Showing 105001 words to 108000 words out of 157423 words
yabar motsi". Ya faɗa a ɗan hasale, Dole na shiga na zauna na haɗe kaina da cinyoyina ina ci gaba da kuka, shi kuma ya zagayo ya shiga ya tayar da motar, shiru banda ƙarar sautin waƙa da kuka na babu abinda ke tashi acikin mota, muryarsa na ji da alamu waya ce yake yi yana cewa, "Zaku iya kyale sa amma ku daukesa ku kai sa asibiti, idan akwai waya a hannun sa kuyi kokari ku kira kuce kun tsince sa agefen hanya ne kafin ku wuce dashi asibitin". A raina jinjina tsageranci irin na Umar Farouk na yi ina sake jin na tsanesa acikin raina, muryarsa na sake ji cikin sanyi tamkar ba shi ba ya ce, "Amaahh ki kwantar da hankalin ki ba dukan da zai yi ma sa illah nasa ayi masa ba, ɗan jan kunne ne aka yi masa akan ɗauko mini mata da yai acikin motar sa, amma na tabbata daga yau bazai sake ba". Jin abinda ya faɗa ya sa ni ɗago kaina cikin jin haushin sa nace, "Anya kai mutum ne wannan wane irin rashin tausayi da imani ne daga gani na da mutum kasa ai masa irin wannan dukan? Wallah Umar Farouk I hate you". Ɗaga kafada yai haɗe da juyowa ya kalleni sannan ya ɗauke kai yana cewa, "Ni kuma i love you and i forever do". Sake maida kaina cikin cinyoyina nayi ina ci gaba da rera kuka na har muka iso gidan su Aunty Nidrah mai gadi ya buɗe gate muka shiga, yana yin parking na kai hannu da niyar ɓalle marfin na fita na ji shi a rufe, juyowa nayi na kallesa ya ɗauke kai tare da ciro wayar sa ya kira, ji nayi yana cewa, "Sis ki fito ina waje". Daga haka ya katse kiran, ba'a jima ba sai ga Aunty Nidrah ta fito, gefensa ya buɗe ya fita kafin ya zagayo ya buɗe gefen da nike, ina fitowa da gudu na nufi inda aunty Nidrah ke tahowa ina kuka haɗe da rungumeta, zaro idanuwa tayi tana faɗin. "Innalillahi Ya Umar ina kuka haɗu da ita, sister lafiya keke faruwa?" Ta faɗa a ɗan rikice tana ɗago ni daga jikinta, shiru yai bai ce komai ba sai can bayan wasu sakanni na ji ya ce, "Gata nan ki kula mini da ita, Amaahh na da taurin kai sosai amma idan tayi kuskuren sake nuna mini shi next time ko waye na ganta tare dashi ba duka kaɗai zan sa ayi masa ba, komai ma zai iya faruwa dashi". daga haka naji ƙarar tashin motar sa ba tare da aunty Nidrah ta ce komai ba ya fice, wanda hakan yasa na sake fashewa da wani kukan ina rungumeta na ce...
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[8/20, 6:08 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435
09079274454
Masu son Vip su bibiyemu a Arewabook@billysfari https://www.arewabooks.com/chapter?id=689b69e619700231f1502019
47.
