Showing 30001 words to 33000 words out of 184118 words
Chapter 11 - Bakar Taada Hausa Novel Complete
kin ga Babban mutum ne Yabi, ga shi kowa ya yi masa shaidar nagarta.
Ki boye ta ba sai an ga ni ba, bana son ya kubuce miki. Bauchi zai kai ki, ba zai ajiye ki anan ba, ko ma Abuja. Babbar waya ce ki yiwa Allah kada ki bari ta salwanta".
Ya juya na bi shi da ido ina raya ina ma yadda ake zuba masa kyakkawar sura kuma cikakkiya haka yake da kyakkawar dabi'a da nagarta.
Inda a ce shine yake da dabiun Yaya J da ya zama komai an hada masa.
Mafi yawan lokacin ina yawan ayyana da Yaya J ne yake ingarma kaman Bulkachuwa da an yi namiji tsayayye mai kyakkawar manufa.
Amma halayyar Bulkachuwa shine nak'asunsa, mussaman na yadda yake iya keta alfarmar shari'a yana aikata kaba'ira, ga rashin ta ido, ga shigar iyashege, yau har barima na ga ni makale a kunnensa, gashin kai ya sha tiri (dying) gashinsa mai kyau ne irin na fulanin Bulkachuwa amma ya mayar da shi cibiri cibiri tsabar fitina da son yaudare y'anmatan da ba susan ciwon kansu ba, ga kafiya akan ra'ayinsa, ko k'uda ya shafa masa lafiya wajen naci.
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
Amma akwai tausayi mussaman idan ya ga kina kuka, to kin karya masa lagonsa, sannan yanzu ya fara sanin kishin kansa har yana taya wani ciwon abin da aka yi masa.
Ashe da ya fita wajen Baban Marina ya raka wannan mutumin da ko sunansa ban sani ba, ya nemi a bashi izinin fara magana da ni.
Baba ya ce "Ya bashi damar neman yardata, amma idan ban amince ba, ba zai mini dole ba.
Shi kenan sai Alhaji Mustapha Zaki yake zuwa, ni da kaina kunyar yadda nake yar mitsil a gabansa nake yi. Dogo ne sosai yana kuma da jiki, ga tumbi sai dai tumbin bai yi muni da yawa ba, ustazu ne sosai domin ya tsayar da gemun sunnah.
Ku'di yake sakar mini da suturu na alfarma, ga kuma mutunta ahalin gidanmu.
Dada kanta sonsa take yi a dalilin idan zai zo sai ya kawo mata rafar sabbin ku'di, y'an 100, da na 50, da na 20.
Yana cewa gashi ta ajiye canji a hannunta, duk zuwa kuwa. Ga ledar tufa da kilishi.
Nawa kuwa y'an 500 da 200 ne.
Bulkachuwa ya zama magayak'insa.
Kullum sai ya masa kamfen, fa'di yake "Gidan ki daban zai baki Asiya, idan kika yi sa'a ma Umrar bana da ke za'a yi, aikin hajji kuwa tabbas ne.
Ba ruwanki da tsufansa, lallaba ki zai yi.
Ni kaina alherin da nake samu a jikinsa ba ka'dan ba ne.
Kin ga "Na kalli hannunsa da yake karkada wa.
Mukulli na ga ni ya ce "Mashin ya ba ni sabo dal, gwamnatin jahar Bauchi take raba wa matasa, shine ya saka sunana.
Dan Allah Asiya ki so mutumin nan, oh wani hanin ga Allah baiwa.
Yarinya kin tako arziki, na tabbatar Gwaggo data haife ki da akwai wutar Nepa a time din Wallahi.
Na miki murna ma da wannan dan tsurut din bai same ki ba.
Ai ke babbar mace ce, sai manyan maza, amma yana tafiya tamkar iska ta hure, kirjinsa duk bai fi allona na makarantar tsangaya ba".
Na b'ata rai na ce "Yaya J din kake yiwa haka akan bare?
Sannan nima ai y'ar tsurut ce ta ina na zama babbar mace?"
Ya murmusa ya ce "Ba sai na bu'de maganar ba, ke ma kinsan yadda ake miki layi ai akwai sirri na mussaman a tare da ke. Na'kasunki biyu ne tsayayyiyar zuciya, kuma taurarriya, da fitsara, dole handle dinki sai tsayyayen namiji k'arfaffa ba lusari irinsa ba".
