Showing 69001 words to 72000 words out of 184118 words
Chapter 24 - Bakar Taada Hausa Novel Complete
ba k'aramin cizo na yake yi ba har yanzu.
Sannan girikin da ya sanya aka shigar mini kicin aka yi masa, sai ya gane ni ba irin matan da za'a yi musu hakan ba ne.
Bai wani jima ba, ya dawo. Sai da ya shiga kicin din sannan ya fito ya yi dakina.
Dada ta zuba mini ido alamun na tashi na bi shi.
Akan dole na je din.
Ya mik'o mini leda mai d'auke da sink'in sabulun wanka da kwalin TURAREN
Ismiyaki.
Na kar'ba galala.
Ya ce "Idan zata tafi sai ki bata".
Na gatsina baki na ajiye a bakin gadon ban ce komai ba, na fita na bar shi a tsaye, ya yi wani iri abin tausayi!.
Ya fito ya dan tsokani Dada sannan ya fice.
Zafi ya sanya na yiwa Dada shimfida a baranda.
Ta fito, muna hirarmu ina gyaran kayan miya.
Ina tunanin artabun da zan yi da attaruhu yayin greting. Don kuwa indai na murtsika attaruhu sai na kwana na yini hannuna na yin mini zugi.
Kwatsam aka kawo wuta. Cikin karambani da giggiwa na ha'da bilandar na fara markade.
Sai da na zuba shinkafa a dalilin ruwa ya tafaso.
Sannan na koma wajen Dada.
Da murmushi ta ce "Oh ashe dai da rabon za'a samu mai tu'amalli da injin markade na zamani a jikokina".
Na yi dariya tare da cewa "Dada kenan.
Bari na zauna ki d'ora mini karatu, ina kewar karatun ki."
Ta gyatta, na zauna kusa da ita.
Ta ce "Tunda Ubangiji ya sanya na ga auren ki har ga ni a gidan ki.
To zan 'dora miki karatun da har abada kin wuce yin boranci a idon namiji. Ban ta'ba koya wa kowa wannan addu'ar ba, saboda jarraba namiji ake yi da ita k'warai da gaske. Kema dan ina son ki tsare mijin ki, daga sharholiya ne!".
Ban ce komai ba.
Ta yi waiwaye dan ta sake samun tabbacin babu me jin abin da zata furta.
Ta matso kusa da ni ainun.
Murya k'asa kasa ta ce "A yayin da kuka shiga mayafin aure sai ki yi Bismillah ki ce "Allah daraja, MA'AIKIN Allah daraja a taimake ni akan aure. Zan jarraba y'an maza wane.. Ibnu wance.
Ki kamo ainihin sunan sa da sunan babar taku, sai ki tofo yawun bakinki akan yatsan sai ki yi matsi da wannan yawun addu'ar. Amma a zuci, zaki yi fa". Ta fa'da da dukkan zuciyar ta.
Duk da na saba jin karatun Dada wannan ya yi matu'kar sanya ni mamaki da dariya.
Amma na sanya jarumta na maze, na yi k'asa da kaina a zuwan kunya ce ta hana ni sukuni.
Ta kuwa dage ta ce "Ba kunya zaki ji ba Yabi! Na baki wannan fahamin ne dan na taimake ki, ku zauna lafiya. Amma fa kada ki yarda ki dinga jansa a k'asa. Domin k'arfin addu'ar yawa ne da shi tamkar yankar wuka take".
Na k'yal-k'yale da dariya saboda bilhakki take maganar zan jarabta shi da wannan karatun surkullen.
Sai da dariya ta tsagaita mini na ce "Allah ya bada lada Dada. Amma ni bazan yi a kansa ba. Baya sona, bana sonsa. Kowa harkar gabansa yake yi."
Ta dauki salati tana fa'din"Ashe har yau baku zama d'aya ba? Tisa ki yayi a gaba yake kallon ki kawai?
To idan na tafi zan fara tsayawa wajen Malam Nata'ala na ji ya ya matsayin aurenku.
Domin nasan duk ma'auratan da suka shafe kwanaki arba'in basu hadu ba, tabbas aure ya haranta. To ku kwanaki talatin da biyu da aurenku. Zan je na sake jin fatawar kada aje ko auren ya b'aci ba'a sani ba".
