Showing 111001 words to 114000 words out of 184118 words

Chapter 38 - Bakar Taada Hausa Novel Complete

kan cinyoyinsa. Ai gaba'daya wani irin k'arfi mai tattare da matsanancin fishi ya taso mini. Da dukkan zuciyata na fisge na ingiza shi ya fadi k'asa warwas.
Na dinga huci mai zafi, amma na kasa bu'de baki na yi magana.
K'irjina sai harbawa yake yi da tsananin gaske.
Ya mik'e ya kafe ni da ido, cikin kad'uwa da tashin hankali. Ya ce "Dan Allah bu'de baki ki yi magana. Fadi me zaki ce, idan kuma na zauna ki mini duka zai fi mini akan irin halin da nake ganin ki, ki yafe wa mijinki, ki yafe wa masoyinki, ki yafe mini, kaddara ce ta hau kaina Asiya".
Na juya na kwanta ba tare da na ce uffan ba.
Kukan kuma bai zo ba.
Ya kasa hakuri ya sake biyo ni inda nake kwance ya hau lalubata, ban hana shi ba, ban kuma yi wani yun'kurin da zan tankwabar da shi ba. Ya yi abin da zai yi. Yana gamawa na lalubi zanina na daura na fice.
Wanka na yi, sannan na dawo na kwanta. Bayan na mulke jina da hadadden man oriflame. Wanda jakadiyar kamfani ce ta za'ba mini shi fa kanta, q cewarta shi zai fi dace wa ta tarar fatata.

*Kunsan dai Aisha Lame make up artist din Guduyo ce. Yanzu ma bata bata bar fatar Yabi babu gyara ba*.
*Kun tandadi fame wash din nan kuwa da na yi ta jaddada muku muhimmancinsa a wajenku?*
*Ku tuntu'be ta a wannan lambar dan samun sabbin kayanta masu kyau da farashi mai sau'ki da ya zarta na saura*.
*07036662633*.

