Showing 153001 words to 156000 words out of 157423 words

Chapter 52 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

512

pool shi da wasu yan mata ana sharholiya ta sake mikawa alkali tana cewa, "wannan ita ce shedar vedio testimony ɗin mu dake sake tabbatar da cewa wanda ake zargin an kashe bai mutu ba. Bayan haka an dora wannan shari'ar ne ba tare da tabbatar da rahoton hawa ba idan kuma babu gawa babu mutuwa, Idan babu mutuwa to tabbas babu kisa. Wannan ita ce doka, kuma ita ce gaskiya." Ta ɗan yi shiru, tana kallon fuskar alkali sannan ta cigaba da cewa cikin karsashi "Ya mai girma alkali ina so kotu tayi la'akari da tarin hujjojin mu ta fahimci wannan ba kawai kuskuren bincike ba ne, wannan sharri ne, an kuma ƙulla dabara domin a hallaka rayuwar wanda ake zargi ta hanyar ƙarya. Mai girma mai Shari'a, shari’ar kisa tana buƙatar gawa, tana buƙatar tabbataccen rahoton mutuwa. Amma yau ga gaskiya ta bayyana wanda aka ce an kashe yana raye, yana wata ƙasa, an boye shi. Idan haka ne, wane kisa ake tuhuma a kai? Wane gawa aka yi bincike a kai? Wannan shari’a ta zama tamkar ginin da aka tasar a kan iska saboda haka dole kotu ta rushe wannan Shari'a domin doka ba ta ginuwa a kan ƙarya tana ginuwa ne a kan gaskiya da hujja, Saboda haka ina roƙon wannan kotu ta soke wannan shari’a nan take, ta kuma sallami wanda ake zargi daga wannan ƙarya mai nauyi da aka ɗora masa domin ba za a iya ci gaba da bin wanda ake tuhuma da laifin kisa ba alhali wanda ake cewa an kashe yana raye a wata ƙasar."...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/4, 3:54 PM] Queen Qee's💎: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            55.

