Showing 141001 words to 144000 words out of 184118 words

Chapter 48 - Bakar Taada Hausa Novel Complete

na zuba wani kudin ba. Dan haka na ware kudinsa na ba shi, tare da yi masa bayanin yadda kudaden suka haihu dan haka zan cigaba da yi da nawa. Yana bude baki sai ce wa ya yi wadananan din ma naki ne. Kin tuna bashin da kika yi ta ranta mini a lokacin da bani da shi?". Na girgiza lai na ce " A a tsakanina da kai babu bashi Baban 2. Ba ka dauke ni yadda na dauke ba Wallahi." Da azama ya ce "Na gode, na yarda babu bashi. To na ba ki kyauta.
Na murmusa na ce "Ka dai biya ni kawai. Shike nan na gode, Allah ya kara budi da lafiya." Ya amsa da "Ameen maman 2."
Ya kanne mini ido tare da ce wa "Na kosa a yiwa su twins Gambo fa".
Na yi dariya na mike na bar shi dan yanzu sai ya fara tsokana ta akan abubuwan da na yi ta yi masa a baya.
Muna cikin haka babu zato sai ga shi ya zo mini da takardar da take nuni na samu gurbin karatu a kwalejin ilimi ta jihar Bauchi.
Ban yi murna ba, domin tun filazal na fi son na yi kasuwanci. Na kuma fahimci Ubangiji ya sanya mini nasibi a cikin juya kudi. To akan me zan damu kaina sai na yi karatun da babu garantin zan ci moriyarsa tunda kullum kasar sake lalace wa take yi. Aikin gwamnati siyar da shi ake yi da makuden kudade, sai kana da hanya ma da ka samu a siyar maka d'in.
Bai yi fishi ba, ya zauna ya dinga zayyano mini tasirin ilimi a wajen mace ba dan ta yi aiki ta samu kudi ba ne kawai. Ilimin mace da gogewarta na taimaka mata k'warai wajen bawa yara tarbiya da sanin yadda zata yi cudanya da mutane daban daban. Ya sanyaya murya ya ce "Ki daure ki sawa zuciyar ki soyayyar karatun nan Asiya dan sai kin yi shi. Fata na ke yi ko na mutu a ce ke din kina da wata madagora da zaki rik'e mini y'aya'na. Duk duniya ke nake da tabbacin ba zaki gaza da hidimarsu ba. Daure ki bani hadin kai mana".
Na dinga kuka domin idan yana irin wannan maganganun gabadaya kidime wa nake yi. Shi kuma baya fasa fada mini lokaci zuwa lokaci, tamkar mai son na yi haddarsu. Tare muka fara makaranta da su Hanif. Domin Nursery da take cikin college din ya snaya su. Da kansa yake kai mu. Sai ya wuce garin da zai je. Bama koma wa gida sai na gama daukar darussa.
Komawa ta makaranta sai ta jawo takaddama mai yawa a cikin gidan Marina. Domin a tarihin gidan ni ce na kammala sakandire har na fara ta gaba da ita da kuma aurena. Dada ta dinga sababin ya rungumi BAK'AR TA'ADAR arna masu barin matansu suna cud'anya da mazaje kullum da sunan neman ilimi. Babu kishi babu komai. Alhalin ma'aiki ya ce wanda baya kishin iyalin sa babu shi babu jin kamshin aljanna.
Yanzu gabadaya gidan Marina ni na tsole ido. Rufin asirin da muke ciki ya na matukar mintsinin ahalin gidan.
Bana damuwa tunda ba a garin nake ba. Wani abin ma har a yi yamididinsa a gama bana ji bare raina ya baci a banza.

Kwatsam sai ga Maijidda a gida, wai ta yi yaji. Al'amarin bai yiwa iyayenta dadi ba. Domin ni da ake son ganina ina cikin tasku da jele da sunan bacin rai ba a tab'a ganin na yi hakan ba. Kuma abin mamaki Jabir din ne ya kawota gidan da kansa. Domin ta k'ure hak'urinsa a yadda ya fada.
