Showing 42001 words to 45000 words out of 184118 words
Chapter 15 - Bakar Taada Hausa Novel Complete
Wanne irin lamari ne mai kama da k'yashi da kuma hassada?"
Dada ta rabka salati tana fa'din "Kawunka kake fa'din wannan kalaman a kansa?
Mai sunan manya anya zaka yi hankali kuwa?
Kusan ma fa saboda kai ya yi wannan al'amarin amma ka ke sakin maganganun da suka yi daidai da zaginsa kake yi."
Ya sake fashe wa da dariya ya ce "a kaina, ni kuma?
Lallai kuwa, zan ga ta yadda za'a yi, wannan bawan Allan ya nufo ni da wani alheri. Rannan ba abin da bai fa'da mini ba, akan sun je kai mini ku'din aure gidan kananun mutane ba'a karba ba.
Ya dinga cin alwashin ba zai sake shige mini gaba a harkar aure ba. Ni kuma abin da bai sani ba, ai kawu ba uba ba ne, dama dangin uba ne a hakku su nemo mini aure, bare ya ce zan wani damu."
Dada ta sake rangada salati tare da cewa "Mai sunan manya wanne irin dibar albarka kake yi ne haka tamkar ka sha k'waya?"
A tunzure ya ce "Ras nake! Na gaji da fitinar mutanan ne, duk wata fitina su suke kitsa ta.
A gabansu uwar Nasiba ta dinga sakin maganganu a kaina ta barranta y'arta da ni, ba wanda ya ce kala a cikinsu. Haka nan shima har yau ba wanda ya kalubalan ce shi akan hukuncin da ya yiwa Jabir na auren Maijidda saboda yana da cikakken iko a kansa. Akan me zai yiwa lamarin Asiya katsalandan alhalin ba kallon y'a yake yi mata ba?
Akan me zai nemi ya dinga nuna ya isa da ni alhalin akan idon uwata suka kasa yi mini alfarma da kawaici."
Ta ce "Allah ya shirye ka, albarkar mai sunanka shiriya zata sauko maka."
Ya bata fuska ya ce "Tare zaki roka ta zo mana da ke, tunda akan idonki ake yin abubuwa na kura kurai amma ba kya iya tsawatar wa. Rannan na ji wani malami yana fa'din ainihin manufar ma'anar kuyanga ta haifi uwargijiyarta. Sak fatawar da ya bayar tamkar ke ya siffanta haka na dinga ji".
Na zuba ido. Ina jiran ta rushe da kukan da zata tara masa jama'a tamkar yadda take yi mana. Amma sai ta share ta yi mirsisi ta fanshe da cewa "Shi ubanta ai ya yarda na isa da shi, shi yasa ya katse al'amarin babu tashin hankali.
Allah ya shirye ka mai sunan Shehu.".
Ya shareta ya kalle ni ya ce "Yanzu kina son wannan ba'kin yaron ko kuwa dole aka yi miki?"
A hankali na ce "ko bana sonsa tunda Baban Marina ya amince ai maganar ta kare".
Ya girgiza kai ya ce "Baban Marina mutum ne Wlh amma ban son ha'kurinsa, any way Allah ya sanya albarka all the best Asiya Toro".
Daga haka ya mike ya fice yana fa'din da kin ce ba kya so. Wallahi da tsaya miki zan yi, komin sharrin mai sharri ba za'a baki wanda ba kya so ba, domin kema y'a ce ba baiwa ba. Kina da hakkin ki so a kuma so ki".
Wannan abin da ya yi mini sai ya rage tsanar sa a raina.
Dada ta dinga fa'din "Sha sha kamar ba saboda shi aka yi komai ba."
Na rasa gane manufar wannan maganar ta Dada.
Tsawon sati da kulla alakarmu da Nura wanda ya yi zuwa uku kenan.
Mamakin kaina nake ta yadda ya shiga raina sosai.
Ko dan sau'kin kansa da yadda ya iya kwalliya da shirya zan ce ne?
