Showing 66001 words to 69000 words out of 157423 words

Chapter 23 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

511

dabba ki sake bari wani ƙato yazo kusa dake har ya zauna tare dake, nan zan nuna maki ainahin ni ko waye". Cike da takaici na ce, "Sannu ubana, na rantse da Allah baka isa ba Umar Farouk, duk abinda kake ji dai-dai nake dakai don baka isa ka tsara mini rayuwa ba, kuma mu zuba ni dakai". Ina gama faɗar hakan nabar wajen raina a ɓace.

Umar Farouk ma bai tsaya komai ba yabar wajen ya nufi Capteria, yana zuwa kai tsaye fridge ɗinsu ya nufa ya ciro gorar ruwa masu sanyi ya kafa abaki saboda yadda yake jin zuciyarsa na turiri haɗe da ƙuna, bazai iya ba ganin Janaam tare da wani waje ɗaya shi yasa ya kasa controlling kansa, wani irin kishinta yake ji mai tsananin kaifin gaske na yankar masa zuciya. Bai ajiye gorar ba sai daya shanye ruwan tas amma duk da hakan bai daina jin abinda yake ji acikin zuciyarsa ba. Ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye a wajen ya samu ya zauna yana dafe kansa duka da hannayensa ya cokale guiwoyin hannuwan akan table ɗin dake tsakiyar kujerun, Ya rasa me ke yi masa daɗi yana son Janaam amma ta ta kasa ta fahimci hakan sai ƙoƙarin abinda zai musguna masa take yi, Meye hadinta da Jabir bayan yasan tunda suka shigo makarantar ko gaisuwa bai taɓa ganin ta haɗata da shi ba sai yanzu saboda ta baƙanta masa har take bashi damar zama a kusa da ita, ya jima a haka kafin ya miƙe ya nufi wajen biyan kudi ya ajiye masu kuɗin sannan ya fice daga wajen.

Ni kuwa cikin class na shige na sha kuka na sosai ba tare dana bari kowa ya gani ba don idan nace abunnan bai bata mini rai ba nayi ƙarya, ina zaune Umar Farouk ya shigo fuska a turniƙe na bishi da hararar da nake da tabbacin bai masan ina yi ba har muka shiga next lecture, daga ni har shi kallo ɗaya zaka yi mana ka fahimci rashin walwala da ɓacin rai a tattare damu saboda abinda ya faru, haka na yita zuba idanuwa ko zan ga Jabir ya shigo don na bashi hakuri amma har aka gama lecture ɗin bai shigo ba, ƴan class ɗin namu na yiwa magana dasu bani lambar sa na samu na kirasa na bashi haƙuri tunda adalilina akayi masa hakan, duk da ni kaina na rasa me yasa Umar Farouk yai wannan abun, sai dai da yake Umar Farouk na zaune cikin ajin duk wanda na tambaya babu wanda ya iya bani lambar Jabir ɗin, takaici ne ya kamani na ɗauki littafaina na fice daga ajin ganin yadda mutum ƙwaya ɗaya ke nema ya hana mana kwanciyar hankali, kai tsaye gate na nufa tunda mun gama lectures, ina tsaye ina jiran abun hawa mutane suka yita wucewa har suka watse, addu'a na shiga yi Allah ya nuna mini na kare karatun nan lafiya ba tare da hawan jinin Umar Farouk ya kamani ba saboda abun nasa ya fara yawa, ina wannan tunanin naga motarsa ya yi parking a gabana, ɗauke kai nayi na mayar gefe ina ci gaba da dube-duben abun hawa ko zan samu, tafiya na fara yi ganin titin na sake zama tsit, abun nan na bani mamaki yadda abun hawa ke daukewa akan hanyar wani lokaci duk da zamowar hanyar kan babban titi take, yadda bai mun magana ba ko daya tsaya haka nima ban ce masa ko uffan ba naci gaba da tafiyata don dama a kufule nake dashi, jira nake yace mun tak nai masa wankin babban bargo, sai Allah ya taimake sa bai ce mun uffan ba sai dai tunda nafara tafiya nake ji yana bina, tsawon wasu mintuna kafin na sake ja na tsaya, shima tsayawa yai sai dai wannan karon parking yai ya fito daga cikin motar ya zagayo ta gefen da nike ya buɗe gaban motar, yi nai tamkar ban ganesa ba tare da tsaida napep ɗin dana hango na kokarin wucewa, har lokacin yana tsaye bai ce uffan ba nayi gaba abina, sai a lokacin na ji ya ce, "Pls Janaam". Ko kallonsa ban yi ba nayi tafiyata na shige napep ɗin na barshi a wajen tsaye. "Ta Allah ba taka ba". Na faɗa bayan na shiga napep ɗin haɗe da sauke ajiyar zuciya.

