Showing 147001 words to 150000 words out of 157423 words

Chapter 50 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

531

hadin kai na biya bukatata kamar yadda kika bawa wancan, ina dai wannan abun shi yasa har yai nasara akanki kika fara son shi ni kuma kika yaudare ni ko? To kin zo inda zaki samu fiye da abinda yake yi maki dama Ni can ba ke nake so ba wannan abun nake so a waje ki kuma dana samu Shikenan banda sauran case dake don ke ba Sa'a ta bace, in dai a iskanci ni uban gidansa ne na fishi iya wa dan a rana zan iya biyawa macen da ta fiki zama mace buƙata sama da bakwai balle kuma ke sabon shiga a iskanc.." saurin runtse idanuwana nayi ina ɗaga masa hannu, sai dai kafin na buɗe idanuwana kawai na ji ya riƙo hannuna ya ɗora akan fuskar shi yana wani shafar ta haɗe da rufe idanuwa yana zuƙar iska tamkar mai jin ya ji, ban tsaya wani tunanin ba na wanke sa mari da ɗaya hannun nawa ina cewa, "Tir da halinka ban taɓa tsammanin a fasa kankara aga dutse ba, dama haka kake ban sani ba? Wallahi nayi nadamar sanin da nayi maka a rayuwata tsakanina dakai Allah ya isa bazan taɓa yafe maka ba, in sha Allah sai Allah ya saka mini". Ina kaiwa nan na ruga da niyar fita kawai na ji ya sake riƙo hannuna, juyowar da zanyi ya ɗauke ni da mari tare da tura ni da ƙarfi na faɗa kan kujerar dake a palourn, cike da tsoro na yunkura na mike idanuwana na tsiyayar da hawaye ina ja da baya don ceton kaina saboda gaba-daya ya birkece idanuwansa sun kaɗa, babu abinda nake hangowa a cikinsu sai tsantsar jaraba haɗe da son keta mini mutunci, kai na ya yo zai rungume ni nayi baya na kauce ya faɗi, cikin sauri na sake rugawa a kiɗime na nufi kofar fita kafin nakai ga fita din sai ganinsa nayi agabana, ganin da gaske keta mini mutunci yake son yi gashi babu kowa acikin gidan yasa nafara rakonsa ina bashi hakuri amma ina tamkar ina sake tunzura shi ya tare mani kofar fita da zan iya guduwa idan nayi nan yayi nan, idan nakoma can ya sake bina yana ƙoƙarin fado mini, ihu na soma yi amma a banza tunda babu kowa a gidan kuma ba lalle a iya koyo ni waje ba, nan muka fara zagaye falon dashi har na isa jikin kofar kitchen ɗin dake ƙasa a parlour nayi saurin fadawa ciki na rufe kofar na jingina a jiki ƙirjina na bugawa da karfi tamkar zai fashe tsabar tashin hankali, wayata nafara kokarin cirowa sai na tuna na saki jakar a palour na sake fashewa da kuka ina faɗin, "don Allah kayi hakuri Nu'aym kada ka cutar dani ka tuna kana da ƙanne da kuma yan uwa.." sai dai kafin na rufe baki naji ya bugo kofar da ƙarfi ta buɗe don dama banga key a jiki ba balle nasa, tamkar raina zai ɗauke na ji zuciyata ta wani tsaya cak lokacin daya shigo kitchen ɗin, ganin ya yi kaina yasa na shiga dube-dube ko zan samu abinda zan iya kare kaina dashi cikin sa'a idanuwana suka sauka akan set din wuƙaƙen dake jere a kitchen ɗin can gefe, da dubara naci gaba da ja baya ina rokon sa har na samu na kai gare su na ciro ɗaya da sauri ina nuna shi da ita.....

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/4, 3:54 PM] Queen Qee's💎: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            70.

