Showing 3001 words to 6000 words out of 184118 words

Chapter 2 - Bakar Taada Hausa Novel Complete

sai na cire mata wani abu.
Da ku'din asusuna ya yi auki na fasa na siya mana kayan kwalliya masu sau'kin ku'di ni da Ikilima da Nazira, har ma da Ubaidan Innah. Sai kuma na sake siyan wani na k'udire niyyar dinki zan yi mana idan kudi ya taru.
Tsawon dauki lokaci ina zubi, kafin na samu na yi mana y'an suturu ni da Iki.
Ai Mama tana ankara da y'ar nutsuwar da muka fara samun kanmu a ciki, sai ta tayar da ballin sai na bar kitso, domin gashi yana yawa a gidan, ba dama ta zubo abinci, zata yi ta ganin gashi.
Ko ina gashi ne, ta gaji da wannan k'azantar.
A wannan karon Babanmu ya yi jarumtar cewar ba zai hana ni yin sana'a ba, tunda shi da kansa ya sani ba k'aramin rufa masa asiri sana'ar take yi ba.
Kusan kullum sai na ba shi naira dari hud'u.
Maganar maganina kuwa idan ba ni da lafiya, na dauke wa kowa.
Dan haka sai muka fara saje wa da su Maijida.
Tunda muma yanzu muna samun yan suturu babu laifi, duk da bai kai nasu daraja ba.
Idan akwai abin da ya yiwa Mama tarnaki rashin kintsuwar Yaya Musa ne.
Gashi dai shi ne babba, amma gaba'daya ya lalace, ya zama d'an iska, hakan kuma yak'i ya zame mata izna, a kullum cikin aibata yaran da ba nata ba take.
Ta kuma gasgata hannu aka sawa d'anta, da kuma bakin mahassada.
Ta kasa fahimtar rayuwa har yanzu.
Tsabar kyashinta ta hana ya'yanta mata su tallafawa Babanmu da d'an abin da zasu iya .
Kullum fa'di take ai hidima ta y'ay'a maza ce. Dan haka komai yaranta mata zasu kawo gidan to nata ne, sai ko idan dafaffe ne sai ta samma wadanda take so, wadanda bata so kuwa ko ta yi babu.
Sai nake mamakin idan tana habaicin ku'din kitson da nake kar'ba, wai Gwaggo ta kasa bari a mori haihuwarta, ko ita wa ta bari ya mori tata haihuwar?
Ko Babanmu da ya yi mata hidimar yaran ba dai tasa su kawo masa wani abu na tallafin gida ba tunda yana da k'ananun yara. Idan ma sun yi hankalin kawo wa to fa ita ce a hakku a kan kayan, ta dinga gadara kenan duk ba wasu kaya masu yawa ba ne, tunda dai ba wai ku'din ne da su ba, rufin asiri ne kawai.
Sai nake mamakin wai mene ne manufarta ne?
Da na kasa gane wa sai na ha'kura, amma hakan ya ja hankalina har nake sha'awar yin bincike da nazari akan gidan yawa mai dauke da mabanbanta iyalai.
*GIDANMU ne kawai kwamacala ta dabaibaye shi?*
*A GIDANMU ne kawai ake yin kasafi irin na kashin dankali ma'ana na sama ya danne na kasa?*
*A GIDANMU ne kawai ake mayar da babba k'arami saboda ba shi da wadata ko kuwa?*
*A GIDANMU ne kawai ake ta'ba yan ubanci ko kuwa?*
*Ba k'aramin caji kwakwalwata take yi ba dan neman sahihohin amsoshi wadannan tambayoyin*.

*Ayi bitar da nutsuwa domin wannan karon gidan yawa zamu kutsa sosai*


VIP 1K.
REGULAR 500.
2384876855
SURAYYA IBRAHIM
ZENITH BANK.


*ASSALAMU ALAIKUM*
*Masoyan rubutun Surayya Dee na gaishe ku, na kuma yaba muku*
*Dafatan zaku yi hakuri, ku bi labarin sannu a hankali, har ku fahimci sakon da nake nufin isar wa.*
*Ba zan ce muku komai ba. Abu d'aya nake da tabbaci ba zaku yi nadamar bibiyarsa ba.*
*Kawai fatana kada ku kosa da yanayin rubutuna.*
*Allah ya taimakemu, Allah ya zaunar mu lafiya da y'anuwanmu da abokan zamanmu*.
*Allah ya bamu lafiya, ya bamu hakuri da k'addarar da muke fuskanta a rayuwar nan*.



*Surayya Dee*
✍️.

