Showing 3001 words to 6000 words out of 157423 words
*'My Mom'* sannan ya mayar a kunnensa ya faɗa mata sunan police station ɗin, bata jira ya sake cewa wani abun ba ta katse kiran, tafiya tayi mai ɗan nisa kafin ta isa police station ɗin, tana fitowa ta fara haɗuwa da d.p.o ya fito da alama masallaci zai je don an soma kiraye-kirayen sallah magrib, sanin ko ita waye yasa ya nufi wajen ta, fuskarta ba walwala suka shiga gaisawa ta faɗa masa abinda ke tafe da ita, da kanta yayi mata jagora zuwa ciki yanayi mata bayanin abunda ya faru da suka sani. Bata iya cemasa komai ba har suka shiga ciki ya buɗe mata office ɗinsa ta shiga, sallah ya faɗa mata zai je ya yi amma yasa a fito mata dashi sannan ya wuce wajen sallah. Police biyu ne suka rirriƙosa suka shigo office din dashi, gaba-daya an bubbuge masa fuska ta kumbura saboda dukan da yasha, shiyasa ko tafiya baya iya yi sai da aka rikosa don duk dukan daya sha akan ya faɗi waya turosa ya yi kisan yaƙi cewa uffan, da sauri ta taso tana kallon halin da ɗan nata ke ciki idanuwanta na kawo kwalla. "Me kuka yiwa yarona haka? Kenan kashewa kuka tashi yi ko?". Ta faɗa a tsawace tana zaro idanuwa tana kallon police ɗin, gaba-dayansu babu wanda ya tanka mata suka ajiye sa ƙasa sannan suka fice daga cikin office ɗin, kuka ta fashe dashi ta zube ƙasa tana shafa fuskarsa da kamanni da gaba-daya an sauya masa su tana cewa, "Me kaje ka aikata haka ka jefa kanka cikin wannan halin, don Allah kafada mani baka aikata abinda ake zarginka dashi ba". Hannunta ya cire daga kan fuskarsa da take shafawa dake matuƙar yi masa zugi ba tare daya ce komai ba, riƙe hannun tayi sosai tana kallonsa ta ci gaba da cewa, "Kayi mun magana my son me yake faruwa? Da gaske ne ka aikata laifin da ake tuhumar ka dashi?" Nan ma bai ce komai ba ya juyar dakai gefe tamkar baya son jin kalaman mahaifiyar tasa, "Shikenan ko ka aikata ko ma baka aikata ba babu abinda zai sameka, jikina yana fadamun sharri akayi maka don haka ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru". Haka taci gaba da suruttanta har ta ƙarasa ba tare daya ce uffan ba, jiki ba ƙwari ta miƙe don dama tasan za'a yi hakan, zafin ransa bazai taɓa bari ya iya sauraren kowa ba ko da kuwa itace har sai lokacin daya huce, police ne suka sake shigowa suna sanar da ita lokacin da aka ɗibar masu ya ƙare, daga nan suka sake ɗaga sa suka mayar dashi cikin cell suka rufe, ita kuwa kwalla ta share ta dauki handbag ɗinta ta fice daga police station ɗin ba tare data sake yiwa kowa daga cikinsu magana ba..
*******
Tunda ta shigo cikin gidan take kuka ta kasa yiwa kowa bayanin abinda ke faruwa, sai da taga ran mahaifiyar tata ya soma ɓaci sannan cikin shesshekar kuka ta shiga faɗa mata halin da ake ciki, sallallami ta shiga yi tana faɗin."Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un amma wannan yaro ya cuce mu, muna zaman zamanmu zai jawo mana tashin hankali da fitina, yanzu ke kina ganin akwai wanda ya isa ya fitar dake a wannan case ɗin, ai ya bar mana baya da kura don babu wanda ya isa ya kare ki sai Allah". Yayan yarinyar da shigowar sa kenan yace. "Tabbas akwai ƙalubale a gabanmu domin yanzu haka da naje sallah baki ji maganganu dake tashi akan wannan maganar ba, don haka na shiga ban ɗauka ba bata fidda ɓarawo sai dai muyi addu'a ko meye Allah ya kawo mana shi da sauƙi". "To Amin ya rabbi, sai dai ai ita gaskiya gaskiya ce, sannan mai ita yana tare da Allah, wannan kukan ba maganin da zai yimaki tunda mai afkuwa ta afku kuma agaban idanuwan ki, kalubale dai ne ya riga ya fuskanto mu sai muyita addu'a". "Shiyasa kika ga bana son alaƙar ta da mutanen gidan amma kina ganin laifi idan ina cewa ta dena shige masu, to gashi yau abinda shiga gidan ya haifar mata da bamu san inda abun zai tsayawa ba". Ita dai mahaifiyar ta su kasa cewa komai ta yi sai uban tagumi ta buga tana tunanin dole fa idan za'a yi bincike zai zo takan yar tata tunda komai akan idanuwanta ya faru.