Ya murje idonsa ya juya ya barta. Hakan ya kawo cece kuce da rashin jituwa a tsakanin Baban Tsakiya da na Kasuwa. Duk yadda suka so boye maganar kada mu ji. Sai da maganar ta fantsama domin aure zai k'ara ita kuwa ta ce bai isa ba, sai dai ya zaba ko ita ko amaryar. Ya so su fahimci juna amma ta tada balli domin da ta ga yarinyar da zai aura tunda dalibar kwalejin da yake koyarwa ce. Ai sai ta gigice domin haka take yar tsurut fara kal tamkar dai abokiyar tagwaitakar Yabi ce. Hankalinta ya rubanya tashi domin ta tabbatar ya sota ne a dalilin yadda suke yanayi da ex love dinsa. Ta kuwa ce ba dai ita ba. Shi kuwa ya ce bata da hurumin zaba masa wacce zai yi zaman aure da ita.
Watanni biyu basa cikin zaman lafiya, gabadaya ya murde mata fiye da yadda ta murde. A karshe ya kawo ta gida ya ce ta zauna ta huta tukun.
Da ya tafi ya kashe wayarsa da dukkan hanyar da za'a same shi. Baban Kasuwa ya dinga fad'a tare da fad'in tozarcin da Jabir ya yi, da shi yake. Kuma ubansa ya kasa tsawatar masa. Saboda yana jin tsoron sa. Rikici ya kaure a tsakaninsu Dada ta kasa shawo kan matsalar domin Baban kasuwa ya dauka da zafi, kuma dama tafi gudun zuciyarsa. Baban marinar da ba'a saka shi ba, shine ya tuntunbesu bayan Dada ta fad'a masa a dunkule ba a bude ba.
Abin mamaki kowa ya ce masa babu komai, duk da Dada ta fad'a masa. Shi kuwa sai ya hak'ura ya zuba musu ido.
Bai gane kan al'amarin ba sai da ta yi sati biyu. Da kanta ta je ta durkusa tana kuka ta fad'a masa yadda abubuwan suka kasance, sannan ta roki Baban Marina akan ya bawa Jabir hak'uri. Gabadaya ta shiga damuwa da tunani domin dukkan y'aya'nta uku suna can tare da shi. Mai shan nono kawai ya bar mata. Bata tab'a zaton zai yi mata hakan ba.
Duk kokarin Baban Marina ya amsa samun Jabir. Washagari ya tisa ta a gaba ya nufi Kaduna da ita. A ransa ya tabbatar dan tana son komawa dakinta ne. Ba dan hakan ba da bai isa ya yi irin wannan ikon ba.
Jabir na ganin sa ya ware fuska ya marce shi da girmamawa. Baban ya dinga yi masa fada tare da tabbatar masa ya yi tsaurin ido.
Cikin jin nauyi ya ce "Ka yi hak'uri Baba! Ta kai ni bango ne da yawa. Ni fa dama hak'uri nake yi domin ba hakan nake so ba, amma tunda kaddara da rabo ya ba ni ita, ban zalunce ta ba. Ga ta nan ta fada maka inda na kuskure domin nasan iyakar adalci ina yi mata. Aure kuwa bata isa hana ni yi ba, bata kuma da hurumin zaba mini wacce zan aura domin ni din ba makaho ba ba ne, bare ta ce zata zaba mini wacce zan aura".
Baba dai ya yi masa fada tare ce wa "Ka dauke ta ka kai mana ita, ka yi tafiyar ka ai rainamu ka yi Jabiru. Duk cikinmu ka rasa wanda zai maka maganin matsalar sai ta hanyar mayar mana da ita? Ko a lahira wani na cin arzkin wani. Kada ka sake irin haka. Kishi kuma ai dole ta yi, ka rarrashe ta, ka kwantar mata da hankali ba wai ka ankara ta ba."