Na yi shiru domin na kasa gane bayanin na ta. Ban ce komai ba, domin kuwa ban ta'ba jin makancin hakan ba.
Ta numfasa ta ce "Yabi kin san duk macen da ta ki d'agawa mijin auren ta k'afa. Zata zama makamashi ne a cikin wutar jahimu?"
Na yi shiru tare da b'ata fuska. Ta sake ce wa "Wannan hukuncin lahira ne. A duniya kuwa babu ita babu ganin hasken rayuwa tunda malaiku dubu maitan ne zasu yi ta kabarbari suna d'ebe mata albarka. Kin san kuwa ko limamin unguwarku ne ya tsine miki, kin yi hannun riga ke da walwalar rayuwa bare kuma ma'asumai irin malaikun Allahu".
Jikina ya yi sanyi da wannan karatun na karshe. Wanda babu kuskure ko shaci fa'da a cikinsa.
Amma da na tuna ai bai ta'ba nema na hana ba, ke nan bana cikin tsinuwar malaiku, sai na samu sau'kin tsoratar da na yi.
Kafin ta sake magana na zabura na tashi ina ce wa "Bari na duba girikina".
Na tace shinkafa, na yi k'asa da wutar na mayar.
Na duba ledar da ya ajiye na ga salak da kuma ledar soyayyen kifi.
A gurguje na yanka na wanke da gishiri na bar shi a kwandon tsane wa bayan na rufe.
Daidai lokacin na sauke sanwar, na d'ora ta miya.
Na juye a flask na fito da tukunyar na jika ta da ruwa.
Na ce "Dada mu shiga ki yi kallo. Rana ta fara kusantomu.
Ta ce "Zan tashi dai saboda rana, amma ba dan na yi kallon shagala ba.
Na kunna na kamo mata wa'azin Malam Guruntun tana saurare can ta nisa ta ce "ya iya karatu kuwa. Amma dai wannan ba namu ba ne ko Yabi?"
Cikin k'arfin hali na ce "Musulmi ai d'anuwan musulmi ne Dada. Bare wannan bijimin Malami ne. Ke dai ba ki ji abin da Allah da ma'aiki suka ce ba ne na ki?"
"Ta kyabe baki ta ce"Masu daddagen wando ai tsakaninmu da su sai a lahira. Tunda suna raina karamar shehu".
Dariya ta kwace mini. Na dinga yi sosai.
Na canja tashar cikin sa'a kuwa sai ga sheikh Mak'ari yana bayani irin wanda ta gamsu da shi.
Na gama abinci tsaf. Bamu ci ba sai da muka yi salla sannan na kawo mana. Tare ta ce na zuba mana. Muna ci tana yaba girkin nawa.
Tana kuma ta yi mini maganganun da suke nuna girman da miji yake da shi.
Ban ce uffan ba, sai da ta ce "Ki kwantar da hankalinki ki zauna lafiya. Nan da kwanaki ka'dan zan sake kewayo ku. Idan har kika bari kwanakin auren ki ya kai arba'in baki bari ya ri'ke hannun ki ba. Tabbas zan fa'dawa mahaifin ki. A san halin da kuke ciki. Kada ku fara zaman haranci".
Na fara kuka tare da ce wa "Ba ruwan ki Dada! Kada ki ha'da ni da ubana, kada ki janyo mini fishin sa."
Ga mamakina sai ta sassauta ta ce "Idan kuwa har irin haka kike gudun fishin uban ki. Kamata ya yi ki guji fishin Allah fiye da hakan. Ai ba Babanku ba ne ya hukunta faruwar al'amarin ba. Allah ne da kansa. Fishin Ubangiji akan bawansa kuwa yana nufin tabarbarewar dukkan al'amuran rayuwa".
Na kasa bu'de baki na ce "Bai ta'ba nuna wa yana da bu'katar hakan daga gare ni ba. Saboda yana samu a waje. Sai kawai na sake tsananta kukan da nake yi. Domin har ciki mak'oshina nake jin ba'kin cikin halin da nake ciki.
Har la'asar ta kawo kai, bata fasa sakin maganganu ba. Wasu na gaskiya, wasu na barkwanci wasu kuwa masu nauyi ne. Ita kuwa ko a jikinta.