Ga shi ma'abocin kyauta duk zuwa sai yasan me ya ru'ko mini wala na ci, ko na amfani, gwargwadon k'arfinsa.
Mahaifiyarsa da ake kira Yaya itama ba karamin son al'amarin take yi ba. Domin da kanta ta zo da kuma ledarta mai shak'e da kayan kwalliya.
Kusan yini ta yi lamarin da ya takura ni, kunyarta sosai na ji. Wanda ko kusan ban ta'ba jin irin hakan akan mahaifiyar Yaya J ba.
Karba ta samu daga ahalin gidanmu, dan kuwa ko Mama bata yi abin kaico ba, har ta tafi.
Dada ce dai bata wani karbe ta da fuska mai yakanah ba, hatta shi da kansa da ya je gaisheta bai ji da'din karbar da ta yi masa ba.
Hankalina ya fara tashi domin kuwa ba hannu Rabbana ya je mata ba, sai da ya siyo mata lafiyyayun lemo da kankana da ayaba tika tika.
Na dinga fargaba da tunanin wata'kila wannan d'in ma, ta yi mini sanadinsa tunda su Baban Tsakiya kullum cikin fadin Alh Tanimu munafiki ne wai yana nuna wa ya fisu kusanci a wajen Dan-uwansu".
Kuma gaskiyar magana a yanzu da muka shafe satika kusan uku ba k'aramar shakuwa muka yi da shi ba.
Ina matu'kar kad'uwa a duk sadda zuciyata ta ayyana mini muna iya rabuwa. Ban ta'ba kuma shiga irin wannan yanayin a baya ba.
Duk kishin Yaya J a kaina ya ha'kura ya bar ni da Nuru domin da kansa ya ce ba zai hana ni kula shi ba, amma shima kada na ce na sallama shi, ya yarda ni din allura ce cikin ruwa mai rabo ka dauka.
Dan haka zai cigaba da lalube cikin ruwa har Ubangiji ya taimake shi ya damk'e abin da yake nasa ne
KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*MASU BUKATAR YON RIGISTA DA G.H.T. KAKARKU TA YANKUE SAKA DOMIN KUWA FASEELAT ZATA MUKU JAGORA HAR KU FAHIMCI KOMAI CIKIN KYAKKWAR MU'AMALA DA KYAUTATAWA*.
*07039269802*
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya, kusancina da Nuru yana sake shahara. Har ta kai ya goge mini rad'ad'in rashin kwamshina a zuciyata.
Rashin Yaya J ne bai bar ni gaba'daya ba, amma ya yi rauni matu'ka da gaske.
Yayin da Bulkachuwa ya d'ora masa karan tsana haka siddan.
Sau biyu yana ganinmu idan Nuru ya ba shi hannu sai kawai ya d'aga masa, amma ba zai yarda ya ba shi nasa ba.
Na cigaba da zuwa makaranta hankalina ya fara kwanciya. A lissafi saura kwanaki talatin da tara na bar gidan.
Tare za'a ha'da da na Nasiba domin tuni wanda za'a bata ya ce ya kammala gininsa dan haka ba za'a kai bad'in da suka ambata da farko ba.
Lafiya lafiya yan uwan Alh Tanimu suka kawo komai na al'adar aure aka karba, cikin mutuntunta juna.
Saboda Baban Marina ya gayyato yan'uwansu na Lame da Kano kan dole su Baban Tsakiya suka zauna aka karbi bak'i da su.
Gidan Nuru da yake bayan gari k'arami mai kyau shigen na Yaya J.
Irin murnar da nake ciki na barin gidanmu tamkar wacce na girma ba'a gaban uwa da uba ba.
Domin na riga na kai makura wajen son na kauce na bar wa su Baban Tsakiya gidan su tabbata a cikinsa.
Ubaida ce farkon wacce aka kai makaranta kwana a gidanmu.
Idan mai karatun bai manta ba diyar Baban Marina ce itama diyar Inna ta biyu.
Yau an yi hutun zangon karatu na biyu.