"Na shiga uku Aunty Nidrah wallahi na tsane sa bana son sa". Duk da sai da aunty Nidrah ta ji wani abu a ranta na ba daɗi akan kalaman da na faɗa haka ta daure ta ce, "Kiyi haƙuri zo mu shiga ciki". Ta faɗa tare da ja na muka nufi cikin gidan, ɗakinta ta kai ni ta zaunar dani a bakin gado sannan ta fice a ɗakin, bata jima ba ta dawo ta zauna akusa dani tana shafa bayana cike da son lallashi na don har lokacin kuka nake yi, bata iya yimun magana ba har akayi sallama daga bakin kofar ɗakin ta bada izinin shigowa, mai aikin su ce ta shigo ta ajiye tray gaban mu a ƙasa da aka ɗoro lemu da ruwa da cup akai sannan ta fita, gorar ruwan Aunty Nidrah ta ɗauko da cup ta tsiyaya mini ruwan ta miƙo mini, ban yi mata musu ba na karɓa na san ina da buƙatar su ko dan na sanyaya zuciyata dake wani irin zafi, sai da na shanye ruwan tas sannan na miƙo mata cup ɗin ina sauke ajiyar zuciya haɗe da ɗago kai ina kallon ta "na gode". Na faɗa cikin muryar da kana ji kasan na sha kuka, Aunty Nidrah ta karɓa tana sakar mini murmushi tare da mai da cup ɗin ta ajiye tana cewa, "Faɗamun me yake faru tsakanin ki dashi ne?" Ban ɓoye mata komai ba na sanar da ita duk abinda ke faruwa tsakanina da Umar Farouk ina ƙarawa da cewa, "Don Allah Aunty Nidrah ki shaga tsakani na dashi, bana son sa kwatakwata ɗabi'un sa duka basu yimin ba". Murmushi Aunty Nidrah ta yi tana kallona na ɗan haɗe rai ganin kamar bata damu da zancen nawa ba kafin ta ce "Janaam kenan! Me kika ce mun ranar ai dama na faɗa maki idan tayi wari ma ji, idan na fahimce ki dai Ya Umar shi ke son ki ke kuma bakya son sa, to matsalar da kenan shi haka ya taso rayuwar sa bai iya son abu ba, idan yana son abu yi yake kamar zai yi hauka har sai ya samu abun nan tukuna za'a samu lafiya, Momynsa kuma ta daure masa indai abun nan bai fi karfin ta ba ko meye sai ta sama masa shi idan har shi bazai iya sama wa kansa shi ba, ba wai ina cewa abinda Umar Farouk ya yi ba dai-dai ne, ina so in faɗa maki matsalar sa ne saboda kisan hanyar da zaki bi ku rabu dashi cikin sauki tunda baya son sa, Kamar yadda na faɗa maki tun farko cewa mutumen kirki ne to haka yake idan aka bishi ta hanyar lallami domin haka aka saba masa, idan kuma aka ce ta hanyar kafiya za'a bi dashi to fa baza a taba gane masa ba kuma ba lallai ne a kwashe lafiya dashi ba, to ina rokon ki don Allah da ki bashi dama ya nuna miki irin son da yake yi maki, idan kin gamsu shikennan idan baki gamsu ba na tabbata zai haƙura, ni dama tun waccan ranar na fahimci akwai so tsakanin shi dake, kece kawai kika yi mun musu". "Aunty Nidrah bana so na yaudare sa saboda ni akwai wanda nake so". "Ok idan haka ne ina ga ki sanar da Yayanki kawai, damuwar ma yanzu ita ce da kika bari komai ya kwaɓe har hakan, na tabbata Baby bazai kyalesa ba musamman akan wannan dukan daya sa akai wa Salis!" Ta ƙare zancen da 'yar damuwa ɗauke akan fuskarta tana dafe goshi, ni kuwa tunda tayi zancen na sanar da Ya Jameel gabana yai wata irin faɗuwa ina zaro idanuwa, jin nayi shiru ya sata ɗago kai tana cewa, "Sisy ya akai naji kin yi shiru baki ce komai ba? Yanzu ya za'a yi?" "Aunty Nidrah ai dole ki ji nayi shiru, Ya Jameel fa kika ce na faɗawa! Wallahi idan ya ji zancen nan komai zai iya faruwa tsakanina dashi saboda babu jan kunnen da bai yimin ba akan kada na saurari