Showing 174001 words to 177000 words out of 184118 words
Chapter 59 - Bakar Taada Hausa Novel Complete
kai ta ce "Shike nan sai ka dawo, ya zan yi?"
Da ga dawo kuwa gabadaya suka rankaya ganin Tijjani. Ni da Babah kawai aka bari a gida. Da ga can zasu biya gidan Iklima su bar ta a can.
Dada ta kalle shi ta ce "Mai sunan manya kana wuridin *RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN kuwa?"
Ya ce "Ina yi sosai, ina kuma ganin tasirin ta Dada. Komai ya saukaka mini, na samu k'arfin zuciya da tawakkali, iyalina kuma suna cikin rufin asiri mai yawa ".
Ta ce "Hakane, Hakane! Cikin tausayawa.
Sun jima sosai suna shirin tafiya ta cewa su Yaya Ummi su yi gaba tana zuwa.
Yaya Ummi ta kalle shi da idonta da suka yi ja. Da rawar murya ta ce "Yaya Bulkachuwa sai mun sake zuwa".
Ya yi mata murmushi ya ce "Ummilolona kullum sai kin yi kuka? Kamata ya yi ki gode Allah ina rayuwa. Ban rasa komai ba sai y'ancina. Wanda duk ya zo kurku bisa zalunci sai ya samu daukaka, so ku tsananta yi mini addu'a ba kuka ba".
Ta share hawaye ta ce "Allah ya nuna mini ranar da zaka fito Yaya Bulkachuwa sai na yi azumi uku da ikon Allah".
Haka kawai ya ji ta bashi tausayi. Tun tana k'arama ta damu da shi ainun. Shima kuwa idan aka dauke Ihisan da su Aliyu ba shi da wata yar'uwar da ta wuce ta. Ya tabbatar ko bai auri Yabi ba, amincinsa da ita mai yawa ne. Sai aurensa da Yabi ya sake girmama amincin nasu domin ya sani, tana son Yabi fiye da komai. Shiyasa ta sake kaunarsa, ta kuma bada gudunmawar shawo masa kan Yabi matuka gaya.
Suka tafi, su mama duk jiki ya mutu, tausayi ya ratsa jikin kowa.
Sai da suka yi nisa Dada ta sassauta murya ta ce "Mai sunan manya wai anan din akwai d'akin sirri ne, ko kuwa a ina kuke haduwa da Yabi?"
Kunya ta kama shi. Ya kasa ce mata komai. Ta ce "A a ba kunya zaka ji ba. Kawai ka fad'a mini domin idan cikin jejin can kuke shiga a samowa jinjirar taimako domin idan aka samu ciki da ranar Allah, kuma a fili irin haka aka yi tarayyar da ciki ya shiga to fa wannan yaron ko yarinyar rashin kunyar da zasu yi sai ya gigita kowa".
Dariya ta k'wace masa. Ya yi kad'an ya gintse tare da ce wa "Ki yiwa Allah ki bar maganar nan haka. Ki nemo mata taimakon ki kuma tsananta yi mata addu'oi kawai".
Ta saki ajiyar zuciya ta ce"Mai sunan manya abin ne yake ta bani mamaki to ta ina kuke kebe wa ne? Ga yarinya nan ta kwaso Aliyu amma cikin ikon Ubangiji doguwa ce sambal. Dazu ana mata wanka da na zuba mata ido gabobinta irin naka ne sak, haka gashin kanta. Oh ni Binta. Kullum ina kuka da zullimin rashin ka ashe kai baka fasa komai ba?"
Ya murmusa ya ce "Kina sauke mini dala'ilalul khairati kuwa?"
Da hanzari ta ce "Duk satin duniya kuwa. Ko wacce juma'a nake sauke wa. Kuma hadiyya ce a kanka. Mai sunan manya na ga gurbinka! Dakina a bushe, babu kayan shayi irin naka. Babu sabulai da turaruka irin naka. Ta hau kuka sosai. Jikinsa ya yi sanyi. Ya ce su Baban Kasuwa basa siya miki ne?"
