Showing 93001 words to 96000 words out of 184118 words
Chapter 32 - Bakar Taada Hausa Novel Complete
ha'kurin.
Kallon ya shige ni, na fara bubbuga k'afa. Ina ce wa "Saboda Allah me na yi maka?"
Ya jijjiga kai ya yi tafiyarsa, ba tare da ya ce uffan ba.
Ni kuwa da na hasaso Dada a masai sai na sake tuntsire wa da dariya.
Sai yamma lis ya dawo. Kai tsaye falo ya shiga. Na bi shi ina masa sannu. Na zauna. Ya ce "zubo mini abincin".
Na fita na kawo masa, ban zauna ba sai da na dauko masa ruwa a fridge.
Sai da ya gama cin abincin. Sannan na kalle shi bayan na d'aure fuska na ce "Ya jikin Dadan kuwa?"
Kai-tsaye ya ce "Da sau'ki. Amma ta samu tagarde a hannunta."
Na sake yin kalar tausayi na ce "Ayyah! Allah ya bata lafiya."
Ya amsa da "ameen" yana daddana wayarsa.
Can na nisa na ce "Tijjani wa ya yiwa Dada bik'in kashin da ta kwaso?"
Kamar ba zai yi magana ba. Sai kuma ya ce "Gwaggo ce".
Na zabura na dafa k'irjina na ce "Gwaggota?"
Kansa na k'asa ya ce "ita fa".
Kawai sai na fara kuka ina cewa "Na rantse da ina nan bazan bari ba. Duk yadda take tsangwamar ta sai kuma ta zo ta yi mata irin wannan wahala alhalin tana da y'ay'anta birjik?"
Kansa na kan wayarsa dai, ya ce "Ai da yake tana mutunta mijinta ne. Baban Marina aikin ya kama, da yake ita mace ta gari ce, sai ta fanshi mijinta".
Na zabura na ce "Wallahi ba shi ya kama ba. Ina ce ga Baban Tsakiya nan, ga kuma dan k'wai Baban kasuwa, dukkansu suna da matan auren kuma".
A fusace ya ce "To basu yi ba, ita Gwaggo ita ce ta yi domin tafi dacewa ta yi aikin".
Na harzuka na ce "Ban gane ba Tijjani. Wato ita ce kaskantacciya kake nufi ko me? Ai ba ita ce babba ba, ga Mama nan".
Ya dago ido cikin ido ya ce "Asiya na ce miki da ita aikin yafi dacewa shiyasa ta yi d'in".
Na mike na ce "Wallahi aikin bai dace da ita ba kai ma ka sani. Y'ay'an cikinta ne a hak'ku. Baba Maryo fa?" Ga mamakina sai na kasa ambato Baba ta Bulkachuwa.
Shima ya mike ya ce "jikinki na yi miki k'aik'ayi Asiya Toro. Bilhiillazi kika yi gigin zaginsu a gabana sai jikinki ya fa'da miki. Bazan dauki wananan mugun halin ba. Ke abu ba zai wuce a wajen ki ba? D'azu dukkansu sai da suka tambaye ki, amma ke kin k'wafesu a cikin zuciyarki".
Na ja tsaki na ce "Kana yi mini dukan da jikina ya fa'da mini. Ka tabbatar kai ma sai naka jikin ya fa'da maka. Domin kuwa dai ka daki aurenka tunda shine lasisinka na dukan jikin nawa".
Ya kasa ce wa komai. Amma na lura ba k'aramin b'acin rai ya shiga ba.
Ya kewaye ni ya fice. Bai dawo gidan ba. Sai wajen goma. Ni kuma tuni na sake fusata. Dan haka da ya dawo ya shigo d'akina ban ko kalle shi ba, bare nasan me yake ciki.
Ga mamakina shima bai kalle ni ba, ya koma k'arshen gado ya kwanta.
Washagari ma da asuba ya fice, k'ofar d'akin ya buga da k'arfi. Wanda na gane tashina ya yi dan na yi sallar asuba.
Ya dawo ya ajiye burodi. Ya ha'da nasa shayin ya karya ya fice.
Na yi abinci na ajiye masa na rana, amma bai dawo ba.
Da yake lahadi ne. Mutum biyu sun zo lalle, haka kitso ma mutum uku na yiwa. Kafin la'asar babu kowa.
