Showing 54001 words to 57000 words out of 157423 words

Chapter 19 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

515

ƙayatar tare da tura mata hotunan dana ɗauka a wajen....

ALLAH KA JIKAN IYAYEN 👏

[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRA N1000 KI KARANTA HANKALI KWANCE.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

                            31.

A ɓangaren Umar Farouk yana zaune tare da Momy kiran farko na Janaam daya saka ma Amaah ya shigo wayar sa ɗazu, miƙewa yai tsam ya nufi ɗakin sa yana ɗaga kiran haɗe da kai wayar a kunnensa, a hankali ya lumshe idanuwa jin yadda zazzaƙar muryarta ta daki kunnensa ba tare daya ce komai ba, wani irin sanyi ya riƙa ji na ratsa masa cikin zuciyarsa haɗe da wani feeling da bazai iya kwatantasa ba, ji yake tamkar tayi ta magana yana sauraren ta ba tare data dena ba, da hakan ne jin ba'a yi magana ba Janaam ta kashe wayar ta sake kira a karo na biyu, nan ma ɗagawa yai tare da sauke ajiyar zuciya yana zube wa a saman makeken gadonsa, a hankali yake jin wani abu mai ƙarfi na yi masa kutse a cikin zuciya yana luguiguita masa ita yana jin sautin muryar ta tamkar ana busa masa sarewa acikin kunnuwan, ya lumshe idanuwa a hankali yana sauke sirrintacciyyar ajiyar zuciya tamkar wanda yai wasar tsere yana ci gaba da saurarar muryarta dake haifar masa da wata irin natsuwa. "Oh God!" Ya faɗa lokacin daya ji ta sake kashe kiran yana jin jikinsa gaba-ɗaya ya mutu, 'Wai me ke shirin faruwa da nine?' ya tambayi kansa yana tura hannunsa cikin sumar kansa, da wannan tunanin bacci ya ɗauke sa baccin da zai iya cewa cike yake da mafarkai kala-kala da bazai ce ga ma'anar su ba.

*********

Kwanci ta shi babu wuya a wajen Allah hutun su Janaam ya ƙare sai shirye-shiryen komawa semester ƙarshe suke yi zuwa sati na sama, kimanin sati biyu kenan tun lokacin da Umar Farouk ya gwada kiran Amaah yaga ta ɗaga sai ya zama kusan kullum sai ya kira don ɗai ya ji muryar tata dake haifar masa da natsuwa, takan ɗaga kiran wani lokaci tayita magana yana saurarar ta amma bazai ce komai ba, wani lokacin kuma tana ganin kiran sai taƙi ɗagawa saboda ko ta ɗaga ba'a magana, daga ƙarshe ta gaji ta sanya number a blacklist, Umar Farouk ya ji ba daɗi amma tuna cewa hutu ya ƙare yasa bai wani tada hankalinsa ba, sai dai shi kaɗai yasan me yake ji a cikin zuciyarsa shiyasa Allah Allah kawai yake a koma school ko zai samu sassauci abinda yake ji, a yanzu ya gama tabbatar wa da kansa cewa son Janaam yakeyi, so irin wanda ke saka zuciya tayi rauni gangar jiki ta jigata, ruhi kuma ya shiga tsumaye, son dake makaftar da idanuwa sannan ya jefa rayuwa cikin gararin da baza ta fice sa ba har sai lokacin data mallaki wannan abun da take so, ya yadda cewa Janaam ta gama sace masa zuciya tun a waccan ranar kuma a shirye yake da yayi komai a kanta.

