Showing 183001 words to 184118 words out of 184118 words

Chapter 62 - Bakar Taada Hausa Novel Complete

na FASEELAT ba. Haka nan babu yajin Annur".
Na yi dariya na ce "Adda Nazi ke ce kadai kike gatsa Yabi! Ina ce ke shaidace bayan hajjin da na yi ina ciki, na yi a yanzu kan girmana ma?
Ta ja tsaki ta ce "Ba zance Hajiyan ba. Yar mitsitsiya da ke sai son girman tsiya.".
Na yi dariya na ce "To kwantar da hankalinki gobe Aish lame zata zo garin zata tsaya ta gaida Dada zata taho miki da su. Kinsan wannan Yaya Ummi aka aikowa ta Jos." Ko ma na baki lambarta sai ki zabi duka abin da kike so yayata".
Ta yi dariya ta ce "Yanzu na ji magana. To sai anjima hakima ta Yaya Bulkachuwa ".
Na yi dariya na cigaba da karatun littafin *Ya za'a yi?* da nake yi a waya na marubuciya *Binta Abbale*. Labarin ya ja hankalina. Tuni na tura kudina ina paid group din ta dan na ji yadda za'a warware wannan dambarwar.
*Tuni kuma nake group din Gaskiyar lamari na Nazeefa Nashe*da yake dad'i kamar kada shafi ya k'are

*YA KAMATA ACE Y'AN JAHAR BAUCHI SUN SAYI LITTAFIN NAN RUTUTU KO DAN SU RAMA MINI K'AUNAR DA NAKE YIWA JAHARSU*
🥰
*IDAN KE Y'AR BAUCHI CE MUSSAMAN TORO KO BULKACHUWA AMMA BAKI SIYA BA, NA TAYA KI JIN KUNYAR WANNAN LAMARIN*
*Fatan alheri GAREKU GABADAYA*.
😀🥲

