Showing 51001 words to 54000 words out of 184118 words

Chapter 18 - Bakar Taada Hausa Novel Complete

zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*

*Dada*
Bulkachuwa zaune a kusa da ita kan baranda sai faman bacin rai ya ke yi.
A hankali ta ce "To menene zaka tisa ni a gaba kana ta faman k'unci kaki fa'da mini damuwar ka?"
A hankali ya ce "Jabir ne mana ba dama Yabi ta fita sai yasan yadda ya yi ya tare ta. Gaskiya abin ya fara tayar mini da hankali, ki fa'da masa ya bari".
"A sanyaye ta ce "zan fa'da masa kaima ka kara hakuri duka kwana nawa ya rage ne? Ai da zarar am shafa mata fatiharka dole kuma su kiyayi juna."
Bai kai ga amsa mata ba, ya ga masu aikin gini da fenti sun shigo da kayan aiki sun shige k'ofar ciki".
Ya kalli Dada ya ce "me suke yi a ciki ne?"
Da walwala ta ce "Tun dazu suke fama, sallah suka je yi. Kawunanka suka saka a gyara maka wajen sun ce bai kyautu su barka da neman muhalli ba".
Ransa ya baci ya ce "Shi Baban Tsakiya ne zai ce haka?
Me yasa bai mini gini irin na Jabir ba?
Idan kuwa Baban Kasuwa ne me yasa ya hana Salisu zama a lokacin da ya roki a bashi ya zauna kafin ya samu sararin yin nasa?"
To bana so, na sani kuma Yabi ba zata so wajen ba, ya yi tsufa da yawa".
Daga haka ya tashi ya barta tana faman buga salati tare da fa'din "Ni Binta ina kallon wuyar zama irin ta y'ay'an yau. Komai aka yi musu babu mutunci bare su yi godiya.
Wannan zamani da wuyar sha'ani yake".
Ta yi k'wafa sannan ta sake cewa "Allah na yi tuba, kai ne mamallakin zamani. Allah ka shirya".
Har washagari bani da sukuni, a kuma wannan ranar aka kawo mini lefe daga Bulkachuwa.
Sosai aka zuba kaya a lefen tamkar na masu wadata. Na sani kuma y'anuwan ubansa da Babah ta Bulkachuwa suka hada kayan, sisinsa bai yi ciwon kai ba.
Maza ne suka kawo kayan dan haka ba ayi gayya ba.
A k'ofar Dada aka taru aka ga ni, masu fatan alheri na yi, masu shagube na yi.
Sai da ya kwana ya yini a wajen Dada sannan ta saka aka kawo kofarmu.
Hatta Babanmu sai da Inna ta bu'de masa kayan ya ga ni, ya yi addu'ar alheri tare da fa'din "Oh haka suka yi wahala mai yawa?"
Ni kuwa ko kallon kayan ban yi ba, bare na ga mene ne a ciki.
Da yamma ina zaune ina k'ulla wa Gwaggo siga.
Sai ga Anas ya shigo ya kalle ni ya ce "Dada ta ce ki je yanzu".
Na bata rai na kasa amsawa domin na tsani na je kofarta saboda dalilai masu dama.
Na farko haushinta nake ji.
Sannan bana son ganin mawuyacin halin da nake ganin Nasiba a ciki. Domin sosai ta mak'ala wa zuciyarta son Bulkachuwa. Kishina sai ya galgalata yake yi, duk da bata bu'de baki ta mini maganar ba, sai ma murnar da ta yi mini na samun miji irinsa wacce na ji tamkar ta caka mini wuk'a ne. Wannan shine daidan wani, karkataccen wani.
Sannan kuma ina sake k'in shiga wajen Dada ne saboda kada na ga Tijjani. Shi yasa ma bana zuwa gaishe ta sai hantsi ya yi sosai.
Gwaggo ta ce "Je ka ce tana zuwa".
Ya ce "To" ya tafi.
Akan dole na dauki mayafi na nufi shashin Dada.