"Kada ka matso ni zan caka maka ita idan har baka ƙyaleni na tafi ba, kayi baya nace ko na soke ka da ita". Na faɗa ina yi masa barazana da dukkanin gaskiya ta don ya kyaleni, ganin daya matsoni sai nayi kamar zan caka masa wuƙar ya sashi ɗaga hannayensa sama yana yin baya ni kuma ina nufo shi da ita har muka fito kitchen ɗin, yadda wuƙar na yi sannan da gudu na nufi kofar fita, sai dai ina taka ƙafata na ji ya fizgo ni da ƙarfi ya maido ni cikin falon na fadi ƙasa, daga kwance na riƙa ja da baya ina lalubo wuƙar dana yar, yana yowa kaina zai faɗo mini na runtse idanuwa tare da sakin wata irin ƙara ta neman ceto, dai-dai lokacin kuma hannuna ya kai jikin wuƙar na ɗagota da ƙarfi, ni dai ban san ya akai ba sai kawai ji nai ya saki kara shima ya faɗi gefe, buɗe idanuwana da zanyi na gansa kasa a shema ashe na soke sa da wukar.." Janaam tayi shiru saboda kukan da yaci karfinta, Momy bata hanata kuka ba don ta cancanta tayi kukan har sai da tayi mai isarta ta gaji sannan ta ciro tissue dake kan side table din dake gefenta ta miƙa mata, Janaam ta karɓa ta goge fuskarta Momy ta kwalawa Tauheeda kira, tana zuwa ta saki baki tana kallon Janaam tunowa da fuskartar da tai ta buɗe baki da niyar yi mata magana Momy ta daka mata tsawa tace ta wuce taje ta kawo mata ruwa, da mamaki Tauheeda tabar wajen ta shiga kitchen ta dauko gorar ruwa da cup ta ɗora akan tray ta kawo gaban Janaam ta ajiye, har zata bar wajen Momy ta ce, "zuba mata mana". Tauheeda ta dauki gorar ruwan ta buɗe ta tsiyaya a cup tana kallon Janaam ta kasan idanuwa, me take yi anan? Me akayi mata? Ta tambayi kanta tana miƙa ma Janaam ruwan, Janaam ta karɓa tayi mata godiya sannan Tauheeda tabar wajen ganin babu alamun wasa a fuskar Momynta da zata iya amsa mata tambayoyin dake ranta, sai da Janaam ta shanye ruwan tas ta ajiye cup tana sake goge fuskarta da tissue sannan Momy ta ce, "Daga nan sai kuma me yafaru?" Ba tare da Janaam ta ɗago ba taci gaba da cewa, "Na shiga cikin tsananin tashin hankali dana tabbatar da cewa lallai na kashe Nu'aym, ina duƙe a gabansa ina kuka na rasa yadda zan yi sai ganin Umar Farouk nayi a bakin kofa, kai na shiga girgizawa tare da komawa gefe ina cewa, "Ba da niya na kashe sa ba Umar Farouk kawai nazo kare kaina ne daga f.." saurin ɗaga mani hannu yai yana bina da wani irin kallo, take naga idanuwansa sun kaɗa sunyi ja ya nufi wajen da Nu'aym ke kwance cikin jini ya sa hannunsa a jikin wuƙar ya cirota daga jikinsa da karfi, nan na sake ruɗewa na saki wata ƙarar da tayi dai-dai da sakin karar da Nu'aym ya sake yi lokacin da Umar Farouk ya ciro wuƙar a jikinsa alamar lumfashin sa ya dawo kafin kuma muka sake jin tsit, hannu Umar Farouk yasa ya girgiza sa bai motsa ba ya sake kai hannunsa ɗaya a hancinsa nan ma ba alamun yana lumfashi, ɗago kai ya yi ya kalleni cikin muryar kuka nace, "Na kashe shi ko?" Girgiza mini kai yai haɗe da cewa, "Ni ne na kashe sa ba ke ba saboda haka kar ki sake cewa kin kashe shi, ba kece kikai hakan ba ni ne". "Amma taya zakace kai ne Umar Farouk bayan ni n.." kafin naƙarasa cikin tsawa ya ce, "Idan kika sake furta kece kika kashesa Amaah wallahi sai na kashe ki kuma na kashe kaina, koma ma meye ni zan jure amma ke bazan juri wani abun ya sameki ba, ina sonki Janaam na yarda Ni na mutu ke ki rayu kin ji ko?". Yana rufe baki sai ga mutanen gidan sun dawo, ganin sa rike da wuƙar yasa suka yadda shi ne wanda ya aikata kisan suka kira jami'an tsaro, nayi yunkurin faɗa masu gaskiya ko a lokacin amma ya sake cewa idan nayi magana sai ya kashe ni kuma sai ya kashe kansa, a sanin da na yiwa Umar Farouk zai iya aikata hakan, na ji tsoron kar ya aikata abinda ya faɗa shiyasa na kasa fadar gaskiya amma tunda hakan ta faru kullum cikin kuka da nadama nake ina mai addu'ar Allah