Showing 144001 words to 147000 words out of 157423 words
dauki Alkur'ani taci gaba da karantawa don zuciyarta tayi sanyi, ba ita ta daina karatun ba sai zuwa ƙarfe sha biyu na rana, ko data fito part ɗin Dady har Tauheeda ta gama masu girkin rana ta shiryawa Umar Farouk nashi a basket, ji Momy tayi yau bazata iya zuwa wajensa ba don haka ta kira kanenta ya je ya kai masa, abincin Tauheeda ta zubo mata ta kawo mata itama, bata jin son cin abincin amma ganin ba laifi tayi kokari duk da taliya ce da source ɗin irish da kwai ta haɗa yasa ta ɗan tsakuri kaɗan taci, Tauheeda dake kallo ta tashi ta tattare kwanon ta kai kitchen ta juye sauran a robar take away ta wanke kayan.
Nu'ayma ji tayi zuciyarta ta bushe a halin yanzu bata tsoron duk wani abu da Dady zai yi mata tunda har ya iya sakin Ummie a gaban su, babu haƙurin da bata bashi ba amma yaƙi yi haka itama Ummie da mamaki ya kasa saki na yadda Dady ya iya yanke alaƙar dake tsakaninsa da ita ta tsawon shekaru tsakar rana akan yar su, ta basa hakuri amma yaƙi saurararta, hakan yasa da safe ta haɗa kayanta ta tafi gidan iyayenta cikin ɗacin rai da ƙunar zuciya, goge fuska Nu'aymah tayi ta sauko ƙasa, Nihla na kwance saman kujera taci kukan Ummi ta tafi ta barta har ta gaji "Addah kema tafiya zakiyi?" Ta faɗa tana kallon Nu'ayma dake faman dube-dube tsakiyar palour saye da hijabinta da tazbaha a hannunta don gama salarta ta la'asar kenan "Ina Dady?" Nu'ayma ta faɗa tana kallon Nihla data taso ta nufo inda take, "Ya fita". Ta bata amsa hakan yasa ta ja hannunta tace, "taso mu tafi gun Ummie". Nihla ta zaro idanuwa tana rufe baki, sai da tayi kasa da muryata sannan tace, "ɗazu Dady yace idan na fita zai yanka ni nima na mutu yadda ya Nu'aym ya mutu, ni bazan je ba". Ta kwace hannunta Nu'aymah tayi saurin sake riko hannun tana cewa, "anan ne zamu mutu Nihla idan bamu gudu ba kuma ai Ya Nu'aym bai mutu ba kin manta a waje yake zama? Zo mu tafi". Ta ja hannunta kawai suka fita, suna kaiwa gate Baba Bala mai gadi ya tare su yana cewa Nihla, "Hajiya karama ina zuwa? Alhaji fa yace kar nabar kowa ya fita gidan nan sannan kar nabar kowa ya shigo". Nu'ayma ta ɗan sosa kai kafin tace, "Kaga Bala ba wani jimawa zamuyi ba yanzu nan zamu dawo abu kawai zamu siyowa a can farkon layi". "Inaaa..ai Alkur'ani baza ki cillani a masifa ba, yanzu haka a tsorace nake akan case ɗin da akayi a gidan nan, haka aka tsaidani gaban kotu nai tsuru-tsuru dani" "to karɓa kaje kaika siyo mana". Nu'ayma ta faɗa tana Miko masa kudi dake hannunta "Wa!" Ya faɗa da ƙarfi yana zare idanuwa sannan yaci gaba da cewa, "Yasin babu inda zan daga daga nan, salon kija Alhaji ya dawo yace ban san aikina ba, kawai ki hakura ki koma ciki idan ya