Da daddare dady na tsakar shirin zai kwanciyar bacci wayarsa ta hau ƙara, Momy dake gefen gado zaune ko kallon wayar bata yi ba duk da tana kusa da ita sai 'yan cike cikenta takeyi a system, Dady ya kara so wajen yasa hannu ya ɗauki wayarsa yana kallonta, gabadaya tun da abunnan ya faru ta sauya masa, yar kulawar da take basa duka ta dena kullum cikin latsar system da buge bugen waya akan matsalar dan gaban goshinta take har yabar part ɗinta, yau kwana huɗu kenan da barin part ɗin nata gashi ya dawo ya taddata akai, wayar ya ɗaga yana kaiwa a kunnensa, ɗaya daga cikin yan sandan police station ɗin da aka kulle Umar Farouk ne ya kira, abinda ya faɗa masa ne ya sashi zaunawa bakin gadon jikinsa a mace, tattaro duka kwarin guiwarsa yai haɗe da cewa, "ok to Shikennan babu matsala Allah yakai rayuwarmu, kuyi duk abinda aka saba yiwa kowa gaskiya daya ce kuma a ko yaushe muna bayanta, za kuma mutabbatar da ita akan ko waye". Shiru ya danyi na sakanni yana sauraren ɗan sandan kafin sukayi sallama. Bayan ya ajiye wayar ya gyara kwanciyar sa yana azo kafafuwansa a samanan gadon, sai daya ja duvet ɗin zuwa saman cikinsa sannan ya zauna yana jingina da kan gadon, kallon Momy yai kafin yace, "police station ne suka kira akan case ɗin yaron nan, ashe mahaifin wancan yaron Dr Abdullahi gwaram ne, babban likitan da ake ji dashi a kaf faɗin jahar nan, ƙwararren likita ne da aka yarda da kwarewar sa wajen aiki wanda hakan ya jawo manya-manyan asibitotan jahohin ƙasar nan ke ruguguwar sa don jagorantar wasu ayyukan tiyata da suka gagare su, wannan baiwar da Allah ya yi masa tasa yake da matukar jin kai da kuma izza ya dauki aikin nasa ba abakin komai ba, don yana da wahala yayi aiki ba'a dace ba, ana haka shekaru biyar da suka wuce yayi aiki a babbar asibitin garin nan na wani patient dake fama da matsalar ruɓewar rabin hanjinsa za'a yi masa dashe, bayan sun shiga tiyata yana kan aiki aka kirasa a waya sai ya tsaya yayi picking Call which is not allowed, to sai wata nurse a wajen tayi kokarin lurar da shi cewa hakan kuskure ne kuma ganganci ne da rayuwar marasa lafiya, daga nan sai ya taso mata da faɗa akan shi zata gwadawa aikinsa to bazai karasa aikin ba sai yaga wanda zai sashi, haka aka taru ana convincing ɗinsa yai hakuri sai dai kafin lokacin marar lafiyar ya mutu, to shine wannan ma'aikaciyar ta taimakawa patient relatives din aka sa ƙararsa a kotun mu, a lokacin an samu kwararrin hujjoji har da na waya da suka tabbatar da ganganci ne don an naɗi bayanan komai acikin waya tunda yanzu zamani ya zo da hatta tiyata akan iya saita Camera a waya a naɗe bayanan yadda aka yi ta, to tanan aka samu hujjar data tabbatar da gangancin da yai wajen rasa rayuwar mara lafiyarsa, nan take kotu ta yanke masa hukuncin rai da rai a tsarin dokar penal code, sannan hukumar su ta medical and dental council tayi punishment dinsa ta hanyar Striking-off dinsa a (sashe na 16 na medical and dental practitioner  Act, cap M8 LFN 2004) wato haramta masa yin aiki a Nigeria aka karɓee license ɗinsa kenan, bayan hakan ma iyalan mamacin sun sake kai ƙara a kotun farar hula wato civil liability aka yanke masa hukuncin biyan diya wanda hakan bazai soke wancan hukuncin na penal code da aka yanke masa ba na rai da rai tunda dai-dai yake da criminal case, kin san idan aka ce wani babba kake a ƙasa kuma kana da daurin gindi komai na iya faruwa, a lokacin babu cin hanci da basu bani ba tare da barazana kala-kala akan na sassauta hukuncin rai da rai dana yanke masa a matsayina na Chief judge a High Court din jahar nan amma naƙi, wannan ya haddasa gaba da tsana mai girma tsakaninsa dani, sai suka ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙasa da yake yana da masu ɗaurin gindi a can sai alkalin CJN ya yanke masa hukuncin biyan diya ga iyalan mamacin da kuma tabbatar dana hukumarsa ta lafiya na karɓe license ɗinsa (Striking-off) wato hanasa aiki a Nigeria aka jaye na kashesa, wannan dalilin yasa ya koma ƙasar waje yana ci gaba da aikinsa, nasan kin tuna hakan ko tunda a lokacin ban ɓoye miki komai ba". Ba tare da momy ta ɗago ta kallesa ba ta ce, "Na tuna amma meye hadin wannan labarin da case ɗin ɗana". "Baki ji me nace ba? Wannan Dr ɗin shi ne mahaifin yaron da aka ce Umar Farouk ya kashe, kuma ya dauki shari'ar ya kaita a kotun mu". Ɗago kai ta yi zuciyarta na wani ɗaci take kallonsa kafin tace, "ka gyara zancenka, ake tuhumar Umar Farouk ya kashe bawai ya kashe kai tsaye ba, ɗana kuma Allah zai yi masa mafita ko a wace kotun ce aka kai shi don nasan haka ba wai zai dameka bane". "Wace irin magana ce wannan Hajiya Maryam, ɗana fa ne kuma nake faɗa maki a kotuna aka shigar da ƙararsa, idan abun bai dameni ba zan sanar dake ne?" "Zan dai sani ko da baka sanar dani ba ko awace kotun ce tunda ɗana ne". "Mtss.." Dady yai tsaki tare da yaye duvet ɗin ya sauko da ƙafafuwansa kasa ya mike ya bar ɗakin, wani irin kuka Momy ta fashe dashi tasan tabbas Indai a kotun mahaifin nasa aka shigar da shari'ar babu ta yadda Umar Farouk zai iya kubuta a hannunsa matukar yana da laifi ba tare daya hukunta sa ba, balle ga abun ya haɗa da adawa da kuma son daukar fansa daga wajen mahaifin yaron, sai data sha kukanta mai isarta da ya zame mata tamkar jiki tunda abun ya faruwa sannan ta share hawayenta ta dauko wayarta, Barrister Nazir ta kira dake matsayin yaya a wajen ta suka yi magana, sun jima akan waya kafin suyi sallama ta mike ta shiga toilet, wanka ta yi ta ɗauro arwala ta fito sallar isha'i ta gabatar tayi shafa'i da wuturi sannan tayi shigar baccinta ta haye akan gado ta jawo system ɗinta ta cigaba da abinda take yi.