Ina kuka sosai amma bata damu ba sai ce wa ta yi "Da kin san kanki ai da tuni kin mayar da shi bita zaizai. Mata irinmu masu k'aramin ruwa ai mafi yawa murza maza muke yi. Kin ga duk haiba da siffar mijin ki. Da kin kwantar da hankalinki, kina masa biyayya, kina ba shi kanki ai wataran ma sai ya shirya zai fita, idan kika ce kada ka fita ce wa zai yi to."
Na cuna baki na ce "Da dai ba dan-iskan duniya ba ne".
Ta kuwa zabura ta jefe ni da kofin kusa da ita.
A ki'dime ta ce "Mijin ki kika zaga kai tsaye babu nadama bare shakka?
Tabbas kin kafurta, kin halaka Yabi. Dole sai kin sake karban shahadar shiga musulunci.
Na kasa kunshe dariya ta. Na k'yal-k'yale da dariya sosai.
Ranta ya baci k'warai da gaske. Ta shiga share hawayen takaici.
Murya na rawa ta ce "Ki aikata kaba'ira sannan ki yi dariya? Saboda ku yaran yau babu darhamin imani a zuciyarku?"
Na ha'diye dariyar a dalilin kukan gaske take yi.
Da sanyin murya na ce "Ki yi hakuri Dada."
Ta ce "Na ha'kura amma, ai dole ki sabunta musuluncinki Yabi. In kuwa ba hakan ba, tabbas kin zama arniya.
Cikin k'arfin hali na ce "Ba ni kalmar shahadar na sabunta din."
Ta rike baki ta ce "Wace ni na shiga sahun Malamai. Ni almajira ce me neman sani. Gaban babban malami za'a kai ki ya baki shahada ki kar'ba. Ko kuma ki yi tuba a gaban mijinki ki nemi afuwa sannan ya baki kalmar ki kar'ba".
Na bata rai na ce "Haba Dada tunda ba'a gabansa aka yi ba, ina dalilin sai ya ji. Tunda kin ce na sabawa Allah. Ki bari na ce Astagafirillah! Amma kada ki fa'da masa. Dukana zai yi, son girmansa yawa ne da shi".
"To shikenan bazan fa'da masa ba.
Amma ki tsananta intigifari Yabi".
Daga haka muka yi haramar sallar la'asar.
Na tattare kwanukan na share wajen kafin ta fito daga bayi.
Mun jima da idar da salla sannan ya dawo.
Kallonsa kawai na yi na gane bai ci abinci ba.
Dada ta dinga yi masa barka da dawowa. Ya amsa yana murmushi wanda na tabbatar na yak'e ne.
Ta zuba masa ido ta ce "Ya na ganka haka ne?"
Ya ce "Babu komai. Sauri nake yi kada ki ce ban zo da wuri ba."
Bata ba shi amsa ba ta kalle ni.
A dole na ce "Sannu da dawo wa".
Ya amsa da walwala sosai".
Ya ce "Na kai ki yanzu, ko na watsa ruwa?"
A tausashe ta ce "Yunwa kake ji, ka fara cin abinci, nasan baka shiri da yunwa".
Ya yi k'asa da kansa. Bai ce komai ba.
Ta ce "Yabi ki kawo masa ruwa da abinci mana".
Na daure fuska matu'ka da gaske sannan na ce "Baya cin abincina ai".
Ta fara fa'din "Allahu Akbar kabiran, wa subhanallahi bukuratan wa asila. Wanne irin zama kuke yi ne na kafirci ni Binta?
Baya cin abincin ki sai na wa to?"
Da yake abin na yi mini ciwo sosai. Cikin rawar murya na ce "Sai na y'ar iska mana."
Dada ta kalle ni da kyau tamkar me yin nazari. Sannan ta mayar da kallonsa kansa. Gaba'daya ya yi laushi tabbacin ya buga bai samu abin da ya sanya a bakinsa ba.
Tsawon lokaci ta ce "Kira mini lambar Alhaji. Da alamun al'amarin naku ya yi munin da ba zan iya gyara shi ba."
