Showing 120001 words to 123000 words out of 157423 words

Chapter 41 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

547

aiki ba'a dace ba, ana haka shekaru biyar da suka wuce yayi aiki a babbar asibitin garin nan na wani patient dake fama da matsalar ruɓewar rabin hanjinsa za'a yi masa dashe, bayan sun shiga tiyata yana kan aiki aka kirasa a waya sai ya tsaya yayi picking Call which is not allowed, to sai wata nurse a wajen tayi kokarin lurar da shi cewa hakan kuskure ne kuma ganganci ne da rayuwar marasa lafiya, daga nan sai ya taso mata da faɗa akan shi zata gwadawa aikinsa to bazai karasa aikin ba sai yaga wanda zai sashi, haka aka taru ana convincing ɗinsa yai hakuri sai dai kafin lokacin marar lafiyar ya mutu, to shine wannan ma'aikaciyar ta taimakawa patient relatives din aka sa ƙararsa a kotun mu, a lokacin an samu kwararrin hujjoji har da na waya da suka tabbatar da ganganci ne don an naɗi bayanan komai acikin waya tunda yanzu zamani ya zo da hatta tiyata akan iya saita Camera a waya a naɗe bayanan yadda aka yi ta, to tanan aka samu hujjar data tabbatar da gangancin da yai wajen rasa rayuwar mara lafiyarsa, nan take kotu ta yanke masa hukuncin rai da rai a tsarin dokar penal code, sannan hukumar su ta medical and dental council tayi punishment dinsa ta hanyar Striking-off dinsa a (sashe na 16 na medical and dental practitioner  Act, cap M8 LFN 2004) wato haramta masa yin aiki a Nigeria aka karɓee license ɗinsa kenan, bayan hakan ma iyalan mamacin sun sake kai ƙara a kotun farar hula wato civil liability aka yanke masa hukuncin biyan diya wanda hakan bazai soke wancan hukuncin na penal code da aka yanke masa ba na rai da rai tunda dai-dai yake da criminal case, kin san idan aka ce wani babba kake a ƙasa kuma kana da daurin gindi komai na iya faruwa, a lokacin babu cin hanci da basu bani ba tare da barazana kala-kala akan na sassauta hukuncin rai da rai dana yanke masa a matsayina na Chief judge a High Court din jahar nan amma naƙi, wannan ya haddasa gaba da tsana mai girma tsakaninsa dani, sai suka ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙasa da yake yana da masu ɗaurin gindi a can sai alkalin CJN ya yanke masa hukuncin biyan diya ga iyalan mamacin da kuma tabbatar dana hukumarsa ta lafiya na karɓe license ɗinsa (Striking-off) wato hanasa aiki a Nigeria aka jaye na kashesa, wannan dalilin yasa ya koma ƙasar waje yana ci gaba da aikinsa, nasan kin tuna hakan ko tunda a lokacin ban ɓoye miki komai ba". Ba tare da momy ta ɗago ta kallesa ba ta ce, "Na tuna amma meye hadin wannan labarin da case ɗin ɗana". "Baki ji me nace ba? Wannan Dr ɗin shi ne mahaifin yaron da aka ce Umar Farouk ya kashe, kuma ya dauki shari'ar ya kaita a kotun mu". Ɗago kai ta yi zuciyarta na wani ɗaci take kallonsa kafin tace, "ka gyara zancenka, ake tuhumar Umar Farouk ya kashe bawai ya kashe kai tsaye ba, ɗana kuma Allah zai yi masa mafita ko a wace kotun ce aka kai shi don nasan haka ba wai zai dameka bane". "Wace irin magana ce wannan Hajiya Maryam, ɗana fa ne kuma nake faɗa maki a kotuna aka shigar da ƙararsa, idan abun bai dameni ba zan sanar dake ne?" "Zan dai sani ko da baka sanar dani ba ko awace kotun ce tunda ɗana ne". "Mtss.." Dady yai tsaki tare da yaye duvet ɗin ya sauko da ƙafafuwansa kasa ya mike ya bar ɗakin, wani irin kuka Momy ta fashe dashi tasan tabbas Indai a kotun mahaifin nasa aka shigar da shari'ar babu ta yadda Umar Farouk zai iya kubuta a hannunsa matukar yana da laifi ba tare daya hukunta sa ba, balle ga abun ya haɗa da adawa da kuma son daukar fansa daga wajen mahaifin yaron, sai data sha kukanta mai isarta da ya zame mata tamkar jiki tunda abun ya faruwa sannan ta share hawayenta ta dauko wayarta, Barrister Nazir ta kira dake matsayin yaya a wajen ta suka yi magana, sun jima akan waya kafin suyi sallama ta mike ta shiga toilet, wanka ta yi ta ɗauro arwala ta fito sallar isha'i ta gabatar tayi shafa'i da wuturi sannan tayi shigar baccinta ta haye akan gado ta jawo system ɗinta ta cigaba da abinda take yi.

