Showing 1 words to 3000 words out of 157423 words

Chapter 1 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

493

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: I just published "002" of my story "IDO A DUHU"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=6824da4be5f14d56e5838155

*IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

RANAR FARAWA: Wednesday on 7th May 2025.

*Wannan littafin haƙƙin mallakata ne ban yarda a juya mani shi ba ta kowace irin fuska har sai da izinina! labarin dake ciki kuma ƙirƙirarren labari ne, saboda haka idan ya zo dai-dai da labarin ki/ka ko kuma rayuwar ki/ka to akasi ne kawai*

_Bismillahirrahmanirrahim_

                            1.

      Wata irin ƙara ce tun daga bakin gate suka jiyo data karaɗe gidan, hakan yasa ko gate mai gadi bai gama budewa ba aka danno hancin motar aguje zuwa cikin gidan wanda kaɗan ya rage a take mai gadi, ya yi wani irin tsalle tare da sakin gate ɗin ya wuntsila gefe, a rikice matuƙin motar wanda da alama shine mamallakin gidan ya yi parking haɗe da fitowa hankali a tashe. Sauran wuɗanda ke cikin motar kuma suka nufi cikin gidan a guje, a iya saninsu basu bar kowa cikin gidan ba kafin su tafi, to daga ina wannan ƙarar ke fitowa kuma wane aciki? Tambayar da dukkaninsu suke wa kansu kenan acikin zuciya kafin cike da ruɗewa ya nufi wajen mai gadi don shi ne wanda ya kamata ya amsa masa wannan tambayar. "Musa waye acikin gidan nan?" Ya faɗa yana wurga masa wani irin kallo cike da tuhuma, cikin rawar murya Musa ya shiga bashi amsa yana cewa, "Allah ya taimaki ranka shi daɗe Wallahi ban sani ba". "what? Kamar ya baka sani ba to motar waye a kofar gidan? Ya akayi har wani ya shigo cikin gidan nan baka sani ba? To meye amfanin aikinka? Me yake faruwa ne acikin gid..?" Bai ƙarasa ba da gudu sai ga wata matashiyar budurwa ta fito tana faɗin, "Wayyo Allah sun kashesa, wallahi sun kashe sa, wayyo Allahna na shiga uku na lalace".  Wata irin juyowa yai da ƙarfi cikin tashin hankali, gabaɗaya ji yai ya kasa fahimtar inda maganganun nata suka dosa, to waye aka kashe? ya tambayi kansa, ji yai ya kasa motsawa tamkar an kafesa a wajen ko ƙafafuwansa ya kasa ɗagawa sai binta yake da kallo, tamkar wanda aka tsikara yai firgigit tare da saurin riƙota ganin yadda gaba-daya ta fita hayyacinta itama saboda tsananin tsoro da tashin hankalin data gano, lumfashinta ta shiga yin sama da ƙasa dashi tana nuna masa hanyar shiga cikin palourn gidan tana sake cewa, "Sun kashesa!". jin haka ya sashi saurin sakinta ya nufi cikin gidan yana jin zuciyarsa na wani irin bugawa da karfi, abunda idanuwansa suka gane masa lokacin daya shigo cikin paloun ya haifar masa da wani irin kaɗawar zuciya ya yi baya zai faɗi yai saurin dafe kujerar dake kusa dashi yana jin tamkar ana tsittsinka masa zuciya.