Ɓangaren Nu'aymah ma a kullum safiya ji takeyi kaunar Umar Farouk na sake samun wajen zama acikin zuciyarta haɗe dayin yaɗon da take da tabbacin babu wani sauran gurbi daya rage da bata mamaye ba, ta gama shirya wa kanta irin rayuwar da zata yi dashi ta kowace irin fuska tare da bayyana masa soyayyarta suna komawa school, kamar dai yadda shima Umar Farouk ya ci alwashin cewa suna komawa makaranta zai bayyanar da soyayyarsa ga Janaam. Yau kwana su biyu kenan da dawowa Nigeriya, ta shirya cikin abaya fara tayi rolling kanta da mayafinta sannan ta ɗauki handbag da car key dinta da wayarta ta jefa aciki, ummie ta samu a kitchen ita da mai aikinta suna girkin abincin rana ta ce, "Ummie zan je gidan su Janaam.." "Adawo lafiya, kice ina gaida Mamah" "zata ji". Nu'aymah ta faɗa kafin ta fice, parking space ta nufa inda motarta take ajiye ta ciro key ɗin motar ta zura ta buɗe kofar, kamar ance ta ɗago kanta ina turo ƙofar gate zan shigo muka haɗa idanuwa, murmushi kwance akan fuskarta ta mayar da kofar ta rufe tana cewa, "Oyoyo Besty, yar halak kin ƙi ambato". Ta ƙare zancen tana nufo inda nike, ina zuwa muka rungume juna don munyi kewar junanmu ba kaɗan ba, kallonta nai haɗe da cewa, "lallai Besty ƙasar UK ta amshe ki, kin ga wani haske da kika yi sai kace ba ke ba?" Ta ɗan harare ni da wasa ta riko hannuna muka nufi cikin gidan tana cewa, "Ba wani nan, baki ga ya Nu'aym ba shi yasa kike fadar hakan, ni da ko wata bamu ƙarasa yi ba acan, Da fa wajen ki zan je tunda kin ki zuwa kiyi mini ko sannu da hanya, mu je ga sakon ki can har na manta dashi sai ki wuce da abinki". Ban ce da ita komai ba har muka isa cikin gidan, Ummie muka tadda a palour cikin girmamawa na gaisheta haɗe da yi mata sannu da zuwa har tana tambayata ya su Mamah na amsa mata da duk suna lafiya, Nu'aymah dake riƙe da hannuna har lokacin tace, "Ummie kin ga yar halak ta hutar dani, Allah da wajenki zan je Besty don na matsu na ganki akwai labari". Ta faɗa haɗe da juyowa tana kallona, Murmushi kaɗai na iya yi kafin ta jani mu hau sama zuwa ɗakinta, sai data kira mai aikin su ta kawo mini ruwa da ɗan abun taɓawa kafin muka hau fira tana bani labarin Ya Nu'aym, dariya nayi haɗe da kallonta don a irin soyayyar da take fadar yana nuna mata da yake yi mini bata kai kaso ko ɗaya ba daga cikin wadda yake nuna mini ba, "Au! besty mahaukaciya zaki maida ni ina baki labari kina dariya". "Ko ɗaya ni har na isa, kawai dai naga wannan tsohon labari ne Besty, son da ya Nu'aym ke yimini anan kusa banga macen da zata samu irinsa ba, kuma nima haka nake son sa tamkar rayuwata ko ma nace miki fiye da haka". "Ehmm naku dai kika sani Besty, amma a labarin so na tabbata baza ki taɓa jin irin nawa dana Umar Farouk ba don soonest zamu tashi kanku!" Ina dariya nace, "Lallai kam naga alama, ai ba ji kaɗai ba har gani ban taɓa yi ba, don mace dai irin ki kyakkyawa da bata rasa komai ba akwai ban al'ajabi da mamaki ace ta faɗa soyayyar wanda bai san ciwon kansa ba kamar sa". "Kin ga Besty ya isa haka bana so gaskiya". Nu'aymah ta faɗa tana haɗe rai, taɓe baki nayi haɗe da ciro wayata da naji tana Turi daga cikin jaka, Nu'aymah kuwa miƙewa tayi ta fita, bata jima ba sai gata ta dawo ɗakin ɗauke da wasu manyan ledoji lokacin muna vedio call da Ya Nu'aym don shi ne ya kirani awaya, mun jima kafin muka yi sallama dashi na kalli kayan da Nu'aymah ta ajiye agabana nace, "Wannan fa?" "Sakon ki ne in ji ya Nu'aym, ni kuma ga nawa". Ta ƙare zancen tana miƙo mani wata ƙaramar leda da ɗan ƙaramin akwati aciki, karba nayi haɗe da buɗe ledar na ciro box ɗin, kyakkyawan zobe ne aciki da kana kallo kasan bada ƙananan kuɗi aka siya ba, nuna mata box ɗin nayi fuskata ɗauke da fara'a tana murmushi ta ɗago mini hannunta tana kaɗa yan yatsun ta, sak kalar zoben dake cikin box ɗin na gani a hannunta komai iri ɗaya babu banbanci, da alama tare ta siya mana. "Thanks Besty". Na faɗa ina tasowa daga wajen da nake zaune haɗe da rungumeta don nuna mata jin daɗin kyautar da tayi mini, a gabanta na ciro zoben ina ajiye box ɗin a saman gadonta sannan na saka a hannuna a kuma dai-dai irin yatsan data saka nata ina sake hugging ɗinta, Nu'aymah tayi dariya haɗe da cewa, "Dama nasan zoben nan zai fi yi miki kyau fiye dani, da na je siya ina dauko sa na hango shi a hannunki, Allah ya yi miki kyau sosai". "Kema haka". Na bata amsa muna haɗa hannuwan mu waje ɗaya, ganin yadda zobban suka yi mana kyau yasa na ɗauko wayata nayi snapping, daga nan kuma muka shiga daukar hotuna abun mu abun dai gwanin burgewa, tarayya ta da Nu'aymah cike take da tsaftatacciyar soyayya da kuma ƙauna da fahimtar juna, hakan yasa ako yaushe idan wani abu ya haɗa mu mukewa junan mu uzuri mu shirya ba tare da kowa ya ji ba. Ban bi takan sakon Nu'aym data bani ba muka ci gaba da firar mu, sai da marece ya yi na ci abinci na yi sallah sannan na shirya tafiya gida, da kanta ta kwaso mini ledojin da taga ban ɗauka ba muka sauko ƙasa, dakin ummie ta raka ni nayi mata sallama itama ta ɗauko turaruka acikin leda ta bani, kin karɓa nayi Nu'aymah ta karɓa ta saka mini acikin sakon ya Nu'aym sannan ta rakani har bakin gate, kasancewar ba muda nisa ta kira wani yaro ta bashi ledojin hannunta tace yabi ni dasu don fir ni naƙi karɓar kayan, "Allah Besty ba kida kirki, wai sakon Ummien ne baza ki karɓa ba ko kuma na ya Nu'aym da kika gama cika mini baki kina son tamkar ranki? A sani na dai ba'a ƙin kyautar masoyi haka kuma ta uwa sai dai in kyautar bata yimiki ba?" "Kai Besty ni dai ban faɗa ba, hidimar ce naga kamar zata yi yawa". "Ba wani yawa, kici da hakuri kawai". Nu'aymah ta faɗa kafin muka yi sallama ta juya ta koma ciki ni kuma nayi gaba yaron na biye dani a baya har muka isa gida.