Dady kuwa yana fitowa ɓangarensa ya koma ya shiga kai da komowa cikin ɗaki yana tunanin ta ina zai fara, sosai damuwa ta rufesa har yana jin cewa daƙyar zai iya gabatar da shari'ar saboda ba abu bane mai sauki danka ya tsayu a gabanka ka yanke masa hukunci bisa babban laifi irin wannan da kowa yasan hukuncin da doka ta tanada akai shine duk wanda ya kashe a kashesa. Tabbas wannan ya san jarabashi ne ubangijinsa yai yaga zai iya tsaida gaskiya akan kansa kamar yadda yake yiwa sauran al'umma ko bazai iya ba. Ganin bai da mafita al'amarin yasa ya ɗauro arwala ya tada sallah, sallolin dare ya yi sosai yana rokon Allah ya bashi kwarin guiwar wanzar da adalci a tsakanin dansa da kuma Dr Abdullahi ga duk wanda ke da gaskiya ya hana shi yin son kai, karo na farko daya ji hawaye sun sauko masa don Allah ya fishi sanin irin soyayyar da yakewa Umar Farouk, duk wannan abubuwan da yake yi yana yine don saita shi akan hanya tare da nuna masa kura-kuransa daga shi har Momy bawai don baya son sa ba, ji yai tamkar ace mafarki ne yake yi a tashesa, da ya ji daɗi da salama a zuciyarsa, a ranar kasa kwana yai yana addu'ar Allah ya karfafesa ya bashi damar yin wannan shari'ar bisa adalci kamar yadda itama Momy ta kwana zaune saman system ɗinta don ko kadan bata bari ta runtsa ba.

*******

Kwance Abba yake ya lumshe idanuwansa, ji yake yi wutar daukar fansa na ƙara ruruwa a cikin zuciyarsa, baya da wani buri yanzu irin yaga ya raba Chief of judge justice Ibrahim Lawal Shanawa da ɗansa da rayuwarsa na har abada, yadda ya tozarta sa a shekaru biyar da suka wuce shima ya tozarta sa idan ya gagara aiwatar da adalci, yadda ya raba shi da aikinsa shima araba shi da aikinsa don duk yadda zai yi bayan ya yankewa dansa hukuncin kisa da kansa sai kuma yasa an sallamesa a kujerarsa. Nu'aymah ce ta shigo ɗakin jiki a sanyaye tana kallon mahaifinta yadda ya shiga damuwa, da yake idanuwansa a rufe yake sai bai ga shigowarta ba ji kawai yai tana magana, "Abba don Allah kasa asaki Umar Farouk, na tabbata ko menene ya janyo haka dasa hannun waccan munafukar, Abba ita ce tayi sanadiyar duk abinda ya faru ciki har da kauracewar farin cikina, kamata yai itama a kamata". A hankali Abba ya buɗe idanuwansa da suka cika da ɓacin ran kalaman Nu'aymah yana cewa, "Anya kina son dan uwanki Nu'aymah kina kishinsa? kin san wa kike cewa nace a saki bayan ya kashe maki dan uwa? To ki buɗe kunnuwanki da kyau kiji, ko da dukiyata duka zata kare bazan bar wannan shari'ar ba har sai naga an zubar da jinin ɗansa, yadda na tsani yaron haka na tsani ubansa, kuma zuciyata baza ta taɓa yin sanyi ba idan har ba naga sun wulakanta ba, an faɗa masa so hauka ne, me yasa bai kashe yarinyar ba sai ɗana? Me ya kawo shi gidana ma shine abun tambaya". Nu'aymah na hawaye ta ce, "ban sani ba Abba wannan ita kadai ce zata iya amsawa, tasan Umar Farouk farko dashi nake soyayya sai ta kwace mini shi bayan soyayya suke yi da ya Nu'aym, tasan zan iya faɗa masa komai shine ta shirya wannan makircin". "What! Nu'aymah kina nufin wannan yaron shi kike soyayya dashi? Dan makiyan nawa da yai sanadiyar raɓani da aikina a kasata, wanda ba don ina da mutane ba ya yanke mini hukuncin kisa saboda wani abu da bai taka kara ya kawo ba shi kike cewa kina soyayya dashi a gaban idanuwa na? To wallahi ko da hakan bata faru ba ko mutuwa zakiyi bazan taɓa bari ki auresa ba, shashashar banza da bata san inda ke yi mata ciwo ba, zaki fice mun da gani ko sai na saɓa miki". Kuka Nu'aymah ta shiga yi tana bubbuga ƙafafuwa Abba ya taso a fusace ya yo kanta yana masifa wanda hakan ya sata rugawa aguje tabar ɗakin tana ɓare baki, Ummi ce ta shigo ɗakin data haɗu da Nu'aymah tana ƙoƙarin lallashin ta taƙi tsayawa, a bakin kofa ta tsaya ganin yadda ran Abba ɗin yai matukar ɓaci yana faman Safa da marwa a tsakiyar ɗakin tace.

