Showing 81001 words to 84000 words out of 157423 words

Chapter 28 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

529

ita bata yi ba, bai fi su uku suka rage a class ɗin ba hakan yasa ta mike jiki a sanyaye ta je tayi submitting, har ga Allah bata so ta fita ajin ganin Janaam ta fita tun bayan fitar Umar Farouk, bata san a wane yanayi idan ta fita zata sake ganin su ba da zai haifar mata da damuwa don hakan sake ƙona mata zuciya zai yi.

Na jima zaune bayan fitowata ina jiran Nu'aymah ta fito mu gaisa tunda tana shigowa malamin ya shigo sai dai har aka gama c.a ɗin kowa ya fito har malamin Nu'aymah bata fito ba, hakan yasa na miƙe na wuce Library saboda akwai abinda nake son dubawa zan ɗan yi research.

Umar Farouk kuwa ganin Nu'aymah bata fito ba ya sa ya koma cikin class ɗin, zaune ya sameta tamkar mai wani nazari ya hau saman desk dinta ya zauna yana kallon ta, mikewa ta yi zata tashi yace, "I hate this Aymah koma ki zauna muyi magana". Tamkar wacce ya yiwa asiri Nu'aymah ta koma ta zauna idanuwanta na cika da ƙwalla ta yi saurin yin ƙasa da kanta, "Am Sorry for that day friendy! Na san ban kyauta ba a yadda nayi miki magana a waccan ranar, sai dai kema kin sani abinda kikai baki kyauta ba". Ɗago kai ta yi jin abinda ya faɗa, ta yi saurin share ƙwallan dake shirin zubo mata ba tare data shirya zubowar su ba tana sakin murmushin karfin hali da iya karawa akan fuska ta ce, "Karka damu a hakan ma ka nuna mini banbanci da tazarar dake tsakanina da Janaam, na kuma tabbata ɗin banyi maka dai-dai ba tunda har ka iya rufe fuska ka faffaɗa mini maganganu ba tare daka yi tunanin yadda zasu cutar dani ba, kaga dole gaba na kiyaye bakina na gode sosai". Ta ƙare zancen tana sake miƙewa, "Bazan ci gaba da dakatar dake ba ko hanaki tafiya don naga hakan kike bukata, amma kiyi tunani akan gobenki da kuma burin ki, wata daya kacal ya rage mu kammala karatun nan, kada ki bari wani abu ya hanaki cimma wannan burin da muka kwashe shekaru muna fafutuka akansa, ni na yarda na yi miki ba daidai ba kema ya kamata ki yarda kin yi kuskure sai duka muyi hakuri mu gyara". Nu'aymah bata ce komai ba shi kuma Umar Farouk yai irin i don't care ɗin nan ya mike yabar class ɗin shima, dama a gabansa Janaam ta wuce Library yana zaune cikin mota har ta shige, yana fitowa sai shima ya nufi Library ɗin, bai nufi inda ya hangota ba sai dai ya nemi kujera ya zauna saiti inda zai iya hangota yana ji tamkar yaje ya sauke mata nikaf ɗinta data ɗage saboda yadda yaga ɗaiɗai kun maza na yawo acikin wajen, wayarsa ya ciro ya dinga zooming camera ɗin yana ɗaukarta hoto ba tare data sani ba kafin can yai saurin ajiye wayar ya miƙe hango wani saurayi ya nufi inda take ya ja kujera ya zauna a gabanta yana kallon ta haɗe da yi mata magana wani irin abu ya ji ya taso masa bai san lokacin daya kawo kansa wajen ba a fusace, Ni kuwa dama duk surutun da saurayin nan keyi ban kula sa ba hankalina na akan littafin da nake karatu, ganin mutum tsaye a saman kanmu ya sa saurayin ɗago kai yana faɗin, "malam lafiya?" Kafin ya rufe baki Umar Farouk ya wanke sa mari, ƙarar marin yasa na ɗago kai, Umar Farouk na gani ya shaƙo wuyan rigar saurayin dake neman yi masa taurin kai, "Menene haka Umar Farouk?" Na faɗa raina a ɓace. Bai tanka mini ba sai daya sake ɗauke saurayin mari har sau biyu, shima sai da ya ji cikin ɓacin rai na sake cewa, "Ka sake shi nace Umar Farouk me yai maka ne?". Sannan ya sake shi da gudu saurayin yabar wajen, Umar Farouk na kallon yadda na haɗe fuska ya juyar da kai gefe ya saki tsaki irin jin haushin nan kafin yace "menene alakarsa dake da zai zo ya zauna a gaban ki yana ƙare maki kallo?" Cike da mamaki nake kallonsa, ikon Allah wannan karfin hali har ina? Na faɗa a raina kafin nace, "Me ya shafe ka aciki? kai yake kallo ko ni?" "Amaahh plsss..." Ya faɗa da ƙarfi kafin yaci gaba da cewa, "Wai kinsan irin tashin hankalin da nake shiga kuwa aduk lokacin dana ganki da wani? Wai me yasa baza ki fahimci irin girman soyayyar da nake yi miki ba?" Ganin kallon mutane ya fara dawowa a kan mu ya sa na ajiye littafin dake hannuna a fusace cikin ɓacin rai na dauki handbag ɗita nabar wajen, dafe kai Umar Farouk yai na tsawon mintuna kafin ya biyo ni a baya, sai dai ko daya fito ko alamar kurarta bai gani ba, ciki ya koma yana dudduba inda zai hango saurayin yai masa shegen duka na ɓata masa mood da yai amma shi ma ba shi ba labarinsa. Haka ya fito wajen rai a ɓace ya wuce class, da yake suna da next lecture bai tafi ko ina ba haka bai sake ganin Janaam ba har sai da lokacin shiga next lecture ɗin ya yi..

