Showing 63001 words to 66000 words out of 184118 words
Chapter 22 - Bakar Taada Hausa Novel Complete
ki fito ki dora abincin rana yunwa nake ji, ko kuma na bar ki da Ubangijin da ya wajaba miki yi mini biyayya".
Na fashe da kuka sosai domin ban zaci abin da zai biyo baya ba kenan.
Tun fil'azal na tsani ace za'a bar ni da Allah.
Cikin kukan na ce "Akan me zaka ha'da mini ba a gabana ba? Na sani ko ka jefa mini wani
abu a ciki".
Ya ja tsaki mai tsananin gaske. Ya ce "oh ina ganin tala jaurar duniya. Wai ke nan kina zaton zan miki wani abu a dole?
Ya girgiza kai ya ce "Babu macen da zan mata hakan. Sai kuma ya fashe da dariya mai sauti sosai.
Da murmushi ya ce "Asiya Toro manyan mata. Ki yi ta abu tamkar wata babbar mace. Dan Allah duka shekarun ki nawa ne?
Kin wuce sha biyar?
Ni kallon kwaila nake yi miki wacce bata gama fitar da halittun ta ba. Wacce bata kai wankan girma ya hau kanta ba. To me kike zaton zan miki da har zan baki wani abu na rashin gaskiya a cikin abin sha?"
Ba'kin cikinsa ya sake makure ni. Na sake fashe wa da kuka mai tsananin gaske.
Ya sa kai ya fice yana jaddada idan ban zo na dafa masa abin da zai ci ba, ya bar ni da Allan da ya kallafa mini yi masa biyayya.
Na jima ina zaune ina kukan ba'kin cikin takaicin da ya cusa mini.
Ga cikina sai kiran ciroma yake yi.
Ala tilas na tashi na fita bayan na goge fuskata da tissue.
Har lokacin yana ta faman hade wayar satellite din a jigin bango.
Na wuce shi fuu na fa'da kicin din.
Na tsaya ina nazarin me zan dafa ne?
A yadda nake jin yunwa zan fi son jalaf din taliya mai dan ruwa ruwa.
Dan haka na zabi kayan miyan da suka fara yin laushi na wanke na fara jajjege dan na rasa inda gireta take, duk da akwai wuta zan iya blanding dinsu. Sai dai na fi son na gansu a jajjegen.
Na yanka albasa mai yawa.
Na bare maggi duk na ajiye a kusa da ni.
Na tashi na daurayo tukunya, ya kalle ni, na galla masa harara.
Ya yi murmushi tare cewa "The great Asiya a kicin dinta".
Na share shi, na shiga falo na dauko naman da ban ci ba a fridge.
Na duba na ga ya cire albasar ciki.
Na nufi kicin din. Na zuba mai a tukunya. Na zuba albasa. Na jere komai na bu'kata a gabana.
Na kalli gas din da yake tsaye sabo dal da shi. Na fara tunanin yadda zan kunna tunda zancen gaskiya ban ta'ba kunnawa ba. Bamu taba amfani da shi a gidanmu ba.
Na yi shahadar murda wa sannan na fara kokarin kyasta ashana.
Sau biyu ashanar tana karyewa saboda rashin k'warinta.
A karo na uku ta k'yastu, na nufi bakin gas din da ita. Ai kuwa gas ya yi wani irin but da karfin gaske! Na furgita, na tsora ainun, na mike na dinga karo da fatali da kayan da na jere a gabana na yi waje a guje cikin ki'dima mai yawa.
Ya fito a band'aki ke nan, ya gan ni a guje na yi dakina.
Ya biyo ni da sauri. Fa'di yake "mene ne, mene ne?"
Ya zuba mini ido yana kallon yadda jikina yake kyarma irin na tsoro sosai.
Da sigar salama ya ce "Asiya! Nutsu ki fa'da mini. Mene ne ya ki'dima ki haka?"
Ganin na kasa magana ya tashi ya nufi kicin din.
Ya tsaya a bakin k'ofar yaga yadda ruwa ya jiqa kasan kicin din. Komai a wancakale tabbacin ta kansu ta bi.
