Showing 123001 words to 126000 words out of 157423 words

Chapter 42 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

530

ta bada izinin a shigo da inspector Ashir". Alƙali ya faɗa cike da bada umurni "Mun gode my Lord". Barrister shamsu ya faɗa kafin ya bada izini a shigo da shi, bayan an shigo da inspector Ashir Barrister shamsu ya koma ya zauna, Barrister Aysha ta taso ta nufi inda yake tsaye tace, "Inspector Ashir ko zaka iya sanar da kotu abinda ya faru ranar 19 ga wannan watan da kuma binciken da hukumar ku tayi?" "Kwarai da gaske, da misalin karfe sha biyu na rana an kiramu an sanar damu cewa an samu wani saurayi ya shiga har cikin gidan Dr Abdullahi gwaram ya aikata kisan kai, na debi yarana muka je anguwar muka samu saurayin acikin gidan riƙe da wuƙa a hannunsa sai kuma gawar wani matashi kwance acikin jini tare da mutanen gidan, daga nan sai muka kama wannan saurayin muka tafi dashi police station, ita kuma gawar muka ɗauketa muka je asibiti da ita don ayi boncike, a binciken da muka yi mun samu shatin hannun yaron a jikin wuƙar daya soka ma wancan saurayin ya mutu, sannan a binciken da likitoci suka gudanar sun tabbatar da wuƙar da aka samu a hannunsa da ita aka aikata kisan, mun yi masa tarin tambayoyi ya kuma amsa mana da bakinsa cewa shiya aikata kisan saboda akwai tsama tsakaninsa da yaron, wuɗannan sune bayanan da muka haɗa dana asibiti sai kuma bayanan da muka nada a wajensa". Inspector Ashir ya kare zancen yana miƙawa Barrister Aysha takardun da kuma wayar da aka naɗi bayanan aciki ita kuma ta ba magatakarda ya mikawa alƙali...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[8/20, 6:10 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            57.