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[8/20, 6:08 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

09079274454

Masu son Vip ku bibiyi Arewabook@billysfari ta wannan link https://www.arewabooks.com/chapter?id=689b69e619700231f1502019

                            46.

Bamu gama lecture ba sai ƙarfe shida ina fitowa Ya Jamil na tsayawa gaban department ɗin namu don tun kafin mu shiga na kirasa na faɗa masa yau zan kai six a school ya biyo ya ɗaukeni, ina hango shi na sauke ajiyar zuciya na je na shiga motar ya tayar muka bar wajen.

Umar Farouk na fitowa ya hango an dauki Janaam, ya gane motar yayanta Ya Jamil ce don haka shima sai kawai ya shiga tasa motar ya tayar ya wuce gida, Nu'aymah kuwa dama bata tsaya yin lecture ɗin ba gida ta wuce.

Haka rayuwa taci gaba da gudana tsakanina da Umar Farouk daya zame mani tamkar ƙarfen ƙafa don ba laifi yanzu nakan dan bashi dama muyi magana saboda zancen Nu'aymah da nake so nayi masa, ta ɓangare na kuwa duk hanyar daya bi wajen nuna mani so rufe idanuwana nayi kamar bansan yana yi ba, naƙi nuna masa yarda da soyayyar naƙi kuma karbar sa sai ma zancen Nu'aymah dana shigo masa dashi, ranar ransa ya ɓaci sosai saboda gani yake yi gaba-daya naƙi na fahimci son da yake yi mani sai nuna masa nake Nu'aymah ita tafi dacewa dashi kuma tafi cancanta dashi, da farko ya mayar da zancen nawa tamkar almara don har dariya ya dinga yi yana faɗa cewa har ga Allah shi yasan bai taɓa jin son Nu'aymah ba a zuciyar sa, haka ma Nu'aymah bata taɓa furta masa so ba duk da yasan tana son sa ɗin, muna tsaye a haka Nu'aymah ta zo t wuce mu yana dariya sai dai bata tsaya ba ta wuce abunta, ban ji daɗi ba data gan mu a haka don kar tayi tsammanin wani abu, na kallesa raina ba daɗi nace, "Don Allah Umar Farouk kayi hakuri ku daidaita da Nu'aymah, duk wannan halin da ta shiga saboda kai ne kuma kaima ka san haka, Bazan ɓoye maka ba ina da wanda nake so nake kuma burin aura don mun tsaida magana ni dashi, da zaran na kammala karatu zai turo Iyayensa a tsayar mana da rana, saboda haka ka musanya soyayyar da kake mini da ta Nu'aymah na tabbata zata baka kulawa da farin ciki sosai". Tun da na fara magana naga yana yi mini wani irin kallo daya sa hanjin cikina murɗawa amma na dake har sai dana ƙarasa magana ta, kallona yai da idanuwansa da suka time suka yi jajir ya ce, "Ban shirya sadaukar da kaina ga kowace ƴa mace idan ba ke ba Amaahh, ina son ki kuma babu wanda ya isa ya dakatar dani, shi wancan ɗin da kike zance ai bai kai kudin aurenki a gidan ku ba ko? Haka kuma bai je ya nemi aurenki ba ko? Don haka sai ki bari tsakanin ni da shi a fafata ba wai ki dakatar dani ba, look Amaahh, shi fa so da kike gani makaho ne baya ganin dacewa ko cancantar da kike hangowa tsakanina da Nu'aymah, bazan iya rayuwa da ita ba duk kulawa da farin cikin da zata bani saboda bana son ta ke nake so, zan iya rayuwa tare dake a matsayin bawa mai kula da rayuwarki har karshen rayuwata ko da acikin kunci nake, pls don Allah kada ki dakatar dani yaƙi a soyayyata saboda ko zan rayu sau dubu, na mutu sau dubu a sake halittata sau dabu wallahi bazan dena sonki ba sannan zan iyayin komai akan ki".  "Oh my gosh! don Allah Umar Farouk ka dawo hankalinka, shin ana so dole ne?" Na faɗa a ɗan hasale ganin yaki fahimtata, sai daya ja iska ya furzar ta baki sannan ya kalleni ya ce, "Ba'a yi Amaah amma akanki za'a fara, na rantse miki da Allah idan har wannan lallashin da bibiyar da nake yi maki bai sa kin karbi soyayyata ba sai na hana kowane namiji ya raɓe ki, na rasa wace irin zuciya kike da ita Janaam da sam bakya tausayi halin da nake ciki akan son ki, kin san ba'a so a dole amma shine saboda cikar burin ki kike so na bar ki naso ƙawarki bisa dole? Wannan ai son kai ne Amaah kuma bazan taɓa amincewa dashi ba". "To Shikennan kafita rayuwata Umar Farouk tunda ba'a yi dole". "Saboda ni nake da ikon yin hakan don ni nasa ma kaina soyayyarki? Hmmm! Amaah kenan, ai rayuwarki yanzu nafara shiga har sai kin aje son kai kin karbi soyayyata". Yana gama fadar hakan ya juya yabar wajen, ji nai komai ya kwaɓe mini na rasa ihu zan yi ko kuka, nasan Umar Farouk tunda ya fada bazai yarda da kudirina ba na son maida soyayyar da yake yimin akan Nu'aymah ba to fa bazai yi ba, ban damu da soyayyarsa ta hauka akaina ba don baya gabana, kawai dai Nu'aymah ce damuwata.

