Showing 15001 words to 18000 words out of 184118 words
Chapter 6 - Bakar Taada Hausa Novel Complete
annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
✍️
*BAK'AR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*.
*Marubuciyar*
*Halin Yau*
*Sabo da kaza*.
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S ONLY*.
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko kuma kina sha'awar yin register da su. Ki tuntubi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn mai kore dukkan kwadayi*.
*07036662633*
https://arewabooks.com/chapter?id=64ff47e14ba2e11c69ef3f2f
9&10.
Na sunkuyar da kaina k'asa alamun kunya, gane hakan da ya yi, sai ya mayar da hankalinsa wajen kwarzanta ni, tare da maganganun masu taushi da nuna kurewar matsayin mutum. A hakan har ya samu na dawo masa Yabin J bata Marina marar ragayya idan an tabo ta ba.
Domin sai da kunyarsa da nake ji ta dawo, walwalar da fuskata take yi idan ina gabansa ta dawo.
Hakanan shaukin da zuciyata take yi ya bayyana.
Sai goma saura ya tafi bayan ya bani ledar atile da kuma turare, wannan karon har da takalmi mai kyau.
Ina shiga gidan na ci burki a dalilin maganganun da suka ja hankalina.
Muryar Mama nake ji daga dakinta tana cewa "Da gangan kake zuba mata ido take yin yadda ta ga dama.
Jiyan nan yarinyar nan ta muzanta gyatumarka, amma tana shigowa ka bita da addu'ar da ban ta'ba jin ka yiwa wata cikin manyan ya'yanka ba.
Ba wacce ta samu lasisin tara samari a gidan nan sai Yabi, nan Indo ta yi farinjii fiye da nata, sai ka fititke akan sai dai ta zabi guda daya, amma wannan da yake y'ar tijara ce ka barta ta zamo wa uwarta haja, dan kuwa nasan baka samun abin da take roro musu. Saboda ba'kin cikin kada wasu su ci.
Yau Jabir ya kawo musu, jibi Audurashid, gata malamin makarantarsu".
A hankali na ji muryar Baba yana ce wa "D'a ai mallakin uwarsa ne Habiba, duk abin da uwa ta ci ko ta samu a sanadin y'ay'anta bai zama abin a yi magana a kansa ba domin ta cancanci dukkan sadaukarwa daga wajensu. Ban da Dada da take da ra'ayin auren wuri wai duka nawa ma suke ne?
Inda za'a bar ni da ra'ayina kamar yadda ake barina da hidimarsu da ba wacce zan aurar sai ta kammala sakandire bare Yabi mai karamin jiki ce".
Ta harzuka ta ce "Waton ba zaka dai dakatar da su, ka bar guda daya ba ko?
Wai yaushe ka zama mai son zuciya ne haka?
Jikina ya yi sanyi da irin amsar da ya bata.
Ya ce "Kinsan talauci ba abin da baya sawa, bana haufin shine ya mayar da ni mai son zuciyar, kamar yadda kika mayar da ni banza ko wacce magana zaki fada mini babu fargaba.
Kin ta'ba jin na yi magana akan yadda yaranki ke ka'dai suke nufa da tallafinsu, ai saboda nasan uwa mafi uba ce ko da kuwa uban sarki ne".
Ban sake jin harshenta ba, na wuce a raina ina ta murnar Babanmu ya fara gwada k'arfin halin taka mata burki, duk da a yanzu ma babu garantin ba zai lallabata ba. Domin ta riga ta jarraba shi ainun.
Washagari asabar da wuri na tashi na ha'da kayan wankin dakinmu gaba'daya.
Na aiki Anas ya siyo mini sabulu da omo tun daren jiya dama.
Na fara wanki, yayin da shi kuma yake janyo mini ruwa a rijiyar bayan shashinmu.
Kafin karfe takwas din safe na kammala na shanya su reras.
Tuni kuma Inna ta kammala abin karin kumallo.
Na karbo mana namu dumamen tuwon da Nazira, ga kuma kokon a jug da kullum Gwaggo sai ta bawa duk wanda yake son sha a gidan.