Na sake b'ata rai na ce "To yadda kake ganin zuciyata, tasa har tafi tawa tsayuwa da jarumta".
"Ke tafi can, me kika sani? Wai har yau son Jabir kike yi? Tabdi jam lallai so ba k'arya ba ne. Jiya fa na gan shi goye da Maijidda a mashin ina ga d'an yawon shan iska suka fito".
Nan da nan idona ya k'ada sosai hawaye ya cika su, ya mike yana fa'din "So sorry Asiya Toro. Ki gode Allah da ya kawo miki Honarable Zaki. Domin da ki yi kuka a inda kike so, gara ki yi a inda ake son ki, da ki yi kuka a gidan cin abinci gara ki yi kuka a gidan daula sosai, domin mu maza da kika ganmu so baya hanamu murza kanku".
Na girgiza kai na ce "Zan amince ne idan kai ma ka yarda
zaka shirya da Nasiba, ni shaida ce akan ba wanda take kula wa saboda kai".
Ya bata fuska ya ce "Kin san Allah?
Zan ci mutuncinki Asiya Toro! Kada ki saurare shi mana, shawara na baki saboda ina nufin ki da alheri, idan baki so ba, ki sallame shi, ki jira wanda zaki dinga kuka a gaban murhun gawayi, da kishiya.
Ga kuma ba'kin cikin da zaki kunsa a wajen ahalinsa, shasha da bata san me ya dace ba".
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*.
✍️
*BAKAR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*ALBISHIRINKU*
*MASOYAN LITTAFAN MARUBUCIYA HAFSAT C SODANGI*!
*DUBA DA YADDA KUKE KEWAR RUBUTUNTA YA SANYA TA YI SHIRIN SAKE DAWOWA DAN TA SAKE MUKU WANI RUBUTUN SABO DAL*
*AMMA KAFIN HAKAN TA DAWO MUKU DA TSOFAFFIN LITTAFAN TA ZUWA KAN WAYA, DAN KU SAKE BITA TARE DA NAZARIN KYAWAWAN SAKON DA TAKE NUFIN ISARWA GAREMU*.
*A YANZU HAKA LITTAFAI HUDU NE RIGIS*
*WAYYO DUNIYA 1-3*
*KYAUTATA 1-3*
*DAGA K'IN GASKIYA 1-3*
*MATA MASU DUNIYA 1-3*
*KO WANNE 1K NE AMMA AKWAI DISCOUNT IDAN ZA'A SIYA SAMA DA GUDA DAYA*
*MISALI GUDA BIYU-1500*
*GUDA UKU 2500*
*GUDA HUDU 3500*
*ZA'A TURA KUDIN TA ASUSUN MARUBUCIYAR KAMAR HAKA*
*0082739293, ACCESS BANK HAFSAT YUNUS ABDULLAHI*
*SAI A TURO MINI SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*SAI NA BADA LITTAFIN DA AKE SO*
*MADALLAH DA KARFAFA GUIWARKU*
*MADALLAH DA SOYAYYARKU GA RUBUTUNMU*
*AKWAI LITTAFANTA SAMA DA GUDA GOMA DA A YANZU SUKE SOFT COPIES, KAWAI KI TAMBAYI DUK WANDA KIKE NEMA A WAJENA CIKIN LITTAFANTA NA BAYA*.
*Saura kiris shaufakan kyauta su k'are*
*Turka turkar da ke cikin labarin nan kabiran ne. Har yanzu shimfi'da kawai muke yi bamu kutsa labarin ba tukun*.
*HANZARTA ki shiga tafiyar dan karfafa guiwarki ga marubuciya da karatun cikin SALAMA.*
*Kudin karatun ki 500/1k*
*Via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Dahiru*
*Zenith Bank*.
*Ko*
*7061488065*
*Surayya Dahiru Ibrahim*
*Opay Bank*.
17&18.
Na bishi da ido yana tafiya cikin gajeren wando tiri k'wata, da riga t shirt mai kama da singeleti.
Ko kunya baya ji.
Na girgiza kai ban ce komai ba dan nasan da dukkan zuciyarsa ya yi magana.
Kwanaki suka yi ta shud'ewa har aka samu wata uku da auren ahalin gidanmu, dai-dai da wata biyu da haduwata da kwamishina.