Duk da zuciyata babu da'di a dalilin yadda na lura Tijjani ya tsananta fishin da yake yi.
Wayata na dauka na shiga manhajar WhatsApp. Sai ganin Umm Nihla ta yi posting hadaddun materials daga Malaysia. Ina matu'kar son irin yadukan. Ba don komai ba, sai dan basu da nauyi, sannan gasu da taushi, ga kuma sau'kin ku'di ainun. Abin burgewa kuma basa kodou sai da ka gaji da su ka bayar.
Wani yellow da blue suka tafi da ni. Kai tsaye na ce mata ina sonsu. Ga mamakina duk ku'din basu yi tsanani ba.
Ta tambayi a wanne garin nake? Na bata amsa da Toro. Ta ce to sai a saka miki a motar Jos kenan?. Tunda kunfi kusa akan Bauchi.
Na ce "A a akwai sister ta Aisha Lame jakadiyar oriflame. Ita zaki aikawa zasu same ni.
Ta yi mamakin cewar nasan Aisha Lame.
Na ce "To ai yar garinmu ce. Sannan muna da alaka ta wajen kakata da ta haifi Babana.
Umm Nihla ta turo emojin mamaki ta ce "Ai kuwa Aisha na da kirki, kafin na bar Nigeria a wajenta nake siyayyar kayan kwalliya da spices. Farashin kayanta mai sau'ki ne ainun".
Cikin alfahari na ce "Ai ko anan haka ahalinsu suke, mutane ne masu kirki kwarai da gaske. Nima da aurena ta bani kyautar fame wash. Yanzu kuwa na tura mata ku'din wani zan siya saboda na gane muhimmancinsa".
Daga haka ta turo mini asusunta da zan tura ku'din.
Sai mamakin yadda duniya ta samu cigaba nake yi. Ina Toro amma na sayi kaya a hannun wacce take zaune a Malaysia. Har na tura ku'din, ta tabbatar mini ta ga ni. Nima kuma ina da tabbacin zuwa gobe zan ji Aisha Lame ta karba mini. Na saki gauron numfashi.
Na fara lissafin ku'dina domin so nake na yi k'undubalar fara shafa man oriflame. Idan nafi haka sheki da d'aukar ido zan fi daukar hankalin Tijjani fiye da yanzu.
Haka na lalubo lambar Aisha Lame cikin sa'a tana online, ita da kanta ta za'ba mini Wanda yafi dacewa da farare. Itama take na tura mata ku'dinta. Na fa'da kuma za'a kawo mata material d'ina ta ha'do ta aiko aiko mini. Muka yi sallama.
Yau ma sai bayan Isha ya dawo. Ban kula shi, shima bai kula ni ba.
Kwanaki uku muna fishi da juna. Abin na cina a zuciyata, amma na daure na matse na share shi. Mussaman da bai shata mini layi da dakin sana'ata yadda yake yi a watannin baya ba.
A kwana na hudu Gwaggo ta yi mini waya a lokacin ina tare da masu lalle.
Muka gaisa ta ce "Yabi ba zaki zo ki gaida Dada ba ne? Kaf yaran gidan nan kowa ya zo ban da ke. Kuma kullum sai Tijjani ya zo ya duba ta. Amma daga ke har shi baku yi hankalin ki zo ki duba ta ba. Sai ta mutu ki zo gaisuwa ne?"
Jikina ya yi sanyi na ce "Zan zo. Shine bai ce na zo ba".
Da sauri ta ce "Ke ma k'aramab niyya ce da ke. Nasan Tijjani ba zai hana ki zuwa gaida Dada ba".
A sanyaye na ce "Ki yi ha'kuri zan zo In sha Allah".
Ta saki gauron numfashi ta ce "Ya dai kamata".
Sannan ta kashe wayarta.
Kamar almara ana idar da azahar ranar sai ya dawo.
Cikin sa'a na gama yiwa wacde nake sawa. Saura mutum biyu su kuma dama sai mun yi sallah.
Ban yi abinci ba tunda ba dawowa yake yi ba. Ko cefane ne idan ya kawo mini. A k'ofar gida zai bawa yaro ya shigo da shi, ya yi juyawarsa.
Na bishi falon. Murya a dakushe na ce "Sannu da dawowa".
Ya amsa babu walwala.