Sai da alƙali ya gama dudduba takardun ya kuma saurari bayanan da suka naɗa wajen Umar Farouk sannan ya ɗago ya kalli gefen da su Momy suke ya ce, "lauyan wanda ake ƙara ko kuna da tambayar da zaku yiwa inspector Ashir?". Barrister Maryam ta miƙe ta nufi wajen inspector Ashir tana kallonsa cikin idanuwa ta ce, "Inspector Ashir ka shedawa kotu cewa ko da kuka isa wajen kun samu gidan cike da mutane, ma'ana dai masu gidan da kuma shi wanda ake tuhuma, shin taya kuka tabbatar da cewa shi ɗin ya aikata kisan bayan ba kuda shedar gani da ido lokacin daya sokesa da wuƙar?" "Mun gano hakan ne ta shacin hannunsa". Murmushi ta saki haɗe da juyawa ta nufi wajen da mutane ke zaune, sandar wani dattijo ta ɗauko tana zuwa ta dagata sama kamar zata bugawa Barrister Aysha ita, hakan yasa da sauri Barrister Aysha ta duƙe ƙasa, juyawa tayi ta nufi wajen inspector Ashir ta miƙa masa sandar, tsaye yai yana kallonta ba tare daya karbi sandar ba tace, "ka karba mana". Kallon alƙali yai sannan ya karɓa. Mommy ta tako zuwa gaban alƙali ta ce, "Ya mai girma mai Shari'a, mu ɗauka na bugawa Barrister Aysha wannan sandar sai kuma aka tasa da ajali wato karen kwana, a zahiri nice na aikata kisan amma ga sandar can a hannun inspector Ashir, idan aka je bincike shacin hannunsa za'a gani ba nawa ba shin wa za'a ce ya aikata kisan? a nawa tunanin ganin shacin hannunsa a sandar bai isa ya zama hujjar da za'a tabbatar da cewa shi yai kisan ba idan jami'an tsaro suka zo bincike har sai sun kara da tabbatar da hujjar gani da ido tunda ba shi kadai ne a wajen ba, gamu ga kuma sauran mutane dole a samu wanda yaga lokacin da aka aikata laifin tunda a gaban jama'a ne, to kamar haka ne, tunda ba wanda ake tuhuma kadai aka samu acikin gidan ba to dole mutanen da aka isko tare dashi acikin gidan duka su zamo abun tuhuma don zai iya yiyuwa wani ya aikata kisan ba shi ba, saboda haka muke rokon wannan kotu data daga sauraren wannan Shari'ar har zuwa wani lokacin don samo gamsasshin hujjoji da zata yi amfani dasu". Tana gama fadar hakan ta koma wajen zamanta ta zauna, sai da justice Ibrahim yai yan rubuce-rubuce masu tsayi kafin ya ɗago kai ya kalle su yace, "akwai mai wata tambaya ga Inspector Ashir". Barrister Nazir ya miƙe ya ce, "Ya mai girma mai Shari'a muna rokon kotu data bamu belin wanda ake tuhuma saboda rashin ƙwararan hujjoji akansa". Gyaran murya Justice Ibrahim yai haɗe da ɗago kai yace, "Kotu zata ɗaga sauraren wannan shari'ar sai zuwa ranar shidda ga wani watan, haka kuma kotu na umurtar kowane ɓangare da su zo da ƙwararan hujjojin su a zamana na gaba, kotu ta gamsu da hujjojin data samu daga ɓangaren masu ƙara saboda haka bazata bayar da belin wanda ake tuhuma ba kasancewar an samu hujjoji masu karfi akan wanda ake ƙara, don haka tana umurtar Hukumar yan sanda data ci gaba da tsaresa". Yana gama fadar hakan ya sallami ƙarar aka gabatar da wata, Momy na fitowa suka bi bayan yan sandan da aka sa Umar Farouk bayan motarsu zuwa police station, suna isa suma suna tsayawa da motar su, sai da akayi yan cike-cike kafin a basu damar ganin Umar Farouk, kallo ɗaya yaiwa Momy ya kauda kai yana cewa, "why Momy?". Harara ta maka masa fuskar nan tata ba alamun wasa kafin tace, "Ban zo wajen nan a matsayin mahaifiya ba don haka kar ka kuskura ka kawo mini wasa a aiki na, ina so ka buɗe baki kayi mun bayani me ya kaika gidan da har ake kokarin yima sharrin kisan kai?" Ba tare daya juyo ya kalleta ba ya ce, "waya faɗa maki sharri aka yi mun Momy? Kin fi kowa sani bana magana biyu don haka abinda na faɗa can haka ne, da kin yi shawara dani tun farko da baki dawo wannan aikin ba don bazai taba  kungiyar Dani ga abinda na aikata cikin sanina da kuma hayyacina ba, don Allah Momy ku hutar da kanku ku bari a yanka mini hukunci dai-dai da abinda na aikata.." kafin ya rufe baki cikin ɓacin rai Momy ta daukesa mari tana cewa, "karya kake Umar Farouk ba kaine ka aikata kisannan ba na hango hakan acikin idanuwanka da kuma wannan kafiyar taka, masu aikata laifin kisa guduwa suke yi idan suka aikata, kai me yasa ka tsaya? Masu kashe rai idan an kamasu rauni zukatansu ke yi su nemi rangwame saboda tsoron mutuwa ba wai suce a kashe su ba, idan kaga dama kada kayi magana ni zan binciko gaskiyar da kaina". Tana gama fadar hakan ta mike ranta a ɓace, taurin kan Umar Farouk yai yawa ta rasa a ina ya gadosa don ba haka mahaifinsa yake ba, "Umar Farouk kayi tunani akan mutuwa, kasan ko waye mahaifinka matukar ka kasa faɗa mana gaskiya har ta wancan bangaren suka fimu tarin hujjoji to tabbas da zai yanke maka hukuncin rai da rai ne wanda mu Bama fatan hakan burinmu a kamo mai lafin a hukuntasa dai-dai da laifinsa". Barrister Nazir ya faɗa cike da son convincing ɗinsa,Wani irin fizgo kai Umar farouk yai idanuwansa sun yi jajir saboda zafin marin da Momy tayi masa tare da zafin kalaman Barrister Nazir da yake ganin ina ruwansa a case ɗin, ya shaƙo wuyansa cikin tsananin ɓacin rai yana cewa "You better Stay away from this case kada ka zure da yawa akan case ɗin da uba ne mai yanke hukunci ɗansa kuma mai laifi yayin da soyayyar mahaifiya ta rufe mata idanuwa take ƙoƙarin karesa, go and convince her first tabar wannan zancen domin saboda baza taɓa sauya gaskiyar ba" Umar Farouk ya kare zancen yana tura Barrister Nazir da karfi da kadan ya fadi sannan yabar gun tun mintinan da aka basa basu ƙare ba, sai da Barrister Nazir yai ta sauke numfarfashi tsabar wahalar da yaji kafin ya fice daga police station ɗin rai a ɓace, kasa shiga motar Momy da suka zo tare yai kawai yai tafiyarsa saboda yadda ransa ya ɓaci, tas ta san me yaron nata zai iya aikatawa don haka bata hanasa tafiya ba ta tada motarta tabar wajen itama.