Kusan kullum sai na tambayi ko ribar nawa take samu?
Yadda bana gajiya da tambayar itama bata gajiyawa wajen cemin "Wanda ake sha ne ribata".
A duk sadda ta fa'di hakan ban cika fahimtar rufin asiri ba ne sai kawai na kalli ita din mace ce mai yin hidima a inda ba'a ganin darajarta.
Kafin Nazira ta gama wanke baki na k'osa domin indai na yi wanki to bani da jarumtar ri'ke yunwa sai na ji tamkar an mini yasa a cikina.
Ta tarar tuni na fara cin tuwon.
Ta zauna tana fa'din "Yabi sark'a, yanzu da ni ce na fara ci ban jira ki ba, sai kowa ya ji kwakwazon ki"
Na rausayar da kai tare da fa'din Ayyah Addah Nazi kinsan bana shiri da yunwa ko kadan.
Muna karyawa ina bata labarin yadda ta kaya a tsakaninmu da Yaya J.
Ta murmusa ta ce "Yabi duniya! Yanzu Yaya Jabir din ma ba zaki dinga raga masa ba?
Na dan daure fuska na ce "Ai matu'kar zai tsokano ni tabbas zan ajiye komai na yamutsa shi inta kama a rabu ma shi kenan.
Ba zan dauki wula'kanci ba ko ka'dan.
Ta girgiza kai tare da cewa"Allah ka shirya mini Yabina".
Dai dai lokacin Baba ya fito da nufin fita.
Muka gaishe shi ya amsa yana cewa Nazira da Asiya albarka ta kewaye mini ku".
Cikin farin-ciki mai yawa muke fa'din ameen Babanmu".
Amma sai na sake cewa "Babanmu Asiya fah?"
Ya murmusa ya ce " Ho Yabi! Da ikon Allah sai kun sauke farali daga ke har y'ar-uwarki. Sai kin zama Hajiyar ta sosai".
Cikin karadi na ce "Ai kuwa dai Babanmu "Dawafi na mussaman zamu yi maka!"
Ya fice yana dariya.
Babanmu wani irin uba ne da yake wasa da raha a tsakaninsa da y'a'yansa, babbar matsalarsa kawai Mama ce, domin yanzun nan sai ta saka ya ci mutuncinka ko na uwarka akan idonka dan ma an yi sa'a abin ya dan fara sau'ki, na sani kuma karfin addu'ar da muke yi ne mu da Gwaggo".
Kwanaki suna ta shude wa har muka yi jarabawar zangon karatu na uku.
Muna tafe kowa da sakamakonsa a hannunsa, Nasiba da su Firdausi sai murna suke yi a dalilin sakamakonsu ya yi kyau.
Nazira ma babu laifi domin ta sha biyu ta zo.
Amma ni kam sakamakona ba zai nunu ba domin kuwa ta arba'in da takwas na zo a cikin mu hamsin da bakwai.
Kowa ya nuna sakamakonsa a tsakaninmu. Amma ni na boye nawa kamar yadda na saba.
Muna tafe Maijidda sai fa'di take "Akan me za ki dinga ganin results dinmu amma ke ba zaki yarda a ga na ki ba?"
Na gallah mata harara na ce "Saboda mahaifina bai fara gani ba, ba kuwa wanda yafi cancantar ya fara gani sai shi".
Ta tunzura ta ce "Kins an Allah yau sai na ga ni, ai na sani ta karshen aji kike yi.
Ban da class master din ajin naku saurayinki ne ai demotion ne ya kamace ki Asiya".
Na fusata kwarai da gaske na ce "Tabdi jam! Yabi kika je fa wa wannan maganar?"
Ba shakka ta ce "An fa'da miki Asiya. Kin dauka ina jin tsoron ki ne? Idan ba jakar aji kika dauka ba to miko mini sakamakon ki kamar yadda na baki nawa kika ga ni".
Na girgiza kai da tare da yin k'wafa mai tsananin gaske.
Nazira kuwa sai fa'di take "ba ruwanki da al'amarin Yabi fa Maijidda".
Ta ce "Na shiga komai zata yi, ta yi ina daidai da ita".