Sannan ya ce "yunwa nake ji. Me kika dafa?"
Na dauke kai na ce "Ban yi komai ba, tunda nasan cikina kawai zan yiwa".
Shima tasa fuskar a daure ya ce "To sai ki dora yanzu. Sauri nake yi kuma".
Ban ce komai ba, na juya na shiga kicin din. Na dora farin ruwa dan nasan ina da miya a fridge.
Daga nan na nufi bayi dan yin alwallah.
Sai da na zuba makaroni sannan na yi dakinmu dan yin sallah.
Bayan na idar na shiga falon na dauko miya. Na tarar ta nuna. Na ta ce na dauraye. Na dora miyar dan ta d'umama.
Na shirya a tire na kai masa. Bai nemi na zauna muci kamar yadda muka saba ba. Nima kuma ban zauna di'n ba. Na tafi na cigaba da yin lallena.
Ya gama ya fita.
Har dare ina ta sakar yadda za'a yi a gobe na je na gaida Dada.
Muna kwnace kowa na k'arshen gado. Dukkanmu mun kasa barci da alamu akwai abin da ya damemu. Ni dai nasan yadda zan fita gobe nake ta tufka da warwara.
Tsawon lokaci muna hakan. Sai kuma na ga ya mirgino ya same ni a jikin bangon da na lafe.
Bai ta'ba ni ba. Amma ya mannu da ni sosai. Murya k'asa k'asa ya ce "Asiya Toro idan muna fa'da ai bai kamata mu sanya aurenmu a cikin rikicin ba. Kawai mu yi harkar aurenmu. Allah bar shi da safe muci gaba da gabarmu tunda bani da darajar da zaki mini laifi ki bani hakuri".
Nan da nan na gano jarumtarsa ta kare ne. So yake mu kebe. Maimakon na yarda tunda nima na kosa da gabar sai kawai na kwabse na ce "Sawa na nawa kuma? Ai tuni ka sanya shi a ciki. Yau kwananka nawa da yin fatali da shi?"
Ya ru'ko hannuna a hanzari ya ce "To yau na cire shi Asiya. Mu shiryasu kin ji. Mu din ma, ko yanzu kika bani hakuri mun shirya. Kin bata mini rai. Wai har ki ce mini zan doki aurena. Ai ban zaci har yau ba kya sona ba Asiya".
Yadda ya yi maganr sai ta yi matu'kar ta'ba ni. Ban san me yasa yake yawan bani tausayi ba.
Na numfasa na ce "Nima ai ka bata mini rai. Akan me zaka dinga duka na? Ko ka dinga yi mini barazana da duka. Ai na dauka ko wani ka ga zai dokar maka jikin nan nawa sai yadda karfinka ya k'are, ba wai kai da kanka ba".
Da sauri ya ce "Bilhiillazi ba wanda zai doke ki a duniyar nan na bar shi ya kwashe kalau. Sai ko Gwaggo da Baban Marina. Amma kowa ye zan motsa k'wannjina a kansa. Ni kuma ai ba haka siddan nake dukan ki ba. Sai na ga zaki kuskure. Sannan kuma ai ba mai yawa nake yi ba".
Na cuna baki duk da a duhu ne na ce "To ni dai bana so, ka daina".
Da sauri ya ce "To. Amma kema ki daina yi mini taurin kai da rashin kunya. Idan na ce miki ya isa, ko bari. To ki bari din kawai".
Ban amsa ba, amma na ji, zan kuma kiyaye.
Ya nisa ya ce "To me zaki ce mini?"
Na fara tirza kafa ina kukan shagwaba tare da cewa"Ai tunda ka buge mini baki shikenan an yi zuza. Kuma ba sharri na yi musu ba. Gaskiya na fa'da.".
Ya ru'ko ni ya ce "Amma tunda raina ya baci, kuma har na fa'da miki ba, sai ki rarrashe ni, ki kwantar mini da hankalina ba?"
Na dinga k'unk'unin ina fa'din "Ni ba wani rarrashin k'ato da zan yi".
Da yake bai ji me nake fa'da ba.
Ya jani jikinsa ya rungume. Ya dinga shinshinata tare da sakin maganganun masu nauyi.