Sai bayan kusan awa uku da isarta gida sannan ta kira Barrister Nazir ta bashi hakuri, tabbatar mata da ba komai yai amma yace ya zare hannunsa a case ɗin ta nemi wani saboda renin Umar Farouk yai yawa, duk yadda tayi ta bashi hakuri haka ya kafe mata bazai yi wannan case ɗin ba kawai tayi hakuri itama, ko kadan bata ji daɗin abinda Umar Farouk ɗin yai ba duk da wai ba faɗa mata Barrister yai ba, amma tasan koma meye yai masa babba ne, tsaki ta ja cikin ƙuncin rai don tunda ta yanke shawarar komawa a bakin aikinta shine ya shige mata gaba yai mata duk abinda ya dace, kama daga kan zuwa sabunta register da kotu wato (Roll of legal practitioners) don tabbatar da sunanta yana cikin register lauyoyi da kotun koli ta Nigeriya wato (supreme court roll), haka ma da taimakonsa ta samu zuwa ta biya kuɗin Bar practicing fees (BPF)  na tsawon adadin shekaru ashirin da bakwai da bata biya ba sanadiyar ajiye aikin da duk shekara lauyoyi ke biya, a tsarin Nigeria akwai bukatar ta halarci wasu kwasa-kwasai kafin komawarta bakin aiki saboda canje-canjen da aka samu lokacin data ajiye aikin wato (mandatory continuing legal education) amma kasancewar a ƙurarren lokaci ne tayi kokarin yin hakan cikin sati ɗaya ta online, da yake tana da kafa kuma aka amince mata don ko abaya jajirtacciyar lauya ce da bata karbar case sai in kana da gaskiya, ta dalilin hakan ne suka haɗu da justice Ibrahim a lokacin bai kai matakin alƙali ba, kasancewar dabi'u da halayyar su sun zo daya da ita yasa ya nemi aurenta, mahaifiyarsa a lokacin tana raye bata so auren ba sai daga baya ta amince bisa sharadin sai ta ajiye aikinta, Mommy na matukar son Dady don haka daya zo mata da zancen ta amince ba don ranta na so ba cike da tsanar mahaifiyar tasa, wannan tsanar ce ta shafi Tauhidi da aka saka mata sunanta wato (zainab) wacce sai bayan rasuwar ta ne ta haifeta.

Barrister Nazir bai tsaya nan ba sai daya taimaka mata ta samu halartar body branchers kamar su (NBA da LPDC) ta tattauna dasu akan 'yan tsare-tsaren da aka sauya, wanda duka tayi wasu abubuwan ne a only, daga karshe ta sake yin rantsuwa akan aikin nata kasancewar ta jima bata yi ba, wanda hakan ya faru ne a ranar case ɗin shi yasa basu samu halartar kotu akan lokaci ba.