dawo yace na buɗe maku ku tafi sai ku tafi amma ni babu inda zanje". Rasa abin cewa Nu'aymah tayi ganin duk dubarar da tayi masa batai aiki ba, juyawa tayi da niyar komawa ciki ranta a dagule sai wata dubara ta sake faɗo mata, da sauri ta juyo ta koma wajensa tana faɗin, "Shikenan to bani aron wayarka sai nakira nace akawo mani sakon sai ka karɓa ka kawo mini a ciki". "Dama-dama haka". Ya faɗa tare da ciro wayarsa ya mika mata, karɓa tayi ta saki hannun Nihla ta koma gefe hannunta na rawa takira lambar Janaam, tana ɗagawa ta sauke ajiyar zuciya ba tare data jira komai za tace ba tace, "Hello Janaam nice Nu'aymah, Janaam ya Nu'aym bai mutu ba yana raye kiyi duk yadda zakiyi ki kuɓutar da Umar Farouk gobe, don Allah kada ki sanar da kowa za'a iya samun matsala, Please kar ki damu da abubuwan da suka faru tsakanin mu gaskiya nake faɗa miki kiyi wani abun cikin sauri kin ji....". Kasa karasa maganar tayi jin tsayawar mota a waje da sauri ta katse kiran ta goge lambar kafin mai gadi ya buɗe tayi kokarin sakata a blacklist ta yadda baza'a iya sake kira ba, tana ɗago kai motar Dady na shigowa, kafin ya yi parking ya fito tayi sauri taba mai gadi wayarsa ba tare da Dady ya kula da hakan ba, sai dai ransa a ɓace ya fito cikin motar ya daka mata tsawa yana cewa, "Ina zaku je?" Ja da baya suka shiga yi Dady ya damko hannun Nu'aymah tasa wata irin ƙara saboda zafinn irin riƙon da yai mata yana cewa, "wato guduwa kike son yi ki je ki tona mini asiri saboda taurin kanki kin manta cewa ni mahaifinki ne?" "Dady babu inda zanje Adda ce tace nazo mu tafi wajen Ummi". Nihla da jikinta ke rawa ta faɗa hawaye na sauko mata, wasu kyawawan maruka Dady ya saukewa Nu'aymah har guda biyu a fuska da suka sa Nihla rugawa da gudu ta koma cikin gida, Nu'aymah kuma ta faɗi ƙasa tana kuka tana rokon Dady ya bar su su tafi wajen Ummi, sake hasalashi tayi ya kai mata wani irin shuri da ƙafa ta dunkule waje ɗaya ya rika hannunta ya shiga janta ƙasa har ya shiga da ita cikin gida, cikin wani ɗaki ya jefata dake nan ƙasa a part dinsa daga ita har Nihla ɗin ya mayar ya rufe da key yana cewa "daga yau baza ku sake fita ba har sai an kammala wannan shari'ar na cimma buri na, shashashar yarinya kawai" ya kare zancen cike da takaicin Nu'aymah yana ji tamkar ba jininsa bace don sa albasa bata biyo halin ruwa ba, dama tuni ya gama hada masu visa dashi da yaransa, kotu na gama yanke hukunci zai kwashe su su koma can waje gabaɗaya da zama, ya san Ummi baza ta taɓa yarda da hakan ba cikin sauki zata iya bashi matsala idan tasan gaskiya shiyása yabi ta wannan hanyar ya fitar da ita cikin rayuwar su, yasan daga ita har iyayenta yanzu ba suda karfin da zasu iya biyar shi wata ƙsar akan ƴaƴanta.