Shi kuma yana kwance sai fa'din "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya ke yi da k'arfi.
Yau duk jarumtar sa kasa yin ayyukan gidan ya yi. Dan haka na yi abuna. Na yi abin karyawa har na gama yana kwance. Na d'aga labule na ce "Ka zo mu karya."
Yana daga kwancen ya ce "Ko na zo d'in ma ai ba ci muke yi ba. Ki yafici abin da zaki ya fita ki rufe".
Wasa wasa yana kwance har azahar, ko wanka bai fito ya yi ba. Abin da ban ta'ba ganin ya yi ba, zama da janaba. Komin dare baya kwanciya sai ya yi wanka. Ko da kuwa zai yi second round. Amma yau safiyar Allah kuma ba barci ba, amma yana nad'e ya kasa tashi bare ko ruwan shayi ya kurb'a. Na sani fishin nawa ne ya fara k'ure malejin jarumtar sa.
Ina zaune ina tunanin al'amurar rayuwa sai na ga fitowar sa, d'aure da tawul da k'yar yake daga k'afafuwansa rauni gaba'daya ya bayyana a jikinsa.
Da ya tashi dawo wa daga masallaci sai ga shi da Malam liman da Malam mai Tafsiri.
Ganin dattawa kuma manyan Malamai na shiga marabatarsu da girmama wa. Shi da kansa ya yi musu jagoranci zuwa falonmu.
Na zuba ruwa a k'aramin tray na ajye a gabansu. Na gaishe su cikin ladabi. Suka amsa suna saka mini albarka. Na yun'kura zan tashi na basu waje dan a tunanina wajensa suka zo.
Sai kawai na ji sun ce "Ina zaki kuma, ai zuwan na ki ne".
Gabana ya yanke ya fa'di to me ya kawosu waje na ni kuwa?"
Malam liman ya yi gyaran murya ya yi addu'ar bude taro, ya nemi tsari daga sharrin shaidan da rundunarsa. Sannan ya ro'ki Ubangiji ya sanya albarka a abin da za'a tattauna.
Aka amsa da ameen.
Ya zarce da cewa "Asiya mijinki ya same mu, ya kawo k'arar kansa da kansa gabanmu. Da bakinsa ya ce ya yi miki laifi da ya amsa sunan laifi. Amma yana ro'kon mu zo mu baki ha'kuri a madadinsa".
Na yi k'asa da kaina, ban ce komai ba.
Domin ba k'aramin nauyi na ji ya kama ni ba. Akan me zai dauko mini manyan mutane irin haka?
Malam liman ya zarce da cewa "falalar hakuri yawa ne da shi Asiya. Mijinki ya yi nadama, irin wacce ake so mumini ya yi. A wannan zamanin idan mutum ya yi kuskure ya yarda ya yin ma, har yake bada ha'kuri ba k'aramin mutumin kirki ba ne. Abin da yasa na yarda na zo kenan da bakinsa ya ce ya yi miki k'aton laifi. Sannan na ga rauni mai yawa a tare da shi, wanda idan ba'a ba shi dauki ba zai iya kwantar da shi. Ki gode wa Allah da ya baki miji mai kiyaye sallah. Sama da shekara da zuwansa unguwar nan ban ta'ba fashin ganinsa a sahun gaba na sallar isha da asubahi ba. Annabin Rahma ya ce wadannan sallolin munafukai basa kiyaye ta. Ki yi hakuri da inda ya gaza mutumin kirki ne, na shaida hakan".
Sai lokacin kuka mai tsananin gaske ya k'wace mini, irin kukan da yake ki'dima duk mai sauraronsa, kuka mai dafa zuciya mai sawa a shid'e.
Kowa ya yi shiru, illah Tijjani da yake fa'din "Alhamdulillah! Alhamdulillah cikin wani irin yanayi. Domin ya sani rashin kukan da ban samu na yi ba. Da rashin furzar da maganganu. Ya sanya na taurare nake dafa shi ta hanyar zuru.
Malam mai Tafsiri da yafi kusa da ni, kuma yafi tsufa, domin ya tsufa ainun, na tabbatar ya haifi kamar Babanmu.
Ya d'ora hannunsa a kaina yana shafa mini, cikin muryarsa ta girma ya ce "Yi hakuri jikata. Kara hakuri, Innallaha ma-assabirin. Ki daina irin wannan kukan zai janyo miki ciwo. Yi salati ki samu nutsuwa. Tsawon lokaci yana shafar kaina tare da maganganu masu taushi har na samu nutsuwar.
Hannunsa na kaina ya ce "Shin Asiya ta huce ta ha'kura, ta yafe wa mijinta?"
Da rawar murya na ce "Akan me zai dauko mini ku? Ni bai mini komai ba, kuma nima ban ce masa ya yi mini wani abu ba."
