan ya ɗaura towel ya fito, tsaye yai gaban mirror yana ƙarewa kansa kallo, kyakkyawar fuskarsa zuwa murɗaɗɗun damatsan hannunsa, faffaɗan ƙirjinsa zuwa cikinsa dake nannade ya fidda wasu layoya, coily hair ɗinsa ya shafa yana sake ƙurawa fuskarsa idanuwa, da sauri ya rintse ido tunowa da marin da Janaam tayi masa yana sake jin saukarsa akan fuskarsa kamar lokacin, wata ƙara ya saki haɗe da duƙawa yana riƙe gashin kansa da hannu biyu tamkar zai cire sa, kamar ni wannan yarinyar zata mara kuma nakasa yin komai? Wacece ita? Ya faɗa cikin ransa yana jin zuciyarsa na sake yi masa zafi, tabbas ta taro wasa mai kyau tsakanin shi da ita, ya ji daɗin da ita ce ta fara buga wasar, don haka dole suci gaba da bugata har lokacin da ɗaya zai yi nasara tsakanin su. Jin Momy na kiransa daga palour ya sashi miƙewa yana faɗin, "Momy yanzu nan zan fito".

Daƙyar ya iya tsayawa ya shafa mai ya samu kaya marasa nauyi ya saka, har ya ɗauki comb zai gyara sumar kansa sai kuma ya fasa ya ɗauki turare kawai ya fesa jikinsa sannan ya fice zuwa paloun, a can ya tadda abincin da Momy ta shirya masa kafin ya fito, zaunawa ya yi don sosai yake jin yunwa bazai iya jira ta dawo ta zuba masa ba, abincin ya buɗe ya zuba ya ci ya ƙoshi sannan ya koma ciki ya ɗauko key ɗin motar sa da wayar sa ya fice zuwa part ɗinta. Sai daya gaisheta sannan ya ce mata zai fita, addu'a tayi masa tana sauke ajiyar zuciya tare da jin daɗin fitar da zai yi, ko ba komai tasan zai ɗan wartsake idan ya haɗu da abokanansa,

Umar Farouk ko daya fita lambar Felicia da Billy yan matansa ya kira su zo su rakasa buga table tennis da yake zuwa yi duk mare ce ko kuma basket Ball, cikin mintuna biyar sai gasu sun iso ko wace taci gayu a tunanin ta ita kaɗai ya kira, nan fa suka shiga kallon kallo da yan harare-harare tsakaninsu, Umar Farouk bai bi ta kansu ba ya buɗe gaban motar da sauri Billy dake kusa ta shige, dole Felicia ta buɗe baya ta zauna tana rufe ƙofar da ƙarfi, shi kuma ya tayar da motar yabar wajen ba tare daya cewa ɗaya daga cikinsu ko uffan ba.