Tsaki ta sake yi a karo na ba adadi don bata ji dadin abun ba ko kaɗan, ta kudurta aranta a yadda ta kashe makudan kudade don ganinta dawo bakin aikinta to tabbas sai taga abinda ya turawa buzu naɗi akan yaronta ko da zata hakura da case ɗin...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU

[8/20, 6:10 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            58.

A kotu kuwa cike da natsuwa justice Ibrahim ya kammala sauraren dukkanin ƙararrakin da aka kawo ya kuma yanke hukunci ga wasu wasu kuma ya ɗaga saurarensu sai zuwa nan da sati biyu masu zuwa kamar dai nasu Umar Farouk, bayan ya dawo office wani irin zufa ne ya keto masa ya cire rigar Alkalai dake jikinsa ya rataye, dama abunda Momy ke nufi kenan da tace zata bi duk hanyar da zata bi ta samawa danta mafita? To yaushe duk hakan tafaru bada saninsa ba kuma bada izinina ba? Yasan ko waye ita tun a shekarun baya, yana da wahala a ja da ita a case ayi nasara duk da a lokacin tana bin bayan masu gaskiya ne saɓanin yanzu da ƙarara tun a karon farko alamu suka nuna tana goyon bayan mara gaskiya ne, soyayyarta ga ɗanta ta rufe mata idanuwan hango gaskiya tana ƙoƙarin yin komai idanuwa a rufe. Iska ya ja ya furzar ta bakinsa yana ci gaba da kai da komowa cikin dakin, yana son ganin Umar Farouk daga shi sai shi saboda ya sake tabbatar masa da gaskiya da kada ya ɓatawa Shari'a lokaci, amma ya san halinsa na kafiya bazai taɓa canza abinda ya faɗa ba kuma idan ma aka ji zancen ya keɓe da ɗan nasa za'a iya zargin wani abun wataƙil ma ayi amfani da wannan damar don ɓata masa suna ko cimma wani abu da ake son yi akansa, 'hasbunallahu wani'imal wakeel' ya faɗa yana jin abubuwan na sake yi masa nauyi a ƙwaƙwalwa haɗe da birkita masa dukkanin lissafi, yana jin wani irin rauni na ƙoƙarin tasowa ya lulluɓe masa zuciya amma daya tuna cewa shi ɗin fa mahukuncin gaskiya ne da aka wakilta ga al'umma sai ya ji wani ƙwarin guiwa ya shigesa, seat ɗin dake cikin katafaren office ɗin nasa agaban wani ƙaton table ya koma ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, sai daya kira messenger dake kula da office ɗin yasa ya fito masa da wasu takardu sannan ya soma rage aikin dake gabansa, ba shi ya kammala ba sai zuwa ƙarfe biyar na yamma, wayarsa ce ta dauki ƙara adai-dai lokacin da yake kokarin mikewa, sai daya mika briefcase dinsa ga messenger nasa yai gaba sannan ya ɗaga kiran yakai a kunnensa yana binsa a baya, "hello Dr Abdullahi gwaram ke magana, Barka da sabuwar Shari'a adalin alkalin Alkalai Justice Ibrahim Lawal Shanawa". Ya ji an faɗa daga cikin wayar cikin wata cunkusasshyar murya da kana ji zaka san cike take da tsantsar bakin ciki, sai daya sauke ajiyar zuciya haɗe da karfafa kansa da wani murmushi sannan ya ce, "Babu bukatar yimini tuni ga mutumen da ni da kaina nayi amfani da doka wajen hukuntasa da akan laifinsa, je kai tsaye ga dalilin kiran da kayi mun ina saurarenka". Wani abu Abbansu Nu'aymah ya ji ya tokare masa a makoshi, ba haka ya so jin muryar justice Ibrahim ba ko kaɗan, ya so ya jita cikin firgici tsoro da kuma ɗimauta akan shari'ar ɗansa da baya da wata hanyar kubutar dashi face ya yanke masa hukuncin rai da rai kamar yadda yai masa a shekarun baya, shin me yake faruwa ne? Yana nufin shi kadai ƙunci da zafi zai cigaba da bibiya na rashin dansa ƙwaya tilo da yai, hmmm bazata saɓuba wallahi dole ya dandani wannan zafin shima don duk yadda zai yi ya tabbatar su duka suka rasa ƴaƴansu ba shi kadai ba to sai yayi. "Shirunka ya tabbatar mini da ko ma me kake son faɗa ka samu amsar shi da kanka, idan tunaninka kusanci,kudi, soyayya, karfin iko ko wani abu kan iya sauya gaskiyar da nake zaune a kanta wajen yanke hukunci bisa adalci to kayi kuskure babu abinda suke iya sauyawa, zanyi sharia da ɗana zan kuma yanke masa hukunci dai-dai da yadda na yanke maka matukar aka tabbatar da laifi akansa kamar yadda aka tabbatar dashi a kanka, saboda haka ka zauna gefe ka jira kaga me karfin adalci zai haifar ba sai kayi ta wahalda gangar jikinka da zuciyarka ba". Wata irin dariya mai karfi Abba ya saki kafin can ya haɗe rai yace, "Wani lokaci ana buƙatar hankali, ba gaskiya ba, gaskiya bata kare mutum a lokacin da tsananin zafin wuta ke ƙona sa, a yanzu ba kada wani zabi daya wuce gida biyu, ka boye gaskiya kaki hukunta danka kayi bankwana da kujerar da kake akai, ko kuma da kanka da hannunka ka yankewa ɗan ka hukuncin kisa ya mutu har lahira kamar yadda ya kashe mani nawa ɗan ya mutu har lahira shima". "Idan kana da wani abun kafada daban domin wannan tsohon abune awajena". Dady ya faɗa cike da kwarin guiwa da yaƙini "Shikenan tunda haka kace, amma ka sani idan har ka fitar da hukuncin ba yadda muke so ba sai ka ga abin mamaki". Murmushi Dady ya sake saki lokacin daya iso wajen motarsa ya zura key ya buɗe yana cewa, "Matsalata ɗaya kenan Dr Abdullahi, ni ba'a yi mini barazana domin bata tasiri a kaina saboda ni alƙali ne dake bauta wa doka ba mutane ba, don haka karka bata mini lokaci akwai abubuwa agabana da suka fi wannan muhimmanci". Yana kai wa nan ya kátse kiran ya buɗe motar ya shiga yana karbar briefcase din tasa a hannun yaronsa ya ajiye a ɗayar kujerar sannan ys rufe motar ya tayar yabar wajen yana mamakin yadda son kai ya yiwa al'umma yawa basa son gaskiya da kum wanzuwar adalci a cikin ƙasarsu.