kowa har sai na kammala karatuna gabaɗaya, a cewar sa shi zai taimaka mini wajen maida himma sosai ga karatuna, yanzu Shikennan kwatsam sai naje nace masa wani na bibiya ta shi yayiwa ya Salis duka kuma akwai wanda nake so? No bazan iya ba Aunty Nidrah". "To yanzu ya za'a yi? Kin ga dai ni matsayin ƙanwa nake ga Umar Farouk, ko iyayen mu basa iya dakatar dashi ga duk abinda yake so balle kuma ni, ni wallahi bansan yadda zamu ɓullowa wannan al'amari naku ba". Rufe bakinta ke da wuya wayarta ta hau ruri, tana ɗaukowa taga Ya Jameel ne ke kira ta zaro idanuwa tana nuno mini screen ɗin wayar, ni ma tsoro ne ya kamani don bansan me zan faɗa masa ba idan har ya ji abinda ya faru saboda hakan zai iya tona asiri na wajensa, ina wannan tunanin ashe har Aunty Nidrah ta ɗaga kiran na ji tana cewa, "Hello Baby!" Bansan me yace ba naji ta ce, "Eh gamu tare da ita". Ta miƙo mini wayar da alama cewa yai ta bani, ina karɓa tun kafin naƙarasa da wayar a kunne na na ji murayar sa hankali a tashe yana cewa, "Auta kina lafiya? In jin basu yi miki komai ba? Hope dai ba abinda ya sameki ko?". Ya jefo mini tambayoyin a jere ba tare daya bari na basa amsar ko ɗaya ba, na ɗan saki muryata dake cike da damuwa haɗe da cewa, "Ba abinda sukai mun amma sun yiwa ya Salis duka sosai?" "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un an kirani an faɗa mini a gefen hanya aka tsince sa yanzu haka ina hanyar zuwa asibiti, hankalina ya matuƙar ta shi idan basu yimiki wani abun ba kema shi yasa na kira, na kikkira wayar ki fin shuri baki ɗaga ba shi ya sake tayar mini da hankali, hope you're safe now?". "Ba abinda sukai mun Yaya". Na faɗa idanuwana na sake kawo ƙwalla, cikin yanayi mara daɗi Ya Jamil ya ce, "alhamdulillah amma kin san ko su waye su? Waya kai ki gida?" "Ban san ko su waye ba Yaya sun rufe fuskokin su duka, abun hawa na hau ya ƙaraso dani wajen Aunty Nidrah ɗin". Na tsinci kaina da yin wannan ƙaryar nan take ba tare dana shirya yin hakan ba, Shiru yai kamar mai wani nazari haɗe da cewa, "Shikennan ki kula da kan ki, koma waye bincike zai ganosa". Gabana ne yai wani irin faɗuwa saboda rashin sanin me zai iya faruwa idan har Ya Jameel suka gano wanda yasa aka yi ma Ya Salis wannan dukan kuma ta dalili na, da sauri na ciro wayar a kunne na jin yana cewa na bawa Aunty Nidrah na miƙa mata ina lulawa duniyar tunani ita kuma ta miƙe ta bar ɗakin tana faɗin "Ka kwantar da hankalinka Baby ba abinda ya sameta". Ni dai ban san lokacin data gama wayar ta ba ta dawo ɗakin sai ji nayi ta dafa ni tana cewa, "Janaam tunanin me kike yi?" Kamar zan yi kuka na ce "Ba komai Aunty". "Hmm Janaam kenan, me yasa baki fadawa yayanki gaskiya ba daya tambayeki?" Hawayen dake cikin idanuwana ne suka sauko akan fuskata kafin nace "Baza ki gane ba Aunty Nidrah, wallahi idan ya Jameel yasan akaina hakan ta faru sai ya mun dukan mutuwa". Yar harara ta tai haɗe da cewa "duka fa kika ce Janaam, Sai kace wata yarinya?". "Hmmm!" Kawai na ce don ni kaɗai nasan a wane yanayi nake ciki akan wannan lamarin, daga haka Aunty Nidrah bata sake cewa komai ba ta miƙe ta fice daga dakin, ni kuma na mike na shiga toilet ɗin dake cikin ɗakin nata nayo arwala na fara gabatar da sallar magrib sannan na hada data isha'i saboda ban jima da gama magrib ɗin ba na ji an kira ta isha'i.