Ya juya ga Maijidda take kuka sosai ya ce "Ke kuma ba ruwan ki da auren sa, matukar yana yi miki adalci, kawai ki yi hakuri ki yi addu'a. Ai kishiya yar uwa ce, ina ruwan ki da ita. Ban da ma sakarci me ya ka ki yin fitina akan wacce ma bata zo hannunsa ba? Kina ahalin gidan Marina ki ce ba kya son kishiya? To ko da kika ga gyatumar ki ita kad'ai ai mu kina ganin kofofinmu mata ne da yawa ba kuma wacce ta kori wata, ko ta hana ta samun arzikin ta."
A ranar ya juyo ya dawo.
Ba jimawa kuwa Jabir ya yi aurensa. Hakan ba k'aramin tasgado ya janyo a taskanin Baban kasuwa da na Tsakiya ba. Da k'yar aka samu suka fara gaisawa. Kunyar mutane da yadda aka san kansu a hade yake ya sanya suke gaisawa. Da kuma yadda Dada ta yi kuka sosai akan gabar da suke yi da juna.
A zahiri sun shirya amma kasan zuciyoyi babu dad'i. Ba yadda zasu yi ne kowa yana ganin shine akan dai dai.
Baban Marina dai bai ce kala ba. Domin yanzu da abubuwa suka fara warware masa a dalilin mafi yawa y'aya'nsa muna cikin rufin asiri. Muna had'a abin da za'a ci a k'ofarmu. Tijjani kuwa ya dauke masa cefanen kayan miya da kudin k'ananun bukatu.
Hakan ya sake janyo masa bakin jinin da babu yadda za'a yi sai zunde a bayan ido.

***
A hakan na cinye shekara d'aya da fara karatun. Na fara nisa a cikin ta biyu. Tun bai shiga jikina ba, har na sanya shi a raina na mayar da hankali, hakan ya faranta ran Tijjani tunda ban sami carry over a shekarar farko ba.
A hankali sai nake ganin Tijjani na d'an sauyawa. Sauyin bai shafi mu'amalata da shi ba. Amma yana yawan zuwa Toro. Kusan kullum sai ya je ko da ba zai je Jos ba.
Ina ta jin rade radin yadda yanzu yake zama ya yi hira da Nasiba da har yanzu bata yi aure ba. Sai ma kasuwanci da take yi sosai. Kayan gwanjo take siyowa a Jos masu kyau. Har ce mini aka yi yana karbo mata sakon kayan.
Tun ina daure wa ina dauke kai daga abubuwan da nake ji har na fara sike wa.
A dalilin kullum dare sai ya fita k'ofar gida ya shafe lokaci mai yawa yana waya. Haka nan kaffa kaffa yake da wayarsa abin da baya yi a da. Da na yi masa magana sai ya balbale ni da fad'an na saka masa ido ne. Ban da hakan me yake yi mini? Dan ya yi wayar da bata shafe ni ba a waje shine laifi?
Na kasa bude baki na ce komai domin ba ni da hujja.
A hankali muka fara samun tazara a tsakaninmu. Na sani bai canja daga kawo mini abubuwan abincin ko na bukata ba. Bai canja a hidimar makaranta ta ko hidimar y'aya'nsa ba. Sannan bai canja mini a mu'amalarmu ta auratayya ba. Har yau din nan a cikin mararina ya ke. Duk da ni din ma kullum a cikin gyara kaina nake da ingantattun kayan Surayya da basu da illah ga lafiya. Sannan ina amfani da kayan g.h.t na FASEELAT.
Amma yawan wayar da yake yi da sintirin zuwa Toro, da sabunta mu'amalarsa da Nasiba da nake ta jin rade radinta, tana matukar ci mini tuwo a k'warya. Na rasa wa zan fad'awa ya fahimce ni. Domin da na fadawa Gwaggo ce wa ta yi "Ina ruwan ki da jita jita? Sannan ai bai zai yi aure bai fada ba. Ki rage kishi mussaman kan abin da baki gani ba, zato ne da shati fadi kawai.
