Showing 54001 words to 57000 words out of 184118 words
Chapter 19 - Bakar Taada Hausa Novel Complete
DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBE TA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
"Tunda Kika kasa gane abin da yake zuciyata ba wanda zai fahimce ni dai-dai".
Na fa'da cikin kuka sosai.
Ta maze ta ce "Ai kuwa dai kinsan na sanki tamkar yunwar cikina. Wata'kila kuma y'an watannin da muka yi ba tare ba ya sanya na soma mance ki. Amma tunda kin ji bacin rai a dalilin maganar ki yi hakuri da wasa nake yi shikenan?"
Da haka na fara goge hawayen idona.
Sai yamma lis ta tafi. Na rakata hanya ta hau abin hawa.
Ina kan hanyar dawowa sai ganin mutum na yi tamkar daga sama yana biye da ni.
Bai yi magana ba, bare ni kuma. Har muka iso gida sannan ya ce "Asiya Toro manyan mata. Na wuce shi na yi shigewa ta. Ina ayyana shi bai san ya kintsa kansa idan za shi wajen budurwa ba.
Ina shiga na tarar da Babanmu a zaune.
Ko hijabi ban cire ba, sai ga yarinya cikin yaran Baban kasuwa ta shigo ta ce "Adda Yabi Yaya Bulkachuwa ya ce "sauri yake yi ki je yanzu sakon zai fa'da miki".
Ba'kin ciki ya tokare ni, wai shi nan masharranci.
Na fito babu b'ata lokaci na fita ba dan komai ba sai dan Baban Marina yana zaune ba dan haka ba sai dai ya bushe a wajen.
Da fishi shinfide a fuskata na isa.
Ya kalle ni ya ce "Me kuma ya faru dan Allah. Dazun nan fa na ganki kina ta murmushi har na yi zaton ko labarin gidanki da Nazira ta gano miki take baki ya saukar miki da farin ciki mai yawa."
Na d'ago na kalle shi ina rasa ma ajin da zan ajiye Tijjani. Na lura kusan halin mahaifina ne da shi. Zaka yi musu abin takaici sai su waske su nuna basu gane ma me kake nufi ba, bare su nuna sun damu a karshe kuma sai su yi maka abin da kai ne zaka shaki takaici cikin salama.
Na wuce shi na yi tafiyata.
A hakan har kwanakin suka zo ya rage saura kwanaki biyu daurin aure.
A wannan ranar kuma aka yi mini jere.
Da yake Yaya Salisu ya na aiki bansan yadda aka yi ba an ce dai an yi mana gado da kujeru ni da Ubaida.
Na tuna irin yanayin damuwa da Nura ya shiga a dalilin rashina. Da hawaye a idonsa yake fa'din "Na tafka asara Yabi! Tijjani ya zama mai sa'a. Na yarda da kaddara. Na kuma karbi auren kanwarki da hannu biyu in sha Allah kuma zan yi mata adalci.
Allah ya sanya alheri. Allah ya sanyamu cikin masu biyayyar iyaye da ha'kuri saboda shi".
Da alhini mai yawa muka rabu.
Kimanin kwanakin sati kenan.
Na nisa ina sake hakaito wa ban da y'an kofarmu ba wanda ya yaba lefe ko kyaun gidana na rasa irin wannan masifar.
Har gara ma an dan yaba gidan Ubaida kadan duk da gidanta gida ne mai kyau sosai.
Amma da yake da ahalinmu aka fi adawa ba a wani yaba an zuzuta kamar yadda aka kurzanta na su Maijida da Firdausi ba.
Haka gidan Nasiba aka yaba aka kod'a lefenta tamkar me? Amma namu mukus kake ji.
A hakan har asabar din da ta yi daidai da 20 ga watan 5 ta zo aka daura aurena da Bulkachuwa, sannan aka daura na Ubaida da Nura.
Daga nan aka d'unguma gidansu Nasiba aka daura nata.
Fa'din halin da nake ciki na damuwa ba sai na fa'da ba.
Amma dai ji na yi tamkar na sheka barzaku.
Ina takure a dakin Gwaggo Nazira sai kai komo take yi cikin kwalliya. Ga cikin jikinta da ya fara tasawa ya kara mata kyau sosai.