Da azama kuma da cikin rawar murya ya ce "Na yi miki Asiya! Ni nasan ban kyauta ba. Amma ki dubi Allah ki yi ha'kuri. Ki bani dama mu tattauna, mu rufe maganar nan ta wuce".
Na kalle shi hawaye na zuba mini na ce "Tunda ka kafe ka yi mini laifi, fadi laifin da bakinka. Fa'da musu su ji".
Ya yi k'asa da kansa ya kasa ce wa komai.
Na juyar da fuskata na ce "Kun ga ni ba. Ai bai mini laifi ba. In ma ya yi Allah ya yiwa, na tabbatar kuma ya nemi gafarsa tunda kwana yake yi yana ibada. Ni kuwa bai mini komai ba."
Malam liman ya ce "Ga shi da bakinki kike shaidar yana kwana sallah anya bai cancanci ki yafe masa ba. Kinsan darajar wanda yake munajati da Allah fil lail kuwa?"
Kamar na ce "Amma ibadar tasa bata hana shi ya yi barna ba, bata hana shi ya tozarta ni ta hanyar yin bak'ar TA'ADAR a gidan aurena ba.
Amma na kasa bu'de baki na fa'da musu hakan.
Ban san da gaske ina son sa ba sai yanzu. Domin bayan matsanancin kishinsa da yake cina, sai na ji bazan iya tona masa asiri ba.
Bazan iya fa'dawa wani mahaluki abin da na ga ya aika ta ba.
Malam liman ya sake cewa "Ki yi ha'kuri kin ji Asiya. Ki yi koyi da mai sunan ki Nana Asiya. Annabi ya fa'da mana falalar ta. Abin da kuma ya janyo mata babban rabo a wajen Ubangiji imaninta da hakurinta akan mijinta ne. Ki yi hakuri, da sannu Ubangiji zai daidaita muku al'amuranku."
Jikina ya mutu tubus. Na ce "To".
Suka dinga saka mini albarka da godiya. Malama liman ya mike ya ce "Tunda ta amsa ta huce ai shikenan, kai kuma ka kiyaye, kada ka sake aikata laifinka."
Da sauri Tijjani ya ce "In sha Allah! Na gode amma Wallahi bata ha'kura ba, kuna tafiya zata cigaba da fishinta. Nima ta ce mini to yafi a k'irga."
Jin haka Malam mai Tafsiri ya sake d'ora hannunsa a kaina ya ce "Asiya na yafe wa mijinki a madadinki, na rufe wannan maganar har abada, shin zaki yi mini wannan lamini, zaki mini wannan mutuntawar?"
Yam jikina ya amsa. Wani irin abu ya tsriga mini a zuciyata wadda tun ranar da abin ya faru ya tokare ni.
A sanyaye na ce "Shike nan Malam na yarda, na kuma yafe masa". Yana jin hakan.
Da k'arfi ya ce "Alhamdulillah! Allah na gode, Allah ka taimake ni, ka tsare ni."
Ya matso yana fa'din "na gode Yabi".
Na galla masa harara na ce "Wallahi ba dan Malam ne ya yafe maka a madadina ba, da har ka tsufa kamar sa baza ka sake ganin walwala a fuskata bare dariyata. Ba kuma zan sake aminta da kai ba. Amma yanzu ka ci darajar masu daraja".
Ya matsa kusa da Malam din ya ce "Na gode sosai Malam. A kuma taya ni da addu'a Allah yasa k'arshen al'amarin kenan. Na gode muku, Allah yasa ku gama lafiya".
Suka tafi suna mini godiyar yarda da na yi sun isa da ni. Sai addu'ar mu samu haihuwa mai albarka suke yi mana.
Shi kuwa jan kunne da tunasar da shi girman hakkina da yake kansa suke yi.
Suna ta jaddada masa idan ya musguna mini da gangan ba zai ga haske a al'amuran sa ba.
Ya jima bai dawo ba, da alamun dai har gidajensu ya musu rakiya.
Ya dawo ya tarar da ni a falo. Na amsa sallamar sa na d'auke kaina.
Ya shigo da d'an kuzarinsa. Ya kalle ni ya ce "little me kike son ci na dafa miki?"
Ba walwala a fuskata na ce "Babu".
Ya matso ya durk'ushe tamkar mai neman gafara. Ya ce "Kin amsa kin yafe mini, kin amsa kin rufe maganar me zai sa kuma ki basar da ni? Na ro'ki dan darajar Annabi ki yafe mini, dan Allah. Shirun ki bala'i ne. Ki fa'di komai na zuciyar ki, zan ha'diye, na sani ban kyauta ba, amma nima bansan me ya same ni ba."
Da kuka na ce "Tun yaushe kuke yin hakan?"
Da rawar murya ya ce "Ranar ne kawai, Wallahi shine na farko kuma na k'arshe Asiya."