ALLAH KA JIKAN IYAYENMU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
3.
Rai a ɓace na yadda taga an maida mata da ɗa ta dawo gida tayi parking ɗin motarta ta kashe ta fito ta fara tafiya tamkar wacce ƙwai ya fashewa aciki, a yanayin da take ciki idan ka kalleta zakayi tsammanin itama dukan tasha saboda yadda gaba daya jikinta ya mutu, sashenta ta nufa da gudu yar tata ta rugo ta rungumeta tana yimata oyoyo, bata iya tanka mata ba sai ma janyeta da tayi daga jikinta ta wuce ɗaki abinta, tamkar yarinyar za tayi kuka tabi mahaifiyar tata da kallo, tasan halinta idan tace zata je ta sameta ɗakinta yanzu nan zata maido duka fushin da take ciki a kanta, don haka sai kawai tabar sashen gabaɗaya ta nufi na matan babanta ta shige cikin yan uwanta, dama tafi samun natsuwa da farin ciki idan tana tare dasu sama da mahaifiyarta dake nunawa kamar ba ita ta haifeta ba.
Saman gado ta jefa mayafinta da jakarta ta zauna gefensa tasa gabaɗaya hannayenta ta tallabe fuskarta dasu. Ya Allah! Ta ina zan fara? Ta tambayi kanta cikin matsananciyar damuwa tana jin baza ta iya zuba idanuwa ba a raba ɗanta da rayuwarsa, koma meye tasan dole ya zama bisa kuskure da tsautsayi yafaru, minti biyu tayi a haka ta miƙe ta shiga toilet ta dauro arwala tayi sallah, tana idarwa bayan tayi addu'a ta miƙe ta shiga kitchen, abinci ta shirya da kanta sanin duk wanda zai girka abinci a gidan idan ba ita ba yaronta baya ci saboda tun yana ƙarami ta sabar masa da haka, bayan ta kammala tafito ta ɗauki wayarta ta kira ƙanenta, bugu ɗaya ya ɗaga ta faɗa masa yazo tana son ganinsa, ba'a jima ba ya iso gidan ya gaisheta sannan suka zauna ta sanar dashi halin da ake ciki, tausayin ta ne ya kama shi duk da koma meye ita ta jawo saboda yadda take nunawa yaron so abun ba'a magana, jajanta mata ya yi kafin ta ɗauko abincin ta bashi tana cewa, "Ka kai mashi abinci kuma ka ƙoƙarta ya samu yaci, akwai magani dana saka aciki ka bashi yasha kafin gobe nasan abinda zan yi don wallahi bazan iya zuba idanuwa ba ɗana na kulle a hannun 'yan sanda suna gana masa azaba, bazan iya ba wallahi". "Shikenan amma kibi komai a hankali kuma kiyi addu'a Allah yayi masa mafita, saboda case ɗin kisa ba abu bane ƙarami". "Koma dai meye ina buƙatar yarona gida akusa dani". "Allah ya kyauta". Ya faɗa sannan ya miƙe ya dauki abincin ya tafi.