Idanuwansa ya ɗago ya zuba akan Kyakkyawan matashin dake tsaye acikin paloun riƙe da wuƙa a hannunsa duk jini, fuskar nan tasa a haɗe babu alamun tsoro ko kuma shiga tashin hankali na riskarsa da akayi cikin wannan yanayi balle kuma nadama, a gefensa kuma wata budurwa ce duƙe tasa hannayenta ta toshe bakinta dasu tana kuka, kukan da gaba-daya kana kallon ta zaka fahimci yadda ya sauya mata kamanni ta hanyar sauya kalar fatar fuskarta izuwa ja, yayin da launin idanuwanta dake farare tas suka yi jajir suna cigaba da tsiyayar da ƙwalla. A gaban su kuma babbar macece rungume da wani matashi ajikinta dake kwance cikin jini ko motsi bayayi tana kuka tana girgiza sa haɗe da sabbatun ya tashi. Ganin da tayi tabbas bazai tashi ba ya sa ta miƙewa cikin wani irin fushi da zafin rai ta nufo wajen saurayin dake tsaye riƙe da wuƙar da kana gani kasan da ita akayi amfani wajen illata wanda ke kwance cikin jinin babu lumfashi a jikinsa, tana zuwa ta ɗauke sa kyakkyawan mari har guda biyu saboda tabbacin da take dashi akan ko shakka babu shine ya yi wannan aika aikan, cikin zaro idanuwa da ƙaraji take cewa "Kai ɗan gidan uban waye? Waye kai? Me ya kawo ka a cikin gidan nan? Waye ya aiko ka ka aikata masa haka? Me yarona ya yi maka ne?". Ta jero masa tambayoyin tana shaƙo wuyan rigar sa kafin ta fashe da wani irin kuka tana zubewa ƙasa, saurayin kuwa kasa amsa mata yayi sai ma ƙasa da ya yi da kansa don har lokacin babu alamun nadamar abinda ya faru ko tsoro a tattare dashi, banda zallar masifa da jin kai babu abinda ke cikin idanuwa da suka yi jajir tamkar an watsa barkono.

Kukan da matar keyi ya maido da mutumen cikin hayyacinsa yana faɗin. "Innalillahi wainna ilaihirrajiun". Kalmar daya iya faɗa  kenan haɗe da ciro wayarsa, bugu ɗaya ya yiwa wata lamba aka ɗaga, cikin wata irin murya dake nuni da cike yake da damuwa yace. "Commissioner ina so ka turo mani da yaranka anan gidana, Please ranka shi daɗe". A ta ɗayan ɓangaren commissioner of Police ya amsa masa da, "Yanzun nan amma yallaɓai ina fatan dai lafiya ko?" "Ba lafiya ba.." nan ya kwashe duk abinda ke faruwa da suka isko ya sanar dashi yana jin idanuwansa na kokarin kawo ƙwalla yana ji duniyar nayi masa wani irin juyi, gaba-daya ya gama ruɗewar da bai san me zai yi ba banda ya kira hukuma.

Bayan mintuna goma sha takwas da kiransa sai ga motar police har guda biyu ta iso gidan, Nan ya basu izinin shigowa tare da nuna masu wanda zasu yi arresting da suna shigowa su da kansu suka fahimci shine mai laifin saboda ganin wuƙa da jini a hannunsa, a take suka zagayesa tare da saita bindigogin su akansa don kar yai yunƙurin guduwa, ɗaya daga cikin yan sandan ne ya fiddo ankwa zai saka mashi a hannu, a take ya fara ƙoƙarin rigima dasu yana faɗin, "Kada kuyi kuskuren kama ni domin ko kunyi hakan ba amfanin da zai yi maku, kun san ko waye ubana saboda haka zan fito ko kuna so ko bakwa so, wannan kuma bazan taɓa nadamar mutuwarsa ba". Bai ƙarasa ba ya ji saukar kan bindiga a saman kansa ya saki wata irin ƙara tare da zube wa ƙasa akan guiwoyin sa saboda tsananin azabar da yaji. Jin hakan yasa matashiyar budurwar dake kuka ta shiga ja da baya tana sake toshe bakinta jin kalaman dake fita abakinsa, mamaki ne ƙarara ya bayyana akan fuskar mutumen ganin babu nadama ko ƙire a tattare da yaron akan abinda ya aikata, cikin ɓacin rai yace , "Shikennan inspector kuje dashi ayi bincike a gano waye ya turosa har cikin gida yazo ya aikata haka ga ɗana! Bana so ku sassauta masa har sai kun tabbatar daya faɗa maku gaskiya, ku gana masa azabar da zata sa da bakinsa ya faɗi ko waye ya aiko da da kuma dalilinsu, wlh ni kuma sai naga wanda zai tsaya masa akaf faɗin ƙasar nan, sai naga wanda ya ɗaure masa gindi da zai hana nayi Shari'a dashi ko da duka abinda na mallaka zai ƙare". Wani dukan suka sake kaiwa saurayin a karo na biyu a saman kafaɗa bayan sun saka mashi ankwa kafin su ɗaga shi suka nufi hanyar fita dashi, suna kaiwa bakin ƙofa ya juyo yana ma yarinyar wani kallo mai cike da gargaɗi, ɗan sandan dake riƙe dashi ya hankaɗasa yana tura ƙeyarsa waje yake cewa, "wuce muje, zakayi  bayani". Suka turasa cikin motarsu ta yan sanda bayan sun fito tare da tayar da motar suka fice daga gidan, ɗaya motar ta yan sanda kuma suka ɗauki wanda ke kwance cikin jini aka nufi asibiti dashi, kallon yarinyar mutumen ya yi da sautin kukanta ya ƙaru yace, "Ya isa haka ki tashi ki tafi gida, idan ma ya hanaki magana yanzu lokaci zai zo da gaskiya zata bayyana idan aka zo bincike, ina fatan zaki faɗi abinda kika sani don bima yarima da jininsa hakkinsa". Jiki ba ƙwari ta miƙe zata fita matar tace.