Dady kuwa yana fitowa ɓangarensa ya koma ya shiga kai da komowa cikin ɗaki yana tunanin ta ina zai fara, sosai damuwa ta rufesa har yana jin cewa daƙyar zai iya gabatar da shari'ar saboda ba abu bane mai sauki danka ya tsayu a gabanka ka yanke masa hukunci bisa babban laifi irin wannan da kowa yasan hukuncin da doka ta tanada akai shine duk wanda ya kashe a kashesa. Tabbas wannan ya san jarabashi ne ubangijinsa yai yaga zai iya tsaida gaskiya akan kansa kamar yadda yake yiwa sauran al'umma ko bazai iya ba. Ganin bai da mafita al'amarin yasa ya ɗauro arwala ya tada sallah, sallolin dare ya yi sosai yana rokon Allah ya bashi kwarin guiwar wanzar da adalci a tsakanin dansa da kuma Dr Abdullahi ga duk wanda ke da gaskiya ya hana shi yin son kai, karo na farko daya ji hawaye sun sauko masa don Allah ya fishi sanin irin soyayyar da yakewa Umar Farouk, duk wannan abubuwan da yake yi yana yine don saita shi akan hanya tare da nuna masa kura-kuransa daga shi har Momy bawai don baya son sa ba, ji yai tamkar ace mafarki ne yake yi a tashesa, da ya ji daɗi da salama a zuciyarsa, a ranar kasa kwana yai yana addu'ar Allah ya karfafesa ya bashi damar yin wannan shari'ar bisa adalci kamar yadda itama Momy ta kwana zaune saman system ɗinta don ko kadan bata bari ta runtsa ba.