Bulkachuwa ne ya taho da ita tunda shi kusan akai akai yake zuwa Bauchi.
Tana GGC Bauchi ne ajinta uku, mutumiyar Ikilima ce haka suke tamkar ni da Nazira sai dai banbanci akwai tazara mai yawa tunda shekaru kusan uku ta bawa Iki. Amma amincin da yake tsakaninsu sai Allah.
Saboda Ubaida, Iki ta nace boarding ita ma zata tafi, duk da dai ta fara day ajin ta d'aya a sakandire su d'in kamar karatunsu ba zai yi sauri irin namu ba.
Tunda a yanzu haka har Dada ta fara maganar auren Ubaida, a dalilin tana da garin jiki, kuma tana shirin shiga shekaru sha biyar ne.
Cikin farin-ciki muke hutunmu, na saje a tsakanin Ikilima da Ubaida tunda ni din ba ni da auki.
Ba abin da yake damuna sai bibiya da nacin yaya J.
Matu'kar kuma na yi saken da muka ha'du yini nake yi babu sukunin a dalilin fama da tsallen badake da zuciyata take yi.
Da yake aurena ba kwatsam ya zo kamar na Nazira ba, Baba ya samu damar siyan dimemiyar katifa mai nagarta.
Ya tanadi labulaye da kafet, da ledar tsakar daki da kuma bargo.
Irin dai kayan da aka yiwa Nazira.
Ya ce idan ya samu dama ko a ranar da za'a kai ni ne idan ku'din gado da kujeru sun samu sai a siya tunda gasu nan a bakin titi ko ina, idan kuma bai samu ba to a hakan zai kai ni arzikin gidan miji yafi na uba.
Ban damu da rashin kayan katako ba, na sani in sha Allah yan'uwana zasu yi mini irin na Nazira.
Sai dai bani da garanti akan manyanmu yan dakin Mama. Domin sun yi nisa a cikin *BAK'AR TA'ADAR* Y'an ubanci.
Su Yaya Salisu ne kawai zasu tsaya mini tunda sun fara daukar albashi duk da dai ba mai wani nauyi ba ne amma dai sunfi da .
Ranar asabar mun dawo daga Islamiya.
Yammaci ne sosai muna tafe da yan ajinmu.
Mun zo daidai wani gida da bai kammala ba, muka ga Bulkachuwa da wata yarinya wacce nafi zaton ita ce Bilkin da na ji yana fa'da a waya kwanaki, sun fito daga cikinsa.
Gajeriya ce, amma fara ce sai dai ko kusa bata kai ni ba.
Sannan ita din yar duma duma ce tamkar su Nasiba.
Kirjinta a cike yake, jikinta irin rugu-rugu ne.
Nan da nan shaidan ya kawo wa zuciyata caffa domin take sai na yi aiki da zato, na zarge su da al'amarin da shaidarsa yana da tsananin tsauri.
Na kalli Nasiba na ga hankalinta na kansu, tausayinta ya kama ni, domin sai yanzu na gane ba son Nasiba yake yi ba, domin ko ka'dan bai yi mata uzziri irin wanda ya yiwa Bilki ba. Ko da yake maganganun da mahaifiyarta ta yi wa uwarsa ne suka yi masa ciwo ba ka'dan ba.
A zuciyata na ce shi kuma Bulkachuwa yana son lukataye masu manyan nonuwa.
Na sake kallonsu na gan shi kamar kullum ba wani wadatatcen wanka, yana cikin yanayin babu yabo babu fallasa.
Amma ni kam duk saurayin da ya zo mini a haka ina da tabbacin ba zan saurare shi ba.
Domin an sanya mini son namijin d'an wanka, haka nan na k'yamaci marar gyara irin Tijjani.
Amma a hakan yake murza zuciyoyin yan mata kintsatssu da watsatssu.
Na sani kuma kyaunsa da zubin k'arfin da yake da shi yake rudarsu.
Gaba'daya a murde yake dukkan physiques dinsa sun bayyana alamun yana motsa jiki yadda ya kamata.