Haka na hak'ura na cigaba da zuba ido tare da hak'uri. Amma sai nake ta d'ad'are wa da shi. Ko a shimfida bana wani katabus shi zai yi kidansa da rawar sa. Wani lokacin ya tambayi dalilin sauyin nawa cikin kwanciyar hankali. Bana iya ce masa komai sai dai na ce "Ban canja ba, babu komai".
Wani lokacin ya ce "Allah ya sauwake. Wani lokacin ya yi tsuka ya juya mini baya tare da fad'in "Zan yi maganin wulakanta ni da kike haka siddan Asiya."
Gabadaya mun koma muna ganin laifin junanmu a dalilin kowa bai gamsu da kokarin d'an-uwansa ba.
A haka na kammala aji biyu. Twins sun yi wayo sosai tunda sun shiga shekaru biyar. Wani irin wayo da fikira a cikinsu tamkar wanda suke siyo dabara a kasuwa. Gabadaya sun juye ubansu sak. Ga shi suna girma suna sake zama iri d'aya. Ni da kaina ina gane su ne ta halayyarsu. Domin har yau din nan Hanif mai hakuri ne, magana bata dame shi ba. Sabanin Hamim d'an hayaniya kuma mafadaci irina. Har yanzu bai bar kuka ba.
Sau biyu ina yin bari. A yanzu haka ina zuwa ganin likita a dalilin hakan. Na karshen nan da na yi Bulkachuwa ce mini ya yi "Ina sane nake bararwa tunda na saka masifa a raina. Ya rasa me yake mini da nake gana masa azaba haka.
Kallon sa na yi kawai. Ba tare da na tanka masa ba. Domin na riga da na saka a raina ce wa hakurin da aka yi ta jaddada mini na yi a lokacin aurena. Yanzu ne zan fara shi. Dan haka na rungumi addu'a, y'aya'na da karatuna hadi da sana'ata. Na tattara shi na zuba masa ido yana yin almuransa yadda yake so.
Muna cikin wannan zaman na fallasa tafi yabon yawa. Kamfani suka sake biyansa kudin hayar filinsa tunda shekaru uku ta cika. A wannan karon har da kari akan wanccan. Duk yadda muke jin haushin juna sai da ya zauna ya mini bayanin komai. Ya kwashe mu ni da yara zuwa Kano. Ya yi mana siyayya. Muka kwana biyu, muka juyo da kaya niki-niki.
Yara na baya duk barci ya sure su. Ya sassauta murya ya ce "Zan canja motar nan. Zan siyo wacce ta fita."
A takaice na ce "Allah ya kara budi".
Ya zarce da fad'in "Ana mini cinikin wani gida mai kyau a Toro zan siya".
Nan ma a gajarce na ce "Allah ya sanya alheri."
Daga haka bamu sake magana ba har muka iso Bauchi. A dalilin ya fusata duk yadda ya kwashe ni ya mini hidima bai sa na saki raina ba. Ni kuma ina masa kallon a yanzu yana ganin yafi karfina tunda yana samun duk abin da yake so. Kasuwa tana gara masa ainun. Shi yasa gabadaya yake neman bijire mini. Duk abin da yasan bana so a yanzu baya jin komai ya yi a gabana. Jiya da daddare ina jin sa a waya yana ce wa "Ga ni kike ba zan iya bata wayar ba? Wai me kika dauke ni ne? Bari ki ga na sayi gidan da zan saka.ki a ciki, ki ga yadda zan fito da maganar gabadaya. Namiji dan zai k'ara aure sai a ce ba zai iya ba? Mata nawa ne a gidansu? Nima kuma mahaifina biyu gare shi. Da ba'a karin aure da ba'a haife ni ba, tunda tawa gyatumar ce amarya a gidanmu ".
Dai dai nan na fito a bandakin. Nan da nan ya katse wayar tare da ce wa "Zamu cigaba da tattauna wa da safe". Ya katse wayar tare da kashe ta gabadaya.
Tun lokacin na sake karaya da shi. Tabbas aure yake nema kuma a Toro tunda har zai sayi gidan da zai saka ta a can.