Zuwa lokacin alherin da ya same mu ba ka'dan ba ne.
Domin ta hannun Yaya Salisu ya saka an gyara mana band'akin k'ofarmu an zamanantar da shi, an yiwa kofar kwaskwarima ta farfad'o sosai.
Sannan ya karbi takardun Yaya Salisu da Yaya Rabi'u da alk'warin zai nema musu aikin yi.
Hatta Yaya Musa sai da ya saka ya samu tallafin injin nik'a da na markade, kuma Alhamdulillah yana zama wajen sana'ar.
Tun Babanmu yana fa'din hidimar ta yi yawa mussamna yadda ake sauke mana kayan abinci, wannan kam duka kofofin gidan ake sauke wa.
Har ya koma yin shiru domin dai kwamshina bai fasa ba, sai dai ma ya ce "Tallafi ko samo aikin yi ga matasa ai hakkinsu ne domin y'an jahar Bauchi ne, hanya kawai na yi musu, ko ba ta sanadin Yabi ba, matu'kar ina da damar yin hakan ai nima hakki ne a kaina na yi hakan."
Nan da nan na canja tunda cimar Gidanmu ta canja, ga kayan kwalliya da dangin shower gel masu kyau. Domin dukkan setin kayan Oriflame na siye su ta online. A hannun Aisha lame 07036662633 tunda na bude account saboda manyan mata masu yin transfer din kudin lalle.
Sutura kuwa duk zuwa sai ya kawo mini su, manyan zannu wa da leshi.
Na sake zama so cute, ga fata tana sheki ga kuma sutura ta d'aukar hankali.
Hijabai har sun mini yawa duk da ina bawa Nazira da Yaya Ummi, bai ta'ba kawo mini mayafi ba, sai dai abayoyi kaloli daban daban, hakan ya tabbatar mini mai ra'ayin kiyaye ka'idojin shari'a ne.
Su Gwaggo kuwa komai zai kawo uku ne tare yake musu babu banbanci, hakan ya sake daga darajarta domin kuwa duk y'ay'an d'akin Mama bata bari ko sabulu suna kawo uku. Sai dai ita ka'dai, idan yan arzikin suna kusa ta samm musu, idan basa kusa sai ta bawa Inna a boye, Gwaggo kuwa ko labari.
Bakin Mama ya mutu murus sai dai dama tun abin da na yi a auren Nazira ta saukaka al'amura masu yawa.
Ba sai kuma aka fara cece-kucen auren kwadayi za'a yi mini ba, ban da haka ta ina za'a dauki yar mitsitsiya kamata a bawa wannan mutum da idan na tsaya a gabansa sai a zaci yarsa ce bama ta fari ba.
Su Baban Tsakiya suka fara raddi, domin ba karamin gyagije wa ahalin Baban Marina muka fara ba.
Dada ta fara taka tsantsan da lamarina, tunda yanzu tana samun kayan ciye ciye da ku'di saboda ni, ga turare da atamfofi da ya kawo mata har sau uku.
Ni da kaina na gamsu ku'di suna kan gaba wajen magance tozarcin d'an-adam, haka nan suna saka wa a ga girman ka aji tsoron zuciyar ka ko da baka da siffa mai kyau.
A raina sai k'yamar wannan *BAK'AR TA'ADAR* nake yi. Domin na hakikance rashin wadata ya sanya aka mayar da ubanmu ya koma k'arami a cikin gidanmu, wai daga d'an zuwan Kwamshina har an fara raga masa, inda ace shine mai ku'din ko wani cikin y'ay'ansa fa?
Sai dai Baban Tsakiya da na Kasuwa basu sanya wa lamarin albarka ba, asalima fadi suke a ina na hadu da shi? Ba d'an gari ba? A sharholiyarmu muka ha'du kawai.
A raina bana sonsa, bana burin aurensa, amma ya zan yi?
Tunda shi ka'dai ne ya tsaya ya na sona a yanzu, sannan gaskiya na gaji da zaman Gidanmu ba dan komai ba, sai dan yadda nake shan matsin lambar na fito da miji da kuma k'iyayya da aibantawa.
Sannan tunda ake yin hassada a lamarin, sai na kudire zan sadaukar da komai na aure shi, ko dan ya zame mana garkuwa a k'ofarmu tunda mutumin kirki ne wanda ya siffantu da dabi'aun addini.
