Showing 78001 words to 81000 words out of 184118 words
Chapter 27 - Bakar Taada Hausa Novel Complete
Amma ko ki nuna kin gane na canja, balle ki yaba mini na ji dadi".
Na bata rai na ce "Akan me zan yaba? Bayan ba dan ni ka yi ba. Ina ce jiyan da ka fita sai da dare ya raba kana zan ce, idan ta yaba maka ai shike nan"
Ya kame baki ya ce "Tabdi jam!
Ya bar maganar ya canja da ce wa "Yanzu zan sake ba ki hakuri, ki manta maganar shiga kicin din ki. Na yarda na yi kuskure, dan Allah ki shafe ta a zuciyar ki. Nima na yafe miki zargina da kika yi jiya. Kin ga dai murna da addu'ar da Baban Marina ya yi. Kamata ya yi mu ha'da kanmu mu zauna lafiya".
Na bata rai na ce "To ai kai abin haushin ka yawa ne da shi Tijjani. Bana son na ga namiji ya cika kule kulen mata, kai kuma kana tafiya a mashin ma kana iya tsayawa ka yiwa mata magana ko baka sansu ba".
Ya sake ru'ko hannuna sosai ya ce "Billahillazi a da ne Asiya. Tunda muka yi aure bana yi, na rantse miki da Allah. Mussaman da kika ce mini mai kamun kai kike so, sai na sake kame wa sosai".
Na yi shiru ya ce "shike nan komai ya wuce zamu zauna lafiya, zaki yarda na zama mijin gaske ba na wai ba?"
Na ce "Sai ka yarda wanccan dakin ya zama zan yi yadda nake so a cikinsa".
Ya ce "Kin san ban iya yaudara ba. Idan kin yarda na zama mijinki na sosai, ai gaba'daya ma ya zama naki, to me zan yi da shi?"
Na ce "Ban gane ba?"
Ya jima yana kallona har sai da jikina ya amsa sannan murya a dashe tabbacin ya shiga cikin shauki sosai.
Ya ce "Idan dakinki ya zama shine nawa, kayana sun koma ciki, kin adanasu tamkar yadda kika adana na ki, sannan a ciki zan dinga kwana, a ciki zan yi komai. Shike nan dakin ya zama na lallen ki da duk bak'on kwana da zamu yi".
Gabana ya yanke ya fa'di tamkar yanzu na fara jin ya kamata ya dawo dakina".
Na yi k'asa da kaina na kasa ce wa komai.
Ya marairaice fuska ya ce "Ki ce to Asiya, na matsu ki zama matar aure ta sosai, na k'osa ki zama babba."
Kunya ta kama ni, na rasa yadda zan yi, sai kawai na fara kananun kukan shagwaba tare da ce wa "Ai yanzun ban girma ba kake nufi?"
Da sauri ya ce "kin girma mana, shi yasa nake son na sake mayar da ke babba sosai".
Na sunkuyar da kai na k'asa domin kunya ce ta sosai ta yi mini k'awanya.
Ya dinga murza mini tafin hannuna wanda hakan ba k'aramin abu ya haifar mini a gangar jikina ba.
Haka shima gaba'daya ya yi sanyi ido ya canja.
Kunya ta sake kama ni. Kan dole sai da ya sake wanka kafin ya tafi sallar la'asar.
Nima dai abin da na gani na kasa gane wanka zan yi ko tsarki. Dan haka sai na yi wankan gudun kokwanto.
Na dinga mamakin lokacin da muka cinye bamu nemi ko abinci ba.
Na shiga kicin na dauko plask din abincin wanda jallof din shinkafa ne.
Na koma na dauko plates da cokula.
Ya dawo ya tarar da abinci. Ya ce "Kamata ya yi muci a plate daya Asiya".
Ga mamakinsa sai ya ji na ce "To."
Na zuba mana, muna ci yana yi mini hira kala kala.