Janaam na jin wayar ta tsinke ta ji wani irin jiri na ɗibarta, me zata yi shin da gaske Ya Nu'aym bai mutu ba? Taya akayi Nu'aymah tasan haka? To make faruwa ne? Ta shiga jerowa kanta tambayoyin da ba tada amsarsu, rudewa tayi ta mike ta nufi dakin Mamah, ta samu Mamah ɗin ta shigawanka don haka ta dawo ɗakinta ta zauna tayi shiru, shin farin ciki ya kamata tayi Nu'aym bai mutu ba ko me zata yi, ko dai takira Ya Jameel ta sanar dashi? Wata zuciyatarta ce tayi saurin gargaɗinta tunawa da abinda Nu'aymah tace, ga alama ita kanta cikin tashin hankali take koda ta kirata gashi ta sake gwada kiran lambar data kirata da ita ɗin bata shiga ba, "Hasbunallahu wani'imal wakeel" ta faɗa tana dafe kanta, Ya Nu'aym na raye how?, Barrister Maryam ta faɗo mata arai ta tuna da kalamanta, tabbas a yanzu tana da bukatar ta faɗa mata gaskiya ta tabbata ita kaɗai ce ya kamata ta sanarwa da wannan zancen, da sauri ta ɗàuki hijab da niƙab dinta ta saka ta fito gabanta na wani irin faɗuwa, ɗakin Mamah ta leƙa har lokacin bata fito wankan ba, kasancewar magrib ta kusa tana so ta samu abun hawa kafin a shiga Sallah yasa cikin ɗan daga murya ta ce, "Mamah zan ɗan je wani waje yanzun nan zan dawo". Tana gama fadar hakan ta fice ba tare data jira me Mamah ɗin zata ce ba, tunanin a wace anguwa gidan Justice Ibrahim Lawal Shanawa yake ta shiga yi, lambar Saleem ta kira da niyar ta tambayesa taji line busy, tsaki tayi kafin can ta tuna da ai sun taɓa firar da Nu'aymah take ce mata a Millineum quarters suke lokacin da take sanar da ita Umar Farouk ko dan gidan waye, napep ta tare lokacin an fara kiraye-kirayen sallar magrib ta faɗa masa inda zata je, tafiyar mintuna goma sha biyar ta kaisu anguwar mai napep ya ajiyeta ta bashi kuɗinsa ya ƙara gaba, bata wani sha wahala ba tana tambayar gidan Justice Ibrahim Lawal Shanawa aka nuna mata, sai data sha tambayoyi sosai don akwai tsaro a kofar gidan kafin aka bari ta wuce bayan ta faɗa masu wajen Barrister Maryam ta zo suka fara kiran Momy suka sanar da ita tayi bakuwa tace su bari ta shigo ba tare da tasan ko wacece ba, gama salarta kenan ta magrib ta tashi ta fito palour, sallama Janaam tayi ta bata izinin shigowa har lokacin fuskar Janaam na cikin niƙab, sai data shigo cikin palourn a bakin kofa sannan ta ɗage niƙab ɗin, wata irin zabura Momy tayi ganita haɗe da miƙewa tana kallon Janaam ɗin itama ita tana kallonta...
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/4, 3:54 PM] Queen Qee's💎: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
69.
"Na zo ne na faɗa miki gaskiyar abinda ya faru a waccan ranar". Cewar Janaam tana sauke idanuwanta ƙasa ganin irin kallon da Momy keyi mata mai cike da mamaki, sai da Momy ta sauke ajiyar zuciya sannan tace, "Bisimillah zaki iya shigowa ciki". Ta ƙare zancen jiki a sanyaye tana nuna mata wajen zama da hannu, bayan Janaam ta ƙaraso ciki ta zauna itama Momy ta koma wajen zamanta ta zauna ta crossing ƙafarta ɗaya akan ɗaya tare da ƙarewa Janaam kallo, jin kaifin idanuwanta a jikinta da Janaam keyi yasa ba tare data ɗago kai ba tafara magana "Sunana Amatul-Alim Isma'il amma ana kirana da Janaam, ina zaune a anguwar Sharaɗa ni da mahaifiyata da kuma Yayana, mahaifina Allah ya yi masa rasuwa tun a shekarun baya, muna rayuwa dai-dai gwargwado ta rufin asiri dan Yayana yana iya kokari a kanmu, gidanmu da gidan Dr Abdullahi gwaram wato mahaifin Nu'aym da Nu'aymah babu