Ɗari biyu na ciro a cikin handbag ɗita na bashi haɗe da yi masa godiya, Mamah da muka samu zaune cikin palour ta kalleni ta ce, "Wannan kayan kuma daga ina?" Gabana ne yayi saurin faduwa don bazan iya ce mata Ya Nu'aym ne ya aiko mini dasu ba don sai ta tambayi meye alaƙata dashi ni kuma hakan ne bana so, dubara ce ta faɗo mini ina cire mayafin dake jikina na ce, "tsaraba ce Nu'ayma ta bani kinga ma har da zobe". Na ƙare zancen ina nunawa Mamah hannuna, shiru ta yi kamar mai wani nazari kafin tace, "To kin gode, amma dai kiriƙa kulawa kin san inda kwaɗai da wulaƙanci..abun da yayanki kullum ke guje miki kenan shiyása kika ga kamar ya fiye takura miki akan yarinyar nan". "In Sha Allah Mamah ba abinda zai faru". Na faɗa ina jawo kayan zuwa gabanta na shiga tonawa, ledar turarukkan da Ummie ta bani na fara buɗewa na nuna mata sai kuma sauran kayan da Nu'aymah ta ce saƙon ya Nu'aym ne, dogoyen abayoyi ne guda uku, sai ƙananan kaya riga da wando set biyu da mayafi ƙwaya uku da kuma takalma set biyu da kananan hand bag sun ji kyau har sun gaji suma ƙwaya biyu, a ɗayar ledar kuma kayan shafa ne da turarukka zasu kai kala bakwai, sai wasu set din kayan bacci masu azabar kyau da kunya sai data rufe ni lokacin dana ciro su, ita dai Mamah kasa cewa komai tayi ganin yawan kayan sai dai ta ce na miƙo mata wayarta dake ɗaki, gabana na faɗuwa na miƙe na ɗauko mata wayar na kawo mata, lambar Nu'aymah na ga ta kira da yake ita Nu'aymah ɗin na kiranta ta gaisheta, bayan sun gaisa tayi mata ya gajiyar dawowa kafin naji tace....