*******

Kwance Abba yake ya lumshe idanuwansa, ji yake yi wutar daukar fansa na ƙara ruruwa a cikin zuciyarsa, baya da wani buri yanzu irin yaga ya raba Chief of judge justice Ibrahim Lawal Shanawa da ɗansa da rayuwarsa na har abada, yadda ya tozarta sa a shekaru biyar da suka wuce shima ya tozarta sa idan ya gagara aiwatar da adalci, yadda ya raba shi da aikinsa shima araba shi da aikinsa don duk yadda zai yi bayan ya yankewa dansa hukuncin kisa da kansa sai kuma yasa an sallamesa a kujerarsa. Nu'aymah ce ta shigo ɗakin jiki a sanyaye tana kallon mahaifinta yadda ya shiga damuwa, da yake idanuwansa a rufe yake sai bai ga shigowarta ba ji kawai yai tana magana, "Abba don Allah kasa asaki Umar Farouk, na tabbata ko menene ya janyo haka dasa hannun waccan munafukar, Abba ita ce tayi sanadiyar duk abinda ya faru ciki har da kauracewar farin cikina, kamata yai itama a kamata". A hankali Abba ya buɗe idanuwansa da suka cika da ɓacin ran kalaman Nu'aymah yana cewa, "Anya kina son dan uwanki Nu'aymah kina kishinsa? kin san wa kike cewa nace a saki bayan ya kashe maki dan uwa? To ki buɗe kunnuwanki da kyau kiji, ko da dukiyata duka zata kare bazan bar wannan shari'ar ba har sai naga an zubar da jinin ɗansa, yadda na tsani yaron haka na tsani ubansa, kuma zuciyata baza ta taɓa yin sanyi ba idan har ba naga sun wulakanta ba, an faɗa masa so hauka ne, me yasa bai kashe yarinyar ba sai ɗana? Me ya kawo shi gidana ma shine abun tambaya". Nu'aymah na hawaye ta ce, "ban sani ba Abba wannan ita kadai ce zata iya amsawa, tasan Umar Farouk farko dashi nake soyayya sai ta kwace mini shi bayan soyayya suke yi da ya Nu'aym, tasan zan iya faɗa masa komai shine ta shirya wannan makircin". "What! Nu'aymah kina nufin wannan yaron shi kike soyayya dashi? Dan makiyan nawa da yai sanadiyar raɓani da aikina a kasata, wanda ba don ina da mutane ba ya yanke mini hukuncin kisa saboda wani abu da bai taka kara ya kawo ba shi kike cewa kina soyayya dashi a gaban idanuwa na? To wallahi ko da hakan bata faru ba ko mutuwa zakiyi bazan taɓa bari ki auresa ba, shashashar banza da bata san inda ke yi mata ciwo ba, zaki fice mun da gani ko sai na saɓa miki". Kuka Nu'aymah ta shiga yi tana bubbuga ƙafafuwa Abba ya taso a fusace ya yo kanta yana masifa wanda hakan ya sata rugawa aguje tabar ɗakin tana ɓare baki, Ummi ce ta shigo ɗakin data haɗu da Nu'aymah tana ƙoƙarin lallashin ta taƙi tsayawa, a bakin kofa ta tsaya ganin yadda ran Abba ɗin yai matukar ɓaci yana faman Safa da marwa a tsakiyar ɗakin tace.

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

*IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            73.

*END*

Shiru ya sake mamaye kotu. Justice Ibrahim ya ɗauki gilashinsa ya saka sannan ya sauke idanunsa akan system din da Momy ta miƙa a matsayin shaida ta biyu yana kallon abubuwan da Nu'ayam yake aikatawa cikin swimming pool ɗin cikin kwanciyar hankali da farinciki, kasa ci gaba da kallon ƙazantar yai ya rufe system ɗin yana sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, "Wannan abu babban lamari ne da kotu zata yi duba zuwa garesa ta yanke hukunci saboda hujjoji ne masu ɗauke da gaskiya da zasu sa wannan shari’a ta rushe gabadaya tazo ƙarshe, amma kafin nan dole ne mu saurari ta ɓangaren masu tuhuma ko suna da abin cewa". duk da rashin ƙwarin gwiwar dake tattare da Barrister Shamsu daya soma yin jiɓi hakan bai hana shi miƙewa ba yana ɓoye sarewar da gwiwowinsa suka yi tare da ƙoƙarin dawo da ƙarfin shari’arsu.Ya ce "Ya mai girma mai shari'a, duk da cewar an kawo hujjar cewa wanda ake ce an kashe yana raye, wannan ba ya nufin cewa ba a aikata laifi ba, akwai yiwuwar an yi ƙoƙarin ɓoye gaskiya, ko kuma an gabatar da shaida da nufin karkatar da hankalin kotu saboda akwai rikice-rikice da yawa da dole mu tantance kafin kotu ta ɗauki matakin yanke wannan hukunci cikin gaggawa." Ya faɗa yana yiwa Momy wani kallo saboda takaicin ƙoƙarin rushe masu plan da take yi sannan ya cigaba da cewa "Don haka Muna roƙon kotu da ta ci gaba da sauraron shaidu domin mu tabbatar da haƙiƙanin abin da ya faru, don kada a yi amfani da wata dabara a ɓoye gaskiyar gaskiya". Murmushi Momy ta saki tare da komawa ta zauna wajen zamant.