Ni kuma na cure jikina, na dunk'ule. Na dinga ja masa rai. Ban yarda na sallama masa ba. Sai da na ce "Yaushe zan je na gaida Dada?"
Murya na rawa. Ya ce "Kina ce mini sorry gobe zan kai ki tun safe ki yini a can".
Da murna na ce "idan ban ce maka ba fa."
Ya ce "Zan kai ki, amma minti talatin tana cika zan tiso ki a gaba mu dawo gida".
Sanin da na yi da gaske yake yi, ya sanya na bu'de baki cikin walwala na ce "Ka yi hakuri Tijjani".
Nan da nan ya sake rungume ni sosai ya ce "Thats my little girl. Na huce, na kuma yafe miki. Daga Nan abubuwan da suka biyo baya masu nauyi ne. Domin Ni da kaina na tabbatar na yi missing Tijjani da jagwalgwalonsa masu sanya ni tsumaye. Abin da ban yi zaton zan yiwa Tijjani ba, sai da na yi masa a wannan daren. Wanda ba karamin gigita shi na yi.
Da safe ya tashi ya dinga yi mini hidima da bare-bare. Ni kuma kunya ta yi mini k'awanya.
Da wuri muka shirya ya kai ni gida da kansa. Ya kuma ce sai an yi sallah isha zai zo mu tafi. Sai da zamu shiga gidan ya bu'de but din mashin d'insa ya fito da lemon maltina guda biyu da lucozade shima biyu a leda. Ya mik'o mini ya ce "Ki bata".
Na kar'ba tare da cewa "Na gode! Ni ban yi tunanin na siya mata komai ba".
Bai ce komai ba, muka shiga gidan. Nan kuwa jakar hannuna cike take da omon viva 85kg zan bawa su Gwaggo. Da kuma alwar da zan raba wa kannena.
Tare muka gurfana da shi a gaban Dada muna gaisuwa cikin tausayi da alhini. Bansan ai haka ta jigata ba. Kanta har a lokacin a suntume ya ke. Ga hannu a targade ya sha nadi da bendeji. Ga fuska da k'afafuwa duk sun kuje sosai.
Duk yadda ta ji jiki, har jikin ya yi yaushi amma bakinta ras. Ta kalle ni ta ce "Ai Yabi Allah ne yasa da sauran kwana a gaba. Gaba'daya ji na yi tamkar wadda k'asa ta dare na afka. Kai wato wanda yake yawaita ro'kon Allah da neman kariya daga tsautsayi da asara zai ga sassauci a lamarinsa. Ni nasan k'addara bata sauya wa. Amma k'arfin addu'a yana rage zafinta. Na gode wa Rabbani da ya sanya ni cikin bayinsa masu yawan ambatonsa masu kuma yawan gode masa."
Tijjani ya ce "Haka ne Dadarmu".
Ta muskuta, na kalle ta tausayin ta ya sake kama ni a dalilin nasan bata ji dadin zaman ba.
Ilai kuwa kafin na yi wani abu. Sai cewa ta yi "Mai sunan manya matso ka gyara mini zaman nawa. Gaba'daya a takure na ke."
Da sauri ya matsa cancakat ya cira ta. Ya ce "Asiya sa hannu ki gyara mata zaninta".
Na gyra mata din cikin azama".
Ya mayar da ita ya tokare mata baya da filo mai tauri. Ta ce "Allah ya yi maka albarka mai sunan manya. Allah ya tsare ka daga tsautsayi da asara. Allah ya sa kafi karfin magauta. Ubangiji ya bu'de maka k'ofofin alheri".
Ya dinga amsawa cikin walwala.
Na k'ulu, wato Tijjani kawai zata yiwa addu'a.
Na daure na ha'diye ban fashe ba.
Can ta zuba mini ido. Sai kuma ta koma ga Tijjani ta ce "Mai sunan manya da alama komai ya dai-daita. Wannan haske da sheki da cikar da Yabi ta yi ba iya na abici ba ne kawai. Ana takar ta sosai gaba'daya ta fara bude wa"
Ba ni ba, hatta shi kansa maganar ta yi masa nauyi ainun. Ya yi maza ya sunkuyar da kansa ba tare da ya ce uffan ba.
Ita kuwa ko a jikinta sai faman murmushi take yi tana fa'din "Alhandulillahi. Allah kasa zan ga jininka kafin duniyata ta kare".