Umar Farouk ji yai tamkar yai kwalla ganin yadda Janaam ta wofantar dashi har tana tare ƙato a gaban shi ta hau abin hawansa, shuri ya kaiwa tayar motar da ƙarfi yana sakin wata ƙara kafin ya buga marfin motar da ƙarfi ya rufe, kansa ya kifa a saman motar bisa hannayensa, ya zai yi? Me zai yi Janaam ta gane yana sonta? Me zai yi yai mata gwaninta ya burgeta? ya zata fahimci cewa yayi nadamar abubuwan daya yimata ta fahimci shifa masoyinta ne yanzu ba makiyin ta ba....

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU👏

[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

09079274454

                            38.

Ya jima a haka kafin yaja kafafuwansa ya koma cikin mota, da kyar ya iya tayarwa ya nufi gida, kai tsaye ɓangarensa ya wuce yana shiga master bedroom ɗinsa ya fara rage kayan jikinsa sannan ya wuce toilet, shaya ya kunna ruwanta na saukar masa a hankali ya shiga lumshe idanuwa yana tuno Janaam, wani yanayi ya fara tsintar kansa a ciki da bazai ce ga kowane iri yanayi bane, tamkar wanda aka tsikara da tsinke yai saurin buɗe idanuwansa yana share ruwan dake zubo masa a fuska jin wani abu na tsira masa daga cikin mararsa, ya jima cikin ruwan kafin ya iya tattaro ɗan sauran kuzarin daya rage masa ya sama jikinsa sabulu, sai da yai wankansa mai kyau ya gama sannan ya fito ɗaure da towel a kugunsa ɗaya kuma a hannunsa yana tsane jikinsa da su, gaban madubi ya tsaya yana kallon kansa na tsawon mintuna kafin ya shiga gyara kansa da mayukan daya saba amfani dasu, yana gamawa ko kansa bai tsaya tajewa ba sai ma tura yatsun sa da yai a cikin sumar ya barbajeta yana kallon kansa ta cikin madubin yadda sumar ta wani mummurɗe sannan ya jawo best da guntun wando ya saka ya nufi wajen Momy yana latsar wayarsa, Momy na zaune cikin palour Umar Farouk ya shigo ya zauna yana gaisheta har lokacin hankalinsa na kan wayar sa da yake koƙarin kiran Janaam dan haka kurum zuciyarsa ta raya masa da yin hakan ɗin duk da yasan ba lallai ne ta ɗaga ba, sai dai yana kira na farko yaji ana sheda masa wayarr a kashe take. Gefe ya ajiye wayar tare da ɗagowa ya kalli Momy dake tambayarsa lafiya yake ya ɗan shafa kansa haɗe da cewa, "I'm fine Mom, abinci fa?" Momy na kallonsa tare da karantar yanayinsa ta ce, "Bari na kira Tauheeda ta zo ta haɗo maka, amma ka tabbata lafiya kake babu abinda ke damunka kuwa na yanka so cool yarona? Faɗamun me ke faruwa waya taɓa ka?" "Ohhh..Mom! na faɗa miki fa ba koma, bar Tauheeda ta huta bari na shiga kitchen ɗin na haɗa abincin da kaina". Ya kare zancen tare da miƙewa ya nufi kitchen, da mamaki Momy ta bisa da kallo, yau dai ta gansa tamkar ba Umar Farouk ɗinta ba don yai wani irin sanyi, ta shi ta yi tabi bayansa zuwa kitchen ɗin ta samu har ya ɗauko plate da spoon, ƙarasowa ciki ta yi ta buɗe kulolin abincin dake jere don ba'a riga aka kai su can dining ba, "Me zaka ci a ciki?" Mommy ta faɗa tana tambayarsa, Ɗan yatsina fuska yai yana kallon abincin duk da kusan duka favorite food ɗinsa ne kafin ya nuna mata white vegetables rice data sha haɗi da kwai, "Shi kake so". Tamkar wani yaro ya daga mata kai ta zuba masa sannan ta dauko source ɗin anta ta ƙara masa dashi a gefe. Wani bowl ta samu ta zuba masa papper soup aciki ta ɗora a karamin plate haɗe da kwalin lemon exotic data ciro