A can asibiti kuwa ko da Ya Jameel ya isa ya isko Ya Salis zaune, bai wani ji rauni ba tsabar dai wahala da dukan daya sha ne ya sumar dashi, sosai yake jin jikinsa na tsami, yana hango Ya Jameel ya karfafa kansa yana sakar masa murmushin ƙarfin hali, kallon sa ya Jameel ke yi cike da mamaki kafin yace, "Wai meke faruwa ne haka? Kira na fa akai aka ce an tsinceka a some gefen titi hankalina duka ya tashi saboda na zata an ji maka rauni" Ya Salis yai dariyar da iyakacin ta akan fuskar sa yana cewa, "Ba fa komai alhamdulillah, ina ba abinda ya sami Janaam ko?" Tamkar mai tuhumar sa ya Jameel ya bishi da kallo haɗe da cewa "Babu amma su waye suka tare ku? Ka san su ne?". "Ko ɗaya wallahi Jameel". "Wannan abun akwai ɗaure kai dole musa hukuma aciki a binciko ko su waye, ina su wuɗan da suka kawo ka asibitin ne?" Bakin Ya Salis har rawa yake yi wajen cewa, "No Jameel babu bukatar hakan, wannan ai ɓata lokaci ne ko su waye kawai a bar su na yafe masu". "Kana nufin an dakeka a banza kenan? To wallahi bazai yiwu ba idan kai ka bari ni bazan bari ba, na rasa me yasa al'ummar mu muka dauki rayukan yan uwanmu ba abakin komai ba, me kayi masu ne?" "Ai sai kayi, ka ga muje ka karbo mini sallama mu wuce gida, ba wata hukuma da zan saka a zancen nan tunda mai faruwa ta riga ta faru, ko ma su waye su tafi su suka sani". Ya Salis ya faɗa haɗe da saukowa kan gadon yana ɗan ɗingisa ƙafa, sosai ran Ya Jameel ya ɓaci ba don yana so ba yabar zancen suka nufi office ɗin likita ya basu sallama haɗe da miƙa masu makullin mota da wayar Ya Salis ɗin ya ce wuɗan da suka tsince sa suka kawosa asibitin suka bayar suka ce a ajiye masa idan ya farka a bashi, mamaki ne ya sake kama Ya Jameel ya shiga tambayar kansa to su waye wuɗannan mutane kuma me abokin nasa yai masu da suka tare sa sukai masa duka amma basu ɗauki komai nasa ba, ga Janaam itama basu taɓa ta ba, da wannan tunanin suka karɓi kayan suka yiwa likitan godiya sannan suka fito suka nufi inda suka baro motar Ya Salis ɗin, tafe suke kowa da abinda yake saƙawa a ransa har suka iso, tare suka fito daga cikin motar suka nufi wajen da motar Ya Salis ɗin take ya buɗe ya shiga, ba abinda aka taɓa komai yana nan a yadda yake ya ciro sakon ya Jameel ya miƙa masa yana cewa, "Kaga tunda mun ma iso wajen ka karasa ka kaiwa amarya kayanta kar kayi laifi ni zan wuce gida sai munyi magana gobe" Jiki a sanyaye ya Jameel ya karɓa yana faɗin, "Ba damuwa abokina sai mun yi waya Allah ya ƙara sauki". Ya Salis ya amsa da amin tare da jan motarsa ya bar wajen, shima Ya Jameel ajiyar zuciya ya sauke ya nufi inda tasa motar take ya shiga ya tayar ya bar wajen yana nufar gidan su Aunty Nidrah tare da jujjuya maganganun Salis a ƙwaƙwalwarsa...