Na ce "Ban yarda ba. Ina ce dama kafin ranar ka ce mini ni bana danne ka yadda kake so?".
Ya daburce ya ce "Billahillazi kawai na fa'da ne, amma ba dan ina yin wani abu ba ne. Ki yarda da ni, ki bani wata damar, kada ki yanke aminci da yarda a tsakaninmu dan Allah".
Ya fa'da hankalinsa a tashe matu'ka.
Ya ru'ko hannuna ya ce "Ki ji tausayina. Zuciyata zata iya bugawa idan kika cigaba da share ni, na yi tuba a wajen Ubangiji, ke ma ga ni durk'ushe a gaban ki, ki yafe mini"
Na kafe shi da ido hawaye na zuba. Shima ya zuba mini nasa da suka kada suka yi jawur.
Da kuka na ce "Kana tunanin zan samu nutsuwa idan kuna rayuwa da it'a a gida daya, kana ganin zan iya mance wa idan ina ganin gittawar ta?"
Ya yi shiru. Na ce "ko ina son na manta ba zai yiwu ba. Dan haka zan fa'da maka gaskiyar magana. Sai dai ka zabi daya a ciikin ni da ita".
Ina rufe baki ya ce "wanne irin zabi ne wanda babu azanci a cikinsa? Ta ya ya zaki ce na zaba a cikinku? Ai ke ce tawa, ke nake so, ke nake burin rayuwa da ke, ke kike burge ni."
Da rawar murya na ce "Ita kuma tana baka sha'awa, kana son ka ji manyan mazaunanta a k'asanka, kana son kama manyan non..".
Ya yi maza ya rufe mini baki jikinsa na bari irin na zullumi.
Ya ce "Na zabe ki, ke nake so Yabi Ubangiji ne shaidar ban so wata mace kamar yadda nake son ki ba. Na kuma yi imanin ba zan so wata sama da ke a bayan ki ba."
Na goge hawayen idona na ce "muhimmi a gurina ka zama kamamme, idan har son da kake yi mini bai yi tasirin da zai kange ka daga ta'ba haramun ba ai banzar wannan son".
Da rawar murya ya ce "Allah ka mayar da ni kamamme. Allah ka yafe mini, Allah na tuba".
Tausayinsa ya kama ni yadda yake daga hannuwansa yana ro'kon da dukkan zuciyarsa.
Na nisa na ce "Mu fuskanci gaskiya. Idan da gaske sonka nake yi to akwai bu'katar na baka gudumawar da zaka tsira daga fa'dawa halaka. Na yarda na kuma gamsu kana sona. Nima kuma idan gaskiyar zan fa'da ina son ka. Amma na sani ban zo maka a yadda kake fatan matarka ta zo maka ba. Na yi amanna jikina bana manyan mata ba ne. Nan da shekaru goma ma ba zan yi girma shahararre ba. Dan haka ka aure ta kawai".
Ya zabura ya ce "Kinsan me kike fa'da kuwa?"
Idona ya sake cika da hawaye na ce "Na sani mana, kuma har cikin zuciyata nake nufin hakan"
Ya sake ni ya na girgiza kai ya na fa'din bana sonta, bana burin na aure ta, ko ina da halin k'ara auren ma kamammiya nake so wacce bata san namiji ba sai a kaina tamkar yadda na same ki".
Maimakon na ji da'di sai na sake shiga rud'u.
Da rawar murya na ce "ka tabbatar ba budurwa ba ce? Ashe ba iya abin da na ga ni ya gitta a tsakaninka da ita ba kenan?"
Cikin ido ya kalle ni da dukkanin gaskiyar sa ya ce "Na rantse iya abin da ya faru kenan. Amma kuma duk macen da bata san namiji ba ai ba zata dinga shige masa ba. Ba ni na je inda take ba, ita ta kawo kanta. Ko da ina son na ta'ba ta sai amince, kin ga ni kuma ba dole na yi mata ba, da son ranta ne, na tabbatar bani ka'dai ta ke yiwa hakan ba, ba ni ka'dai take sakarwa ba. Dan haka ina cikin nutsuwata bazan auri shasha ballagaza ba".
Y'anmata kalubalenku abin da mijin Yabi ya fa'da shine gaskiyar magana, saurayin nan da kike amince yake ta'ba ki ba zai aure ki ba, sai tsananin rabo. Idan rabon auren ya rantse kuwa har ki tsufa a hannunsa ba zaki fita daga zargi da wula'kancinsa ba.
Ba shakka wayewar da ta sanya kika bar shi yake lalube ki, to shifa a ballagaza wacce ta saba cudanya da maza daban daban yake miki kallo. Sannan ticket din kaskanci kika yankarwa kanki.
Ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali ya yi wanka.