daga cikin fridge sannan ta bi bayansa da shi don tuni shi ya fice, akan dining ta samesa ta ajiye masa tray ɗin agaban sa ta jawo kujera ta zauna tana kallon yadda yake cin abincin tamkar wanda aka yi masa dole, ko rabi bai yi ba ya ture abincin gefe don sam baya yi masa daɗi a baki Momy tayi saurin tura masa bowl ɗin peppe soup din a gabansa tana tsaresa da idanuwa, narke fuska yai nan ma yana kokarin ture bowl ɗin gefe cike da gargaɗi Momy ta ce, "Karka soma". Fuskar sa ɗauke da yar damuwa, ba don ransa ya so ba ya jawo bowl ɗin ya soma ci, Mommy ta sauke wata ƙarfaffar ajiyar zuciya tare da ɗaukar cup ta tsiyaya masa lemun ta ajiye masa, sai da ya dan ci kaɗan kafin ya ɗauki lemun yasha, ba laifi sai daya shanye lemun tas sannan ya ajiye cup ɗin yana cewa. "Thanks Momy". Ta lumshe idanuwa ta buɗe tana kallonsa haɗe da cewa. "What's wrong with you? Na kasa fahimtar wannan yanayin naka gabaɗaya, Umar Farouk Ni mahaifiyarka ce ka faɗamun me ke damunka". Ganin yadda ta damu ya sashi karfafa kansa daga yanayin da yake jinsa aciki ya ce, "Momy na faɗa miki ba komai, kawai dai dan stress ne na school kinsan semester ɗin ƙarshe muke". "Duk da haka, indai ta bangaren karatu ne alhamdulillah ni nasan ba kada wata matsala i trust you ɗari bisa ɗari, Saboda haka don Allah ka kwantar da hankalin ka wa mu kaji ko?" "Shikennan Momy zan yi hakan". ya faɗa murmushi ɗauke akan fuskarsa haɗe da zagayawa ya rungumata yana sauke ajiyar zuciya tare jin soyayyar mahaifiyar tasa mai karfi a ransa saboda irin kauna da kulawar da take bashi. Sun ɗan jima a haka kafin yace mata zai ɗan fita, addu'a ta yi masa shi kuma ya fice ya dauki motarsa ya bar gidan, Inda yake zuwa buga basket Ball da table tennis ya nufa, yana zuwa ya isko Bello peres da suke buga wasar tare, tun kafin ya ƙaraso wajen ya jefo masa ƙaramar kwallon Umar Farouk yai saurin caɓewa da hannu, yana isowa ya ɗauki abun buga ball ɗin suka fara, sau biyu yana kada Umar Farouk don gabaɗaya tunaninsa na wajen Janaam, tunowa da abinda tayi masa ɗazu shiya haifar masa da wani irin ɓacin rai ya shiga tare Ball ɗin da wani irin zafi yana mayar masa ita da ƙarfi, ihu aka sa masu kallon ball ɗin a wajen ana tafi, tun Bello peres na iya tare kwallon har hannuwansa suka soma gajiya saboda yadda Farouk ke bugo masa ita da sauri da sauri ba ƙaƙautawa, daga ƙarshe ma da ya wani bugo masa Ball ɗin da karfi sai a fuskarsa, cikin zafin zuciya Umar Farouk yai jifa da abun buga Ball ɗin ya koma gefe yana dafe kansa, me yake damunka haka gaba-daya soyayyar yarinyar na nema ta lalata maka tsarin rayuwa haɗe da lissafi, wani daga cikin abokan buga wasan nasu ne dake wajen ya ƙaraso riƙe da gorar ruwan swan a hannu ya miƙa wa Umar Farouk yana dafa kafaɗarsa, karɓa yai sai daya shanye ruwan tas yai jifa da gorar yana goge bakinsa da bayan hannu kafin abokin wasar tasa ya ce, "Mutumen hope dai lafiya ko?" Bai tanka sa ba ya miƙe ya shige motarsa yabar wajen, wayar sa ya ciro ya lalubo number Janaam da yai saving da Amaah, kawai so yake yi yaji muryarta ko zai samu zuciyarsa tayi sanyi duk da yasan ba lallai ne ta ɗaga ba, 3 missed call yai mata bata ɗaga ba dama yasan hakan zata faru ya ɗan daki steering yana ji tamkar ya nufi gidan su tunda Nu'aymah ta faɗa masa babu nisa tsakanin su.