Muna gamawa ya kalli agogo ya ce kwaso kayan ki na wanke miki".
Na girgiza kai na ce "Bar shi zan wanke da kaina".
Ya mike ya na ce wa "Bari na debo da kaina.
Kan dole na bar masa wankin nan ya yi, ina baranda yana ta faman zuba mini hira. Ni kuma na kasa tanka masa, sai dai eh ko a a.
Da daddare yana tafiya sallar isha na rufe k'ofata. Da ya dawo ya ga na rufe. A hankali ya dinga buga mini tare da kiran sunana, amma na kasa bu'de masa. Wata irin fargaba ta dinga ratsa ni. Kan dole ya hakura ya bar ni.
Da safe da na fito ya amsa sallamar da na yi masa, kansa na kan doguwar rigata da yake goge wa.
Tausayinsa ya tsirga mini, duk yadda na rufe masa k'ofa, kuma ban yarda na bu'de masa ba, bai sanya ya fasa goge mini kayana ba.
Gasu nan birjik a gabansa da alamu ya jima yana yi. Tunda rigar da yake kan yi ne ta k'arshe. Sai da na yo brush na ce masa "Ina kwana?".
Ya amsa babu yabo babu fallasa"
Da ya gama zai fita na ce "Zaka dawo ne da rana?"
Ya girgiza kai tare da ce wa "To me zan dawo na yi?"
Na yi shiru sai na ce "To idan an zo k'unshi zamu shiga d'akin, kada ka zo ka dizga ni."
Ya girgiza kai alamun bai yarda ba.
Ya bu'de baki ya ce "Ban yarda ba. Kada ki fara, idan kuma kin ki ji, to ki tabbatar zaki ga abin da baza ki so ba".
Na Kwakkabe fuska tare da fa'din "Amma dai kai ne ka ce zai koma nawa".
"Na fa'da tabbas. Amma ai na fa'di sharadina. Baki yi abin da na ce ba, dan haka kada ki sake ki kai mini mutane d'aki".
Daga hakan ya fita. Ina gama abun da zan yi. Na fara tunanin yau laraba, zan samu masu kunshi sosai har zuwa gobe. Ina matu'kar son sana'a ta, ina samun nisha'di da walwala a cikinta. Sannan ina son na dinga aika wa iyayena wani abu. Idan bana sana'a kuma bazan samu wannan alherin ba.
Na tabbatar kuwa matu'kar da kayan Tijjani a dakin da nake son ya zama na zaman sana'ata, to kuwa da sannu zai kore mini jama'a.
Na zabura na shiga dakin na dauko jakar kayansa. Na kai ta d'akina. Na sake dauko kwalin makorinin da ya zuba takalmansa a ciki.
Na fito da shi tsakar gida na bu'de. Kafa hudu ne da alamu biyu a lokacin aurenmu ya siyesu tunda sabbi ne.
Na goge su na kai su daki.
Jallabiya da tawul din da suke rataye, na fito da su na shanya tunda da danshin ruwan wanka a tare da su.
Bargo da filon kawai na ninke na barsu gefe daya.
Na dauko kaskon turaren wuta da yake ci a dakina na saka na sakayo k'ofar.
Cikin sauri na d'ora shinkafa da wake.
Na kammala na ji almajiri yana bara.
Na kira shi na bashi naira dari ya siyo mini salak da kokomba, domin kayan ganye sau'ki ne da su a Toro tunda muna kusa da Jos.
Nan da nan ya siyo mini, na bashi guntun burodin jiya.
Ina tsaye na yanka na wanke na rufe shi.
Na ha'da kwanukan da na bata na wanke.
Na shiga wanka. Na shirya cikin doguwar riga cotton mai gajeran hannu.
Na saka hular da ta dace da rigar.
Na kalli agogo na ga shad'aya ne da rabi.
Ai kuwa sai ga wata ta zo kunshi da kitso.