Ina hasashen menene dalilin kiran?
A zauren Dada na tarar da shi a tsaye. Zuciyata ta tsinke sosai. Na yi kamar ban gan shi ba. Na wuce da nufin shiga cikin gidan.
Ya bu'de baki ya ce "Ni ne mai kiran na ki ai".
Na tsaya cak. Ba tare da na iya ce wa kanzil ba.
Ya saki gauron numfashi kafin ya ce "Ga ni na yi abu ya matso kusa sosai amma babu fahimta a tsakaninmu bare nasan abubuwan da kike bu'kata".
Na ja tsaki na ce "auren so ake yiwa irin wannan tagomashin".
Fuskarsa ta yamutse kadan. Ya ce "To na biyayya fa?"
Nan da nan idona ya ciko da hawayen takaici. Na yi k'asa da kaina na kasa ce wa komai.
Murya babu amo ya ce "Abokina da muka yi karatu a Gad'au gobe zai zo.
Ya dame ni akan na ba shi lambar amarya ko na kawarta dan ya ji irin yadda ake sallamar amarya da kwayenta a nan, da kuma abubuwan da kike bu'kata".
Na ja tsaki tare da ce wa "Komai zai fito ta hannun ka ko ta sanadin ka bana sonsa ba kuma zan kalle shi ba."
Ya zuba mini ido sosai cikin damuwa mai yawa.
Cikin wani irin yanayi ya ce "Asiya Toro alfarma d'aya nake so ki mini, ko da kuwa ita ka'dai ce alherin da zaki yi mini. Ki taimake ni kada ki tsinka ni, ki yi mini wannan arzikin dan Allah".
Ban san ya aka yi ba, jikina ya yi sanyi, mussaman yadda na ga ya yi kalar tausayi tamkar ba Bulkachuwa ba.
Na yi shiru amma fuskata a cukune sosai.
Ya sake ce wa "ki bani lambar wacce zai yi magana da ita Asiya. Sannan idan sun zo mini ranar daurin aure kada ki wula'kanta ni a gabansu. Na yarda bayan sun tafi ko menene ki yi mini, zan jure".
Na sake gallah masa harara tamkar idona zasu fa'do k'asa. Tare da ce wa ban iya Yaudara ba, ba kuma zan fara yanzu ba. Ai na sha jin kana fa'dawa abokan naka ba macen da zaka aureta alhalin kasan bata sonka. Ba ayi macen da zata ce baka yi mata ba, sannan ka nace sai ka aure ta, duk wanda ya sanka yasan wannan alwashin na ka. To me yasa yanzu ka yarda zaka aure ni alhalin kasan bana son ka, bana farin-ciki da al'amarinka gaba'daya?"
Kuka ya k'wace mini sosai.
Murya babu amo ya ce"Kaddara ta ce a hakan Asiya! Ni kaina na kasa gane kaina.
Wata'kila cika bakin da na yi ta yi ne, ya sanya aka jarrabe ni da son auren wacce ta washe ni, wata'kila kuma Ubangiji ne zai mini wani alherin ta sanadin ki shiyasa ya jingina mini sonki mai yawa."
Na sake jan tsaki na ce "Ba wani alheri domin da zan ga sadda zai tunkare ka zan karkatar da shi na bawa wanda suka fika mutunci da so na".
Ya girgiza kai ya kasa magana domin ransa ya baci idanuwansa har canja wa suka yi.
Tsawon sakwanni bai iya ce wa uffan ba.
Ni kuma sai fama nake da kuncin zuciya. Sannan sai yanayinsa ya sanya na ji babu da'di, domin duk yadda na tsane shi. Sai na ji ya d'an ba ni tausayi ka'dan.
Muna haka Baban Marina ya dawo, ya zo wuce wa ta babban zaure ya hango mu a zauren Dada.
Ina kallon yadda yake murmushi yana amsa gaisuwar Bulkachuwa da walwala.
Ni kaina a wannan lokacin ya sace da fishin da yake yi mini. Domin da murmushi a fuskarsa ya amsa barka da zuwan da na yi masa.