Ban ce komai ba sai da muka isa zauren Gidanmu ba zato na shake Maijidda da dukkan k'arfina, ina kai mata duka ko ta ina.
Kafin ta yi yun'kurin ramawa na jibge ta sosai, sannan kuma muka ci gaba da gwabza wa.
Aka rasa mai rabamu domin duk wacce ta ta'ba ni kanta fa'dan zai koma sun san haka dabi'ata take.
Nazira sau fa'di take Yabi sake ta, amma bata ri'ke ni ba, domin ta san ce wa zan yi bata taya ni fa'da, ta taimake ni ba tunda bata kishina, akan me zata ri'ke ni?
Na turmushe ta ke nan na debo k'asa ina shirin cika mata bakin da ya yi mini izgilanci sai ga Bulkachuwa ya shigo.
Ya hau fa'din ke Asiya Toro wanne irin abu kike yi haka ne?"
Ganin na fara kokarin danna mata a baki ya sanya shi iso wa garemu, bai jira komai ba ya saka hannunwan sa ya cira ni cak kamar y'ar tsana ya yi wurgi da ni.
Na yi sa'a na dire akan sayyadata.
Da yake a hassale nake sai na durfafe shi ina cewa "To kai ma din ai ba tsoronka nake ji ba, ka zo ka zaune mana a gida ka uzzira mana haba.?"
Na kalli yadda ya harzuka amma ko gezau ban yi ba, duk da ban fi iya cikinsa ba.
Ya kalli Nazira ya ce "Me ya ha'da su?"
Ta tsara masa yadda aka yi ba ragi babu kari.
Ya juya ga Maijidda da take hawaye ga jini a hancinta tabbacin habo ne ya goce.
Ya ce "Dube ki gansamemiya da ke amma wannan y'ar tsakon ta lallasaki haka, wanne irin mutuwar zuciya ce ta same ki?"
Na galla masa harara tare da murguda baki na ce "To ni komin girman gardi ma ba zai hana na zubar masa da jini ba, bare kuma mace yar-uwata".
Ya nuna kansa ya ce "Asiya Toro ni kike tunanin zaki buga?".
Na ce "Ba dan ha'da jiki da kai sai ballagazaye ba, ba abin da zai hana na zage mu gwabza y'ar k'ashi Wallahi".
Ya nuna ni da yatsa ya ce "Asiya Billahillazi zan sumar da ke, yar iska marar mutunci kawai.".
Yana rufe baki na ce "Ga ka nan babban dan-iska mai shiga fa'dan mata, yabi bayan wacce take da abin da zai lallaba ya cuce ta."
Ya yo kaina yana fa'din ashe "Izgilancinki mai girma ne haka?"
Ga mamakinsa sai kawai na yi shirin kai masa naushi tamkar bacaniya.
Wannan dunukule hannu da saitin da na yi, ya yi matu'kar bashi dariya da tu'ajjibin k'arfi halina.
Ya tsaya ya ce dambe zaki yi da ni?
Na ce "Allah suturu bu'kui na yi dambe da mai daudar zunubi irin ka, kuma ni ba ballagaza ba ce, kawai zan kare kaina ne daga cutarwar ka".
Ya jima bai ce komai sai ya kalle ni ya ce "shahsa da bata iya komai ba, sai fa'da da rashin kunya a aji kuwa ita ce dalkiya".
Ba'kin ciki ya mamaye ni, idona ya ciko da hawayen takaici na ce "Na gode wa Allah da na yarda ina zuwa makarantar, wani ma tsabar akuyanci korarsa aka yi daga karatun nasa. Me za'a yi da mai halin bunsuru?"
Ya rasa yadda zai yi da ni sai kawai ya shammace ni ya dauke jakata yi wuf ya zaro takardar sakamakon da take a farko farko.
Ya juya zuwa waje ya bu'de ya ga yadda jan biro suke mamaye sakamakon.
A karshe ya ga ta yadda na zo sannan ya mayar ya shigo ya kalli yadda na tumbatsa ya ce "Anya Asiya ba dusa kike ci ba kuwa?
Ace har kin doshi hamsin?