Na bude dakin muka shiga, na fara yi mata lallen, cikin kankanin lokaci na gama saka mata. Na dauko kujera a kicin muka fara kitson.
Mun yi rabi sai ga tawagar yan mata wajen su bakwai har da amarya.
Murna ta kama ni, domin ku'di zan samu ba ka'dan ba.
Sannan bana cikin zullumin wula'kancin Tijjani.
Ina gama kitson na fara yiwa amaryar tunda nata yafi wahala na salatif ne.
Na gama yi mata, na fara yiwa daya cikin kawayen na ji k'arar mashin dinsa.
Ya shigo da sallama. A zabure na mike na fita y'an dakin suka bini da kallo.
A bakin kofar na tare shi da ce wa
"Sannu da dawowa".
Bai amsa ba ya sha kunu ya fara kokarin shiga d'akin duk da na tare k'ofar.
Baki na rawa na sake ce wa "Sannu da dawo wa, muje ka sha ruwa, ka ga ni".
Bai musa ba. Ya yarda ya bini zuwa d'akina. Na nuna masa jakar kayansa da take gefe akan kwalin takalmansa.
Na ce "Babu kayan ka a dakin Wallahi. Ka ga tawul dinka ma?" Na d'aga labule ya gan shi akan k'ofa.
Ya daure fuska ya ce "Indai a hakan zaki bar mini su, to kawai ki mayar mini abina can."
Idona ya ciko da hawayen takaici. Murya na rawa na ce "Kawai dai sana'a ce baka son na yi Tijjani. Ban da haka, ga yadda ka ce na yi, zaka bar mini d'akin, na yi kuma ka ce ba haka ba".
Ba wasa ya ce "Ai ba ki adana mini su kamar yadda kika adana na ki ba. Kin ajiye su tamkar suna wancan d'akin dan haka mayar mini su can din kawai."
Da sauri na bu'de masa durowar na ce "Ka ga inda na bar maka fa, bana son na bu'de maka kaya ne baka nan. Da sai dai ka dawo ka tarar na jere maka".
Ya saki fuskar ya ce "To shike nan. Amma kin yi sallah kuwa?"
Na ce "dama d'aya zan k'arisa wa sai na yi kafin na fara yiwa wata".
Ya kalli agogo ya ce kusan uku saura, kina neman duniya baki yi abin da aka halicce ki yi ba? Yau ne rana ta k'arshe da za ki ji ana kiran sallah baki bar k'unshi kin yi ba".
Na ce "To".
Ya ce "Je ki yi alwallah ki zo ki yi sallar a nan".
Na fita ban ce komai ba.
Yayin da Tijjani ya cigaba da ambaton *RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN.* Cikin farin cikin ganin tasirin addu'ar akan lamarin Yabi. Domin tunda ya ga al'amarin ta babu ragayya, babu soyayyar sa ko kad'an sai ya nace wajen yin wannan adduiakan al'amarin. Ya kuma fara ganin sassauco mai yawa. Mata ku rik'e wannan addu'ar sirrikanta yawa ne da shi.
Na idar, na mike na kai masa abincin falo. Na dawo na gan shi kwance shame shame akan gadona. Gabana ya yanke ya fa'di. Saboda ya tube riga daga shi sai gajeran wando. Wani irin tsoronsa ya kama ni a dalilin duk jikinsa gashi ne. Kirjinsa kuwa yafi ko ina gashi.
Ranar da ya tub'e a gaban su Hajiya da yake a kidime nake ban ga gashin irin haka ba. Na dauka iya kirjin ne kawai.
Murya na rawa na ce "Abinci yana falo".
Muryarsa a dashe tabbacin yana jin barci ko wani al'amari daban.
Ya ce "Sannu da aiki".
Na amsa da ce wa "Na tafi".
"Tom, idan na ci zan fita, nasan ba son na lekoku zaki yi ba".
"Na ce "Eh. To sai ka dawo din".
Na saki labulen na je na cigaba da yi musu.