Ga gas kuma yana ta yi fahh.
Ya rage karfinsa. Sannan ya dora sanwar. Domin ya saba girki tun yana makaranta.
Ya gyra wajen. Bai bar kicin din ba sai da ya tsaida ruwan girkin tunda ya ga taliya ta yi niyyar dafawa.
Ya koma ya zauna kusa da ita a bakin gadon. Zuwa lokacin ta dan shiga nutsuwar ta.
Ya sassauta ya ce"Asiya wai mene ne? Kadangare kika ga ni ko tsaka?"
Na zum'bura baki na ce "Wutar abin nan ne ta yo kaina gaba'daya".
Ya kwashe da dariya sosai. Hakan kuma ba karamin kular da ni ya yi ba.
Cikin bacin rai na ce "Yi dariyar ka son ran ka Tijjani, ai ko k'onewa na yi baka da asara tunda ba sanin darajata ka yi ba".
Na fara hawaye. Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi. Nan da nan ya gintse dariyar da yake yi.
Ya ce "Very sorry Asiya Toro. Abin ne ya bani dariya yadda kike yar gayu kuma wayayyiya amma gas ya yi miki wula'kanci irin haka?".
Sai kawai ya sake tintsire wa da dariyar da ta fi ta farko k'arfi.
Ba'kin ciki har mak'oshina nake jinsa. Na rasa me zan yi na sanya takaici akan zuciya da fuskarsa.
Kafin na yi magana ya yunkura ya tashi a dalilin kamshin da ya fara cika hancinmu wanda alamu ne na ya tafaso.
Bai dawo dakin ba, sai da girkin ya kammala.
Ya dawo da plate biyu a hannunsa. Ya dire a k'asa, ya sake fita. Kaamshin girkin ya cika d'akin, hakan ya sake sabunta mini yunwar da nake ji.
Ya dawo dauke da pure water da lemo akan tire.
Hannunsa kuma da fork guda biyu.
Ya zauna ya ja plate daya gabansa ya bu'de murya ya ce "Bismillah Amarya".
Na bata rai na ce " Asiya Toro dai. Ina na kai darajar amarya bayan ni din yarinya ce kwaila kuma kankanuwa".
Ya murmusa ya ce "Oh wai maganar ciwo ta yi miki ne?
Tsakani da Allah ba gaskiya na fa'da ba? "
Na girgiza kai ba tare da na kula shi ba.
Na sauko na ja abincin da yake jirana.
Na kai bakina duk kushena ban isa na ce ga inda girkin yake da tasgado ba.
Na dinga zura loma.
Sai da ya ga na kusa cinyewa ya kaikaice ya ce "Asiya Toro iyashegen ki yawa gare shi. Jibi yadda kike zabga loma kina zare ido. Me ya janye tunanin zan zuba miki wani abu a ciki Kuma?
Kunya ta kamani ka'dan. Amma na daure na yi kamar ban ji komai ba.
Na share shi. Sai da na gama na yi gyatsa, na kalle shi na ce "Na tabbatar da Yaya J ne ya dafa abincin nan, zubowa zai yi a waje daya. Sannan ya manta cikinsa har sai ya tabbatar nawa cikin ya cika."
Na saci kallonsa na ga har wata zufa ce ta karyo masa.
Zuciyata ta fara harbawa da tunanin hukuncin da zai yi a dalilin yadda yanayinsa ya nuna maganar ta buge shi.
Ga mamakina sai kawai ya yi yak'e ya ce "Ba ki yi karya ba Asiya! Domin jiya mun je gidansa ni da Salisu a dalilin an sace mashin dinsa.
A gabanmu ni da Salisu yake tarairayar Maijidda akan ta daure ta ci ayaba. Kinsan cikinta ya tsufa ba komai take iya ci ba.
Ai Jabir kam yana mutuntunta maganar tsohonsa akan Maijidda. Sosai yake sonta yake tattalinta. Har mamaki na dinga yi tare da shakkun idan har ya taba son wata mace kafin ita.