Na ja tsaki muka wuce, yayin da ya yi kamar bai hango mu ba.
Ba zato na ji Nasiba ta barke da kuka mai sauti.
Wani har tsayar da mu ya yi yana tambayar ba'asin kukanta, domin dai ya dauka ta samu labarin rasuwar uwa ko ubanta ne.
Kukan nan na Nasiba ya yi matu'kar dukan zuciyata, domin na san pain din da ake ji na kubuce war masoyi domim ni din katuwar victim ce.
Muna tafe, tana kukan bata fasa ba, duk yadda nake bata ha'kuri da kalamai masu nutsar da zuciya.
Kukan nata sai ya zama sanadin tabarbare war sassaucin da na yi akan al'amarin Bulkachuwa.
Domin na dauke shi a mai son kansa, mai fifita bare akan jininsa.
Sannan fitowar da suka yi daga kongon gidan da babu kowa a ciki ya sanya na sake k'yamarsa da dukkan zuciyata, domin kowa ya shaida shi din mai BAK'AR TA'ADAH ne.
Da k'yar na shawo kanta ta yi shiru.
Amma a k'asan raina haushin makauniyar soyayyar da take yi masa nake yi.
Gaba'daya ta lalace, ta zube bata farin-ciki ko ka'dan da auren da za'a yi mata.
Uwarta kuwa ta ja ta dake akan sai dai ta canja uwa matu'kar ta ce ba zata yi wa mahaifinta biyayya ta so d'an-uwanta da ya za'ba mata ba.
Duk da k'arancin shekaruna na fahimci Tijjani ne kawai mahaifiyarta bata so, domin kuwa mahaifin su Nasiba bai cancanci ya yi irin wannan ikon ba, tunda gaba'daya fita ya yi daga hidimarsu, ba wanda ya taba ganin an kawo musu wani abu daga mahaifinsu, ko danginsa, duk wahalarsu uwarsu ce da danginta.
Amma an zo batun aure ya nuna ikonsa na uba, ita kuma duk ba'kin cikin da ya k'unsa musu daga ita har Dada sun manta.
Abin da nake tambayar kaina shine shi wanda Baba Maryon ta fifita akan dan yar'uwarta tana da tabbacin nagari ne?
Ko dan kawai ma'aikacine, ya kuma gina gidansa?
Na yi imani da ace Bulkachuwa yana da ku'di to ko yafi haka lalace wa za'a ba shi, duk wani na'kasunsa sai an yi masa kwaskwarima ya zama abin uzziri.
Amma da yake bashi da ko sisi, sai take ta akilon y'arta ta nisan ce shi, ta so d'an-uwanta na dangin ubanta, na d'an yar'uwarta kuma ya tabbata a lalace.
Muna isa gida Dada ta hau tambayar makusidin kukanta.
Kai tsaye na shiga rattaba mata dalilin.
Ta yi tsaki ta ce "Kare ya cinye miki zuciya Nasiba. Ina ce jiya a gabana ya tsaya yana miki kashedi akan ki sakar masa kurwarsa?
Bakaken maganganun da ya cusa miki, ai masu cizo ne da kina da hankali.
Domin bai ji kunyar idona ba ya ce miki komin k'wadayin ki shi yafi k'arfin ko dandana shi ki yi, bare kuma ki mallake shi a matsayin miji.
Amma dan lalace wa har ki zauna kina kuka dan kin gan shi da wata? Bayan Allah ya baki mai son ki, nutsatssatse ba irinsa ba. Bayan hakan kuma mai abun hannune ta ko ina ya yiwa mai sunan manya fintikau. Ban da ma darajar jini me zai sa ki so shi haka?
Ko an yi auren ma wahala zaki sha tunda ba sonki yake ba, ga kuma talauci da takaicinsa."
Jikina ya sake mutuwa ina ayyana duk soyayyar da take tsakanin Dada da Bulkachuwa amma take iya fa'din hakan a kansa saboda Nasiba?