*******

Fitowa ta wanka kenan naga wayata dake kan standing mirror na haske da yake a silent na sakata, ƙarasowa nayi na ɗauka ina zaunawa gefen katifata haɗe da ɗaga kiran duk da sabuwar lambace na kara a kunnena. "Amincin Allah ya tabbata agareki matata". Naji an faɗa cikin wata irin sanyayyar murya mai cike da natsuwa, wadda ta tabbatar mini da cewa Ya Nu'aym ne, murmushi nayi haɗe da cewa. "Tare dakai ya Nu'aym, ya ka isa gida ɗazu?" "Lafiya ƙalau kyakkyawata, Allah yasa ban tasheki bacci ba?" "Ko ɗaya, idan ma kayi hakan to girmanka ne." "Godiya nake yi, dama nakira naji muryarki ko zan samu nayi bacci mai daɗi, baccin da nake da tabbacin daga shi bazan koma yin bacci mai daɗi ba kuma". "Saboda me ya Nu'aym?" Ya ɗan sauke ajiyar zuciya sannan naji yace, "saboda zanyi nesa da masoyiyata abar kauna ta, Janaam ni fa a yadda naso iyaye su shiga maganar mu kafin na tafi, son samu ma ace har aure an daura mana in ɗauke ki na tafi dake don samun cikakkiyar kulawarki, sai dai yanzu lokaci ya ƙure da bazan samu wannan damar ba, zan yi hakuri na fara renon soyayyaki tayi girma tare da rassa a zuciyarki har zuwa lokacin da zan sake dawowa, nasan a lokacin ma kun kammala karatu sai na shigo da karfina ayi komai a gama ko kuwa?" "Idan haka ka tsara Shikenan ba laifi, amma a son samu na mu samu cikakken lokacin da zamu fahimci juna, watanni basu fi takwas ba ya rage mu ƙare school, gashi nisa ya sanya katanga a tsakaninmu da baza mu samu damar kasancewa tare ba akoda yaushe, Ni ina ganin yayi wuri lokacin idan iyaye suka shiga maganar". "But amma hakan ya dace Janaam indai har da gaske muke son juna". "Haka ne, amma muna bukatar lokaci sosai domin yiwa soyayyar mu kyakkyawan ginin da bazai rushe ba agaba." "To Shikennan zan jira har wannan lokacin, amma ki kula mini da kanki, ki killace mini gangar jikinki ni kaɗai, ki bawa zuciyarki kyakkyawan tsaro wa ni kaɗai Janaam, ina sonki ina kuma jin kishi sosai da zan tafi na barki wasu mazan na kalle mini ke a makaranta, na baki amanar kaina Janaam don Allah kada ki barni". Murmushi nayi cike da jin daɗin kalamansa nace, "Ka dauka Janaam acikin makafi take karatu da idanuwansu baza su taɓa ganinta ba, haka kuma dukkansu guragu ne bazasu taɓa zuwa inda Janaam ɗinka take ba, zan kula maka da kaina har lokacin da zaka dawo in sha Allah". Wata irin ajiyar zuciya mai ƙarfi naji ya sauke haɗe da cewa, "har kinsa na ji sanyi, abu daya ya rage shine kimun alƙawarin bazaki sauya ni ba saboda bana kusa dake". Nayi dariya ina mamakin to wane irin sauyasa zanyi tunda babu wani namiji dake zuciyata face shi, na amsa amsa masa da cewa, "nayi maka alkawari ya Aym daga kai ba ƙari ba kuma canji". "Alhamdulillah nagode sosai Janaam, I will forever love you". "Me too". Na faɗa nima don tuni ya gama tsuma ni da daɗaɗan kalaman sa. Hira mukayi sosai don har ƙarfe sha biyu muna maƙale da juna, A ranar Ya Nu'aym bai barni ba sai daya gama sanyaya ko wace gaɓa ta jikina da salon soyayyarsa, ya kuma tabbatar mini shi ɗin cikakken masoyi ne da a shirye yake ya bani farin ciki na har abada, hakan yasa na miƙa masa dukkanin yarda da kuma soyayyata, na kuma amince ya ja ragamar rayuwata har zuwa lokacin da zamu kasance cikin inuwa ɗaya a matsayin miji da mata...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            11.

Tun da asubar fari wayar Ya Nu'aym ce ta tashe ni daga bacci, mirginawa nayi tare da miƙa hannuna a jikin socket na ciro wayar dana saka a chargy da zan kwanta jiya. Cikin magagin bacci na ɗaga kiran tare da kai wayar a kunnena nayi sallama, sautin muryarsa naji ya ce, "wake up kyakkyawata, me kike har yanzu baki tashi ba gashi na gama shiri zan tafi". "Da wuri haka Ya Nu'aym?" Na faɗa ina ware idanuwana daga baccin da nake tare da miƙewa zaune, murmushi Nu'aym ya saki jin abinda ta faɗa yana cewa, "Morning kin tashi lafiya?" "Lafiya ƙalau kai fa?" "Ehhh to alhamdulillah zance don nasha mafarkanki har ba iyaka jiya, ciki kuwa hadda na munyi aure kin haifa mini kyawawan yara masu kama dake." Cikin jin kunya na yaye bedsheets ɗin dana lulluɓa dashi na sauko da ƙafafuwana ƙasan katifata ina cewa, "Kai ya Nu'aym!" "Kai ya Nu'aym." Shima ya faɗa yana kwaikwayon muryata tare dasa dariya, nima dariyar nayi kafin na miƙe ina cewa. "Bara nayi sallah sai muyi waya". Cike da amsa umurnina ya katse kiran ni kuma na shige toilet na ɗauro arwala na fito na saka hijabina tare da shimfida abun sallah na tayar, ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login