Rannan kwatsam na fito daga inda nake koyon kwalliya sai ganin Yaya J na yi a zaune kan wani dutse da alamu suka nuna dakona yake yi.
Na zo zan wuce ta gabansa tunda ba zai yiwu na koma na fasa tafiyar ba.
Sanye nake da k'aton hijabina har kasa irin wadda ake ya yi mai hula ta baya.
Ban ce masa k'ala kanzil ba, asalima ban nuna na ganshi ko na san shi ba.
Da azama ya biyo ni a fusace ya ce "Yabi ashe zaki iya ganina ki mini irin wannan wula'kancin?"
Ban ce komai ba, ban kuma fasa tafiya ta ba.
Yana bina yana fa'din "Tun jiya ban runtsa ba, ba abin da nake so irin na ganki na tambaye ki abin da ya rikita mini al'amura".
Na tsaya cak na ce "Tambaye ni Jabir, ina jin ka".
Ya zuba mini ido, nima na zuba masa tsawon lokaci, ga mamakina sai kawai abin da na binne a kansa ya nemi taso mini da k'arfin gaske.
Na yi maza na dauke kaina, tare da sake d'aure fuska.
A sanyaye ya ce "Da gaske ne Mustapha Zaki yana son ki?"
Ba ja in ja na ce "Da gaske ne".
Ya kadu amma sai ya ce "Ke nan kin amince masa?"
Na kalle shi cikin ido, na ce "ko ban amince dan ra'din kaina ba, idan kaddara ta amince masa ai shike nan kamar yadda kaddara ta amince maka zama da Maijidda".
Na yi gaba na fara tafiya, ya biyo ni yana fa'din"me kike nufi Yabi?"
Ban kula shi ba, domin gaba'daya wani irin abu ya cushe mini zuciya da mak'oshi.
Sai fa'di yake "Kina nufin zaki aure shi ke nan?"
A tunzure na juyo na ce "A a ba aurensa zan yi ba, debe mini kewa zai yi, kafin a sahale maka ka nemi aure na".
Ya girgiza kai ya ce "Wacce irin magana ce haka Yabi?"
Kai tsaye na ce "Mai da'di kuma ta gaskiya".
Ya rasa yadda zai yi, hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi.
Ya saki gauron numfashi ya ce "To ni kuma mene ne makomata ke nan?
Na kadu na ce "Ban gane ba? Nusar da ni."
Kai tsaye ya ce "Ina nufin ya maganar tawa soyayyar, ya batun aurenmu?"
Na kafe shi da ido cikin tsananin kad'uwa.
Kawai tambayar kaina nake yi "Ko dai ya samu mental disorder ne?
Amma sai na shanye mamakina na ce "Jabir ke nan".
Da sauri ya ce "ki ha'da ki ce Jabir Badamasi Toro, ba komai ba ne watarana In sha Allah zaki dawo da yayan domin ko kin yanke alakar da ta ha'damu ai baki isa ki wanke jinin da ya cakudamu ba"
Na daure fuska ainun ban ce k'ala ba.
Ya ce "Fa'da mini inda kika ajiye ni Yabi! Ina son ki, ina son na rayu da ke, ki yiwa Allah kada ki zalunci zuciyoyinmu, ki mini adalci ko da kina mini kallon azzalumi."
Na murmusa na ce " Wanne irin adalci kake nufin na yi maka?"
Ba nauyi ya ce "ki aure ni Yabi, ki bani damar da zan rayu da ke".
Ido cikin ido na ce "To kuma ya zaka yi da Maijidda da aka baka dan ana ganin ta fini nagarta, kuma y'ar babbar k'ofa ce?"
Ya ha'de rai ya ce "Ni da ke ne anan ba ruwanki da kowa, ni nake tsaye a gabanbki, kin sani kuma ina son ki, ina kaunar ki, idan kin bani dama ina da sauran dama uku a gaba da shari'a ta bani".
Na jinjina k'arfin halinsa na murmusa na ce "zaka ha'da ni da Maijidda kishi? D'iyar attajiri irin Baban Kasuwa da ta fak'iri irin Baban Marina?"
Ya naushi hanunsa ya ce "Kina da bak'ar magana Yabi! Ki yi kokarin kiyaye harshen ki, gubar harshe ta fi ta maciji dafi".