Kasancewar yau ita keda girki har goma ta wuce bai gane ta ba yasa ya ɗaga waya ya kirata, kamar bazata ɗaga ba sai kuma tayi wani tunani da sauri ta ɗaga wayar kafin ta katse ta kai a kunnenta ba tare data ce uffan ba, jin tayi shiru yasa shi cewa. "Ina jiran ki?" Kafin tace wani abu ya katse kiran, haushi ne ya kamata don so tayi ta danƙara masa maganar da zata hanasa bacci yau kamar yadda ita da ɗanta suma baza su runtsa ba, sai gashi ya katse kiran, kwafa tayi haɗe da yaye duvet ɗin data lulluɓa dashi ta sauko saman gadon don tuni ita ta kwanta tana faman karanta wasikar jaki don baccin bai iya ɗaukarta ba, babban hijabi ta saka kasancewar kayan bacci ne ajikinta sannan ta nufi sashen maigidan nasu, tura kofa tayi ta shiga sannan ta mayar ta rufe ta jingina aijkin ƙofar ta naɗe hannayenta a kirji fuskar nan babu ɗigon walwala ko ƙire a tattare da ita. "Ƙaraso daga ciki mana". Ya faɗa yana ƙoƙarin canza channel a tv ɗin dake jikin bango a gefen gadon. Sai da ta taushi zuciyarta sosai sannan ta iya cewa. "Kafadi abinda kake son faɗa ina so na kwanta". Hankalinsa ya maido kanta yana ƙare mata kallo kafin yace, "Kizo ki kwanta anan mana". "Bana buƙatar hakan domin babu natsuwa atattare dani". "Ban gane ba?" Ya faɗa yana kafeta da idanuwa, tsananin takaicin yadda yake magana tamkar bai san abinda ke faruwa ba da halin da take ciki ya sata fashewa da kuka tana cewa, "Dole zaka faɗi hakan tunda kai hankalinka a kwance yake kama manta da halin da ɗana yake ciki saboda baka son sa baka ƙaunarsa". Takaici ne ya rufe sa shima cikin zafin rai yace, "Indai akan wannan maganar ce eh ɗin mu barshi a bana sonsa tunda ba jinina bane! Wai me yake damunki ne? Ya kike so nayi shi ɗin ai ba yaro bane, abinda ya aikata yana sane da cewa kuskure ne zai iya jefasa awannan halin da yake ciki amma yaje ya aikata sai kace shi yafi kowa baƙar zuciya, Yanzun nan muka gama waya da d.p.o ya kirani ya faɗa mani sunyi sunyi ya buɗe baki yayi magana ko report ne a dauka yadda za'a iya bada belinsa amma yaƙi, ke da kika je ma ya tabbatar mani da cewa bai tanka maki ba to me kike so ayi masa? Ko zamu zo mu sanya bakin cikinsa ne a zuciya mu mutu?". "Ba haka nake nufi ba, gaba-daya fa ka nuna tamkar ba kai ka haifesa ba, ka nuna kamar ba ɗanka bane shi, ka kuma ƙi ɗaukar wani mataki don taimakonsa, bayan ina da tabbaci akan waya ɗaya idan za kayi za'a sako mani yarona, gabaɗaya tunda na dawo zuciyata ke faman tsuke mani waje ɗaya takeyi idan na tuna yadda suka bubbuge mani fuskar yaro, sun sauyawa masa kamanni ko tafiya baya iyayi da kansa". "Haka ya zaɓa don haka wlh bazan taɓa sa a fito dashi ba, ai zama a cell ko gidan kaso, gyara hali ne, don haka yaje tunda mu mun gaza a matsayin mu na iyayensa su sai su gyara mana halinsa, lauya ɗaya bazan ɗaukar masa ba sannan kuma bazan nemi abada belinsa ba don sunce idan har yakai gobe bai ce komai ba to jibi zasu miƙa sa kotu". "Abun da zaka faɗa kenan? To wallahi bazata yiyu ba kuma idan ka ƙi ɗaukar masa lauya ai ni mahaifiyarsa ina da rai kuma kasan zan iya yin komai, idan nace komai to fa ina nufin komai ciki har da abinda baka yi tsammani ba". Tana gama faɗar haka ta juya ta bar ɗakin. Ji yai gabaɗaya kallon ya fice masa arai sai kawai ya kashe tv ɗin ya shiga kai da kawo a tsakiyar ɗakin, ba wai baya jin damuwa bane shima akan halin da ɗan nasu ke ciki ba ne, kawai baya so ya nuna mata ne saboda ta gano kuskure da girman laifin da take aikatawa na nuna ma yaron son da daya wuce wuri. Da haka ya nemi waje ya kwanta ko zai samu bacci ya ɗaukesa.