*BAK'AR TA'ADA*

*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*MARUBUCIYAR HALIN YAU DA SABO DA KAZA*


•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*GODIYA*
*INA MATUKAR GODIYA BISA ADDU'AR DA KUKA YI WA MAMA*!
*ALLAH YA KARBA, YA BADA LADA*.
*HAKA NAN INA NEMAN UZZIRINKU BISA RASHIN AMSAWA. DOMIN NA KARBI SAKON MUTANE SAMA DA DARI BIYAR, TUN INA AMSAWA HAR AL'AMARIN YA GAGARI KUNDILA*.
*DUK WACCE BAN AMSA BA, INA AMFANI DA WANNAN SHAFIN WAJEN GODIYA TARE DA YABAWA A GAREKU GABADAYA*
*ALLAH YA JIK'AN DUKKAN MAGABATANMU*.


*KUNSAN DAI YADDA AISHA LAME MAKEUP ARTIST DIN GUDUYO, TA KWARE WAJEN SANIN HAKIKANIN MAN DA ZAI DACE DA KOWACCE FATA, WALA DRY KO OILY*.
*BABBAN ABIN BIRGE WA DA KAYANTA FARASHI MAI SAUKI NE DA YA ZARTA NA SAURA SALAMA*
*HANZARTA KI TUNTUBE TA DAN KI GA JERIN KAYAYYAKIN ORIFLAME KALA DABAN DABAN*
*SANNAN TANA DA HADADDEN GANYEN SHAYIN DA AKA YI SHI DA GANYAYYAKI MASU SAISAITA JINI DA KITSE A JIKIN DAN ADAM.*
*LAME TEA YAFI SHAYI MAE MADARA*.
*IDAN KUWA KIKA CI LAME POPCORN INA TABBATAR MIKI KIN YI ADABO DA SAKE CIN WANI GUGGURU MATUKAR BA LAME POPCORN BA NE*.
*07036662633*.