Bai fita ba sai da la'asar ta yi.
Sai wajen biyar na gama yi musu tunda na yiwa mutum biyu kitso a cikinsu.
Ina gamawa na karkade jikina na wanke hannuna da sabulu.
Na shiga kicin, na ga akwai donot sai kawai na dafa shayi na cika filas tunda akwai ragowar abincin rana da na yi
Ana kiran magariba suka tafi bayan sun bani kudina.
Na kirga na ga alherin da na samu ba ka'dan ba ne. Na ha'dasu na adana.
Na yi sallah, sannan na shiga wanka. Nasan sai ya yi isha zai dawo.
Amma abin mamaki har goman dare bai shigo ba. Haka kawai sai na fara jin zuciyata tana b'aci. Sai shad'aya saura ya dawo lokacin na gama fusata.
Ya shigo ya ga ban ko kula shi ba. Na hau na yi suntum. Ya ce "Asiya na yi ta kiran wayarki a kashe."
"Uhum" kawai na ce na kame bakina.
Ya ce "Wallahi Maijidda ce zata haihu, haihuwar ta zo da matsala, zan taho, Dada ta ce na kai ta asibitin ta gano ta. To abin ba da'di, ganin mawuyacin halin da take ciki ya sanya Dada kasa barin asibitin, nima kuma sai na yi alkunya na zauna jiranta kada ta ce dama a dole na kai ta".
Na ce "Sannu! zaman jiran matar da kake jiran a mutu ka aureta ta haihu ai wajibi ne.
Na mike zan bar masa d'akin. Ya yi maza ya ru'ko ni. Ya ce haba Asiyata wacce irin magana ce wannan?"
"Na ce k'arya na yi, baka fa'da ba?"
Ya ce "Allah ya sauwake, ai na fa'da ne saboda kishin hure miki kunne da yake yi. Amma ni ko d'aura mini wata macen aka yi ba fincike wa zan yi na zura a guje ba."
Na saki raina ka'dan. Ya ce "Dazun nan Dada ta gama ce wa yau watan aurensu goma da kwana goma.
Cikin Ikon Allah gasu da y'arsu a hannunsu. Baki ji yadda ake ta saka musu albarka tare da diyarsu ba. Su tun a ranar suka manta da komai suka rungumi junansu". Ban kula shi ba. Maimakon ya yi shiru sai ya sake ce wa "Ni da na duba key holder din aurensu na lissafe sai na ga a lissafin bature watansu tara ba kwana uku ma".
Kuka ya kwace mini, na ce "Na gode sosai da yarfe Tijjani".
Ya marairaice ya ce "Mene ne abin yarfe Asiya? ".
Na k'wace na koma gefe ina gunjin kuka.
Ya numfasa ya ce "Amma kin san dai bana son kukanki ko?"
Na zabura zan ce a gidan uwar wa? Ai ina tuna barin makauniyar da yake yi mini idan na fa'di hakan, na yi maza na ha'diye maganar na buge da jan tsaki da kara k'arfin kukan nawa".
Shi da kansa ya a fahimci da zaginsa zan yi, sai kuma na fasa.
Ya murmusa ya ce "Ban da abin Asiya Toro wai mene ne abin kuka saboda Allah? Ina ce da kin ji duk abin da ake fa'da miki da yanzu kina da cikin da ya yi daidai da kwanakin auren ki. Kina haihuwa sai dai a fahimci ke ma kin yi biyayya, kin manta da wanda ya manta da ke".
Na mik'e na bar masa d'akin. Kai-tsaye band'aki na shiga. Na juyo zan rufe k'ofar na hango shi ya daga labule yana kallona.
Sai da na ci kukana, na wanke fuskata na fito. Na ga ya koma ya bar ba'kin kofar.
Na lallaba na shige falo na saka sakata na yi kwanciyata akan doguwar kujera bayan na kure gudun fankar.