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[8/20, 6:10 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            56.

"Wai me ke faruwa ne haka Alhaji? don Allah ka lallaɓa yarinyar nan kana gani su kaɗai suka rage mana". A fusace ya juyo yana faɗin. "Akan justice Ibrahim Lawal Shuwa da ɗansa zan iya jurewa ganinta cikin ko wani irin hali da zata shiga, ni zata zowa da maganar banza don tana shashasha har ta kalli idona tace wai nasa asaki wanda yai sanadiyar raba dana da duniya saboda tana son shi, har yaushe hakan ta faru acikin gidana ban sani ba kuma ba'a sanar dani ba?" "Ban fahimceki ba Alhaji". Ummie ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin tare da zaunawa akan sofa, shiru yai kafin can yace, "Gobe za'a shiga kotu da wannan yaron kuma nasa a shigar da karar a kotun mahaifinsa, shine take roko na wai nasa a sakesa saboda tana son shi kuma ke kin san yadda na tsani mahaifinsa don da a yanzu marayu ake kiran su saboda shi, na sani Nu'aym ya riga ya tafiyarsa kuma bazai dawo ba, shi yasa nake so da kan sa shima ya yankewa yaronsa hukuncin kisan kamar yadda yai mun abaya, ya kuma dandani raɗaɗin da naji akan abinda aka aikatawa ɗana idan da daɗi". "Hakan ai shine dai-dai, ni na rasa wace kalar zuciya ce da yarinyar can da sam bata damu da ɗan uwanta ba tun wancan lokacin da yana raye balle yanzu daya mutu, ba kai ba ko ni da nasan tana soyayya da yaron da tuni na saɓa mata, wallahi bazan taɓa yafe jinin ɗana ya tafi a banza ba kuma abinda kayi shine dai-dai Alhaji". Sun jima suna tattaunawa tare da kwashewa Umar albarka don abun dawo masu sabo ya yi har dare ya raba suna zaune basu kwanta ba..