ya kawo hanyar da zata kubutar dashi cikin sauki ko da hukuncin zai dawo akaina tunda nice mai laifin?" "To me yasa kika canza shawara yanzu kika zabi ki faɗi gaskiya, shin kin miƙa wuya ne ko kuwa?" "Wata gaskiyar ce ta sake bayyana da zata iya kuɓutar dani da kuma shi, shi yasa na zaɓi nazo na faɗa maki gaskiya nasan ubangiji ne ya amshi addu'a ta". "Ina jinki" Momy ta faɗa tana sake hango gaskiyar bayanin da Janaam ke yi mata acikin idanuwanta, Janaam ta share kwalla tare da jan majina sannan ta ce, "Barrister, Nu'ayma bai mutu ba yana nan a raye". "What?" Momy ta faɗa da ƙarfi haɗe da miƙewa tana kallon Janaam irin kallon nan na kin tabbata abinda kike faɗa, Janaam ta kaɗa mata kai alamun tabbatar mata da abinda ta faɗa ɗin, "Hmmm dama nayi tsammanin hakan, yanzu wasan zai fara Dr. Abdullahi, idan ka kuɓuta ga hukuncin da mijina ya yanke maka a shekarun baya to a wannan karon zan tabbatar da baka kubuce hukuncin da kaifin ɓacin ran uwa zai jawo a yanke maka ba, kayi matukar kuskure wasa da ƙwaƙwalen lauya da kuma alkali akan ɗan su". Sai data kalli Janaam sannan taci gaba da cewa, "A ina kika samu wannan bayanin?" "A gun Nu'aymah, ita ce takira ni ta sanar dani ta kuma ce kada na fadawa kowa". Ta ƙare zancen tare da miƙo mata wayarta bayan ta kunna mata recording ɗin da tayi lokacin data tabbatar da Nu'aymah ke magana, karɓa Momy tayi ta saurara bayan ta gama ji ta dauki wayarta data gama naɗar duka bayanan da Janaam ta gama yi mata aciki sannan takira Barrister Nazir, Yana ɗagawa tace "Our suspicion is confirmed Barrister Nazir, ya kamata yau komi dare kaga inspector Ashir, idan yasa taurin kai yaƙi fadar gaskiya ka nuna masa evidence ɗin da muka haɗa, zan turo maka wasu bayanan ta WatsApp yanzu ka duba". Shiru tayi na sekanni kafin tace, "Ba damuwa, Janaam na tare dani yanzu haka, duk abinda yakamata mu sani ta faɗa mana har da tabbacin cewa Nu'aym na raye, damuwar daya ce yanzu! Shin a wace ƙasar ce ya boye shi? Dole mu gano hakan kafin gobe". Nan ma shiru ta sake yi tana sauraren Barrister Nazir kafin tayi wani miskilin murmushi tace, "wato Dr . Abdullahi ya rena mana da hankali matuka amma zai ga yadda wasar zata kaya tsakanin mu dashi gobe". Sun ɗan jima suna waya kafin Momy ta katse kiran, Number da Nu'aymah ta kira Janaam ta karɓa tare da tura recording ɗin da Janaam tayi, tana gamawa Janaam ta maida niƙab ɗinta ta ɗaure a kai haɗe da miƙewa tace, "Na barki lafiya". Tana kare fadar hakan ta fice, har ta kai bakin kofa Momy tace, "Yana da kyau ki kula domin yanzu kina cikin risk, son samu ki jira nasa driver ya ajiye ki gida". "A'a in Sha Allah zan isa lafiya". Janaam ta faɗa sannan ta fice, tana fita Momy ta sauke ajiyar zuciya haɗe da komawa ta zauna ta rufe fuskar ta da tafin hannuwanta tana furzar da iska ta baki, tafi minti goma a haka kafin ta ɗauki wayarta ta shiga WatsApp ta turawa Barrister Nazir bayanan data nada gun Janaam da kuma wudanda ta tura, sannan ta Turawa ilyas dake bangaren c.i.d office Number da Nu'aymah ta kira Janaam da ita tace ayi mata tracking daga ina akayi kira da ita. Bayan ta gama ta ajiye wayar Tauheeda ta shigo, kallonta Momy tayi tace, "Ya akai?" "Momy ina bakuwarki? Aunty Janaam fa ce, mun hadu da ita bukin Aunty Nidrah tana da kirki ki sosai, halama Momy me akayi mata take kuka?" Kamar Momy baza tayi magana ba sai kuma tace, "Shiga ciki ki dauko mun key ɗin motata dole naje naga Umar Farouk yau duk da ban so hakan ba". Ta faɗa ba tare data bi takan tambayar da tayi mata ba, "Momy.." Tauheeda zata sake yin magana da ɗan karfi Mommy ta ce "Tauheeda!" Tana kwatseta, ba shiri tabar wajen ta je ta dauko mata key ɗin motar ta kawo mata, Momy da dama saye take da hijab dinta wayarta kaɗai ta ɗauka ta karɓi key ɗin ta fice daga gidan.