"Ki sani ke kadai ce zaki iya bada tabbacin abinda ya faru, idan har kika ɓoye kuma bazan taɓa yafe maki ba".  Bata iya cewa komai ba tana kuka ta fice daga gidan, yara yan mata biyu suka zo suka rungume matar suna kuka, shi kuma mutumen ya fice yabi bayan yan sandan zuciyarsa cike da damuwa, driven yake amma tunani yake yi yaushe ɗansa ya dawo ƙasar nan ba tare da saninsa ba? Me yakawo wancan saurayin acikin gidansa har hakan ta faru? Waye shi meye alakarsa da ɗansa da zai shigo har cikin gidansa yayi masa wannan mumunan aika-aika. Ji yai zuciyarsa ta bushe ta cika da wutar son ɗaukarwa ɗan nasa ƙwaya tilo da yake matuƙar ƙauna fansa, a take ya ɗauki alwashin ko waye yaron kuma ko dan gidan waye shi sai an hukunta sa shima dai-dai da laifinsa don bazai yafe ba, bazai taɓa bari jinin ɗansa ya tafi a banza ba.

*06:35pm*

Zaune yake a farfajiyar cikin gidan nasa daga wajen gate can cikin wani ƙaramin waje da aka tanada don shan iska, a gefensa wata kyakkyawar mace ce bafulatana da shekarunta duka baza su haura shekaru arba'in da wani abu ba, Labari suke yi cike da kulawa, k'auna da kuma soyayyar juna, wanda kana gani kasan ba sai an faɗa maka su ɗin miji da mata bane dake tsananin ƙaunar junansu. wayarsa dake ajiye agaban sa ce ta shiga yin ƙara, hakan ya tilastasa dakatar da firar da suke yi da yake matuƙar jin daɗin ta, wayar ya fara ɗagawa kafin yakai a kunnensa bakinsa ɗauke da sallama, shiru ya yi na wasu yan sakanni kafin yai wata irin zabura yana miƙewa tsaye yake cewa. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wace police station aka je dashi? Laifin kisa kuma? To shikenan commissioner, kar ku ji komai ku gudanar da duk binciken daya dace akansa, Nagode". Ya faɗa bayan gama sauraren dalilin kiran nasa da akayi yana cire wayar daga kunnensa. Nan take kyakkyawar fuskar matar nan dake tare dashi ta sauya kamar yadda tasa fuskar ta sauya daga sassauƙan mutum da ɗazu a kallo ɗaya zaka iya fahimtar hakan tare dashi zuwa wani mutum da bazaka taɓa cewa ya taɓa yin dariya ba, hannayensa duka ya zuba a baya ya shiga kai da komowa a tsakiyar wajen, kwarjininsa da kuma yanayin da nan take ya shiga ya sa matar duk yadda hankalinta ya tashi ta kasa furta masa kalma ko ɗaya da nufin tambayar sa abinda ke faruwa, sai dai fa gaba-daya jikinta ya saki tsoro ya dabaibaye mata zuciya tare da yimata wani irin kullin goro daya sa fitar lumfashinta da wani irin ƙarfi, daƙyar ta iya tattaro ɗan karfin daya rage mata cikin rawar murya tace...