Ta ce "suna siya amma har sai sun k'are, kai kuwa kafin su k'are ka kawo wasu. Sabulai da turare masu kyau ba masu s'aukin kudi ba. Amma yanzu fa?"
Ya ce "Ammar da Jabir basa yi miki ne Dada?"
Ta kyabe baki ta ce "Jabiru kam ai yanzu fama yake yi da kansa. Har ya gama samun damarsa kuwa ban wani more shi ba. Kasan sun k'ullace ni akan ku. Wai nafi sonku. Iyayensa kawai yake yiwa. To yanzu an yi mutuwar kasko, kowa ma ya rasa.
Shi kuwa Ammar yana yi mini bazan masa k'aharu ba".
Amma sai ta waiwaya ta sassauta murya ta ce "Da uwarsa muke raba daidai. Idan ba'a hannuna ya bani kudi ba kuwa, basa zuwa mini".
Ya yi shiru, tausayinta ya kama shi ainun. Abin da ya fahimta Baban Marina da mahaifiyarsa sun fi dukkan y'aya'nta yi mata biyayya da kyautatawa a gareta. Sune kuma wadanda ta rayu tana nuna musu rashin soyayya. Komai sune a baya. Amma kuma shi da kansa ya tabbatar Dada tafi sonsa akan kowa cikin jikokinta. Domin Ammar bai samu sukunin yi mata raddi da fito na fito da ita ba. Da ace shine yake da nutsuwarsa da bai san yadda zata ririta shi ba. Ya tuna sadda zai sadada ya kwashe mata yan kobbonta da kayan amafaninta ya siyar. Bata yi masa fada a gaban jama'a. Bari take sai dare ya raba kowa ya kwanta sannan ta shiga dakinsa su yi sababi, tana yi kuma tana ce wa murya kasa k'asa mai sunan manya kada a gane halin da muke ciki.
Shi kuwa sai ya bude muryarsa ya ce "Aji mana tunda sharri zaki k'ala mini saboda kin washe ni. Duk yawan jama'ar gidan nan m, babu mai yi miki sata sai Tijjani!
Nan da nan zata bar maganar ta ce "Alfarmar shehu zaka bari. Darajar sunan da ka ambata na yafe maka, Allah ya shirya mini kai, ya tsare ka daga hau da sharrin zamani".
Ya nisa ya sake murmusawa ya ce "Ki yi hakuri zan fad'awa Aliyu ya dinga yi miki. Ki kuma cigaba da yi mini addu'a Dada. Sannan ki yafe mini ta'adin da na yi miki a shekarun baya.
Da azama ta ce "Wallahi na manta komai. Kuma menene baka yi mini ba da ka samu dama? Aliyu kuwa ai shima a k'ullace yake da ni. Ya sha fad'a mini ina nunawa uwarku butanci. Wanda sharri ne kawai, to wa zai haifi d'a ya ce baya sonsa saboda Allah? Jiya kuwa a gidanka ya ce "Yasan nafi sonka a kansa. Sannan kasan matarsa d'iyar Alhaji ce, su kuwa gabadayansu sun kwashe kayansu a gaban ma'aiki akan sha'anina. Yabi ce kawai take mini sassauci, itama dan tasan ni da kai ba dai mutum ba. Duk tsiyatakunta, duk yadda ka jarabtu a kanta, ba zaka k'i jin kaina ba, ba zaka k'i ni ba!
Ta fad'a cikin sigar tausayi.
Ya saki gauron numfashi ya ce "Ki yi hakuri Dada. Za'a gyara. Yanzu ki daina damuwa. Sannan kada ki koma Toro. Ki zauna anan BAUCHI ki dan huta. Idan jama'a sun tafi zansa a kawo miki kaji Babah ta gyara miki, ki dinga cin abin ki. Idan sun kusa karewa za'a sake soya miki wasu. Sannan yanzu a hanya za'a siya miki kayan shayin ki, ki ajiye a wajen ki. Naki ne ke kad'ai kada Yabi ta yi miki k'auron nata".