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[8/20, 6:08 PM] Jiddah Aliyu: IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
48.
Ran sa a dagule ya ƙarasa gidan su Aunty Nidrah ya kirata a waya ya sheda mata yana waje yana jiran ta, lokacin suna tare da wasu yan uwan Mamie da suka iso ta je gaishe su a masaukin su, bata tsaya ɓata lokaci ba tana gama hausawa dasu ta yi masu sallama ta koma ɗakin ta, Janaam na kwance tana waya da ya Nu'aym da sai faman tsokanar ta yake yi wai itama ta kusa zama amarya tana dariya, bata ce da ita komai ba ta ɗauki mayafinta ta fice, a yadda taga yanayin Ya Jameel ta san har lokacin yana cikin damuwa da kimanin abinda ya samu abokin sa, bayan sun gaisa ta ɗan jingina a jikin motarsa tana cewa. "Baby in jin ba jikin Salis ɗin ba ne yai nauyi? Ka je asibitin da sauki dai ko?" A jiyar zuciya ya sauke haɗe da cewa. "Ki bari kawai Nidrah, ni abun ne ya matuƙar ɗaure mini kai, tare muke da shi yanzu ya ɗauki motar sa ya bar wajen"."Toh! Kace alhamdulillah abun da sauki ba kamar yadda mukai tunani ba, don a yadda Sisy ta shigo gidannan na matuƙar tsorata na zata ma an ji masa rauni ne sosai, ashe da sauki har an sallamo shi daga asibitin?" Ya Jameel ya haɗe tafin hannayen sa waje ɗaya yana ɗan murzawa kafin yai folding ɗin su a kirji haɗe da cewa, "Eh ko da naje asibitin a zaune na samesa, babu inda yaji ciwo kawai dai yace jikinsa ne yake ji ba daɗi, na so saka hukuma acikin zancen nan Nidrah saboda ba daɗi abinda ya faru dashi ta dalilin mu, amma ya ce a'a shi koma su waye ya yafe, abun da kenan ya sake ɗaure mini kai a lamarin, sannan da muka je inda motar take ba abinda aka taɓa ba kuma alamun kai masu attack ne akayi don komai lafiya lau, a iya sanina kuma Salis ba mutum ne shi mai rigima ba kuma bai da abokin faɗa balle nace ko abokanan hamayyar sa ne suka aikata masa haka? Sannan ko su waye ba ɓarayi bane kuma ba kashe sa suka zo yi ba tunda basu yi masa dukan da ko da rauni zai iya ji ba ko karɓe wani abun sa". Shiru Aunty Nidrah ta yi itama tana mamakin abinda ɗan uwan nata yai don kawai yaga mutum da wacce yake so kafin ta ce, "Yanzu dai ko ma meye Baby abar zancen tunda yace ya yafe kuma mu godewa Allah tunda ba abinda ya samesa daga shi har Sis, ubangiji Allah ya tsare gaba". "Amin amma dai binciken na da amfani saboda gaba kar irin haka ta sake faruwa". "In Sha Allah hakan ɗin baza ta sake faruwa ba, ya kake?" Ta ƙare zancen tana tambayar lafiyarsa, ya ɗago kai yana kallon ta haɗe da yin murmushi sannan ya ce, "Yadda amaryata ta ganni haka nike ko tana so taga wani abunne da yafi hakan don tabbatar da lafiyar tawa". Aunty Nidrah ta yi dariya haɗe da sinne kai ƙasa jin yadda ya juyar da zancen tana cewa, "Ni dai ba haka nake nufi ba". "To faɗa mun me kike nufi?" ɗago kai tayi tayi idanuwan su suka sarƙewa waje ɗaya suna aikawa da junansu wani irin kallo da yasa jikinsu duka amsawa, hakan yasa Ya Jameel buɗe gaban mota ya fito mata da kayanta yana miƙa mata yake cewa, "Ungo saƙon ki naga alamar so kike ki jefa ni a wani halin