Gaskiya ina taya Baba ba'kin cikin asarar ku'din taran da ya wanzu yana baki".
Cikin rawar murya na ce "Bulkachuwa Yadda ka tozarta ni a gaban wanda suke son na tozarta in sha Allah sai an tozarta budurwarka fiye da yadda ka mini, da ikon Ubangiji sai ka ha'du da sharrin mace, sai ka muzanta a idon duniya".
Ya make kafa'da alamun ko a jikinsa tare da cewa "Yabi yanga mai kwakwalwar kifi".
Ganin hakan ya sanya Maijidda ta mike tana jin karfi yana shigar ta tunda ta ji abin da take son ji.
Ta mini gwalo tare da cewa "Na ji dai, dama nasan baki tsinana komai ba".
Ta shige wajen Dada da saurin ta.
Yayin da ragowar suke fa'din "Yi ha'kuri Yabi, ai kin nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane. Ba gashi ta tsere ba".
Na jijjiga kai na ce
"Ai dan ta ga Bulkachuwa ya tsaya mata ne".
Yayin da shi kuma ya ce "Ba dole na tsaya mata ba, tunda ke din karfinki na aljanu ne, na tabbatar ba ke ka'dai kike fa'da ba, kina samun tallafin aljani mai kilabo da gwaigwai".
Duk wajen aka fashe da dariya illah ni dana sake fusata na daga murya "Ina ce wa "Allah ka dora wa matar Bulkachuwa aljanun da zata dinga daga shi sama tana danfara shi da k'asa".
Ya wuce yana fa'din "Duk bala'in aljani ba zai shigo mini gida ba, domin hafiza zan aura mai hazakar gaske a ilimin boko da na addini.
Safiya da marairaice ta yi ta tofe mini gidan da azkhar, idan kin ga aljanu sun yi tasiri, sai a gidan wanda basa mayar da
kai a wajen bautar Allah irin ki".
Na wuce shi zuwa shashin Dada.
Na tarar da Maijidda tana ta kuka yayin da Dada take sakacen hakori da tsinken zabori hankalinta a kwance.
Na bu'de baki na ce "Dada sannu da gida, mun dawo".
Ta amsa ba alamun damuwa a tare da ita.
Na juya na tafi sai na ji kukan Maijidda ya karu tana cewa "Kin bar ta tafi baki bi mini kadina ba?"
Na yi tsam dan na jiyo amsar Dada.
Kamar ba zata tanka ba sai kuma na ji tana ce wa "Na k'i na yi mata maganar. Yar kankanuwa a gabanki, sannan kin bata kwanaki arba'in cif amma kin kasa kwatar kanki a hannunta sannan dan asaranci ki ce na tare miki fa'da?
Ai kinsan fa'dan ta baya mutuwa akan me zaki tsokano abin da yafi karfinki?"
Maijidda da bata yi zaton haka Dada zata ce ba, domin mun saba yin fa'da da yan k'ofarsu ta basu gaskiya ko da kuwa ni ce mai gaskiya.
Dada ta ja tsaki ta ce "Sadda nake cikin shekarun kuruciyata haka nake nima duk girman mace bata bani tsoro, haka nan duk wanda ya mini kan ice sai na yi masa na kara.
Sai yanzu na fahimci wannan tijarar ta Yabi sawuna ta biyo domin komin sharrin mai sharri ba zai ce ubanta mafadaci ba ne ko kuma uwarta.
Dukkan iyayenta sanyin kalau ne, dan kuwa inta sune kiyama ba zata tsaya ba."
Kukan Maijidda ya tsananta ta dinga yi tana ce wa "Ai dai kinsan bata isa ta kai ni k'asa ba, dunbular mini kirji ta yi ta yakushe ni a wajen."
Salati Dada ta dauka tana cewa "Ikon Rabbani, tarihi na maimaita kansa ni Fadimatu.
Wallahi Maijidda sadda aka mini auren fari ina kankanuwa aka kai ni babban gida, matar wan miji ta saka ni a gaba, duka, kyara zagi.
Har na fara girma a cikin fargabar wannan baiwar Allah na ke.