Tun daga ranar da hakan ta faru tsakanina da Umar Farouk komai ya sake kwaɓe wa na dena sake masa fuska kamar yadda na faro, duk wani abu da zai hadani dashi na dena shigarsa, a lokacin kuma bukin Ya Jameel ya tashi ana saura sati uku don tun lokacin da aka kai kayan jin magana aka sa ranar buki wata biyu masu zuwa, sosai aka fara shirye-shiryen buki hakan yasa Ya Jameel ya zama busy baya samun lokacin daukoni school, dole ba don ina so ba na koma hawan abin hawa cike da tsoro da kuma fargaba don Umar Farouk ba fa ƙyaleni ya yi ba, duk wani motsina yana akan idanuwan sa haka kuma baya ɗagawa duk wanda ya gani tare dani ƙafa, lokacin ni kuma mabiɗa suka taso mini daga makaranta har gida abun har tsoro da mamaki yake bani, don Umar Farouk bai karya alkawarin sa ba duk wanda ya gani tare da ni sai ya yi masa duka wani lokacin har jini yake fitar masu, daga wannan lokacin zuwa yanzu anyi case da shi a school office ɗin student affairs yafi sau takwas akan dukan dalibai saboda ni, wasu ma ba abinda yake tunani ba ke saka su tsayawa dani sai dai kawai kaji an rufe ka da duka, wannan abun ya sa na shiga damuwa mai yawa na rasa inda zan sa kaina, ga Nu'aymah tun lokacin ta dena kulani, idan na kirata a waya bata ɗagawa haka idan na yi mata text ko magana a WatsApp duka bata amsa mini balle nasa ran samun reply dinta, ta sauya mini sosai fiye da tsammani na, ana bukin Ya Jamil saura sati ɗaya na tura mata da invitation a WatsApp, da alama tayi blocking ɗina shi yasa bai nuna mini sakon ya tafi ba, na tura mata program din da za'a yi ta text message shima ba reply, na ɗauki invitation ɗin da kaina na je har gidan su ban iskota ba na barwa ummie saƙo a bata tunda ko na kira wayarta ba ɗagawa take ba, na kuma tabbata wannan karon sakona ya je hannunta amma har aka fara shirye-shiren da za'a yi ban ga Nu'aymah ba, kasa hakuri nayi da muna waya da ya Nu'aym na faɗa masa don tsakanina dashi babu wata matsala har kudade ya turo mini wai nai hidimar biki na mayar masa na sheda masa Ya Jameel ya yi mun komai, ya nuna mini rashin jin dadinsa amma nayi ta bashi hakuri daga karshe na samu ya hakura.