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRA N1000 KI KARANTA HANKALI KWANCE.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

                            32.

"Naga tsaraba Janaam ta zo da ita da kuka bata keda Ummie, shine nace anya Nu'aymah wannan hidimar bata yi yawa ba?" Ban san amsar da Nu'aymah ta bata ba na ji ta ce, "To shikennan Allah ya yi muku albarka, ki mana godiya ga Hajiyar an gode sosai Allah ya saka da alkhairi yabar maku zumunci ku har ɗiyan ɗiya". Na amsa da amin ina sauke ajiyar zuciya don tun dazu ƙirjina sai duka yake yi kar Nu'aymah ta ɓallo mun aiki, sallama sukayi kafin Mamah ta ajiye wayar tana cewa. "Sai ki kwashi kayanki kai ɗaki kin gode Allah ya biya su". "Amin ya Allah, Mamah to ga naki kema". Na faɗa ina cire mata wata doguwar riga da naga ta yi masifar kyau tare da turarukka, dakatar da ni tayi ta hanyar cewa, "A'a bar abunki na gode Allah yasa ki kashe lafiya". "Amin amma Mamah ki karbi ko da turare ne don Allah ko na mayar mata da kayanta." Na ƙare zancen ina turo baki cike da shagwaɓa, murmushi Mamah ta saki tare da maida hankalinta ga tv tana cewa. "To ai shikennan duk yadda kikayi". Ta faɗa tare da ɗaukar remote tana kara volume, turarukkan da Ummie tabani na ajiye mata na haɗa sauran kayan na wuce ɗakina dasu, sai dana rage kayan jikina sannan na zauna abakin katifata, Nu'aymah na fara kira na sake yi mata godiya kafin na juya akalar kiran nawa ga Nu'aym, kamar yadda yake yi aduk lokacin dana kirasa zai katse kiran ne sai ya kira da kansa to yanzu ma hakan ya yi, cike da fara'a na ɗaga ina kai wayar a kunne na, "Ranki shi daɗe barka da rana duk da dai nasan yamma ce a wurin ku" Tamkar ina a gabansa na turo baki cikin sigar shagwaɓa ba tare dana amsa masa tambayarsa ba ina cewa, "Ya Aym me yasa?" "Me yasa me?" Na ji ya faɗa cikin basarwa tamkar bai san abinda ya aikata ba, sake narke masa nayi ina kukan shagwaɓa na ce, "Tambaya fa kake yi tamkar baka san me kayi ba, fisabilillahi wannan hidimar dai kai kanka kasan tayi yawa kuma ka wahalar mini da kanka". Sautin fitar murmushinsa na ji a kunne na kafin yace, "Yanzu wannan shine laifi don na yiwa matata hidima? Ai kuwa ki shirya tanadar hukuncin da zaki riƙa yi mun don yanzu ma nafara".  "Amma.." "Shiii...". Yai saurin katseni yana ci gaba da cewa, "Amma me kyakkyawata? Kaɗan fa ya rage dukkanin wasu responsibilities naki su dawo a hannuna, ina bai fi wata biyu zuwa uku ki kammala karatunki ba ai, kin ga Shikennan da zaran kin gama kuma ba abinda yai saura sai maganar turo iyayena asa mana rana ko ba haka ba?" "Haka ne, amma duk da haka da ka yimana tanadi ba wai tun yanzu kana kashe su ba". "Janaam kenan! aiki fa nake yi kuma kullum biyana ake yi, wane tanadi zan yimana da kike tunanin ban mallaki abinda zan iya yimiki fiye da wannan hidimar ba? Pls kidena wannan zancen you deserve much more than this kyakkyawata, saboda haka karki wani dami kanku don nayi maki wannan yar hidimar". "Tam shi kenan Allah ya ƙara budi da wadata masoyina kuma ya kula mini dakai". Na faɗa ina sake bawa soyayyarsa matsugunni acikin zuciyata, shi kuma ya amsa mini da "Amin, wannan addu'ar yakamata tun farko kiyi mini ba sai mun tsaya yin dogon zance da muka yi ba, ya Mamah ina fatar duk kuna lafiya?" "Lafiya ƙalau, kai ma ina fatan haka?" "Eh to Alhamdulillah duk da ni kam lafiyata har yanzu bata samu ba sai naga na mallakeki". Ban iya amsawa ba sai dai nayi murmushi muka ci gaba da fira muna faranta wa junan mu.