Ita ma bata jin kunyar mu din yayunta ba ne sai tabara take yi masa son ranta.
Take na gano mata irinsu ba zasu ta'ba barin mijinsu ya yi tunanin wata macen ba. Wanda duk ya samu irinsu ya gama morewa, ga cikar halitta ga shagaba ga kuma biyayyar iyaye da aure. Wanda bai samu irinsu ba ai zai dauwama cikin cizon yatsa ne.
Sannan tagomashin biyayyar da suka yiwa iyayensu ya sanya gidansu ya zama gidan farin ciki."
Maimakon na b'ata masa rai, sai ya zamana nawa ran ne yafi b'aci. Bayan kod'a Maijidda da ya dinga yi, tare da kwarzanta ta, sai na fahimci yarfe yake yi mini akan ban yiwa nawa tsohon biyayya na mutuntata aurena ba.
Na yi shiru na kasa cewa uffan. Ya gaji da jiran kalamina, ya tokara ya tashi. Bai dauke kwanon da ya ci ba, bare ya ha'da da nawa. Ya bar gidan ba tare da ya yi mini sallama kamar yadda ya saba ba.
Tun da ya fita bai dawo ba, sai bayan sallar isha. Ga mamakina sai na ji haushin hakan. Rashin dawowar tasa ta mintsinin zuciyata sai dai ban bari ta bayyana akan fuskata ba.
Ya leko ni, ina zaune a daki. Bai shigo sosai ba. Ya ajiye mini leda ya juya bayan ya ce "Sai da safe".
Bansan ya aka yi ba kuka ya k'wace mini.
Ni da kaina ban san dalilin kukan ba.
Amma so na yi ya shigo yana lallaba ni, da ro'kon na ci abin da ya siyo, ina botsare masa.
Ko duba ledar ban yi ba, na yi kwanciyata bayan na rufe k'ofar dakin.
Cikin dare na tashi da wata azababbiyar yunwa.
A gigice na janyo ledar na hau cin awara irin manyan nan ga kabeji. Da k'yar na iya janyo leda a lungun gado. Maman kawata Shafa'atu ce ta je Kano ta siyo yajin Annur food mai dan karen dad'i. Shine ta ba ni roba d'aya.
*Annur food Delicious*
*Ba iya yaji ba har da garin danwake da man Shani, da yajin daddawa*
*Tuntube su a wannan lambar dan k'arin bayani 08039183880*.
Na sani sadda ya kawo da zafinta.
Sai da na cinye tas, sannan jikina ya daina rawar yunwa. Take na tuno ashe jiya iya taliyar nan kawai na sanya a bakina.
Na jima barci bai dauke ni ba. Sai kawai na yanke shawarar na doro alwallah na yi nafilah. Na mike ina da tabbacin Gwaggo na kan sallayarta a irin wannan lokacin da bayi suke barci.
A hankali na zare sakatar na fita. Abin mamaki sai na ga Tijjani akan barandar yana sallah. Yana sujjada. Na dakata ya idar tunda ba zai yiwu na wuce ta gabansa ba.
Na jingina da kyauren kofar dakin nawa. Ina kallon yadda ya kyautata sujjadar. Tsawon lokaci bai dago ba.
Wani abu ya sake tsirga mini a kansa. Na tuna a duk sadda Gwaggo ta tashe ni cikin dare dan mu yi nafila. Cewa take yi daure ki tashi ki nemi yardar Ubangiji Yabi. Irin wanna lokacin sai zababbun bayi ne suke rabauta da yin ibada. Duk kuma abin da mai yin ibadar dare yasa a gaba sai ya ga sau'kinsa.
Allah da kansa yake saukowa sararin subhana yana shelar ina mai bu'kata na biya masa?"
Zuciyata ta sake harbawa domin ni kaina da bana son Tijjani. Kallonsa yana sujjadar nan sai da na ji wani irin abu, to ina kuma Ubangijin da ya kyautata sujjadar saboda shi.
Har lokacin kuma bai dago ba.