Ina kwance kan gado ya shigo yana sab'e da Halifa. Na kalle shi ya zama CIKAKKEN mutum mai cike da Kamala. Tuni na fara hango shi a matsayin gwamnan gobe. Wato jihar BAUCHI ta jima tana yin zatan gwamnoni dogaye farare masu farar aniya. A fili na ce "Allah ga Baban 2 a cigaba da yi masa afuwa da rahama. A Buda masa kirijinsa a bashi ikon sauken nauyin jama'a babu gajiyawa. A cika zuciyarsa da son Hajiya Yabi da tausayinta da mararinta babu gundaura."
Ya kwashe da dariya sosai ya ce "Ubangijinma sai kin ce masa ke Hajiya ce?"
Na ce "To ai tunda zuwa gabar ne sharadin zama Hajiya ai tuni ita ce tun banzo duniya ba"
Ya rungume ni ya ce "Hakane Hajiya little. Ina matukar farinciki da ya burina ya cika na kai ki gabas Hajiya. Dukkan burikan sun cika fatana Allah ya cigaba da bani lafiyar da zan ciyar da ku halali na jiyar da ke dad'in duniya dan ki gane ba komai a gabana da ya wuce ki idan kika cire Babah".
Na langabar da kaina a jikknsa na ce "Ina godiya. Ubangiji ka so Tijjani, ka karba daga gare shi. Ina godiya bisa kaddara mini ya zama mijina, ina fatan ka tabbatar mini da shi har a aljanna."
Ya dinga Ameen dear Hajiya. Allah ya cigaba da iya miki, ya mayar da makiyanki fadawanki, ya shirya mana zuriarmu. Muddin rai ke ce tauraruwar zuciyata."
Daidai lokacin naji dirin mota tabbacin Yara sun dawo, daga school na yi maza na zame nasan Hamim idan bai ganni a falo ba sai ya biyo ni daki.
Ilah kuwa ya murda kofa ya shigo. Ya ce "Baban 2 Sannu da gida".
"Sannu dai Baban Marina. Tijjani ya fad'a da murmushi.
Ya iso gare ni ya rik'e hannuna ya ce "Ammi mun dawo".
Na ce "To sannu a je a cire uniform a yi wanka tunda kun yi sallah a school".
Ya ce "To ya juya zuwa dakinsu."
Yana fita Hanif ya shigo. Ya bude baki ya ce "Baban 2 yau baka je ofis ba?"
Ya ce "Hutawa nake yi Baban Bulkachuwa".
Ya rik'e baki ya ce "Gaskiya Baban 2 ba'a haka. Babu kyau fashi tamkar tauye mudu ne. Mai tauye mudu kuwa d'an wuta ne".
Ya janyo yaron jikinsa ya ce "Na gode da tunasarwa Babana. Zan kiyaye".
Ya sake shi ya matso gare ni ya dafa ni ya ce "Ammi sannu da gida ina Husna my dear?"
Da murmushi na ce "Tana wajen Dada! Ka je ka yi wanka sai ka je ka ganta."
Ya ce "Tom". Ya ja hannun Halifa da yake zaune a k'asa yana wasa da kayan wasan da Tijjani ya ajiye masa. Ya juya ya tafi amma Halifa ya saka kukan sai ya dauke shi. Haka ya dawo ya dauke shi ya tafi da shi. Ni mamakin yadda Halifa yake banbance shi da Hamim nake yi.
Kafin na yi magana Bulkachuwa ya ce "Wato Hamim ba k'aramin miskili ba ne. Ke ce kad'ai idan bai ganki ba zai damu.
Amma daga ni har yan'uwansa baya damuwa da rashinmu. Gara ma ya damu da Hanif".
Na ce "Ai Hamim danja ne, ance ni ya gado, ni kuwa ai mai son jama'a ce. Mussaman yan'uwana ".
Ya ce "Hakane shima zai warware. Allah ya shirya mana su gabad'aya.
Na ce "Ameen dear".
Da daddare daga ni har yara muna wajen Dada ana ga sharholiya cikin farin ciki ya shigo ya gaishe ta a tsaitsaye.
Ta ce "Alhaji Shehu daga tsaye yau?"
Ya ce na gaji ne Dada. Ina son na kwanta.
Ta ce "To babu laifi. Mu kwana lafiya."
Ya tafi Yara suka bi bayansa a guje. Ta kalle ni ta ce "Haba Hajiya tashi mana ki bi bayansa. Kya bar shi da yara?"
Na ce "Rabu da shi Dada ai yaji na yi masa. Yau tun safe bai kira ya ji lafiyata ba. Na k'ira bai d'aga ba".
Ta dauki salati ta ce "Haba Hajiya kinsan hidimarsa mai yawa ne.
Ban da abin ki irinsu Shehu ai ba'a samunsu da sakwa sakwa. Tashi ki je ai ki fahimtar da shi cikin hikima kin ji Hajiya Yabi"
Na yi dariya na ce "Tom".
Na isa falon na tarar da shi da yara akan dining suna cin abincinsu.
*
Muka kwanta ya ja ni jikinsa yana.ce wa "Sarka mai rikicin gangan Hajiya little".
Na share ya ce "wai ke ba zaki girma ba. Kullum sai kin samo laifin da zaki jingina mini? To ki huce komai na yi ma, ba da gangan ba ne. Ki yi hakuri kin ji My Hajiya love?"
Dariya ta k'wace mini na ce "Na lura dai yadda kake nacin ce mini Hajiya har da gayya"
Shima cikin walwala ya ce "To ba burinki ke nan ba? Zan ta ce miki Hajiya. Kuma duk shekara sai na raka ki umrar azumi tunda Annabi ya ce tamkar aikin hajji ce. Kin ga sai ki ta sabunta Hajiyar ta ki".
Muka yi dariyar jin dad'i muna fad'in Allah mun gode maka ka cika ni'imarka a garemu".

K'arshe.

Alhamdulillah.


*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login