Ihisan k'anwarsu Bulkachuwa ta shigo wai na je abokan ango na jirana.
Akan dole na yarda na bita bayan na ce sai dai ta tsaya ni idan mun je.
Haka na dinga yak'e ina gaisawa da su. Ala tilas na yarda aka yi hotuna. Shi kuma ganin ya samu dama har da sawa ayi mana daga ni sai shi.
Cikin rufin asiri aka yi hidimar bikinmu.
Ubaida aka fara rakawa da yake bamu da nisa.
Ni kuwa Baban Marina hannuna ya kama ya damkawa Babah ta Bulkachuwa.
Ya ce "Rakata dakinta Hauwa! Allah ya kawar da dukkan abin da muke tsoron faruwarsa a cikin aurensu. Ki kula da ita, ko bani ne na haifa miki ita ba, ta zama y'arki tunda surukuta ta mayar da ke uwa a gareta. Bare kuma ni din cikinmu guda. Ina ro'kon ki duk kuskuren da zata miki a zamantakewarku kada ki mata hukunci cikin zato. Kada kuma ki bari shaidan ya rinjayar da aibunta a zuciyarki. Yarinya ce ita din a gaban ki koda kuwa ta kai shekaru hamsin a duniya. Na damk'a miki ita, cikin gasgata cewar na bayar da ita a amintaccen hannun da ko bana raye za'a yi adalci da sassauci. Ina fatan wannan ya zama sanadin karin zumuncinmu ba wai sanadin tabarbarewarsa gaba'daya ba".
Duk da fuskata a rufe take amma na lura da yadda jikin Babah ya yi lakwas. Domin ta kasa bu'de baki ta ce uffan. Na dai ga tana goge fuskarta da na tabbatar hawaye ne.
Tsawon lokaci ba wanda ya yi magana a tsakaninsu.
Sai Baban ne ya katse shirun ta hanyar fa'din "Ki saurare ni da kyau Yabi.
Aurenki ya banbanta da na dukkan y'ay'an gidan nan. Ina fatan kuma ya zama mafi da'din misali a cikinku.
Ki dauka ibada zaki yi. Kinsan kuwa ibada wajibi ce ba wai ra'ayi ba. Ina ro'kon ki zauna lafiya da mijinki.
Ina alfahari da ke tabbas Asiya. Amma zan sake alfahari da ke ne idan har kika taka muhimmiyar rawa wajen mayar da Tijjani yadda muke son ganinsa. Na sani babban aiki ne mai nauyi. Amma tunda an yi sa'a yana sonki to matu'kar kin kwantar da hankalinki za'a samu dai-daito.
Ina fatan na ganku da iyali masu yawa kuna cikin rufin asiri. Tashi ki je, Allah ya bada sa'a ya maki albarka".
Ina kallo yadda Babah ta tashi da k'yar amma bata yarda ta saki hannuna ba tunda Baban Marina ya damka mata.
Ta tayar da ni ta fita da ni har lokacin kuma bata iya cewa komai ba.
Har muka shiga mota, muka isa gidan tana rike da ni.
Da kanta ta shigar da ni dakina bayan ta jira ni na karanta falaki da nasi da attahiyatu har zuwa inda ake yin sallamah a bakin kofa. Ita ce ta bani umarnin yin hakan wanda sai lokacin na ji ta yi magana, rawar da muryarta take yi ya sanya na gane kuka take yi sosai.
Duk yadda jama'a suke shiga da fita na ganin dakin amarya bai sanya Babah ta tafi ko ta saki hannuna ba.
Matan gidanmu duk wacce ta shigo ta ga Babah sai ta yi turus.
Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*
Hatta mamah da matan Baban Tsakiya da suka rakoni tare da ita sai da suka tsokane ta suna cewa "To ko dai ba zaki bar ta a dakinta bane kamar yadda aka yiwa kowa?"
Duk da hakan kuma bai sa ta bar ni ba. Har sai da Aliyu ya dauko mata Bulkachuwa cikin abokansa da suke dakon a gama watsewa su rako shi.
Yadda mahaifina ya damka mata ni a hannunta, bata saki hannuna ba duk tsawon lokacin nan.