Tana zuwa police station ta nemi izinin ganin Umar Farouk, bayan an fito mata dashi ta kalli yadda ya koma ta girgiza kai kawai tare da ciro wayarta ta kunna recording ɗin da ta yiwa Nu'aymah ta ajiye masa gefe, kallon Momy yake yi lokaci ɗaya yana sauraren maganar da Janaam keyi daga cikin wayar, a hankali kamanninsa suka fara sauyawa ɓacin rai na sake bayyana a fuskarsa musamman jin abinda ya faru da yadda Janaam ke kuka, rumƙe hannunsa yai yana wani irin cika tamkar zai fashe idanuwansa sunyi jajir, hannu Momy ta saka ta kashe a dai-dai inda Janaam ta tsaya tasa Tauheeda ta kawo mata ruwa tana cewa, "momy's boy ashe ban sani ba ka zama lover boy har haka? To yanzu me zaka ce? Zaka ci gaba da amsa cewa kai ne kai kisan ko zaka karɓi gaskiya kamar yadda ta bayyana?" Cikin zafin rai da ƙunar zuciya Umar Farouk ya ɗago kai yana kallon Momy yace, "Wallahi Momy da na san a waccan ranar wancan karen ya taɓa Janaam ba cire wuƙar kaɗai zanyi daga cikinsa ba sai na yita bubburma masa ita har sai na tabbatar na raba cikin nasa gida biyu kayan cikinsa sun fito, menene amfanin rayuwar irin su a doron duniya da har za'a tsaya shari'a akansu don sun mutu, da za'a dawo da ransa sau dubu da agaban kowa zan kashesa har sau dubu in yaso nima akashe ni sau dubu". Ya kare zancen wasu hawaye bakincikin rashin nasarar aikatawa Nu'aym abinda yake ji a zuciyarsa na taso masa da bai yi ba, kallonsa kawai Momy keyi bata ce komai ba har ya gama sannan ta miƙe tana cewa, "dama na faɗa maka zan gano ainahin gaskiya, sai mun haɗu a kotu gobe yarona". Ta ƙare zancen tana shafa kansa tare da ficewa tabar police station ɗin ba tare data sanar dashi cewa Nu'aym ɗin na raye ba...