A gajiye ya iso gida kai tsaye ya nufi sashensa, bai jima da shiga ba Momy data ga dawowarsa ta shigo ɗakin, juyowa yai ya yi mata kallo ɗaya ya ɗauke kai yana rage kayan jikinsa a hankali yake cewa, "Me yasa kika aikata abinda kika aikata bada izinina ba." "Saboda ba kida wani zaɓi sama da hakan don bazan iya zuba idanuwa a kashe mun yaro ba". Ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin, kallonta ya sake yi da idanuwansa dake cike da gajiya kafin ya riko hannuwan ta su zauna bakin gado yace, "Amma kinsan hakan ba karamin damuwa zaki sake jawo mini ba, abubuwa zasu sake taruwa ne waje ɗaya su cunkushe mini? Kiyi tunani ya zan ji matata a tsaye gaban kotu tare da ɗana a gefe a matsayin mai laifi, abun zai matukar bani wahala kema kin sani". "Shi yasa tun farko naso kasa baki a lamarin ko ka daukar masa lauya amma ka ki". Momyn ta faɗa tana jaye hannuwanta daga riƙon da yai mata, dafe goshinsa yai cike da damuwa haɗe da sake dago kai ya kalleta yana cewa, "zaki ajiye case ɗin nan kibar Barrister Nazir yaci gaba dayi, bana ra'ayin na sake ganinki a kotu". Wani kallo tayi masa haɗe da mikewa ta juya masa baya tana cewa, "Bazai yiwu ba, kana ganin tare dani ma Umar Farouk yaƙi bashi haɗin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login