Har yana fa'din "Sannunku Yabi"
Kunya ta saka na yi nufin shige wa wajen Dada. Sai ce wa ya yi "Dawo ku cigaba da tattaunawarku. Allah ya yi muku albarka. Allah ya sa ku zamo abin alfahari, Allah ya shiga al'amarinku".
A hankali Tijjani yake amsa wa yayin da ni kuma ban amsa ba ko da a zuci ne.
Yana shige wa ya kalle ni a sanyaye ya ce "Asiya Toro Baban Marina bai dauki auren nan namu da wasa ba fa. Mu ha'da kanmu, kada mu ba shi kunya dan Allah".
Na ja tsaki tare da ce wa "Ni Malam na gaji tafiya zan yi".
A sanyaye ya mik'o mini wayarsa ya ce "Saka mini lambar"
A tunzure na ce "Ba ni da k'awa".
Da sigar lallashi ya ce "Yanzu duk ro'kon da na yi miki?
Farin cikin da Baban Marina ya yi a dalilin ganinmu bai sa zuciyarki ta rusuna ba?"
Na murguda baki na ce "To ai dai kasan ba ni da k'awaye, Adda Nazira ce kuma ta yi aure, sai kuwa Nasiba ita ma kuma ai auren ta za'a yi ko?"
Ya girgiza kai ya ce "Hakane! To Ina wannan fara mai dan jikin nan da yanzu kuke dawowa daga boko tare? Sannan tare nake ganinku a wajen koyon kwalliya".
Na zuba masa harara na ce "Tsabar sawa mata ido har ka gane halittar ta?
Har abada ba zaka burge ni ba Tijjani. Ba kuma zan baka lambar ba, domin dai da bakin ka ka tabbatar mini nema cikin nema haramun ne. Bari na shaida maka tuni an kai ku'din aurenta. Dan nasan kana iya lallabawa wajen ta".
Ya yi sororo sai kuma b'acin ran fuskarsa ya ragu.
Ya ce "Bana ma son lambar, na fasa, zan ba shi lambarki sai ki fa'da masa ta yadda zai turo miki ku'din kunshi da na kitso, ya damu akan a sallame ki ke da kawayen ki ne".
Na yi shiru ban ce komai ba.
A hankali ya ce "ya yi miki hakan?"
Na sake yi masa banza.
Ya sassauta ya ce "please mana Asiya Toro".
Na harzuka na ce "Gaskiyar magana baka yi mini adalci, idan ina kaunar yadda kake gatsa sunana ha'de da na garina Allah ya tsine mini!.
Ya dan murmusa ya ce "Da sannnu idan kin kwantar da hankalinki zan daina fa'da, na samo miki sunaye masu da'di da tsuma zuciya".
Ba'kin ciki ya sake turknike ni. Na ce zuciyar waye din zata tsumu?"
Ya make kafa'da ya ce ta "Asiya Toro".
Na yi kwafa na ce "Ai na gane zuciyarka babu alheri ne shi yasa kake k'yashin ce mini Yabi. Da'din abin ma dubun ka suna fa'da mini cikin girma da arziki".
Ya ce"Nan da lokaci ka'dan komai zai zama tarihi. Kin ga dai na nemi arzikin ki, ban kuma mayar miki da martanin bakaken maganganun da kika yi ta yab'a mini ba. Ina sake ro'kon ki idan abokina ya kira ki, ki taimake ni kada ki bayar da ni."
Ban amsa ba. Ya sake cewa dan Allah Asiya Toro".
Cikin fishi na ce "Na ji".
Da'di ya kama shi ya dinga fa'din "Na gode sosai. Ina fatan na ga ranar da zaki fahimci irin tarin alkhairorin da suke zuciyata mussaman akan lamarin ki".
A hanzarce na ce "Ai kuwa dai ba zaka ga ranar ba".
Ya girgiza kai tare da ce wa "Babu damuwa time will tell".
Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ina son na tambaye ki, zaki iya zama a wanccan daya bangaren na Dada?"