Ta kamo hannunsa ta ha'da da nawa ta damk'e cikin nata.
Ta ce "gata nan ubanta ya bani amanarta na kawo maka ita da kaina saboda ya nuna mini ita ce tawa ba kai ba.
Na karbi amanarta, ni kuma na baka amanarta. Ka dinga tuna dalilin ha'da wannan auren. Ka zama cikin mutane masu halarci da kuma sakanta alheri da alheri.
Ban ta'ba farin ciki irin na yau ba. Ka sani na ha'diyi takaici da wahalolinka daban daban. Zan mance komai na yi alfahari da kai har ma na daga maka sawuna ka shiga aljannah idan Yabi ta kubuta daga tozarcinka da gangan.
Ko bana raye idan ka kyautata mata tamkar ni ka yiwa.
Albarka da farin-ciki zasu kewaye ka.
Ka kula da tarbiyarta, kada ka bari ta bijire wa ka'idojin shari'a. Amma ka zama mai sasauci da kawaici domin dai yarinya ce y'ar k'arama.
Ina fatan auren nan ya bud'a maka k'ofofin arziki da kuma fahimtar rayuwa daidai. Àllah ya shirye ka ya shirya maka iyali.
Allah ya albarkaceku gaba'daya".
Ta mik'e ta bar shi a durk'ushe yayin da nake kan gado, hannunmu kuma suna sark'e.
Sai da na tabbatar ta yi nisa na fincike hannuna, na ja tsaki na koma gefe.
Murya a dushe ya ce "Na yafe miki Asiyata! A gabanki Babah ta ce amanarki ta bani, na tausaya miki, na kuma yi miki sassauci."
Na sake jan tsaki fiye da na farko.
Ya mike ya fita bayan yan tsirarrun kawayena sun fara hayaniyar ba'a sayi baki ba dare na yi.
D'aya ce ma k'awata a ciki ragowar hudun duk wanda suka zo daga Kangire ne wato cousin dina na dangin Gwaggo. Sai kuwa Ihisan k'anwarsa. Ita kuma a takure take a dalilin yayanta ne angon.
Ba jima wa suka zo. Suka taba barkwancinsu, sannan aka yi nasiha da addu'a.
Suka gwangwaje k'awaye da ku'din sallama mai auki. Sannan suka tafi da su.
Ina ganin sun fita, shi kuma ya bisu da niyyar rakiya.
Na tashi na rufe kofar dakina.
Da ya dawo ba yadda bai yi dan na bu'de kofar ba na ki.
Ta windo ya leko ya ce "Ga leda nan ki dauka ki ci nasan da yunwa a tare da ke".
Washagari ina jin ya fita sallah na yi maza na fita na doro alwallah a bandaki, takaicina daya bandaki a tsakar gida yake ba a cikin daki kamar yadda na ci buri ba.
A gurguje na kammala uzziri na koma na rufe dakina. Ina idar da sallah na yi kwanciya ta. Sai tara da kadan na bu'de k'ofar dakin, domin barci na yi mai nauyi.
Ina bu'de wa kuwa ya shigo da sauri.
Ya ce "Kin tashi? Sannu ya kwanan bakunta?"
Uffan ban ce ba.
Amma wani irin bakin ciki ne ya turnike ni. A dalilin rashin bandaki a cikin daki.
Na hakaito kusan duk wadanda muka taso tare ko wacce band'akinta a dakinta ne.
Na tuna gidan J da na Nura, hatta Nasiba band'akinta a dakinta ne sai ni ce na samu dakuna tamkar na Islamiya tunda na ga falon ma daban ne ba'a hade suke ba".
Sai kawai na fashe da kuka mai sauti sosai.
Ya diririce ya ce "Daga tashi sai kuka Asiya?
Tun dazu fa nake zaman jiran ki tashi ki karya.
Ina son na fita muyi sallama da abokaina zasu koma garuruwansu".
Ban ce masa komai ba. Illah kukan da nake yi mai tsananin cin rai da nuna k'ololuwar ba'kin cikin da mai yinsa yake ciki.