_Bayan kwana biyu_

Duk da irin alwashin dana ɗauka akan Umar Farouk da kuma zumuɗin da nake yi na komawa makaranta na ƙarasa kammala karatuna saboda cikar burina da kuma mafarkina ni da Ya Nu'aym na ganin mun mallaki juna hakan bai hanani jin faduwar gaba ba aduk lokacin dana tuna kwana biyu kacal ya rage na koma school naci gaba da yin rayuwa waje ɗaya da mutumen da nafi tsana akan kowa a duniya, naci gaba da ganinsa yana ganina, ina jin muryarsa yana jin tawa, mutumen da bana fatar ko a mafarki ina ganinsa balle kuma a zahiri, sai dai babu yadda na iya domin ni ko wani nawa baya da ikon hana faruwar hakan tunda yadda na biya kuɗin makaranta haka shima ya biya balle nayi tunanin dakatar dashi daga zuwa makarantar, idan ma samun ikon yin hakan ne to ya fini samun dama kasancewar yana da ɗaurin gindin da komai zai iya aikatawa ko kuma zai iya sa mahaifinsa ya yi masa. Ina wannan tunanin na ji muryar Mamah da Ya Jamil a falo suna magana, hakan yasa ni fitowa don ko wace magana ce na tabbata ta farinciki ce jin yadda muryayinsu ke nuna hakan, ina fitowa na samu falon cike da kayan drinks dasu biscuit da chocolate, kayan dai da al'ada ta tanada da ake kaiwa na na gani ina so, kallon Ya Jamil nai da farin cikin dake shimfiɗe akan fuskarsa ya kasa ɓoyuwa na ce, "Ya Jamil wuɗan nan kayan fa, na waye?" "Naki ne". Ya faɗa yana dariya, wani faɗuwar gaba na ji na faɗa daɓas akan kujer dake kusa dani zaune, ban ankare ba na ji hawaye na sauka akan fuskata jikina ya soma rawa ina jin zancen tamkar a mafarki, yayinda soyayyar mu da ya Nu'aym ta fara dawo mini a ƙwaƙwalwa na shiga tambayar kaina shin ba dai bada aurena ga wani Ya Jamil ya yi ba, da sauri na ciro kaina daga ƙasa ina cewa, "Kamar ya nawa Ya Jamil? Ba dai auren dole zaku yimin ba da wanda zuciyata bata so wanda ban sani ba?" Da mamaki mamah ta kalli

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login