Na sake tuna jawabin Gwaggo da take fadin kada ki ce sai kina cikin damuwa ko bu'kata zaki yi sallar dare. Domin idan ta zame miki dabi'a, to lah shakka duk wata bak'ar k'addara da zata zo miki, sai ta zo da sau'ki, sannan komai kika roka zaki ga biyan bu'kata duk nisan jinkiri. Ban da ma dai dan adam mai shagala ne, ai ya kamata ace yana yawan yin godiya ga Ubangiji bisa dinbin niimomin da ya masa.
An yika musulmi, an baka lafiya, an kuma hore maka abin da zaka ci komin kankantar sa.
Ashe kuwa ba sai da damuwa za'a yi ibada ba.
Na nisa ina jin na fara gajiya da dakonsa.
Har zan koma daki sai kuma ya d'ago.
Na dinka fatan ace sujjadar karshe ce ba zai koma wata ba.
Ai kuwa sai na ga ya zauna, alamun attahiyatu yake yi.
Ina ganin ya sallame na yi maza na wuce a dalilin fitsari ya kama ni ba ka'dan ba. Yana zaune har na fito na shige shi. Sai dai Ina wuce wa ya sake mikewa tabbacin dama ya jinkirta mini ne na wuce.
Raka'a biyu na yi mai dauke da gajerun surori.
Na yi yan adduoina. Ban san me yasa na kasa addu'ar da nake nacin yi ba.
Na Ubangiji ya tarwatsa aurenmu. Na tsinci bakina da fa'din Àllah ka mini zabin da zai fi mini alheri. Karon farko da na yi addu'ar da dukkan zuciyata.
Na yi addu'oi, na yiwa mahaifana addu'a, na ha'da da al'ummar ma'aiki.
Na koma na kwanta ina fa'din "da wanda yayi doguwar sujjada, da wacce ta yi gajeriya, Allah dai ake yiwa, to Ubangiji ka karba mana gaba'daya".
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
Ina kwance ina jin dukkan k'uncin da yake raina yana zagwanye wa da kaso mai yawa.
Ban makara sallar asuba ba, a dalilin ya buga mini k'ofa na tashi.
Wajen k'arfe takwas da rabi na ji ana kwankwasa k'ofar dakin.
Na tashi na bu'de.
Na gan shi a tsaye. Ya kalle ni ya ce "Ki zo ki d'ora mini abin karyawa na fara jin yunwa."
Na yun'kura da nufin na yab'a masa bak'ar magana. Amma ina ganin yadda ya d'aure fuskar . Sai ya yi mini kwarjini sosai.
A sanyaye na kawar da fuskata na ce "Ni bazan sake kunna shi ba".
Ga mamakina sai ya sassauta ya ce "Wanko fuskar ki zo na kunna miki. Ai jiyan ma shi kika fara kunnawa kafin ki kyasta ashana. Sa'a ma kika yi ai da gaba'daya jkinki zai bi.
Na sake tsorata na ce "gaskiya ka siyo mini gawayi. Idan baka nan wa zai kunna mini?"
Ya murmusa ya ce "Zaki iya a hankali."
Ya dakata na yi brush, na wanke fuskata, sannan muka nufin kicin din.
Cikin nutsuwa ya ce "Sai kin gama hada komai na girkin ki, sai ki kyasta ashana sannan ki murd'a gas din ki.
Amma a fara kunna gas da sakwanni kafin a k'yasta ashana hatsarinsa yafi na had'arin mota muni."
Ina tsaye ya kunna. Sannan ya fita yana cewa "Sai ki dora abin da zaki yi".
Na yi jim ina nazarin abin da zan yi. Sai kuma na yi azamar daukan tukunya na dauraye na d'ora bayan na zuba citta da kaninfari.
Na sake nutsawa cikin nazarin me zan yi ne.
Idona ya sauka akan doyar da ya zo da ita.
Na dauko wuka na yanki ka'dan tunda manyan ne sosai.
Ina gama ferewa shayin ya tafasa.
Na juye, na mayar da doyar.
Ina zaune ina fatan na soya doyar nan ta yi kyau.
Zancen gaskiya ba saba soya doya da kwai muka yi ba.