                           

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU

[10/4, 3:54 PM] Queen Qee's💎: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            71.

Wata irin ƙara Umar Farouk ya saka yana jin gaba-daya duniyar na juya masa saboda tsantsar tashin hankalin abinda zai iya faruwa ga Janaam a kotu gobe, don ya tabbata tunda har Momy ta gano gaskiya yanzu hukuncin akan Janaam zai koma, miƙewa yai daga inda yake yana faman haɗa hanya saboda yadda jiri ke ɗibarsa har ya koma cikin cell ɗin da yake ba tare daya jira yan sandan sun zo sun maida shi ba, yana zuwa faduwa yai kwance hawaye na biyo masa a fuska, cikin wata irin raunarniyar murya da karyewar zuciyar da tunda aka kawo shi wajen bai taɓa tsintar kansa aciki ba yace, "I so much love you Janaam, taya kike tunanin rayuwata zatayi surviving idan ba ke? My life has no meaning. Every breath i take feels empty if it’s not filled with your presence. You are the reason my heart beats, the light in my darkness and the hope in my soul. If i lose you, i lose the world itself, because nothing matters to me except you. You are not just part of my life you are my whole life Amaahh! Only you..." Ya kare zancen haɗe da kumshe idanuwa.

Momy kuwa tana fita police station ɗin inspector Ashir na shigowa hankalinsa duka a tashe, magana yai da wani ɗan sanda sannan ya wuce office ya kira Abba, bugu ɗaya ya ɗaga haɗe da cewa, "wai menene haka inspector Ashir?" "Ranka shi daɗe yanzu nan muka rabu da Barrister Nazir ya sameni har gida ya gabatar mini da wasu hujjoji da zasu iya zama barazana a garemu, yanzu kuma ina shigowa Police station Barrister Maryam na fita, Ni fa bana tunanin zamuyi nasara matukar suka gano Nu'aym na raye". "Ka kwantar da hankalinka ko da sun gano baza su iya gano kasar dana ɓoye sa ba, bayan haka ma duka wasu evidence da zasu tabbatar da anbar ƙasar nan da shi baza su taɓa samu ba saboda a ranar jirgin ƙasar U.k kaɗai ne ya tashi, shi kuma kasan sai washe gari nayi masa duk wani abun da ya kamata na fitarsa zuwa India kuma duka na goge hujjojin, abinda kawai nake so da kai shi ne ka aiwatar da plan ɗinmu na karshe, Barrister Aysha da Barrister Shamsu zasu kula da komai a kotu. zuwa ƙarfe goma da rabi idan komai bai tafi yadda muke buƙata ba akwai ticket dana tanadar maka zaka iya zuwa duk ƙasar da kake buƙata, zan saka maka kudi a account dinka amma ka tabbatar zuwa lokacin plan ɗin mu na karshe ya fara aiki don kar mubar baya da ƙura". "Angama ranka shi daɗe". Inspector Ashir ya faɗa cikin kwarin guiwa jin za'a cika masa account dinsa da yan canji, bayan sun kammala wayar ya fito, cell ɗin da Umar Farouk ke rufe ya nufa, lokacin Umar Farouk na zaune ya haɗe kai da guiwa yana jin babu abinda ke yi masa daɗi, Janaam kawai yake son gani kuma yake son jin muryarta, kallon ɗan sandan dake tsare da kofar wajen yai yace, "Ya ci abinci kuwa?" "No sir an kawo masa amma bai ci ba". Jinjina kai yai yasa ya buɗe masa wajen ya shiga ya tako har zuwa inda Umar Farouk ke zaune, duƙawa yai agabansa yana ƙare masa kallo kafin yace, "Zan iya taimakon ka?" Shiru Umar Farouk yai yana nazarin kalmar har sai da inspector Ashir ya sake maimaita maganar sannan ya ɗago kai, kallo ɗaya yai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login