*A police station*
Duk wani duka da horo da ake yiwa mai laifi don ya buɗe baki yayi magana ko ya amsa laifinsa anyi masa amma yaƙi furta ko da kalma ɗaya ce, tsabar dukan daya sha gaba-daya idanuwansa basa buɗuwa, tsanin tausayinsa ne ya rufe ƙanen mahaifiyar tasa daya kawo masa abinci, cikin sigar lallashi ya fara yi masa magana, "Bana tunanin a wannan gaɓar taurin kan rashin buɗe baki kafadi gaskiyar magana zai amfaneka, idan kuskure ne ko tsautsayi yakamata kafaɗa don anemi hanyar da zaka iya samun sassauci, kasan irin shakuwar dake tsakaninka da mahaifiyata baza ta iya jurewa ganinka cikin wannan yanayin ba, gashi acikin daƙiƙu yan kaɗan da kamaka duka ta fita hayyacinta, don Allah ka faɗa masu abinda ke faruwa ko belinka ne mu samu bayar kafin agama bincike". Nan ma dai kansa na sunkuye ƙasa bai buɗe baki ya yi magana ba har ƙanen mahaifiyar tasa ya gama maganarsa, haka ma abincin daya kawo masa yayi juyin duniya dashi ya samu yaci ko da kaɗan ne yasha magani amma yaƙi karɓa, a dole haka ya miƙe yabar police station ɗin da abincin ba tare da ko kallon abincin yai ba, sanin halin yayar tasa idan tasan bai ci komai ba zata tashi hankalinta yasa ya samu almajiri akan hanyarsa ta komawa ya rabar masu da abincin..
******
Duk wanda yasan ƙauna da soyayyar dake tsakaninsu da ɗansu dole ya tausaya masu halin da suka shiga ciki bayan tabbatar da cewa lallai sun rasa shi rasawa ta har abada, dukkansu sun shiga cikin matsanancin tashin hankali daya haifar masu da matsananciyar rashin lafiya musamman mahaifin yaron, wanda hakan yasa har akayi komai na mutuwar yaron aka rufesa bai san inda kansa yake ba, ya koma tamkar mutum mutumi yake yi don ya kasa gasgata faruwar lamarin. A ɓangar ɗaya zuciyarsa ta cika da son ɗaukar fansa ta hanyar ganin yasa shima wancan saurayin an kashewa kamar yadda ya kashe masa ɗa, Mahaifiyar yaron ita ta koma lallashinsa tare da bashi baki wanda ita kanta karfin haline kawai takeyi.
A ɓangaren bincike sau biyu yan sanda na zuwa ganawa da wannan matashiyar budurwar, sai dai yanayin data shiga ciki na zazzaɓi mai nauyi yasa basa samun damar yi mata tambayoyin da suka dace sai ɗan abinda baka rasa ba dangane da ita da alaƙar dake tsakaninta da ahalin gidan, wanda yayanta ne ke rakata ayi komai a gama su dawo gida, yau kwana na uku kenan da faruwar lamarin ranar da ake tunanin washe gari za'a tura case ɗin zuwa kotu, zaune take tayi zuru-zuru yayan nata da mahaifiyarta sun tasata agaba ganin ta samu sauƙi, yayan nata yace. "Wai ni abinda ke damuna kuma nake son sani shine, shin meye alaƙar wanda aka kashe dashi wanda ya yi kisan? Shin kinsan shi ne koko a gidan da kika taddashi kika fara ganinsa?" Ɗago kai tayi tace. "Eh Yaya nasan shi". Zaro idanuwa yai haɗe da cewa. "Makashin? Taya?". "Lalle kam tambaye mana ita don ni nafara wani tunani akan lamarin nan, a ina kika san shi?" Sai data share ƙwallah sannan ta fara basu labari....