Barrister Nazir ya taso cikin natsuwa ya kalli gefen da masu tuhuma suke ya ce "Ya Mai girma mai shari'a, idan mai tuhuma ya yi zargin cewa an kawo shaida don ɓoye gaskiya, to wajibi ne ya kawo hujja da ta nuna haka. Amma tabbas abin da muke da shi yanzu shi ne hujja ta gaskiya cewa mutumin da ake cewa an kashe yana raye, wannan ba baƙon labari ba ne, ba kuma shaci-fadi ba ne, wannan asalin gaskiya ce muka fito da ita a gaban kotu domin bawa mai gaskiya gaskiyarsa, bayan haka muna so kotu ta sake bamu dama a shigo da hujjar gani da ido da masu tuhuma ke ikirarin cewa itace zata tabbatar da wannan kisan ta faru a gaban idanuwanta wato Amatul-Alim Isma'il." "Kotu ta bada dama a shigo da Amatul-Alim Isma'il." cewar Justice Ibrahim yana rafke hannuwa waje ɗaya tare da zubawa ƙofa ido cike da mamaki, shigowa akayi da Janaam kanta na a ƙasa, a bayanta ya Jameel da Mamah ne, sai da aka zo tsakiyar kotu sannan su Mamah suka nemi waje suka zauna aka wuce da Janaam gaban alkali, bayan ta tsaya a inda aka tanada ta kasa ɗagawa ta kalli kowa saboda tashin hankali da take jinta aciki, ɗauke idanuwanta Momy tayi daga kan Janaam ɗin ta ɗora akan Umar Farouk da gaba-daya kamar hankalinsa baya kansa, domin har Janaam ta shigo ta tsayu inda aka tanadar mata dake fuskantar inda yake tsaye bai iya dagowa ba ya kalleta balle yasan da wanzuwar ta a wajen, alkali ya kalli Janaam yace, "Amatul-Alim zakiyi rantsu a gaban kotu zaki fadi gaskiya akan abunda kika sani ba tare da kin ɓoye ba". "na amince zan faɗi gaskiya ya mai shari'a". Ta faɗa muryarta na rawa tare da jin zuciyarta ta kare, don tuni ta tabbatar da cewa ita kanta sai ta fuskanci hukunci don ba tada tabbaci da gaske ko Nu'aym ɗin na raye, nan Justice Ibrahim ya bata rantsuwa tayi sannan ta fara yiwa kotu bayani kamar haka, "Sunana Amatul-Alim, Nu'aym saurayina ne da muka yiwa juna alkawarin aure bayan haduwata dashi a watannin baya da suka wuce daya zo hutu kasar nan..." Nan taci gaba da bada labarin yadda alaƙarta take da Nu'aym da kuma ƙanwarsa Nu'ayma da abinda ya faru tsakaninsu har zuwa lokacin da ya zo yimata fyade ta caka masa wuƙa a ƙoƙarinta na kare kanta, yadda Umar Farouk ya same su acikin gidan da yadda ya karbi laifin akansa tare da yimata barazana akan kada ta fadi gaskiya don ya kareta har zuwan kiran da Nu'ayma ta yi mata ta sanar da ita cewa Nu'aym na raye wanda alkali ya ji recording din dake cikin system din Momy". Ta gama bada labarin cikin tsananin kuka da kuma tashin hankali, jinjina kai Justice Ibrahim yai yayin da zauren kotu ya karaɗe da jimami duk wanda ka kalla sai faman girgiza kai yake cike da ta'ajibi, Barrister Nazir ya sake tsayuwa gaban alkali riƙe da wasu takardu ya ce, "Ya mai girma mai shari'a, Umar Farouk ya je neman Janaam a gidan Dr Abdullahi da ta je wajen kawarta kamar yadda tai bayani, a dai-dai wannan lokacin ne ya ji karar Janaam, hakan yasa ba tare da wani tunani ba ya shiga cikin gidan kai tsaye don kai mata ɗauki ya isko abinda ta aikata wanda shi ne silar ikirarin da yai cewa shi ya aikata kisan, amma yayi hakan ne duka don kare masoyiyarsa, har wayau lokacin daya cire wukar dake jikin Nu'aym ya yi ƙara a wannan lokacin ne iyayensa suka dawo gidan, wanda ya faru ne bisa tsarin Dr. Abdullahi da ɗansa Nu'aym bisa son cimma burin ɗan nasa na yiwa Janaam fyade kamar yadda ta faɗa yanzu.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login