Maimakon na yi masa magana da baki, ai sai kawai na d'ora hannu aka na fashe da wani irin kuka na tashin hankali.
Murya na rawa na ce "wato dai a cikin masifar gidan nan zan tabbata? Idan kuwa har a cikin gidan nan ake nufin na zauna da sunan zaman aure Allah ya dauki raina kafin hakan ya tabbata. Na shiga uku ni Yabi".
Ya rikice ya hau fa'din yi shirun ki dama na fa'da mata wajen ya miki local da yawa, sannan baki samu sauyin muhalli ba. Yau din nan duk inda gida yake zan nemo kafin dare. Da ku'di a hannuna.
Yi hakuri ki daina irin wannan kukan. Kin ga yadda kika koma kuwa Asiya?"
Da k'yar ya lallaba ni, na yi shiru.
Ya zura hannunsa a aljihu ya ciro cakulet manya masu da'di da tsada k'waya biyu ya mik'o mini.
Bansan ya aka yi ba na fashe da dariya ga kuma hawayen ba'kin ciki na ziraro mini.
Da yake d'an duniya ne sai kawai shima ya fashe da dariyar yana cewa "Ni nasan Ubangiji zai cusa miki soyayyata dan yasan yadda ya gina ki a tawa zuciyar. "
Da k'yar na samu dariyar ta tsaya.
Da hawaye a idona na ce "me zan yi da wannan abar?"
Ya zuba mini ido yana wani lumshe su ya ce "Wai fa dan kada na zo hannu na dukan cinya ya sanya na taho miki da su"
Na rasa me zance masa tsabar takaicinsa da ya d'ada makure ni.
Na ce "To ajiye idan ka ga Yarinya k'arama ka bata amma ba ni ba".
Ya waske ya ce "Asiya Toro maraina ka'dan fa barawo ne. Kowa ba iya karfinsa zai yi kyauta ba?
Kin san wahalar da na sha kafin na samo miki wannan cakulet din a garin nan? Saboda nasan kina son ta ne. Amma ban burge ki ba? Idan kin yi hakuri wataran katon zan siyo na ajiye miki."
Da sauri na ce "da dai ace ba hannun jinjirai ne da kai ba tsabar rowa."
Ya nuna kansa da yatsansa ya ce "Ni ne mai hannun jarirai? Lallai kuwa zan baki mamaki Asiya Toro local government. Bauchi state of Nigeria".
Ko kula shi ban yi ba na wuce shi na tafi na bar shi a tsaye. Tsabar takaicinsa da ya sake kular da ni.
Ya d'aga murya ya ce "Sai gobe zan dawo, ko da anjima ma na dawo?"
Da kansa ya bawa kansa amsa da ce wa "To zan dawo da daddaren ran ki ya da'de."
Har na isa k'ofarmu mamakin Bulkachuwa kawai nake yi. Ban da dai ya riga ya same ni a araha ya rasa me zai kawo mini sai cakulet k'waya biyu. Shi ko kunya bai ji ba? Amma da na tuna halin rowarsa sai kawai na janye mamakinsa. Na shiga tambayar kaina wanne irin zama zamu yi ne da shi?
Na tabbatar sassaucin da ya yi dan baya son na yarfa shi ne.
Amma da tuni ya baje mini kalolin rashin mutuncinsa.
Na zauna na fara kokarin cigaba da k'ullin sigan.
Zuciyata ta shiga hakaito mini kayan jikinsa.
Shadda ce a jikin sa kalar ganye wato kore sosai. Ya d'ora hular sanyi mai tambarin kungiyar Manchester United. Na sani kuma d'an ya boye wa Baba curarriyar sumarsa ne tunda zafi ake yi ba sanyi ba.
Daga ni tun farar safiya ya sanya kayan a hakan kuma shi ya k'ure malejin kwalliya ne.
Na ja tsaki tare da ce wa "Idona ya saba ganin samari ma'abota wanka da gayu. Irinsu Yaya J da Nuru Tanim. Ta ya ya Bulkachuwa zai burge ni?."