Ina zaune tare da Nu'aymah a gidansu don kai tsaye can nace mai napep ya sauke ni saboda na kasa samun natsuwa yanayin da naji Nu'aymah aciki har sai na je na dubata, muna zaune tare da ita naga ana kirana da lambar da kwanakin baya aka yi ta damuna da kira da ita har na gaji, ban ɗaga ba muka ci gaba da firar mu da Nu'aymah data sheda mun cewa taƙi zuwa makaranta ne saboda soyayyar da take yi wa Umar Farouk tunda gabadaya ya kasa fahimtar ta, ganinsa da take yi kullum zai iya haifar mata da damuwa shi yasa take so tayi nesa dashi ko zata samu sassauci a zuciyarta, sanin tarin kaunar da take yi masa ya sa bance komai ba don gudun kada ta ji haushi na, amma na so na bata shawara akan ta kyalesa ta fitar dashi a zuciyarta ta samu ta kammala karatun ta lafiya sannan koma me zata yi tayi, fashin zuwa makarantar ba amfani bane a wajenta saboda abubuwa da dama da za'a yi karatu akai zasu wuce ta. Sake kiran wayar tawa akayi a karo na biyu shima ban ɗaga ba har ta tsinke, ba tare da mai kiran ya hasala ba naga an sake kira, wannan karon tsaki nayi tare da dakile kiran gaba-daya yadda zan dena jin karar wayar, kallona Nu'aymah ta yi haɗe da cewa, "Wa yake kiranki haka besty baza ki ɗaga ba". "Mtss manta da ko waye Besty can ya ƙarasa, tun kafin mu dawo hutu ake damuna da kira da ita, tun ina ɗagawa ba'a magana har na zo na dena ɗagawa gabaɗaya, ko ma waye zai gaji yadena kiran idan yaga ba'a ɗaga ba". Murmushi Nu'aymah ta yi haɗe da cewa, "ki saka lambar a truecaller zaki ga sunan ko waye". "Ai fa kinsan halina Bazan iya ba don wannan biyar diddiƙin ba damuna yai ba, ko waye ma shi ya sani". "Hmm!" Nu'aymah ta faɗa tare da ɗaukar wayar ta ce, "Karanta mun lambar bari na duba maki ko a tawa trucaller ɗin muga ko waye kar abamu labari". Ta faɗa cikin sigar zolaya muka kwashe da dariya haɗe da tafewa". Digit ɗin na karanto mata ta kwafe a wayarta, a take naga ta ɗan sauya fuska da bansan dalilinsa nayin hakan ba, "lafiya?" Na faɗa ina kallonta ta saki murmushi haɗe da cewa, "kin ga wani sunane can ya fito daban don dai ban san mai wannan sunan ba". Ta nuna mani sunan naga ansa devid iliya, dariya na yi haɗe da cewa, "Kin ga ma ashe bayarbene dana ɓata lokacina a banza". "Haka suke fa may be ma wrong number ne ba ke yake nema ba". Nu'aymah ta faɗa tana ɗan jingina kanta a jikin allon kan gadonta tare da rufe idanuwanta, ganin haka yasa ina dariya nace, "Tam kogin soyayyar zaki faɗa kenan besty?, to ni bari na tashi na tafi dama na zo naduba ki ne kuma tunda lafiyarki ƙalau alhamdulillah, zan wuce amma don Allah gobe ki ƙoƙarta ki fito". Na ƙare zancen haɗe da miƙewa ina ɗaukar handbag ɗina da littafaina, mikewa Nu'aymah ta yi itama ta rako ni har bakin gate sannan nace ta koma ni kuma na nufi hanyar gida.