Tana rufe baki na fashe da kuka Ina cewa "Saboda son kai sai ki kira mahaifina ki bata ni a wajensa, ki tayar masa da hankali. Alhalin tunda na zo gidan nan ba abin da nake ga ni sai wula'kanci da tozarci. Ai ni an cuce ni karshen cuta kuwa".
Na fa'di hakan cikin kuka mai tsananin gaske.
Ta saki ajiyar zuciya ta ce "To kira mini Hauwa tunda ita din kin yarda uwar ki ce".
Shima cikin sauri ya ce "A a Dada kinsan dai bayan ta zata bi. Sannan fishi zata yi da ni! Yanzun ma ya nake fama ne a rayuwar nan bare kuma ace ina cikin fishin uwa. Rabu da ita kawai Dada. Idan na fa'di na mutu ba shi kenan ba. Sai ta je ta auri wanda take so."
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.
Yadda ya yi maganr ya yi matu'kar dukanmu. Ko ni da ba sonsa nake yi ba. Ya bani tausayi kwarai da gaske. Bare Dada da kowa yasan bata jure ganinsa cikin damuwa.
Ta rasa inda zata tsoma ran ta. Ta kasa cewa komai.
Can ta ce "Tashi ki kawo masa abinci".
Na zum'bura baki ainun na ce "Ba fa ya ci Dada. Akan me zaki ce sai na ba shi, salon ki sa zuciyata tafi hakan b'aci tunda barinsa zai yi".
Da sauri ya ce "Wallahi bazan bar shi ba Asiya. Ci zan yi, yunwa nake ji rabona da abinci tun daren jiya. Na gaji da abincin siyarwa, ban saba ba, tun fil'azal."
Jikina ya mutu murus.
Cikin murya marar amo ta ce "Kin ji ya rantse zai ci".
Na sake d'aure fuska ban tanka ba.
Ta kalle shi ta ce "Kai me yasa idan ta dafa kake k'in ci?"
A hankali ya ce "Zubin wula'kanci ta yi mini. A bu'de kuma a farantin roba".
Dada ta fara ce wa "Eh dole ranka ya b'aci, duk namiji sarki ne a gidansa komin kashinsa kuwa. Lalle Yabi wula'kanci da tozarcin ki kabiran ne".
Nan da nan ya ce "A a Dada ya kuma zaki sake ankara ta. Ai ban ce ki tayar mata da hankali ba. Ke dai kawai ki rarrashe ta, ai dazu ma kin ce yarinya ce zata daina ne".
Ta yi sukuri tana kallonsa cikin tu'ajjibi mai yawa.
Jin ya fa'di hakan, na k'ara kukana na ce "Bar ta ta yi son kan da ta saba yi a tsakaninmu.
Kuma kai ma dan me baka fa'da mata ka kira budurwarka har falona kun yi hira ba. Me yasa baka fa'da mata bayan hakan da ka yi, bai ishe ka ba. Har umarnin ta yi maka girki a kicin d'ina ka bata?"
Na fada cikin kuka sosai.
Dada ta dauki salati tana ce wa "A cikin gidan auren ki, ya yi irin wannan ba'kin zunubin? Eh lallai ba laifin ki ba ne, nasa ne. Wato ni a lokacin da nake kamar ki yaushe za'a mini hakan na bar al'amarin salin alin ba tare da na fitarwa da ja'irar jini ba. Na goge hawaye na ce "Ban yi komai ba na kai k'ara wajen Ubangiji. Sannan kuma har abada bazan sake ba shi abincina ba. Ba kuma zan huce ba, daga nan har na tsufa".
Dada ta yi maza ta ce "Eh to ba dan ina jin tsoron kada kwanaki arba'in din ta cika auren ya samu karaya ba. Dana goyi bayan wannan tutsun na ki. Amma yanzu ki yi ha'kuri, ki yafe, ki huce! Ubangiji yana son masu afuwa da sassauci. Idan ya kuma ni da kaina ne zan sanar da iyayenku. Ai bazan yarda ki yi irin wannan zaman na kuttu ba".
Na girgiza kai na ce "Ai Dada babu maganar huce wa. Babu ni babu sake shiga shirginsa tunda juninsa wula'kanci da nema mini raini ne".