ALLAH KA JIKAN IYAYENMU👏

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: I just published "003" of my story "IDO A DUHU"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68259177e5f14d56e5981044

*IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            2.

  "Am.am me yake faruwa ne naga ka shiga damuwa da tashin hankali haka? Please don Allah ka sanar dani saboda bazan iya jurar cigaba da kallonka cikin wannan yanayin ba, me yake faruwa ne?" Ajiyar zuciya ya ja ya sauke kafin yace. "A kullum ba ni da damuwa sama gata yaron nan! Na rasa wane kuskure na aikata ubangiji ya jarabceni da haihuwarsa, sau ɗaya ban taɓa butulcewa ubangiji ba akan ni'imomin da yai mani, ya kuma sani tsaye nake akan tarbiyar duka ya'yan daya bani ba tare da gazawa ba, amma na rasa samun farin ciki akan ɗa ƙwaya tilo, maganar da nake faɗa maki kenan a kullum akan matsalar yaron nan da gaba-daya ke sauka akan tarbiyar da muka ɗorasa amma se kike ganin kamar takura masa nake yi, to gashi nan yanzu baƙar zuciya ta ɗebesa ya je ya aikata abinda daga ke har shi zakuyi nadama, abinda kika taya sa shukawa sai kuje ku girbe domin ni bazan taɓa saka hannuna ko naira ta acikin wannan maganar, ya je har gidan mutane ya aikata kisan kai saboda yana taƙamar shi ɗana ne! to wallahi ba abinda zan iya yi masa yaje can duniya ta ishesa riga da wando". Tunda ya fara magana gabanta ya yanke ya faɗi, take taji wani irin jiri na ɗibar ta duniyar tana juyawa da ita har ya dasa aya, kai ta shiga girgiza wa kafin tace. "Wannan ba gaskiya bane, wlh ɗana bazai taɓa aikata hakan ba, kisa fa kace taya zai ya iya kashe ɗan mutum kuma har cikin gidansu?" "Kin mance ko waye ɗan naki da baƙar zuciya kenan da kuma kafiya bisa ra'ayin kansa? To meye bazai iya aikatawa ba?" "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, amma ko hakane ai hannunka bazai ruɓe ka yanke ba, ya kamata kayi wani abu don Allah kada kabari ai rasing case ɗin nan akansa tunda kana da hanyoyi da dama da zaka iya bi ka kashe sa". Da mamaki yake kallonta kafin yace, "Wanda ya kashe ɗin shi baya da gata ne? Kisan kai fa akace maki! Anya kina da zuciya a kirjinki? Kin san a wane hali su iyayen yaron da aka kashe suke ciki? Kin san me suke ji a zuciyarsu, kin san irin so da shaƙuwar da suke da ita da ɗan su? Yau she kika koma haka son zuciya ya hana ki hango irin halin da uwa take shiga idan ta rasa ɗanta? Ciwo kaɗai idan yaronta nayi rasa duk wata natsuwarta da farin ciki take yi ta shiga tashin hankali da damuwa, balle kuma mutuwa dake nufin tayi bankwana dashi na har abada kenan! Shine kike cewa nabi duk hanyar da zan bi na fito maki da yaronki? Bazan yi hakan ba wallahi koda za'a yanke masa hukunci ne dai-dai da abinda ya aikata". Hawaye na sauka akan fuskarta ta shiga girgiza kai tana faɗin, "Bazai aikata hakan ba na tabbata har sai da babban dalili, don Allah kada ka biyewa zafinsa da kake ji a zuciya ka wofantar dashi, kafa tuna shi kaɗai kake dashi da zai zamo magajinka". "Sai akace sauran ya'yan nawa da nake dasu baza su iya zama magadana ba? Na fahimci kallonsa da kikeyi a matsayin ɗa namiji tilo a cikin yarana shi yasa kike ɗaukar kamar bazan iya rayuwa babu shi ba, to ki farka tun wuri ko babu shi na tabbata 