*3&4*
K'aramar hukumar Toro tana cikin k'ananun hukumomin jahar Bauchi. Duk wani mai nazari yasan yadda Ubangiji ya wadata Toro da girman k'asa.
Ita ce k'aramar hukuma mafi girma a dukkan fa'din tarayyar Nigeria dama Africa ta yamma gaba'daya.
Garin Toro an kasa shi zuwa Gundumomi uku.
Gundumar Toro, gundumar Jama'a da gundumar Lame.
Sannan akwai kabilu daban daban bayan Hausawa da Fulani.
A karkashin jahar Bauchi ta ke amma tafi makwbataka da jihar Filato.
Shi yasa garin kewaye yake da ni'imomin kayan itatuwa da rashin zafin rana sosai.
Ba dan ina y'ar garin ba, Ubangiji ya dabaibaye garin Toro da tarin faloli Alhamdulillah.
Dare ne amma ba ainun ba, mafi yawa mun ha'du a kofar Kakarmu Dada ana ta hira da tatsuniya. Kannenmu kuma sai wasan d'an dunmi suke yi.
Dukkanmu y'anmata mu bakwai da muke kai d'aya muna zaune akan tabarma, idan aka dauke shalele Nasiba da take kishingi'de a jikin Dada.
Sannu a hankali Dada take taunar goron bakinta tana mulmulawa.
Kyakkawar dattijuwa mai kyakkawan jiki. Asalin Bafulatanar Lame ce, kowa kuma yasan asalin mutanan wannan garin fulanin Mali ne da kiwo ya saka suka tsallako Nigeria suka yi sansani a yankin na Lame.
Wani ikon Allah mafi yawa na ahalinta sun samu kyawun halittar fulanin Lame.
Haka muke y'an gidanmu son kowa k'in wanda ya rasa.
Wani irin kallo take mana na kurillah.
Ta kasa ha'kuri ta ce "Na fa'da muku dukkanku ku zauna cikin shirin ko ta kwana.
Domin kuwa ba zaku fi haka gandare wa a gabanmu ba.
Dukkanku abubuwa sun cika muku k'irji. Ko wacce a cikin ku wanki take yi a gabanmu, ina kallon zamani ni Binta! Muna cikin alhini. Allah yasa intingifarin da muke nacin yi mun samu rabauta ana karban sallarmu".
Dariya ta kama mafi yawanmu.
Ni da nake da kaud'i na ce "Dada Ashe ba'a karban sallarku ne?"
Ta rausayar da kai gwanin tausayi ta ce "Ai matu'kar kana da yarinyar da ka yi saken da ta fa'di a gabanka, to kuwa babu makawa sallarka bata isa gaban zati, daga bakin k'ofa ake dakatar da ita!"
Nasiba ta ce "Allah ya kawo mafita. Yanzu biya mana karatun na yau".
Nan da nan ta furzar da goron bakinta dan girmama karatun da zata d'ora mana.
Ta tsume ta ce "Mu karanto na jiya".
Muka ha'da baki wurin rera karatu cikin sigar wake muka ce "Idan attishawa ta sauko mana, idan wani bawa a kusa da mu ya ce mana "Rai ya hadu da Gafarar Allah!"
Sai mai attishawa ya ce "Ya-hadi kumalle.
Idan kuwa zamu ci adda'ami.
Zamu fara da ambaton Allah. Idan koshi ya zo mana sai mu ce "Sawaba ta sauka akan me nemo wa da mai dafa wa".
Dada ta murmusa tabbacin ta gamsu mun ri'ke karatun nata da kyau.
Ta ce "Madallah!". Cikin alfaharin muna da fikirar fahimtar karatun da take yi mana.
Ta muskuta ta ce "yau karatun yiwa kai rigakafi daga shaidanu da makarai zan dora muku".
Muka ha'da baki wajen fa'din "Mun gode Dadarmu, Allah ya kara miki nasibi.
Annabi yasan da ke".
Ta numfasa ta ce "Ameen, a kuma tsananta yi mini rokon dacewa da shiga cikin masoyan SHEHU".
Na kasa jure wa na ce "Ashe Dada ba zaki bar zancen Shehu ba?
Kowa ya bar Allah da ma'aiki ai ya bar hanyar tsira."
Nan da Nan ta fusata ta ce "kaico da Yabi! Yabi ba zaki tsira ba, waya yake inkari da jikan Manzo? Tabbas sai gafalalle".
Na ci je na sake ce wa, Annabi dai aka ce mu ri'ke ba waninsa ba Dada, iyalan gidansa suna da girma da hakkin mu so su mu kare mutuncinsu.
Amma ba'a ce a kai su wani bigire da zai iya zama halaka ba.
Da kansa ya ce "Zan bar muku kura'ani da sunnata wato (Hadisansa) idan kuka bisu kun tsira.
Amma ku kun shure komai, kun dauko shehu kuna neman mayar da shi abin bauta?".
Ai kuwa ta sake harzuka ta ce "Wahalar rayuwa akan ki Yabi! Mai gadon taurin rai da kafiya, kaicon ki, kaicon ki! Da yi mini izgilanci Asiya".
Jikina ya sabe da rawa a dalilin ba irin jan kunnena da Gwaggo bata yi mini ba, akan kada na sake na janyo abin da Dada zata dinga yi mini mugun fata. Ga shi ban ji ba, na yi sanadin da take fatan na dauwama cikin wahalar rayuwa.
Kafin na ce komai sai ga Tijjani wanda mafi yawa an fi k'iransa da sunan garinsu Bulkachuwa.
Wani irin zabgegen saurayi.