Amma kwanaki mun kalla a wata tashar girke girke a YouTube mun gwada a gidan Nazira kuma ta yi kyau.
Na dudduba na ga babu k'wai a kicin din.
Na fita na gan shi yana ta faman janyo ruwa a rijiya.
Na cuna baki na ce "Kwai za'a ba ni".
Da walwala ya ce baki kula da shi a fridge ba?"
Ban ce komai ba. Na koma kicin na dauko bowl, na nufi falon da shi.
Na debo guda hud'u.
Cikin ikon Ubangiji na kammala aikin lafiya, kuma ta yi dadi da kyau, k'amshi ya cika gida.
Na zuba masa a plate mai zurfi irin na dafaffiyar roba, na dauko robar yaji na zuba masa a gefe. Na dauki flask din shayi na kai masa falon.
Na dawo na dauki kofin shayi da cokali da kuma cokali mai yatsu, na kai, sannan na rufe nawa a kicin din da zummar sai na yi wanka.
Na fito, na ga ya yi wanka ya shirya yadda ya saba.
Ma'ana kaya babu guga.
Takaici ya mak'ure ni. Nan da nan idona ya kad'a a dalilin tausayin kaina da ya kama ni.
Ni d'an gayu nake so wanda ya iya wanka da soyayya ba marar kintsi irin Tijjani ba.
A shak'e na ce masa "Na ajiye maka a falo".
Ya share tamkar bai ji ba. Na shige band'akin na rufo kofa da k'arfin gaske.
Ya yi sakare domin ba karamin haushi ya ji na wannan tumbatsar da take yi ba. Sannan ta yi magana tamkar da yaronta, bugu da kari ta buga masa kofa tabbacin raini na gaske ta yi masa.
Ya ha'diye bacin ran da ya taso masa.
Ya isa falon, ya tarar da wani sabon bacin rai.
An ajiye masa abinci a bude babu sayawa. Sannan duk farantan tangaran din da ya ga ni ta kasa zuba masa a ciki ta rufe sai a wnanan?
Duk yadda doyar ta yi masa kyau a ido, ga kamshin da ya cika hancinsa. Duk irin yunwar da yake ji sai ya ji ba zai iya cin doyar ba.
Ya mik'e ya fice ya bar gidan gaba'daya.
Na fito na shirya tsaf. Sannan na shiga falon da nufin kwashe kayan sannan na zubo nawa.
Sai ganin abincin na yi yadda na bar shi.
B'acin rai ya sake baibaye ni. Wato dama ba yunwa yake ji ba? Tsabar k'yashi da adawa da barcina yake yi kawai?
Na ja k'wafa.
Har zan zauna na cinye, sai kuma na yi tunanin ko sallamah aka yi da shi, ko kuma wani uzziri ya fita, zai dawo ya ci.
Na zuba nawa abincin, har na gama bai shigo ba.
Dan hakan na dauke, na kai kicin na rufe. Amma zuciyata tamkar ta fa'do k'asa.
Na hau shara, ina yi, ina hawaye tare da tir da auren dole.
Ina cikin mopping barandar ya shigo da leda a hannunsa. Kai-tsaye dakinsa ya fa'da jim ka'dan na ji yana fa'din"Asiya Toro".
Kamar bazan amsa ba, sai kuma na amsa d'in tare da ajiye aikin na nufi inda ya ke.
Daga ba'kin k'ofa na ci burki a dalilin yadda kuka yake neman k'wace mini.
Ganinsa na yi yana cin masa da k'uli k'uli ga kunun gyad'a a leda yana zuk'a.
A tausashe ya ce "Samo abu ki diba idan zaki ci".
Na rasa inda zan saka raina, da ba'kin cikinsa.
Murya na rawa na ce "Dama ka katse mini barci dan kawai ka saka ni aikin da ba ci zaka yi ba?"
Cikin rashin damuwar komai ya ce "Ci zan yi mana".
Na kasa bu'de baki na ce uffan, na juya ina jin tamkar na yi ta rusa ihu da kururuwa.
Kirjina