Na mike bayan na tura mata ledar gabanta na ce "Ga shi nan Dada. Allah ya k'ara lafiya bari na tafi inda nima za'a yi nan nan da ni. Kin riga kin saba da hubbu ra'as. Tunda muka zauna ba kya ta tawa. Sai mai sunan manya, mai sunan manya. To na barku ku k'arata".
Ta k'yal-k'yale da dariya bayan ta ja ledar tana ce wa "Wayyo Yabi mai dogon hannu. Da'dina da ke akwai ungo. Duk cikin jikokina na d'aki ke ce kika kawo mini tsarabar dubiya. Ko wacce da sun zo da mijinta ta ga ya bani dubu ko dari biyar shike nan sai ta ja ta tsuke. Wai suna nufin mazansu sun fanshesu. Har Nasiba haka ta zo mini hannu na dukan cinya. Ita kam mijinta bai zo ba, bare ya bani.
Amma mijinki kullum ne. Sai ya kawo mini kunshin nama, ko lemo da ayaba. Ai yanzu na ga ne biki mai zuciya a ke fa'dawa ba mai dukiya ba".
Na ce "Ke kuma Dada da son a baki ki ke. Ban da haka ina lafi ma da aka zo aka duba ki?"
Na kalli Tijjani na ga ya kyafta mini ido, alamun na bar maganar haka".
Na sanya takalmi na ce "masa na yi cikin gida. Sai ka shigo".
Na tafi na bar shi tare da ita. Ina jin tana cewa "Ah yarinya ta yi bundum ta yi cikar daki. Ni dama nasan ruwan wankan aure duk zai sanya muku nutsuwa."
A zaure muka yi kicibus da Yaya Anwar yayan Nasiba. Na gaishe shi da mutunta wa domin shi d'in kamamme ne.
Ya amsa tare da ce wa "Yabin Bulkachuwa yau a gidan Marina? Tunda aka yi aurenku ke ce ban ga kin zo ba. Bulkachuwa ya rufe ki ruf. Ma sha Allah! Allah ya k'ara ha'da zuciyoyinku".
Kunya ta kama ni. Na wuce ban ce komai ba. Amma sunan da ya kira ni da shi ya sanya mini wani irin shauki a zuciyata. Duk kame kamena na fara gasgata cewa na fara son Bulkachuwa. Irin son nan mai shiga a hankali ya yi karfi mai tsananin gaske. Ga shi wani irin kishinsa nake yi irin wanda ban ta'ba jin irinsa akan ko wanne namiji ba.
Kawai ina waske wa ne dan kar ya fahimci halin da na ke ciki. Tunda shima na fahimci mai iyashege ne.
Ina shiga k'ofarmu aka dinga yi mini oyoyo tamkar ba Yabin da kowa ya ga ji da ita ba. Hatta Mama sai da yi mini barka da zuwa cikin sakakkiyar fuska. Inna kuwa sai kiran kananun y'ay'anta take yi tana fa'din "ku je ku yiwa Adda Yabi oyoyo."
Na fito da alawa na dinga bawa kowa a hannunsa. Tun fil'azal kyautar alawar da nake yi musu ya sanya suka fi sakewa da ni. Dakin mama na fara shiga na gaisheta na ajiye mata omonta zare guda. Sannan na shiga na Inna na bata nata.
Sai kuma na dawo dakinmu na baje.
Na fa'da kan gado na fashe da kuka a hankali.
Ta zauna jikinta na rawa ta ce "Duk yadda jikinkinki ya nuna kina zaune k'alau ashe ba hakan ba ne. Daga zuwanki zaki daga mini hankali, ki shafe murnar da na ke ciki ta ganin ki, cikin yanayi me kyau?"
Na share idon na ce "Ai ke ce "Baki taba zuwa mini ba. Kowa a gidan nan ya je amma ban da ke. Ko har yau fishi ki
ke yi da ni Gwaggo?"
Ta ri'ke hannuna ta ce "Ba komai a zuciyata game da ke sai alheri mai yawa Yabi. To me zan je na yi miki ne? Babanku ya je. Mama ta je, Inna ta je, yayarki tana zuwa. To su duk kin raina k'ok'arinsu?"
Na juyar da fuska na ce "Ban raina ba Gwaggo. Amma ina so ki zo".
Ta