Dogon gaske har d'an rankwafa wa ya yi ka'dan.
Fari ne tas, irin fulanin Bulkachuwa, a murde yake, shi ba siriri ba, kuma ko ka'dan baya cikin masu kiba.
Ga dogon hanci da ya k'awata doguwar fuskarsa.
Baya ga hakan manyan idanuwansa ka'dai sun isa abin burge wa.
Ban ta'ba ganin namiji mai jajayen lebe ba sai Tijjani kyakkawan gaske.
Wani irin mutum mai saurin fishi, da k'arfin zuciya.
Amma mai saurin saukowa da mantuwa.
Illarsa d'aya manemin mata ne, a yadda a ke fa'da. Na shaida kuma duk wata budurwa ballagaza a Toro to kuwa budurwarsa ce ko kuma suna d'asa wa, shiyasa kowa yake jan kunnen y'arsa a kansa, barin ma ni, kullum ne sai Gwaggo ta ce kada na sake na bashi fuskar da zamu dinga doguwar magana.
Gaba'daya dabi'unsa na tantiran yan-iska ne, sannan k'azami ne, baya damuwa da yin wanki sai kayansa sun k'are.
A hakan kuma shashan y'anmata suke sonsa, ko da yake baya yarda ya fita da dattin sosai, yana wanke wa ya jira su bushe, guga ce sai ya samu ku'di, sai ya bayar da kayan ma a wanko a gogo masa, amma da wahalar gaske ya yi guga da kansa.
Duk yadda Dada take kulafacinsa, matu'kar ya shigo muna nan sai sun haura da shi, domin yafi kowa takalarmu da magana, yana yi yana lumshe ido ta yadda zai sure zuciyoyinmu.
A hakan ya yi nasarar yin wuf da zuciyar Nasiba.
Idan Dada ta ga yana sakin maganganu ko lumshe ido a gabanmu ta dinga bagarar da shi, ko ta tsiri aiken sa, ko kuma ta ce mu je ta sallame mu, duk yadda take sonsa to bata son doguwar magana a tsakaninmu, kazalika kuma bata son a k'i gaishe shi.
Burgar da yake yiwa mata ya sanya har yanzu bai bar dauke dauke ba, komai ya gani zai dauka ya siyar ya kashe wa budurwa ku'di. Amma iya kayan Dada yake dauka.
A duk sadda take yi masa fa'da kuma zai waske ya ce bashi ba ne, ko kuma sharri ta yi masa, haka kuma sai ya d'auke mata wuta, har sai ta nemo shi ta bashi ha'kuri. Bayan soyayyar da take yi masa, yana sake samun alfarma a wajenta saboda sunan SHEHU ne da shi.
Kullum bakin ta akan ya nutsu ne, ya bar shiririta ya kawo matar aure, tunda ga Yaya Salisu nan da yake sa'an sa tuni ya yi aurensa har matar ta haihu, amma shi ko maganar aure baya yi saboda sharholiya da mutuwar zuciya.
Duk da k'arancin shekaruna ina tambayar kaina ko waye zai iya d'aukar y'arsa ya bawa Bulkachuwa aurenta?
Tabbas sai idan yarinyar ta kasance shasha ce irinsa.
Na tabbatar mahaifiyar Nasiba ba zata ta'ba bari a bashi ita ba, domin kuwa kowa nasa yake so, bare idan maganar gaskiya za'a yi bai cancanci a bashi ba, domin bashi da sana'a, gashi manemin mata, shiyasa kowa yake masa kallon shasha.
A duk sadda Dada take yi masa fa'dan shigar da yake yi ta gajerun wanduna yana yawo a gari babu kunya, ko tara suma ya gegareta daga gefe, ko kuma wani zubin ya sauya launinta bayan ya mayar da ita cibiri cibiri.
"Akan kunnena na sha jin tana ce wa "Saboda bamu da mutunci a idonka shiyasa kake iya zuwa gabana a hakan ko kuma gaban kawunanka".
Ba jin nauyi yake ce wa "Tunda nake yin sallah a hakan, ai kin ga bai zama aibu dan kun gan ni a hakan ba. Domin Ubangijina ma a hakan yake gani na, kin takura mini fa Tsohuwa"
Nan da nan ta zabura ta ce
"Imaninika ai a makogaro yake shi yasa kake hakan, amma da za'a jarrabe ka da son wata yarinyar ba zaka yarda ka je mata a hakan ba. Alfarmar Shehu sai ka samu wacce sonta zai hanaka yin wannan shakiyancin. Tunda ka ki daina wa saboda Allah da Ma'aikinsa."
Dariyar iyashege yake yi ya ce "Ni da nake da y'anmata kamar jamfa a Jos suna bina dan na so su, shine har son wata zai canja ni?
Lah! Ba dai Bulkachuwa ba".
Da wani kuma a Cikinmu ko a cikin samarin gidan matu'kar ba Yaya Anwar ba ne zai saka musu baki, a take Dada zata nuna wa mutum shine bare a tsakaninsu.
Tana kuma sake kambaba shi da kawar masa da kai saboda alfarmar mai sunansa ne, domin ko ta yi masa sababi, sai ta yi ta tuba tana kamun kafa da mai asalin sunan akan a saka mata jikanta cikin shirayayyu. Hatta shi kansa dariya take bashi akan yadda take tuba idan ta saki harshe a kansa.
Amma wani ikon Allah jarumi ne na gaske.