wata jayawa gida huɗu ne tsakani, su suna farkon layi mu kuma muna karshen layi, ni da Nu'aymah kawaye ne tun yarinta amma ƙawancen mu bai yi ƙarfi ba sai lokacin da muka shiga jami'a, a lokacin ne kuma bayan yayanta dake zama a kasar waje ya dawo muka fara soyayya dashi, ya so turo iyayensa a gidan mu saboda ya nuna min soyayya kamar ba gobe amma sai naki amincewa duk da yadda nima nake jin soyayyarsa a zuciyata saboda jan kunnen da yayana ya yi mani akan kar na kula kowa sai na kammala karatuna, a haka dai muka ci gaba da soyayyar mu ni dashi a boye ba tare da kowa ya sani ba sai Nu'aymah da niyar ina kammala school zan gabatar dashi a gidanmu a matsayin mijin da nake so na aura, kwatsam sai ga Umar Farouk ya shigo rayuwata ya dinga bibiyata da sunan soyayya tare da kokarin saka shamaki tsakanina da kowane namijin ko da ba wata alaƙa tsakanina dashi, ban yi ƙasa a guiwa ba na sanar dashi ina da wanda nake so kuma na yi masa alkawarin aure amma duk da haka yaki hakura ya ƙyaleni, a ɓangare ɗaya tun farkon shigarmu school ƙawata Nu'aymah ta nuna mani tana sonsa, ta yita nuna masa soyayya amma zuciyarsa bata wajenta, haka nima nayi ƙoƙarin nuna masa irin son da take yi masa amma ya dage lallai shi ni yake so ba ita ba, lokacin da Nu'aymah ta fahimci Umar Farouk na so na sai ta canza mini, duk wata alaƙa, shaƙuwa da amincin dake tsakanina da ita ta manta dasu ta koma ko magana bata yi mini, hakan ya jefani a damuwa matuƙa na kuma ji ba daɗi har yakai na fadawa yayanta halin da ake ciki cike da sa ran zai dai-daita tsakanina da ita amma ban faɗa masa dalilin abinda ya haɗa mu ba, sai dai har muka fara jarabawa muka kammala tsakanina da Nu'aymah ba abinda ya canza, dama ya Nu'aym yayi mana alkawarin cewa zai dawowa lokacin bukin kammala karatun mu, haka nayita zuba idanuwana ganin lokaci na matsowa amma bai ce mini komai ba daga karshe ma sai na dena jinsa a waya, baya kirana idan kuma nima na kirasa bana samunsa, dama Nu'aymah ba daga waya ta take yi ba saboda tana fushi dani da alama ma tayi blocking number ko na kirata ban samu, don haka banyi wahalar nemanta a waya ba har ranar da za'a yi graduation ɗin mu, akwai abokin Umar Farouk wato Saleem, tun a school ya so shirya mu ni da Nu'aymah amma taki amincewa da hakan sai ya kirani washe garin da za'a yi graduation ɗin namu yace yana da kyau ace na biyawa Nu'aymah mun taho tare saboda muba maraɗa kunya dake tunanin cewa namiji ya rabamu ni da ita, da yake nima ina bukatar ji daga gareta da labarin ya Nu'aym sai na amince da shawararsa ina jin yakamata atleast ko da wajen taron nan ne aganmu tare, bayan na shirya na fadawa Mamah cewa zan fara biyawa Nu'aymah a gidansu mu tafi tare in yaso ita da Ya Jameel sai su same mu a can, gabana na faɗuwa na nufi gidan su Nu'aymah, ban tadda mai gadi ba abakin gate don haka kai tsaye sai na nufi cikin gidan tunda ba bakuwar zuwa nike ba na wuce ciki har palorn ƙasa ina sallama, na fi minti biyar a tsaye amma ban ji an amsa min ba kuma ban ji motsin kowa ba, hakan ya sani juyowa da sauri da niyar fita ina tunanin ko sun riga har sun tafi tunda da karfe tara za'a fara gashi ko dana fito gida karfe tara saura kwata, juyowar da zanyi kawai naga mutum a tsaye ya bani baya naji gabana yai wata irin faɗuwa, yana juyowa naga ashe Ya Nu'aym ne hannuwan sa zube cikin aljihun wando sa, kallona yake yi tun daga sama har ƙasa yayin da ni kuma wani irin