*******

Washe gari ko da Dady ya tashi wani irin karfi da natsuwa ya ji ya samu a zuciyarsa, sai da yayi duka abubuwan da zaiyi ya gama sannan yayi wanka ya gyara ya wuce kotu lokacin ƙarfe 10:00am na safe dai-dai, a office ya fara tsayawa yayi yan cike-cike kafin ya wuce kotun data cika tayi makil da yan saurarar ƙara, justice Ibrahim shanawa na shiga duk aka mike har sai da ya zauna kafin mutanen wajen suka koma suka zauna suma, sai da kotu tayi tsit na sekanni kafin maga takarda ya miƙe ya karanto ƙararrakin da za'a saurara yau, case ɗin Umar Farouk shine na uku, ƙarar farko ta wasu marayu ce da kanen mahaifinsu ya canyewa gado, ta biyu kuma ta wata budurwa da iyayenta suka gurfanar da saurayinta a gaban kotu da zargin yai wa yarsu ciki, sai ta Umar Farouk da kai tsaye ake tuhuma da aikata kisan kai, cikin ƙwarewa da kuma gogewar aiki justice Ibrahim ya fara gudanar da shari'arsa har aka zo kan ta Umar Farouk, magatakarda ya miƙe ya aske karanto ƙarar kamar haka, "A yanzu samu saurari ƙara akan kisa da ake zargin wani matashi mai suna Umar Farouk Ibrahim da iyayen wani saurayi mai suna Nu'aym Abdullahi Gwaram da hukumar yan sanda ta gabatarwa kotu, inda suke tuhumar saurayin da shiga har cikin gidansu ya aikata kisan kai ga dansu wato Nu'aym Abdullahi Gwaram, hukumar yan sanda tayi iya kokarinta wajen bincike ta kuma tabbatar da tuhumar da ake yi akansa". Tunda aka fara karanto ƙarar Umar Farouk justice Ibrahim ya runtse idanuwa ta cikin glass ɗin idonsa na ƙasa har aka gama, ciro kai ya yi yana gyara zaman gilashin idon sa tare da bada umurni a gabatarwa da kotu wanda ake tuhuma, nan take yan sanda suka shigo da Umar Farouk daure da ankwa a hannunsa, gaba-daya mutanen dake cikin kotun suka juyo suna kallonsa har aka iso dashi wajen da aka tanada da masu laifi ke tsayawa kowa na fadar albarkacin bakinsa saboda an riga an san ɗan justice Ibrahim ne, hatsabibin yaron daya gagari kowa tun daga makaranta har zuwa cikin gari, cike da sanin kokarin mahaifin nasa wasu ke kyautata masa zaton zai yi adalci wajen Shari'a da kuma yanke hukuncin daya dace, yayin da wasu ke faɗar cewa ba lallai ne mahaifin nasa ya iyayin adalci a wannan shiri'ar ba kasancewar ɗansa ne na cikinsa da shi kaɗai Allah ya ba shi namiji, kallo ɗaya justice Ibrahim yai wa ɗan nasa ya dauke kai, sai da yayi yan rubuce rubuce ajikin takardun dake gabansa kafin ya ɗago yace, "kotu na buƙatar lauyan mai ƙara da lauyan wanda ake ƙara su bayyana kansu a gaban kotu". Barrister shamsu da kuma Barrister Aysha sune lauyoyin dake kare wanda ke ƙara shi kuma Umar Farouk babu lauyan dake karesa, hakan yasa kotu ta basu dama suka tashi suka gabatar da kansu kafin su nemi izinin yi masa tambayoyi, har kotu ta basu dama sai ga Barrister Nazir ya bayyana a gaban kotu yana bada hakuri bisa Lattin da sukai tare da neman izinin gabatar da abokiyar aikinsa a matsayin lauyoyin da ke kare wanda ake ƙara, izini kotu ta basu don haka ya je ya shigo da Barrister Maryam Hafiz Hakim wato mahaifiyar Umar Farouk saye da kayanta na lauyoyi, mamaki ne matuka ya kama mutane musamman wudanda suka santa, nan take kotun ta kareɗe ko ina da surutu, shi kansa justice Ibrahim sai da ya girgiza da ganin iyalinsa a wajen ba zato ba tsammani, ya kura mata idanuwa yana kallo, shekaru kusan ashirin da bakwai kenan sharabonsa da ganinta cikin irin wuɗannan kayan sai yau, ajiyar zuciya ya sauke yana