Ai kuwa da tura ta kai bango na fara rama abin da take yi mini.
Har muka kai jallin da muka fara dokuwa, sai dai kashi take bani da yake ta fini sosai, ai sai kawai nake fakar ido idan muna damben ina mintsinin nonuwanta ko na na cije su. Shi kenan na yi maganin gallazawarta, ta shiga kiyayata.
Yau ga Magajiyata na samu a haulata".
Ta fa'da tana tafa hannu tana sake jan salati.
Na wuce ina son yin dariya amma ba'kin cikin Bulkachuwa ya dabaibaye ni.
Na wuce shashinmu ina jaddada wa kaina ko a gaban Baban kasuwa ne Maijidda ta tsokano ni sai mun sake cire raini, bare Dada.
Bamu jima da dawowa ba sai ga mahaifiyar Maijidda da kanta ta kawo togaciya.
Fadi take "Tura ta kai bango kullum Yabi sai ta yi mini sanadin bacin rai jiyan nan ma sai da ta dakar mini Kaltume akan sun samu sabani da Ismail, akan me zata tisa mini yara a gaba irin haka?"
Ha'kuri kawai Gwaggo take ta bata, Inna da ta rage tsananta gaba da ni a dalilin ina yiwa yaranta hidima tamkar yan dakinmu, sannan ba mai tab'asu a waje matu'kar ina wajen sai hakan yayi tasiri, ta rage daukar zugar Mama.
Dan haka sai ta ce "Ban da ke ma Abu da shiga shirgin yara ina ce Maijidda ta girmi Yabi ne?
Sannan idan kinsa ha'kuri anjima ka'dan zaki iya ganinsu tare".
Nan da na ta harzuka ta ce "To Yabi ni kaina ai sai ta dake ni tunda fa'dan yan-iska take yi, ban da dai ta riga ta rik'a ta yaya zata dinga dumbular kirjin y'anmata, tabbas dayan biyu ne, ko dai niyyar kisa take yi ko kuma ta shiga sahun masu *Bak'ar Ta'adar* neman mata."
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko kuma kina sha'awar yin register da su. Ki tuntubi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn mai kore dukkan kwadayi*.
*07036662633*.
Gwaggo ta ce "Dutse a tsakaninmu da duk masu wannan al'amarin, muna neman tsarin Allah da su, muna kuma nema musu shiriyarsa."
Ta ce "ASMA'U Wallahi kin siffatu da agwagwa, ace wai baki isa ki sarrafa y'ar cikinki ba, ta gallabi kowa a gidan amma ba k'ya yi mata fa'da, saboda tana samun ku'di shiyasa ta gagareku?
Sai ayi ta fankamar ku'din kitso da na lalle ne, alhalin munsan samarin da suke mata layi ne suke bata. Wallahi idan ba sa'a kika yi ba sai Yabi ta hana ki shan ruwa kamar yadda ta fitine mu".
Na fito na ce "Umma ya isa haka nan, ba zai yiwu fa kizo k'ofarmu ki zagi Gwaggo ba".
Ta mini dakuwa ta ce gidanku tabbataciyar yarinya marar albarka".
Tana rufe baki na ce "yarinya tana bayan uwarta Wallahi, albarka kuwa da ikon Ubangiji sai na yi ta".
Gwaggo ta yo kaina na ki guduwa tasan kuma matu'kar ta kawo mini duka ban gudu ba, na riga na shiga yanayin da nake bu'katar a kashe ni kawai na huta.
Inna ta yi maza ta karbe itacen hannun Gwaggo tana fa'din "Wannan ai sai ki sabauta ta".
Yayin da Umma Abu ta juya tana fa'din "Zaman babban gida ko masifa, ba dama a ganka da haske sai an tisa ka a gaba da ba'kin ciki da hassada tamkar dai kai ofne ka tare wa mutum nasa arzikin".
Tana fita Gwaggo ta kalli inda nake a tsaye kik'am tana fa'din "Kin ji da'di ai da wannan wula'kancin da kika janyo mana".
Ban ce komai ba, sannan kuma ban ji a raina cewar zan koyi ha'kurin dole idan an ta'ba ni