Ya dinga rarrashi yana Fa'din "Ki yi ha'kuri Asiya komai zai dai-daita, daure ki tashi ki yi wanka anjima ka'dan zaki fara yin baki, duk wadanda zasu tafi yau sai sun biyo sun gan ki. Ina ganin kafin Babah ta wuce Bulkachuwa ma sai ta zo, idan ta ganki a hakan kinsan ba zata ji da'di ba."
Gaba'daya ya rikice ya ce wannan ya saki, ya ce wancan.
Da kuka na ce "Ni ban ta'ba hasko zan shiga gida mai bandaki a waje ba. Gaskiya an cuce ni, an gama da ni. Na saka fashewa da kukan da yafi na farko tsanani.
Hankalinsa ya tashi domin a ki'dime ya tattaro ni.
Na zabura na k'wace ina sake jin taikacinsa tamkar na rufe shi da duka. Jikina har bari ya dauka domin lokacin ne karon na farko da jikin namiji ya rab'i jikina irin haka.
Da muryar kuka na ce "kada ka kuma ta'ba ni. Bana son ka, bana ko son ganin ka".
Ya rasa yadda zai yi da ni. Ya zauna a gefena cikin rashin abin yi.
Tsawon lokaci ina shesshekar kuka.
A hankali ya ce "Ko na samo miki katon baho sai ki yi wankan anan idan kin gama sai na dauke na gyara wajen".
Yadda ya yi maganar sai na ji wani irin abu mai kama da tausayinsa yana neman kama ni.
Na sassauta kukan nawa. Amma ban kula shi ba, bare na tanka masa.
Ya sake lank'awasa harshe ya ce "Ki yi ha'kuri Asiya! A yanzu bani da halin irin gidan da kike mafarkin samu. Ban ta'ba jin takaicin ta'adin dukiyata da na dinga yi ba irin yau. Amma ina ro'kon arziki ki yi mini ha'kuri . Da ikon Allah zan yi aiki tukuru dan na cika miki burin ki. Na miki al'kawarin matu'kar rayuwata da taki ta kai lokacin da zan yi miki ginin da zai dace da ke, to ke zan bawa zabin yadda za'a fasalta ginin".
Na ja tsaki na ce "Duk kana nufin ina nan tare da kai, ina kuma dakon ganin wasikar jaki irin taka?"
Idonsa ya kad'a ya ce "Ni na sani Allah zai taimake ni, dan haka ba wasikar jaki nake yi ba".
Na ja bakina na tsuke. Ya dinga magiya tamkar zai fashe da kuka akan na je na yi wanka.
Da k'yar na yarda na tashi sai dai ban yarda na tube kayana akan idonsa ba.
Sai da ya fita. Sannan na cire. Na dauko sabon zanina gyauto guda. Na daura na saka hijabi. Na bu'de akwatin da na shirya kayana a ciki.
Na ciro soson wanka da sabulu da burush, hadi da makilin. Na ajiye tawul akan gadon.
Na fito na tarar da shi zaune akan baranda duk jikinsa ya saki babu kuzari a tare da shi tamkar ba Bulkachuwa wanda baya barin ta kwana ba.
Yana ganin na fito ya mik'e ya dauki botikin da yake gabansa cike da ruwa.
Ya nufi band'akin.
Na dakata ya fito, ya kalle ni ya ce "yanzu na janyo miki a rijiya da dumi tunda garin da zafi."
Ta tafasa ban ce ba.
Na shiga na turo kofar na sanya sakata.
Ina wanka ina ayyana, ina ma a cikin daki bayin yake?
Dan karami amma ko ina tayals ne.
Na fahimci sabon gini ne mune muka fara zama a ciki.
Sosai na yi wanka.
Sai da na alwala da kuma brush sannan na fito. Na shiga daki na tarar da tsintsiya a hannunsa tabbacin shara ya yi mini. Ga gadon ya gyara tamkar gyaran mace.
Daga kasa kuma kwanukan abinci ne.
Ko kallonsa ban yi ba, bare na yaba masa ta hanyar cewa sannu ko na gode.
Ya kalle ni ya ce "Bari na baki wuri ki shirya".
Ya juya ya fice.
A hankali nake shafa mai tamkar mai ciwo sannan na goga powder. Na shirya cikin sabuwar atamfa ta Buyers Batik. Doguwar riga ce amma dinkin ya yi kyau domin a Jos aka dinko mini.