tattaro natsuwarsa tare da bubbuga gundumar dake gabansa yana faɗin, "Silent..silent". Sai a lokacin Umar Farouk da yai wani irin baƙi ya ɗago kansa, ido biyu suka yi da Momy fuskar nan tata a haɗe ta kauda kanta gefe, cike da girmamawa kamar yadda Barrister Nazir ya gabatarwa da kotu kansa a matsayin lauyan wanda ake ƙara itama ta fito gaban kotu tana ɗan rissina kanta kadan take cewa, "Ya mai girma mai Shari'a sunana Barrister Maryam Hafiz Hakim, lauyan wanda ake ƙara ina bada hakuri bisa jinkirin da muka yi na bayyana a gaban kotu". Jinjina kai Dady kawai ya iya yi tare da maida kansa ƙasa yayi yan rubuce rubuce yana sake dago kan hade da ba lauyoyin masu ƙara izinin yiwa wanda ake ƙara tambayoyin da suka nemi izini, Barrister Aysha ce ta fara miƙewa ta nufi wajen da Umar Farouk ke tsaye tace, "Me yasa ka kashesa, wane laifin ya yi maka". Cikin zafin rai Momy ta miƙe tana cewa, "objection my Lord, ya kamata abokiyar aikina ta gyara kalamanta akan wanda ake ƙara domin har yanzu tuhumar sa ake yi da aikata kisa ba'a tabbatar daya aikata ba". Justice Ibrahim daya kasa ɗauke idanuwansa akan Momy saboda mamaki yace, "Barrister Aysha ki gyara tambayoyin ki domin har yanzu tuhumarsa akeyi ba'a tabbatar da laifin a kansa ba". rissina kai Barrister Aysha tayi haɗe da cewa, "Sorry my Lord". Sannan ta juya tana kallon Umar Farouk Momy kuma ta koma ta zauna tana jin zuciyarta na tsuke mata waje ɗaya, ji takeyi tamkar ta zura da gudu saboda tsananin kunya amma bazata iya yin hakan ba, baza ta zuba idanuwa ɗanta ya zama tamkar wani marasa gata ba bayan tana da ikon tsaya masa sam bazata iya ba. "Kotu na buƙatar ka sake gabatar mata da sunanka da kuma alakarka da wanda ake tuhumarka daka kashe." Barrister Aysha ta faɗa tana kallon sa, Shiru Umar Farouk ya yi ba tare daya ce komai ba yana kallon ta shima, so uku tana maimaita tambayar Umar Farouk bai yi magana ba, lumshe idanuwa Momy ta yi don dama tasan za'a yi hakan, Barrister shamsu ne ya taso ya kalli Umar Farouk sannan ya kalli Justice Ibrahim ya ce, "Ya mai girma mai Shari'a idan har bazai buɗe baki ya yi magana ba hakan na nufin tabbas ya amince da tuhumar da ake yi masa shi yasa baya da jayayya akai, don haka babu bukatar kotu ta ɓata lokacinta wajen sauraren wannan ƙarar kawai ta yanke masa hukunci dai-dai da laifinsa". Dago kai justice Ibrahim yai haɗe da kallon Umar Farouk ya ce, "Malam Umar Farouk ka ji tuhumar da ake yi maka shin ka amince kai ne ka aikata wannan kisan?" Ba tare da tunanin komai ba ko ɓata lokaci Umar Farouk yace, "Na amince ranka shi daɗe". Cike da tashin hankali Momy ta sake mikewa tana cewa, "Ya mai girma mai Shari'a mu muna da ja a matsayin mu na lauyoyinsa, zai iya yiyuwa an tirsasashi ne ya faɗi hakan ko kuma sanadiyar dukan da hukumar yan sanda tayi masa baya cikin hayyacinsa, muna rokon wannan kotu data bamu dama muje mu binciko hujjojin da zamu kare wanda ake ƙara duba da bamu samu isashhen lokacin yin hakan ba aka gurfanar dashi a kotu". "Objection my Lord, hukumar yan sanda tana da hujjojin da zata gabatar don tabbatar da laifin wanda ake tuhuma kamar yadda yayi ikirari da kansa, saboda haka muna neman izini mu gabatarwa da kotu inspector Ashir don gabatar mata da hujjojin mu". Barrister shamsu ya faɗa cike da girmamawa, "Barrister Maryam zaki iya komawa ki zauna, Barrister shamsu kotu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login