Gwaggo ta shigo ta ce "me ya faru da kika je?"
Na yi kasa da kai na ce "Ba Dada ba ce ashe".
Ta ce "To waye?"
Na bata rai duk da kan nawa yana kasa na ce "Tijjani ne".
Daga hakan bata kara ce wa komai ba ta dauki abin da zata dauka ta fice tsakar gida.
Washa gari da azahar ina kwance a tsakar daki sai ga Nazira ta zo. Karon farko da ta zo gida tunda aka yi mata aure. Duk rud'anin da nake ciki sai da na tashi da azama na rungume ta.
Muka haye k'aramin gadon Gwaggo da muke kwana a kansa ni da ita tun fil'azal.
Da murmushi a fukskata na ce "Yau Adda Nazira ce a gidanmu?"
Ta d'aka mini duka tare da cewa"oh har kin cire ni a cikinsa, to kema kwana nawa ya rage miki mu yi kunnen doki?"
Na bata fuska sosai. Ta ce "daga wajen Dada nake suna can, suna artabu da Yaya Bulkachuwa akan inda zaku zauna.
Wai akan me zai je ya kama haya tamkar ba shi da kowa a Toro?
Shi kuma ya kafe ba zai zauna a cikin gidan nan ba.".
Na bata rai na ce "Ai Wallahi na fa'da masa indai ya yarda da tsarinsu to kuwa sai dai a tsine mini dan bazan zauna a gidan nan ba'kin ciki ya karasa ni tun ajalina bai zo ba"
Adda Nazira ta ce "Haba ashe tirjiya ya samu daga gare ki, kin ga yadda ya fitittike akan ba zai zauna a wajen ba?
Dada har da kukanta wai sai da ya bari su Baban Tsakiya sun gama gyara masa wajen sannan ya ce zai fita ya kama haya tamkar wanda bashi da galihu a Toro? Shi kuma kinsan shi ya ce "Salisu da yake hayar rashin galihu ne ke nan?
Ashe ashe Gimbiya Yabi ce ta saka ya rikice ya turje.
Ya kama miki gida mai kyau a bayan sakatariya. Ba ki ga gidan ba. Yanzu muka dawo a mashin dinsa ya goye ni muka je ya nuna mini gidan. Ni Wlh har na ji na daina k'insa. Kin ga rawar jikin da yake yi. Sai fa'di yake ya kika ga wajen Nazira? Nasan idan ya burge ki to zai burge kanwar ta ki ma.
Gaskiya Yabi ke d'in mai sa'a ce. Gaba'daya kin rikita namiji irin Yaya Bulkachuwa. Murna nake yi, da dukkan zuciyata nake jin addu'armu ta karbu. Da ikon Ubangiji sai kowa ya yi mamakin alherin da zai biyo bayan wannan auren."
Na tab'e baki na ce "Hmm ai ni dai an cuce ni kawai. D'azu muna maganar k'awayen amarya. Na ce masa ba ni da k'awaye, ke ce to kuma kin yi aure.
Yana bu'de baki da yake shi d'in bunsuru ne sai ce wa ya yi wai ina k'awata fara mai dan jiki. Kin san wa yake nufi?"
Kafin ta ce komai na zarce da ce wa "Shafa'atu yake nufi fa. Har ya k'yalla ya ga halittu a tare da ita shine zai silala me za'a yi da Tijjani ne. Na fa'da cikin kunan rai.
Ga mamakina sai ganin Nazira na yi ta k'yal-k'yale da dariya sosai. Sannan ta ce da wuri haka Yabi?"
Na bata rai na ce 'ban gane ba?"
Ai kuwa cikin ido ta ce" tun yanzu kin fara kishin Yaya Bulkachuwa ina kuma idan kin shiga hannunsa?"
Hawaye ya b'alle mini ina ce wa "Allah ya sauwake, ashe ba ki fahimce ni ba Adda Nazira?"

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*

*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.


*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login