ALLAH KA JIKAN IYAYENMU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
4.
A gurguje na fito daga cikin ɗakina ina saƙale jakar da nake zuwa makaranta da ita, Amatul-Alim cikakken sunana kenan da iyayena suka raɗa mani amma suna yi mani laƙani da *Janaam* sunan da kenan akafi sani na dashi kuma ake kira na dashi, sauri nake yi riƙe da niƙaf a hannuna ina ƙoƙarin ɗaurawa akan fuskanta don na kusa makara, na kuma tabbata Nu'aymah ƙawata da muke wucewa tare a motarta ta fito tun ɗazu ni kaɗai take jira, hakan yasa ban damu na tsaya karyawa ba na nufi hanya, Muryar Mamah baki tana cewa, "A'ah! Janaam ina zuwa bakiyi kari ba". Da sauri na juyo na ƙaraso wajen ta ina cewa, "Mamah na makara zan tafi sai na dawo, kin san halin mutuniyar tana can tana jirana, yanzun nan zaki ji tafara yimun horn idan ta gaji da jira". "To haka zaki fita baki karya ba". Na juyo kamar zanyi kuka jin muryar yayana dake fitowa daga ta sashensa yana faɗa, cike da girmamawa nace, "Ina kwana Ya Jameel?" Fuskarsa a sake ya amsa mani yana murmushi haɗe da ƙarasowa wajen yana cigaba da cewa. "Lafiya ƙalau Janaam, me yasa kullum bakya son yin kari kafin kifita? So kike yi wani ciwon yazo ya shige ki ki tada mu tsaye?" "Kai ma ka faɗa, kullum faɗan da nake yi da ita kenan akan fita ba kari amma bata ji!" Mamah ta faɗa tana kallona, sai dana daura niƙab ɗin dake hannuna akan fuskata sannan na ɗage sa nasa hannu cikin flate ɗin da Mahmah ta zuba abun karyawar da zata ci na ɗauko yankan soyayyen arish ɗaya na tura abaki sannan na ciro tissue dake kan table ɗin ajiye na goge hannuna ina cewa. "Afuwa ya Jameel gashi naci, in Sha Allah kuma na dena yin hakan bazan sake ba, amma dai yanzu zan tafi saboda 10 zamu shiga lecture kuma mintuna kadan ya rage ta buge, mun kusa makara kuma kasan halin mutuniyar". na faɗa haka tare da ficewa daga falon cikin ɗan ɗaga muryarya ina yiwa Mamah sai na dawo, "To adawo lafiya kiyi addu'a kiyi addu'a kafin kifita?". "Ok Mamah bye". "Bye Janam ki kula da kanki".
Ina fita kai tsaye gidansu Nu'aymah na nufa, cike da natsuwa nake tafiyata har na ƙaraso cikin gidan, dai-dai lokacin Nu'aymah na kokarin fitowa da mota ta maka maka mani harara, dariya na saki daga cikin niƙab ɗina na ƙarasa wajen ina faɗin, "Tuba nake yi muje ko?" Ina shiga sai ga yayanta Nu'aym ya fito cikin shirinsa yana gyara clip ɗin hannun rigarsa, knocking ɗin glass din ƙofarta yai ta danna glass ɗin ya zuge, "Fito ki koma baya Aymah". Ya faɗa fuskarsa ba wasa, Nu'aymah ta ɗan turo baki tana cewa, "School fa zamu je ya Aym". "Na ce baza ku je bane? Fito mana nace". Ina ganin Nu'aymah zata fita nima nafara ƙokarin fita yai saurin dakatar sani, "No ki zauna abunki". Ya faɗa yana zaunawa inda Nu'aymah ta tashi tare tada motar muka bar wajen, cike da natsuwa yake driven duk da yadda ya fahimci sauri muke yi mu isa school, dukkanin mu babu wanda ya iya cewa uffan daga ni har ita, Allah ya gani ba ƙaramar takura naji ba zamana a wajen, a hankali ya juyo yana kallona nayi saurin