To wai wa take so ke nan a tsakaninsu?
Take na yanke hukuncin Nasiba take so.
Na tsinci kaina da jin haushin yadda bai san ciwon kansa ba.
Kullum a fa'din ya daina mugayen dabi'aunsa yake, ashe ba hakan ba ne.
Ina tsaye tamkar gun ki aka fara kiraye kiraye sallar maghariba.
Murya a dashe na ce "sai anjima Dada".
Na tafi na barta tana ta kumfar baki da dan mulmulallen bakinta.
Muna idar da sallar na kalli Gwaggo na hau rattaba mata bayani.
Ina fa'din "Gwaggo ashe har yau Bulkachuwa yana yin iskanci?
Dazun na gan shi da wata sun fito daga kongo".
Ba zato na ji ta gwabe mini baki. Tare da cewa "A ina kika san iskancin?
A ina kika ga yana iskancin?
Kinsan girman al'amarin da kike fadi kuwa?.
Dan sun fito daga kongo shike nan sai ki yi shaidar zurr?
Annabi ya tsananta jan kunnenmu akan shaidar zurr.
Kinsan matakan da sharia ta gindaya kafin a zartar da ce wa mutum ya yi zina?
Sai an ga mutum turmi da tabarya, kuma daga bakin muminai da aka gasgatasu har guda hudu.
Ba dan komai ba saboda kiyaye nasaba da mutunci.
Amma mutanan yau sun manta wasiyyar ma'aiki a kan kazafi da shaidar zurr. Ki kiyayi yada sharri Yabi."
Na kasa ce wa komai a dalilin ba k'aramin azaba na ji ba, domin da k'arfi ta bugi bakin nawa.
Ta zarce da fa'din " Àllah ka shiryi duk wanda ya kauce hanya, Allah ka shirya zuri'ar al'ummar Annabinka. Allah ka shirya Tijjani, ka bashi sana'a, ka tsare shi, ka mayar da shi nagartacce".
Na amsa ameen a zuciyata, ina alkalancin maganganun Dada da na Gwaggo akan Bulkachuwa.
Shike nan sai na kame bakina ban yarda na sake fa'din wannan maganar ga wani ba.
A hakan har aka shafe sati dai-dai lokacin saura sati biyu aurenmu.
An kawo lefen Nasiba.
Lefe kuwa mai kyau, komai sai son barka, domin komin kushen mai kushe na zai kushe kayan ba.
Amma gare ta babu wata murna. Dan ko dazun nan sai da na ga tana wanke wa Bulkachuwa kayansa.
Ba kuma sata ya yi ba. Ajiye wa ya yi a inda ake wankin ita kuma ta jika ta wanke tare da na Dada.
Kwanaki biyu a tsakani aka kawo lefena.
Sun yi kokari kwarai da gaske domin duk ha'duwar kayan Nasiba, nawa sun zarta nata da ka'dan.
Amma abin mamaki ahalin gidanmu basu zuzuta kayana kamar yadda aka yi ta kuranta na Nasiba ba.
A lokacin kuma Dada da y'ay'anta kullum sai sun zauna, Babanmu ne kawai ba'a sa shi a cikin zaman sai Baba ta Bulkachuwa ita kuwa ba a garin take ba.
Saura kwanaki goma sha biyar auren Dada ta zaunar da Babanmu.
Bamu san me ta ce masa ba, amma dai mun ga ya shiga cikin rashin sukuni har washagari.
Ashe ce wa ta yi auren Yabi da Nuru ba zai yiwu ba matu'kar tana da iko akansa.
Ya nemi sanin ba'asi ta ce ya saurare ta zuwa jibi.
Bai sanar da kowa ba, har sai ranar da ta ambata.
Dukkansu suna zaune a dakinta.
Cikin rashin damuwar komai ta ce "Alhaji! Yanzu ya kyautu ace an bar mai sunan manya yana gararanbar neman aure ana hana shi, alhalin akwai yara a gabanku?
Kullum da abin nake