farin ciki ya rufeni na kasa sanin me zanyi sai murmushi kawai nake sakar masa ina ji tamkar na rungumesa tsabar farin cikin dana tsinci kaina a ciki, nan take sai naga ya fara sauya fuska zuwa wani kalar mutum da bazan taɓa yarda shi bane yana matsowa inda nake, gabana ne ya faɗi cikin dabarbarcewa ina ja da baya a hankali nace, "Y..ya.Ya Nu'aymah yaushe kadawo? Nazo gun Nu'aymah ne mu tafi school tare, am speechless wlh ban ɗauka irin wannan surprised ɗin zaka yi mun ba, ina su Ummie ne da Nihla naji duka gidan tsit ba kowa ko har sun tafi, Besty". Na ɗan faɗa da ɗan ƙarfi ina kallon gefen upstairs ɗin ɗakinta, sai dai ko taku uku ban ƙara ba naga shi agabana tamkar zai rungumeni, ja da baya na sake yi yayi saurin riko hannuna yana lumshe idanuwa haɗe da cewa, "Ina kuma zaki je? Baki yi tsammanin ganina ba saboda kin saki jiki kina cin amanata ko? kin ɗauka tunda ban ganin ki bazan san komai ba akan abinda kike aikata wa ba ko? Me nai miki haka Janaam zaki yaudare ni? Me yasa zaki wofantar da soyayya da kaunar da muka nuna miki ni da yar uwata kici amanar mu?". Kwace hannuna nayi jikina na rawa na ce, "Wace irin magana ce wannan Ya Nu'aym? Cin amana fa kace? Taya za'a yi na iya yin hakan wa ku? Wallahi banci amanarka ba ya Nu'aym saboda duk duniya babu wanda nake so sama dakai, babu wani namijin da nake burin nayi rayuwar aure dashi bayan kai don kai kaɗai ne na mallaka wa zuciya..." Ban ƙarasa ba ya daka mani wata uwar tsawa data sa na ƙarasa haɗe sauran kalamaina cike da tsoro har ina zabura, ya ce "Karya kike yi Janaam Nu'aym ta kirani ta sanar dani komai, zaki ce ne shi wancan ɗan iskan baya daukar ki a motarsa kuna fita, ko zaki ƙaryata cewa kusan ko yau she a school kuna tare dashi? Na rasa dame na rage ki a soyayyata da kika zabi tozartani akan wancan ɗan iskan da babu wanda bai san halinsa ba". Shiru yai yana riƙe ƙugunsa yayin da ni kuma hawaye ke sauko mini a fuska ina jin tsanar tsayawa dana riƙa yi da Umar Farouk da kuma motarsa da Mamien su Aunty Nidrah ta sani shiga wanda duk su suka jawo wannan tuhumar da Ya Nu'aym keyi mini, wanda da zai saurareni zan yi masa bayani dalla-dalla da zai fahimci cewa wallahi hanci amanar sa ba kuma ban yaudare sa ba kamar yadda yake tunani, ina wannan tunanin naji yaci gaba da cewa, "Na ji zafi da kishi matuƙa a zuciyata dana ji cewa kina tare da wancan ɗan iskan duk da bawai don ina son ki ba na ji hakan sai don nasan shi ne zai fara saninki kafin ni, na jima ina jin ƙishirwa da sha'awar ki tun kina yarinya, kyan ki, surar ki da komai naki ba ƙaramin tado mini da sha'awar ki suke yi ba, mun sha yin faɗa da yayanki idan ya ji ina zancen yanayin ƙugunki, breast ɗinki da sauransu acikin anguwa wanda hakan yasa bama shiri dashi sam har nabar ƙasar nan, duk dana haɗu da yan mata kala-kala dake ɗebe mini ƙishirwa ta fannin sha'awa aduk lokacin da naso ban taɓa jin na hakura da taki sha'awar ba da kullum ke sake ta'azzara a zuciya musamman idan na tuna da surar jikinki, na zabi na dawo kasar nan ba tare da sanin kowa ba don na samu na kashe kishirwa ta akanki na koma ba tare da kowa ya sani ba in ba Abbah ba tunda yanzu kin zama yar hannu, shi yasa na haɗa kai da Saleem ya jawo mini ke har gida bayan sun fita ta yadda zanci karena babu babbaka, na kuma aika mai gadi je yai mun wani abu saboda gudun kar a samu matsala, don haka babu kowa agidan nan daga ni sai ke, cikin sauki ki bani