Idan na ce jarumi ina nufin zai tsaya ya fafata da kowa akan hakkinsa, matu'kar kuma ya sanya kansa zai yi abu, to duk tsananin wahalar abin sai ya ga abin da ya turewa buzu nad'i.
Baya ga hakan kuma tausayi ne da shi, duk zafinsa inda zai ga kana kuka to zaka ga ya bar yi maka tijara.
Sai dai kallon marowa ci nake yi masa na gaske, ni dai ban ta'ba ganin ya yi kyauta ba.
Ko garinsu ya je ya dawo, duk abin da zai samo ba dai ya kawo gidanmu ba. Amma kullum a cikin karbe wa jama'a nasu yake, mussaman Dada da ko ta hana shi a k'arshe take kasa juriyar ganinsa cikin rashin sukuni, sai kawai ta bashi.
Mazan gidan kuwa basa bashi duk irin yadda zai karyar da kai yana fa'din bashi da lafiya, tunda suka gane matu'kar ku'di ya shiga hannunsa y'anmata banza yake kashe wa, sai kowa ya kulle bakin aljihunsa dama kuma masu k'aramar niyya ne. Sai dai gara shi ma suna bashi, amma da a ce wani ne cikin y'an k'ofarmu baza su bayar ba, daman kuma bamu isa mu ce a bamu ba.
Haziki ne na sosai, kwarai da gaske yake ja, amma lalacewar da ya yi ya sanya da k'yar ya iya kammala Diploma a kwalejin Tatari Ali data ke cikin Bauchi.
Ya riga su Yaya Salisu samun gurbin karatu a jami'ar amma yak'i mayar da hankalinsa akan karatun har sai da aka kore shi. Hankalin mahaifinsa ya yi tashin gauron zabi, domin zaryar da ya dinga yi tsakanin Bulkachuwa zuwa Toro ba ka'dan ba ce.
Haka ya sake samo masa yin diploma akan shaanin tsaro da tafiyar da gwamnati wanda da k'yar ya kammala dan ma shekaru biyu ne.
A hakan kuma sakamakon ya yi kyau, domin ya wuce fallasa. Duk da hakan Babansu bai bar shi ba, sai da ya sake samo masa gurbin karatun digiri a jamiar jahar Bauchi ta garin Itas-gad'au. Inda zai karanci ilimin halayyar dan Adam. Wannan kam da taimkon Ubangiji ya kammala domin ba ya zuwa sai an kusa fara jarrabawa, sannan bai fasa al'amari da y'an mata ba.
Shekaru biyu da rasuwar mahaifinsa kenan. A kuma wannan shekarar ya tafi bautar k'asa, da shekara ta dawo ya kammala. Yanzu zaman kashe wando kawai yake yi. Sai dai yana yar buga bugarsa domin kusan kullum sai ya je Bauchi.
Haka ya dinga satar jiki yana siyar da kadarorin da ya mallaka. Abin kaico kuma ba komai ya yi da kudin ba sai sharholiya da burga a mata.
Wani k'aton fili a Bauchi kawai ya tsira da shi, shima dan an zuba masa matakan tsaro ne.
Yau da wata sana'a yake da ku'din ko kuma wani gini yake fa'da'da wa da an samu sau'kin bacin ran da ake ciki.
Ya zauna kusa da Nazira da take kusa da karshen tabarmar.
Murya ba amo ya ce "Madallah da Dada da y'anmatantanta".
Duk suka hau rige rigen gaishe shi Amma ban da ni.
Ya amsa hankalinsa na kaina.
Ya kasa ha'kuri ya ce "Asiya Toro how far?".
Na yi banza da shi.
Domin dai na tsani yadda yake gatsa ainihin sunana, dan kuturun wula'kanci har sai ya ha'da da Toro.
Kusan kowa Yaya Bulkachuwa yake ce masa, ni da bama shiri bana ce masa Yaya Bulkachuwa.
Amma sai nake mutuntunta shi wajen kiransa da Yaya Tijjani amma bai yaba ba, bare ya gode. Yabin da zai ce ne yake ganin asara saboda an cika zuciyarsa da k'yashi. Shi yasa nima na janye yayan tuntuni nake gatsa Tijjani gatsal wanda na lura shi ko oho.
Ina nan, ina kallon wadanda basa ce mini Yabi, duk ranar da Ubangiji ya sanya na je Saudi akan girma da hankalina ko tsarabar abin da ba'a so ba zan basu ba.
Tijjani na cikin sahun farko.
Yaya Ummi ce mutumiyarsa, baya zuwa gidan kowa amma yana zuwa gidanta, har idan da ku'di a tare da shi ya yi wa ya'yanta alheri. Sosai suke d'asawa, mutimiyarsa ce ta sosai.
Dada ta fusata ta ce "Mugun nufi ya k'are miki Yabi! Ko wacce ta gaishe da dan-uwanku amma ban da ke, bai yi fishin wula'kanta shi da kika yi ba, ya sake bu'de baki ya yi miki magana amma kina ji sarai kin k'yale shi, saboda ke din kina gaji nunkufurci da ba'kin hali ko?"
Raina ya baci domin a kullum kalaman Dada a kaina kenan, bansan me Goggo ta tsare mata da a kullum sai ta jingina mata munafurci da ba'kin hali ba, ko da yake na taba jin labarin cewar tun haihuwar Yaya Ummi da dangin Goggo suka zo suna daga garinsu na Kangire cikin k'aramar hukumar Birin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login