Sannan tun yanzu na dame ta tunda har tana masa shaguben tsorona yake ji ba zai iya aure ba. A raina na shiga yiwa mutanan da suke ganin Bulkachuwa tsorona yake ji Allah ya isa ta fi goma. Domin a yanzu da kowa yake mini kallon ina cikin rufin asiri da jin dad'i a gidansa. Ni kad'ai nasan me nake fuskanta. Nafi samun nutsuwa a lokacin da ba shi da ko sisi. A yanzu ba abin da bani da shi a gidan na cima, tunda ga kan nama, kifi, madara, dankali, doya, bare kuma kayan miya, da duk nau'in kayan abincin. Ruwa da lemo basa yanke wa. Komai baja baja yake ajiye mana. Haka sutura ta wadace ni ainun. Amma kuma bani da nutsuwar da nake da ita a da. Ba ya shiririce mini kamar lokacin baya. Dan haka sai na fi son waccar rayuwar da kowa yake mini kallon tausayi.
Babah ta kawo mana ziyara. Ta dinga rarrashi tare da shan cikina akan matsalar da ta sanya bana girma, da na fara murmure wa zan sake tsomare wa. Ban yarda na ce komai ba, saboda nasan ba zata yi masa ta dad'i ba, idan ta tafi kuma ya hau sababin ina had'a shi da uwarsa duk da ba komai yake mini ba, ni ce nake zaluntarsa.
Da kanta ta fahimci a yanzu ni da shi kowa harkar gabansa yake yi. Gamu nan ne dai, babu warkajabi irin na da, babu nishadi a tare da mu duk da ba gaba muke yi ba.
Da daddare bayan yara sun yi barci ta zaunar da mu tana bincikar matsalarmu a kokarin ta na son ta sulhunta mu ta dinke barakar da kullum take sake bunk'asa a zukatanmu ba tare da mun ankara ba.
Tsawon lokaci ban iya bude baki na ce uffan ba. Ta hakura ta koma kansa. Cikin kwanciyar hankali ta tambaye shi me yake faruwa. Ai tamkar gudawa haka ya b'arke da zano laifukana. Ya kaurara murya ya ce "Gata nan gabadaya ta ki sarrafuwa mini. Ko dariya take yi da y'aya'nta idan na zauna a cikinsu ta gintse dariyar ke nan. Idan tana zaune a falo na zauna sai ta san abin da zata kirkiro da zai sa ta tashi ta bar mini wajen. Ba zan mata abu ta nuna ta ji dad'i ba, zata dai ta ce ta gode a takaice. Gabadaya ta fitini kanta ta kuma fitine ni. Gara ma da Allah yasa kika fahimci masifar da d'orawa ranta. Gata nan ta fada miki mene ne bana yi a gidan nan da zata kwarzabe mu irin haka. Yanzu idan na fita har fargabar dawo wa nake yi tsabar yadda take shagulatin bangaro da ni, da dukkan al'amarina. Ban sani ba ko miyagun kawaye suke hure mata kunne. Na tabbatar cikin da baya zama idan ta samu ma akwai dalili, idan an tsananta bincike, tunda ta riga ta taurare mini, ita tasan me take nufi da zaman".
Na yi k'asa da kaina ina hawaye mai cin rai. Zuciyata tamkar ta fad'o k'asa idan yana danganta b'arin da nake yi ni ce da alhakin hakan.
Babah ta dawo kaina cikin tausasa harshe ta ce "Haba Yabi me zai sa ki abin da baki yi a da ba, sai yanzu da kike girma, kuma Ubangiji yake ta yi muku Alam nasharaha. Me zai sa ki yi haka?"
Na fashe da kuka mai ciwo na kasa ce wa koma a dalilin yadda nake gunji da shessheka mai nauyi.
Baba ta yi zuru tana kallon yadda nake kukan.
Ta koma kansa ta ce "Kai ne kake musguna mata, kai ne ka janye dukkan rarrashi da tarairaiya a tsakaninku saboda kana ganin kana ajiye mata komai na bukata."
Ya yi shiru. Ta sake juyo wa gare ni ta ja ni zuwa jikinta tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login