Gata shudiya ce sosai aka yi mata yarfen ja.
Tsaya fa'din yadda farar fata ta haska atamfar bata lokaci ne.
Na goga rol on din Nivea a raina sai tsaki nake yi ina fa'din da an bar ni da kwamishina ko Yaya Jabir da tuni roll on din oriflame zan dinga tu'amalli da shi dama sauran product dinsu gaba'daya.
Tunda su zance a zubo mini a lefena.
Na fesa turaren Far-away, na shafawa lebena jan baki mai jan duhu.
Gefe na ajiye jan mayafi Wanda ya dace da atamafar.
Da yake yanzu a hutar da mata bata lokaci wajen daura dankwali ana ta yin huluna.
Nima hular aka yi mini.
Ai kuwa na kafata a kaina na isa gaban madubi ina daidita zamanta.
Ni da kaina na dinga fa'din "Fatabarakallahu ahsanul khalik'in.
Sosai na yiwa kaina kyau.
Maimakon na zauna sai na tsinci kaina da son yin walaha tunda na yi alwallah kafin na fito a band'akin.
Na idar na tsaya ina kallon dakin.
Madaidaici ne sannan kayan gadona suma matsakaita ne masu sau'kin ku'di. Amma sun yi kyau babu laifi.
Labulayen sun fi komai dqukar hankalina, ledar tsakar dakin ma mai kyaun aka saka mini wacce za'a kwana biyu bata fatattake ba.
Na bude akwatin na dauko wayata na kunna. Na koma bakin gadon na kishingida ina dakon ta gama daidaita.
Ina cikin dube dube ya shigo shima tamkar alamara ya sanya shudiyar shadda irin shud'in atamfar jikina.
Zuciyata ta harba da tsananin gaske. Domin komin k'in da nake yi masa tun fil'azal nasan yana cikin yan ka'dan da Ubangiji ya yi masa kyaun fuska da kuma ciakken zati.
Da walwala ya ce "Amarya kin sha kyau. Nan gaba fa idan zuciyoyinmu suka zama aminai ba karamin gidan farin ciki zamu gina ba.
Tun yanzu zabin zuciyoyinmu ya zo d:aya.
Mun sanya kaya iri daya ba tare da mun shawarci juna ba".
Na zabura na cire hular na bu'de akwati ina laluben wasu kayan.
Da sauri ya karaso kusa da ni.
Ya ce "Dan Allah! Ba dan ni ba. Dan alfarmar Annabi ki bar kayan ki, sun miki kyau ainun. Ina ta fa'da miki baki zaki ta yi yau. Ni fita ma zan yi".
Magiyar da ya yi ta sace mini guiwa na fasa canjawar.
Ya bu'de flask din abinci ya ce "Wannan doya ce da kwai Salisu ne ya aiko mana.
Ya bu'de d'ayan kuma masa ce itin tamu ta mutanan Bauchi da kuli kuli.
Ya ce wannan kuma daga gida aka kawo ga kuma kunu".
Yana nuna mini jug din.
Ya sake cewa "Na tafasa miki shayi na dauko miki?"
Ina kallonsa amma ko motsi ban yi ba bare na tanka shi.
Bai yi fishi ba, ya mike ya dauko flask din shayi wanda nawa ne a cikin kaya ya dauko.
Ya koma ya dauko kofina da kayan hada shayin a leda wanda alamu suka nuna siyowa ya yi.
Ya zauna ya ce "Sauko to mu karya".
Na sake sharewa.
A hankali ya ce "Da ace kin ji nasihar da aka yi ta yi Miki, iya ta jiya kacal da kin raga mini, domin dai ko ya ya nake ni din Ubangiji ya za'ba miki ya zame miki miji. Shi kuwa miji komin kashinsa ai daraja ne da shi."
Na yi kamar ban ji ba, na cigaba da danne danne wayata.
Ya karya, ya kwashe kwanukan da ya yi amfani da su.
Ya dawo ya ce "Zan fita Asiya. Zamu je yiwa iyayenmu ban gajiya. Nasan ba zaki yini da kewa ba yau".
Ya sake cewa sai "Na dawo".
Daga hakan ya juya ko uffan bai