A ɓangaren Umar Farouk bai koma nema na a waya ba haka kuma baya takurani ko kaɗan da zai sa wani abun ya sake haɗa mu, sai dai fa duk inda za ni ashe ya sa a bibiye ni wani lokacin da kansa ma yake bibiya ta, sau da dama nakan je wuri na samesa agun ko kuma ina gun ya isko ni, hakan ya sa na gano cewa bibiya ta yake yi, ana gobe ranar buɗar kan Aunty Nidrah ta roƙi Ya Jameel da naje can gidan su na kwana, da marece kafin ya dawo sai ya turo wani abokin sa da zai je kaiwa Aunty Nidrah ɗin kayan da zata yi amfani dasu jibi ranar dinner ya ɗauke ni ya wuce dani saboda bazai samu dawowa gida dawuri ba don akwai yan shirye-shiryen da ake yi masa a can gidansa da bai ƙarasa ba, muna kan hanyar mu ta zuwa akan titi kafin mukai gidan su Aunty Nidrah ɗin wasu samari su biyu suka tare mana hanya sun rufe fuskar su da wani bakin abu, Ya Salis ya yi parking tare da fitowa yana tambayar su akan me zasu tsare mana hanya, bai rufe baki ba ya ji saukar icce akansa daga nan suka rufesa da duka, ina cikin motar ina ihun a cecesa sai ganin Umar Farouk nai fuskar nan a haɗe ya buɗe gefena yana cewa na fito, kuka na fashe dashi ina roƙon sa yasa su kyale sa kada su ji masa, sai daya ɗan murza goshin sa kafin yace, "ki fito ki shiga motata shi zai sa nace su kyalesa, amma idan kika ki zan ce suyi ta dukan sa ne har sai sunga ya dena motsi". Kallon yadda suke jibgar Ya Salis nayi na juyo ina kallon Umar Farouk da niyar sake roƙon sa ya kauda kansa gefe, sanin banda wani zaɓi bayan nayi abinda yace yasa na fito ina sharar kwalla ya juya nabi bayansa ina yi ina juyowa ina kallon yaransa dake dukan ya Salis har lokacin, buɗe mani gaban motar ya yi yace na shiga na tsaya naƙi shiga ina cewa, "kace su dena dukan sa don Allah". "Idan baki shiga ba na rantse bazan ce su dena ba sai yabar motsi". Ya faɗa a ɗan hasale, Dole na shiga na zauna na haɗe kaina da cinyoyina ina ci gaba da kuka, shi kuma ya zagayo ya shiga ya tayar da motar, shiru banda ƙarar sautin waƙa da kuka na babu abinda ke tashi acikin mota, muryarsa na ji da alamu waya ce yake yi yana cewa, "Zaku iya kyale sa amma ku daukesa ku kai sa asibiti, idan akwai waya a hannun sa kuyi kokari ku kira kuce kun tsince sa agefen hanya ne kafin ku wuce dashi asibitin". A raina jinjina tsageranci irin na Umar Farouk na yi ina sake jin na tsanesa acikin raina, muryarsa na sake ji cikin sanyi tamkar ba shi ba ya ce, "Amaahh ki kwantar da hankalin ki ba dukan da zai yi ma sa illah nasa ayi masa ba, ɗan jan kunne ne aka yi masa akan ɗauko mini mata da yai acikin motar sa, amma na tabbata daga yau bazai sake ba". Jin abinda ya faɗa ya sa ni ɗago kaina cikin jin haushin sa nace, "Anya kai mutum ne wannan wane irin rashin tausayi da imani ne daga gani na da mutum kasa ai masa irin wannan dukan? Wallah Umar Farouk I hate you". Ɗaga kafada yai haɗe da juyowa ya kalleni sannan ya ɗauke kai yana cewa, "Ni kuma i love you and i forever do". Sake maida kaina cikin cinyoyina nayi ina ci gaba da rera kuka na har muka iso gidan su Aunty Nidrah mai gadi ya buɗe gate muka shiga, yana yin parking na kai hannu da niyar ɓalle marfin na fita na ji shi a rufe, juyowa nayi na kallesa ya ɗauke kai tare da ciro wayar sa ya kira, ji nayi yana cewa, "Sis ki fito ina waje". Daga haka ya katse kiran, ba'a jima ba sai ga Aunty Nidrah ta fito, gefensa ya buɗe ya fita kafin ya zagayo ya buɗe gefen da nike, ina fitowa da gudu na nufi inda aunty Nidrah ke tahowa ina kuka haɗe da rungumeta, zaro idanuwa tayi tana faɗin. "Innalillahi Ya Umar ina kuka haɗu da ita, sister lafiya keke faruwa?" Ta faɗa a ɗan rikice tana ɗago ni daga jikinta, shiru yai bai ce komai ba sai can bayan wasu sakanni na ji ya ce, "Gata nan ki kula mini da ita, Amaahh na da taurin kai sosai amma idan tayi kuskuren sake nuna mini shi next time ko waye na ganta tare dashi ba duka kaɗai zan sa ayi masa ba, komai ma zai iya faruwa dashi". daga haka naji ƙarar tashin motar sa ba tare da aunty Nidrah ta ce komai ba ya fice, wanda hakan yasa na sake fashewa da wani kukan ina rungumeta na ce...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[8/20, 6:08 PM] Jiddah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login