Ina kwance ba abin da nake so irin barci ya sure ni. Amma na kasa, zuciyata sai k'unci take yi. Ban san dalilin k'uncin ba, tunda na laluba ba haihuwar Maijidda ce ta dame ni ba.
Jin shiruna ya yi yawa ya sanya ya biyo sawu.
Ganin da ya yi k'ofar bayi a bude, ya sanya ya shiga d'akinsa. Nan ma wayam bata ciki.
Ya nufi falo ganinsa a rufe, ga fanka na kad'awa da k'arfin gaske ya tabbatar da tana ciki.
A fili ya furta "Bilhiillazi an jarrabe ni akan wannan azinanniyar yarinyar. Allah ka hore mini ita".
Ya koma ya kwanta, amma barci ya yi masa tutsu. Idan ya tuna jaririyarsu Jabir sai ya ji tamkar ya wayi gari ya ga Yabi ta haifa masa tasa.
Ya saki ajiyar zuciya tare da cewa "Wannan yar darun ma, ko sai yaushe zata bari ta girma, rimi rimi na fara shawo kanta, ta sake botsare wa tamkar me bugun aljan.
Ya muskuta sai kawai ya tuno uniform din ta da ya karbo sai kawai ya murmusa sosai. Tare da ce wa "gobe da ikon Ubangiji zan rage wannan tutsun na ki na iyashege. Na riga na gaji da kallon ki tamkar hoto".
Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
Washagari ko da na fito na tarar ya tafi gidan burodi.
Dan haka na k'ira layin Gwaggo.
Ta amsa tare da ce wa "Inji dai lafiya kika k'ira ni da duku dukun nan?"
Na ce "K'alau Gwaggo. Na gaishe ta, ta amsa. Na k'ara da ce wa "Ki turo mini Anas ya zo ya karbi ku'di, za'a siyo mini lalle da mahallabiya. Sannan salatip din mai kala za'a siyo mini.
Zan bashi da ku'di, dubu biyu naki ne, dubu uku kuma ki bawa Baba ya yi cefane, sauran kisa mini a bankina".
Ta amsa da "To" tare da saka albarka mai yawa.
Sai kuma ta ce "Zan dauki dubu a cikin wanda za'a jefa a bankin na bawa abokan zaman nawa,kowa drmaei biyar ko omo ne sa siya Yabi".
A dole na ce "To domin dai mama idna yaranta suka kawo asafi sau tari ma ba'a ji. Idan kuwa an ga ni ma, to mafi yawa baka sanin yadda aka yi da shi.
Na kasa komawa barci. Sai kawai na tsiri shara, na gyara ko ina.
Sanin zai dawo da burodi ya sanya ban yi haramar dafa wani wani abu ba.
Na yi wanka, na shirya, na zauna a falo. Babu wuta bare na yi kallo.
Ina ta sake sake har ya dawo.
Ya shigo ya kalle ni ya ce "Asiya Toro kina da kunnen k'ashi. Wata'kila dai kin fi son sai na fito na fa'di gaskiyar yadda muke zaune".
Na sha kunu ban tanka masa ba.
Ya zauna ya ce "Abin da kika yi jiya ya yi dai-dai ke nan? Kin b'ata mini rai. Amma na yafe miki, sai dai ki sani idan kika sake bazan yafe ba".
Na sake yin shiru.
Ya tashi yana ce wa ni fa yunwa nake ji".
Na fito, ganin yana janyo ruwa na tabbatar wanka zai yi, tunda sai zufa yake yi. Bayan aikin k'arfi da da ya yi nasan kuma da gudu gudu yake dawowa saboda ya saba da atisaye.
Na duba ledar da ya ajiye, burodin ne da donot din. Sai madara da milo na sacet ko wanne guda daya.
Tausayinsa ya kama ni, nasan ni ya siyo wa, shi kuwa sai ya sha ba'kin shayi abinsa.
Muka karya, yana ta