Kafin Dada ta yi magana ya yi fit ya ce "Ban san zaki ji haushi ba Asiya. Na rantse ban yi da gayya ba. Amma tunda ban kyauta ba. Allah ya baki hakuri. Ba zan sake ba."
Na dauke kai ina harara tamkar idona zasu fa'do k'asa.
Ya ce "Dada ki ce ta yi hakuri mana."
Ta nisa ta ce "ki yi ha'kuri kin ji. Ta shi ki ba shi abincin ba dan halinsa ba. Dubi Allah, ki duba Manzonsa."
Ban sake ce wa komai ba. Na mik'e din.
Ban san ya aka yi ba, da na isa kicin din na samu kaina da d'auko plastic plates masu fadi guda biyu.
Na zuba masa na rufe na dora cokali a kai. Na dauka na nufi falon. Ina jin Dada na fa'din "kada ka sake kuskuren saka wata ta yi maka girki. Ban da sakarci ma ina kai ina doguwar magana da ita, bare har kasa a yi maka girki akan idon matar ka. Ai gwara da ta murd'e maka. Kasan halin fa'dan ta ai, bare kuma an tsokano ta".
Murya ba amo ya ce "ki bar maganar nan, sai na zo dakin ki. Yanzu dai lallaba mini ita Dada kawai".
Na shiga na ajiye a gabansa. Ya saki murmushi ya ce "
"Madallah da Asiya". Na cuna baki na dauko ruwa na ajiye masa a gabansa na koma gefe na zauna.
Ya dauki abincin ya dinga ci tamkar bai ta'ba cin abinci irin hakan ba. Cikin kankanin lokaci ya tashi da uban abincin da na danne farantin da shi.
Fanka na kad'awa amma zufa sai yanko masa take yi.
Ya ta'ba ruwan ya ji sanyi sosai.
A hankali cikin kwantar da murya ya ce "Asiya idan kina da ruwan Lipton taimake ni da shi mana please" .
Na dauke kai, kamar bazan amsa ba, sai kuma na tashi na fita ba tare da na ce komai ba.
Dada ta bini da ido tana fa'din "Kasaitacciyar mace. K'aramar halitta mai babban al'amari".
Sai da na isa kicin na yarda na yi dariya.
Na dauko kofi da cokali. Sannan na dauki filas din ruwan zafin.
Na sake ajiye wa a gabansa ba tare da na ce komai ba.
Na zauna na dauki waya ta ina danne danne.
Dada ta ce "Ba ki kawo masa sigari ba."
Kafin na yi magana ya ce "Idan zata dafa take zubawa, dan rage masa tasiri."
Ta murmusa ta ce "Yabi mutanan turai".
Shi ma ya taya ta murmushin. Ni kuwa ban ce komai ba.
Ya kammala, ya yi gyatsa tare da hamdala.
Ya ce "Har na ji ni a duniya. Na gode sosai Asiya. Allah ya yi miki albarka."
Ban amsa ba. Dada ta amsa da sauri tare da fa'din "Barka da arziki Yabi! Kin rabauta tunda kika samu farar addu'a daga mijin ki".
Na yi shiru ban tanka ba. Yayin da shi kuma ya mik'e yana cewa "Bari na canja riga na zo na mayar da ke."
Yana fita Dada ta ce "Yabi maganar nan ta wuce. Ku zauna lafiya. Ko makaho ya zo gidan nan sai ya gane mijin ki na son ki".
Cikin fishi na ce "Baya sona Dada. "
Ta murmusa ta ce "Yana son ki. Ke ma da gangan kike inkarin hakan. Yanzu bazan fa'dawa kowa ce wa ba k'alau kuke zaune ba.
Amma fa idan na dawo gidan nan, na fahimci baku shirya kanku ba. Ku tabbatar sai na ha'da muku iyayenku da Malamai. Dan bazan yarda da zaman kafirci ba."
Na dinga k'unk'unin babu ruwanta da shiga al'amarin da bai shafe ta ba.
Ta gyada kai ta ce "komai zaki ce Yabi ki fa'da. Amma ki sani, ni bazan ha'inci shari'ar musulunci ba. Tilas ne ku bi ka'idojin shari'a a kan aurenku."
Ya lek'o daga bakin k'ofa ya ce "kin gama Dada, ko na je na dawo bayan maghariba