*Cikakken labarin zai fara zuwa muku ranar 09/09 wanda a wannan ranar mahaifiyata zata cika shekaru ashirin da uku da barin duniyar nan*.
*Dan haka zan yi amfani da wnanan damar dan ku taya ni mika mata addu'oin gafara da rabauta a wajen Ubangiji*.

*Na gode sosai Ubangiji ya saka muku da alheri bisa soyayyar da kuke yiwa rubutuna*.

*VIP 1K*
*REGULAR 500*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM*
*ZENITH BANK.*
*A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08032773332 KO KUMA 09069067488*
*NA GODE SOSAI*

✍️.



*ANTI KULSUM BAUCHI HOW FAR?🥰*
*KIN TUNA RANAR DA NA CE MIKI INA RUBUTU?😄*

67&68.
Na daskare a zaune, wato duk tantirancin namiji shi kamila yake so.
Duk yadda zaki sadaukar masa da komai da sunan soyayya shi fa a zuciyarsa ba haka ba ne.
A yau na k'ara fahimtar darasin rayuwa. Na kuma k'ara gode wa Allah da na tsallake sirad'in yanmatanci lafiya.
Na kalle shi cikin tu'ajjibi na ce "To ka sani Wallahi bazan zauna a cikin gidan nan ba. Matu'kar kana son kwanciyar hankali da walwala to kuwa bana son gidan, ba kuma zan zauna a cikinsa ba."
A rikice ya ce "Asiya kin san dai da yadda aka biya ku'din rabin shekara yanzu wata guda tal muka yi, ta ina zan fara neman wani gidan?"
Ido cikin ido na ce "koma ta ina ne, na baka nan da sati if not Bilhiillazi bazan ha'kura ba. Sai dai ka nemi ni ka rasa shike nan sai ta tattaro ta maye maka gurbina."
Ya yi muk'us ya kasa zaburo mini.
Ya nisa ya ce "Haba little nan da sati me zan yi na samo ku'di? Kin san dai ba dawo mini da kudin zasu yi ba, bare na kama wani".
Na ce "Sai na baka aro, ka karbi zobena ko dan kunne ka siyar, sai ka biya ni idan ka samu hali".
Ban san ya aka yi ba kawai ya fara nuna ni da yatsansa cikin sababi yana fa'din "Nafi karfin ki kama gida na zauna a ciki Asiya. Ba zan yi wannan lalacewar ba, har abada da ikon Allah."
Na kafe shi da ido tsawon lokaci har ya fara kame kame. Na nisa na ce "Tijjani ni kake yiwa wannnan shouting din?".
Na girgiza kai na ce "Ba laifin ka ba ne. Laifina ne da na yarda da afuwar da Malam ya yi maka ba tare da na bayyana tozarta ni da ka yi ba. Afuwar da aka tilasta ni na yi maka ne ya baka kuzarin yi mini sababi irin haka ko?
To Wallahi bazan zauna a gidan nan ba. Komai za'a yi da ni kuwa".
Na mik'e na bar shi, ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye shi. Domin ya ga na koma Yabin Marina marar sassauci.
Ban jima da shiga d'akin ba sai ga shi ya biyo ni jikinsa a sanyaye. Ya zauna kusa da ni ya tausasa harshe ya ce "Ke little ba ki fahimce ni ba ne. Ki yi hakuri, zamu tashi, amma pls ba nan da sati daya ba dan Allah."
Na ce "To".
Ai kuwa nan da nan ya hau fa'din "Na rok'e ki fa Little. Ban son irin wannan to din na ki".
Na share shi. Ya dinga jaye-jayen magana amma ban tanka masa ba.
Sai kuma ya bani tausayi yadda ya yi shiru ya rasa abin yi.
A zuciyata sai hango girman gatan da Ubangiji ya yiwa mazaje nake yi. Domin duk girman laifin da zasu yi wa mace sai Ubangiji ya sanya hakuri da sassauci had'i da rauni a zukatan mataye. Nan da nan mace zata yafe ta kuma manta musganwar miji.
Na tuna ranar da ya rufe mini gida dan kawai na je na na yi sana'ar da zan samo masa ku'din da zamu rufa asirinmu. Amma har washagari yana sababin sai na tafi gida.
Amma ni na fita unguwa na dawo na tarar yana shek'a ayarsa. Na girgiza kai domin nasan da ace ni ya ga ni a cinyar Yaya J sai ya masa dukan mutuwa tunda ba k'arfinsu daya ba. Ni kuwa zai yi wahalar gaske idan bai sallama ni ba.
Na kalle shi na ce "Na tambaye ka?"
Ya d'aga mini kai tabbacin eh.
A hankali na ce "Idan ni ka ga ni a cinyar wanin ka ya zaka ji?"
Ya ce "Wata'kila zuciyata bugawa zata yi, wata'kila kuma na had'u da mummunan hawan jinin da zai kanannad'e ni."
Na sake zuba masa ido na ce "Amma me yasa baka yi zaton nima sakamakon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login