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU

[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

09079274454

                            39.

Nu'aymah na shiga ɗakinta ta faɗa kan gado ta fashe da kuka, wato dai da gaske Umar Farouk ke yi mata jiya daya faɗa mata yana son Janaam ta taya shi bata haƙuri akan abubuwan daya yi mata? Ashe ba tun yanzu yafara son ta ba tuntuni har yana kiran ta awaya shine ita da ɗai rana bai taɓa gwada kiranta ba babu dalili in ba jiya da daddare daya isar mata da wannan baƙin sakon nasa daya hanata bacci ba, Shikennan yanzu ya yake so tayi ne? Ina yake so takai tarin ƙauna da soyayyar da take yi masa? Me yasa zuciyarsa bata zaɓeta ba ta zaɓi Janaam? Me yasa ya kasa hango dacewar sa da ita sai Janaam da a kullum cikin faɗa suke da tsanar juna?. Tambayoyin da kenan ta riƙa yiwa kanta amma ta kasa samun amsarsu. Just a weeks ta dawo kasar nan cike da alwashi da kuma burin bayyanawa Umar Farouk soyayyarta sai gashi nauyin bakin rana ɗaya yasa Umar Farouk ya rigata bayyana mata soyayyar wata a zuciyarsa daban ba ita ba, watan ma ƙawarta da take kira Besty data san ciki da bai ɗinta akan soyayyar da take yi masa, yanzu ya zatayi? Zata yi masa fighting ne wajen Janaam ya samu soyayyarta ita kuma ta wofanta ko zata yiwa kanta fighting ne? A iya sanin ta dai tasan Janaam bata son Umar Farouk kuma ta tabbata har duniya ta naɗe baza ta taɓa sonsa ba, saboda haka zata kyale sa ba tare data bari Janaam ta san itama ta san da zancen ba. Wataƙil idan yaga baya gaban Janaam ɗin zai karbi tata soyayyar daga baya idan ta bayyana masa, da wannan shawarar ta tashi ta share hawayenta ta wanke fuskarta a toilet sannan ta wuce kitchen tana taya ummie aiki. Bayan sun kammala ta koma ɗaki ta samu missed call ɗin Umar Farouk babu adadi a wayarta, wani abu ta ji ya taso ya tokare mata zuciya, bata bi takan kiran ba don tasan dalilin yin sa sannan an riga an kira sallar magrib, sai da ta yi har sallahr isha'i ta watsa ruwa sannan ta fito, wayar ta daka chargy data laƙa ta ɗauko ta bi bayan kiran da Umar Farouk yai mata, ringing ɗaya wayar tayi aka kashe aka kira,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login