Na yi gajeriyar dariya na ce ", Gaskiya na fa'da amma tunda ba'a sonta, to na janye"
Nan da nan ya sace ya ce "To ki yafe mini, ina son ki, idan har kika ba ni dama zan tsaya miki, ba zaki yi kuka da ni ba. Zan fafata da duk wanda ya nemi shatale farin-cikinki da iznin Lillahi."
Idona ya k'ada tsakanina da Allah ina matu'kar son Yaya J ba kowa zai fahimci hakan ba sai wanda suka yi soyayyar k'uruciya ta rikide ta zama ta gaske, irin wannan soyayyar tana matu'kar tasiri a cikin zuciyar banu adam.
Amma na sani idan zan yaudari kowa, bazan yaudari kaina ba. Ba za'a ta'ba bari ya aure ni ba. Bayan k'iyayyar ubana to ni kaina wata irin kiyayya iyayensa suke mini wanda basu ki su gan ni da abin kunya ba.
Dan haka hawaye ya b'alle mini, da rawar murya na ce "Yaya J ba kowanne Dan Adam ba ne yake nasarar rayuwa da wanda yake so.
Mata da yawa ba wanda suke so k'addara ta aura musu ba, hakan nan mazan.
Yarda da k'addara kuma sharadi ne na cikar imani. Ka sani, na sani ba za'a ta'ba barinka ka aure ni ba. Na tabbatar za'a bari ka auro ukun da kake kirari a ko'ina amma kuma ba za'a bari ka aure ni ka'dai ba, na gamsu kana sona, nima kuma har yau din nan ban so wani kamar ka ba, ba kuma zan so din ba.
Mu yi addu'a Ubangiji ya sanyamu cikin masu soyayya dominsa wanda sakamakon hakan Aljannah ce".
Idonsa ya k'ada ya ce "kin yi magana ta hankali Yabin J. Rabon da na samu aminci irin na yau, tun kafin ki juya mini baya. Abin da nake so da ke na yarda na gasgata ki, amma ki bani dama na sake jarraba wa ko za'a dace a wannan karon, zan yi iya kokarina dan na same ki, ai na yi biyayyar a farko".
Na murmusa na ce "Shari'a bata hana hakan ba, amma zan ji nauyi mai yawa a ce ina kishi da Maijidda! Sai kuka ya subuce mini na gaske".
A rikice ya ce "Wallahi zan iya rabuwa da ita matu'kar ita ce cikas din cikar burin ranmu.
Sai dai ace na aikata *BAK'AR TA'ADAH* na saki aure akan wata macen da bata zo hannuna ba".
Na girgiza kai na ce "Ba za'a kai ga hakan ba".
A hanzarce ya ce "To ki huce da ni, ki bani damar auren ki".
Hawaye na zuba na ce "Na baka Yaya J. Nan da sati biyu ka fito, idan har ya wuce baka bayyana a gaban Baban Tsakiya da Baban Kasuwa da nufin ka je neman aurena gabansu ba, ka tabbatar magana ta k'are a tsakaninmu ta soyayya har abada, na kuma baka dukkan damar da zan iya, sai dai ka sani ba zaka ha'da ni zama da ita a gida guda ba".
Ga mamakina sai gani na yi ya zube a kasa yana sujjada.
Ya dago ya ce "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah.
Zaki ji sakona kuwa daga yanzu zuwa ko wanne lokaci. Sannan na miki al'kawarin a Bauchi zan nema miki inda zaki zauna kafin na samu halin gina miki naki gidan".
Ya tako mini har titi ya tarar mini Napep ya biya, na tafi yana d'ago mini hannu cikin matsanancin farin-ciki.
Ni kaina wani irin shauki ke fizgata mai danne dukkan bacin rai.
Na manta k'iyayyar da Baban Tsakiya yake mini azima ce.
Sannan Baban kasuwa ba yadda za a yi ya goyi bayan ayi wa diyarsa kishiya da ni.
Amma dukkanmu hankalinmu ya gushe duk da ni din gatse na yi masa, amma TASIRIN soyayyar da nake yi masa ta taso mini haik'an ta saukar mini da farin-ciki mai tsananin gaske. Har nake fatan al'amarinmu ya kasance.
Na isa gida na ci abinci na yi sallah na hau kitso tunda mutum