'ya'yana mata sun isheni samun rayuwar farin ciki sama dashi, a yanzun ma ki faɗa mani banda baƙin ciki, ɓacin rai da damuwa me yake ƙulla mani a matsayinsa na wanda kike tunanin shine kaɗai zai iya zama magajina?" Share hawayen da suka sauko mata a fuska tayi sannan ta ɗago ta kallesa ta ce, "Shikenan, yanzu me kake nufi?" "Bana nufin komai amma bazan taɓa sa bakina ba akan wannan zancen, ya je can duniya ta horasa tunda haka ya zaɓa". Sake share ƙwallan dake akan fuskarta tayi a karo na biyu tare da ɗagowa ta kallesa, bata ce komai ta nufi ɓangaren nata cikin tsananin ɓacin rai ta ɗauko mayafinta ta yafo tare da makullan motarta ta ɗauki handbag ta fito,  sai data iso kusa dashi sannan ta ja ta tsaya tana cewa. "Idan bazaka saka baki akan zancensa ba ni zan saka saboda ina son ɗana idan har kai baka son sa". Tana gama maganar ta wuce kai tsaye wajen motarta ta buɗe ta shiga ta tayar, reverse ta fara yi sannan ta yiwa maigadi horn da sauri ya je ya wangale mata gate ta fice daga gidan aguje, runtse idanuwa yai ganin yadda ta fita gidan da mugun speed, a irin son da takewa yaron yasan sam bazata jura ba kuma komai zai faɗa mata baza ta taɓa fahimtarta ba ko me zai faru, lumfashi ya ja a hankali tare da fitar da iska mai zafi ta bakinsa, shi kaɗai yasan me yake ji ƙasan zuciyarsa da tarin ƙalubalen da zai iya fuskanta akan faruwar wannan lamarin, a yanzu baida wani abu da zai iya yi har sai yan sanda sun gama binciken su akai, ji yai ina ma ace faruwar wannan abun mafarki ne da yayi gaggawar tashi daga baccin da yake yi don sauƙaƙawa zuciyarsa raɗaɗin da yake ji acikinta. Yana tsaye yarinya ta fito da baza ta gaza shekaru goma sha biyar ba ta nufo wajensa tana tambayar ina mahaifiyar tata zata je taga tafita cikin ɓacin rai, hannunta ya kamo ya sanyata acikin jikinsa yana cewa. "Karki damu yanzun nan zata dawo". ta ɗago kai tana kallon yanayin mahaifin nata haɗe da cewa, "Me yake faruwa ne naga ranka a ɓace kaima?" "Ba komai mamana?" Ya faɗa yana shafa kanta, "Okay". Ta faɗa tana sake kwantar da kanta cikin jikinsa, duk da ƙaramcin shekarunta idan akwai abinda ta tsana duniya bai wuce taga iyayen nata cikin ɓacin rai ba, duk inda hankalinta yake idan yayi dubu to zai tashi.

Gudu takeyi sosai a mota cike da tashin hankali da damuwa, tabbas komai akace ɗanta zai aikata bazata yi musu ba, amma wannan kisa ne fa? Taya zai aikata hakan kuma akan me?  Sai da tayi nisa sosai sannan ta tuna bata masan inda aka kai yaron nata ba, ta dai ji yai zancen police station Amma wace police station ɗin ce shine abinda bata sani ba, gudu ta rage ta ɗauki wayarta dake saman steering wheel ɗin motar, rasa wanda zata kira tayi ta tambayi a wace police station aka kaimata ɗa, har zata kira mahaifin nasa sai kuma ta fasa ta kira lambar yaron nata, bugu ɗaya ana biyu aka ɗaga. "Hello my.." kasa karasawa tayi sakamakon jin wata muryar daban daba tasa ba, rintse idanuwa tayi cikin ƙunar zuciya kafin tace, "Ina yaro na?" Ɗan sandan daya ɗaga wayar yace, "Yana cell yana karɓar horo". Cikin dakewa duk da yadda maganar ta dakar mata zuciya tace, "A wace Police station kenan?" Sai daya fito wayar a kunnensa yaga sunan dake yawo a screen ɗin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login