Ta yi maza ta ce "A a itama tana yi mini alheri, sannan tunda aka sakaye ka soyayya ta sake kulluwa a tsakaninmu, kullum muka hadu sai mun yi kuka. Kasan yanzu ta yi hankali. Gara na fad'i gaskiya ko ba haka ba".
Ya yi dariya ya ce "Ho Dada ta Yabi. Tsoron ta kike ji ne yanzu?"
Ta rausayar da kai ta ce "Uum kaidin mata mai yawa ne. Yanzun nan idan ta murde kai ma sai ka juya mini baya a kanta. Barta dai tunda ta nutsu, kuma tana mini ya kamata. A lallaba a tafi a haka, domin na riga na yi imani da kiararin da na ji ubanta yana yi mata. Na ce wa ita kad'ai gayya ce a gidan Marina. Ko kasan kaf zuri'ata babu mai ruwan kudi a hannunsa irin Yabi? Yadda na gasgata karamar Shehu haka na gasgata kudinta na halali ne. Ka ga yadda ta mayar da dakin uwarta ne? To ragowar matan uban ma duk ta yiwa dakunansu kwaskwarima lokacin auren Ubaida. Idan ka ga bajintar da ta yi a auren kuwa sai ka rik'e baki. Matar gwamna har tawaga ta turo su wakilce ta a bikin.
Kofarsu tafi ko ina haske da kyawu yanzu, kuma duk ita ce. Ko kai ma irin yadda kake yiwa ubanta ai saboda ita ne. Yabi, Yabi duniya ce? K'aramar halitta sai babban al'amari".
Ya kwashe da dariya ainun.
Ta ce "Allah kuwa. Mata ai yanzu sun ri'ka. Idan basa yin ka to mijinsu ma ba zai maka kallon rahama ba".
Ya sake yin dariya ya ce "Duk zan fad'a mata ne".
Ta kyabe baki tare da ce wa "To hudawa cikinka wuka da kanka.
Ta jima kafin ta dingisa ta tarar da su a mota suka tafi.
**
*Watanni uku a gaba*
Zuwa lokacin Husna ta yi gubibi da ita. Shayarwa na matukar ciko da Yabi . Saboda kirjinta suna cika, ita kam tana cikin mata kad'an da goyo yake karbarsu.
Bata da matsalar komai sai ta rashin miji.
Har zuwa lokacin Dada na tare da su.
Ba zato ba tsammani Aliyu ya zo ya kwashe su aka yi musu passport.
Sai da passport ya fito yake fad'a musu kudin hayar filling Tijjani ne. Shine kuma ya ce Yabi da Dada su tafi su yi Umrah su yi masa addu'a."
Ai kafin ya rufe baki Dada ta zabge da kuka tare da ce wa "Ashe zan koma gabar ni Binta? Hauwa kin iya haihuwa! Shehu ya haifu. Allah ka yiwa Shehu abin da mai zato bai yi zatonsa ba ". Sai kuma ta rushe da kuka wurjajan.
Aliyu ya ce "Ganin hakan ya sanya na biyawa tawa uwar sai ku tafi tare"
Nan ma Dada ce ta yi fit ta ce "Wayyo Ali Allah ya yi albarka, yasa kai ma ayi maka tagwaye."
Ya ce "Ai tuni ya bani Dada. Wadannan da suke gittawa ta gabanki ba nawa ba ne? Ko kuwa dan a gidan Marina kowa d'an da ya haifa ne nasa shiyasa kike ganin sai na haifi wasu tagwayen?"
Da yake babu wata shak'uwa a tsakaninsu, asalima tsoro tsoronsa take ji. A sanyaye ta ce "A a kuskure ne, da mantuwa Ali. Yanzu dai ba zamu yi fad'a ba, bayan ka zo mana da babban albishirin da babu irinsa. Allah ya saka da alheri, ya yi muku albarka gabad'aya".
Ya ce "Ameen".
Babah itama ta yi masa godiya da fatan alheri da bunk'asar arziki. Yabi tana bude baki ta ce "Na dad'e ina son na tura Baban Marina Umrah. Na dad'e ina fatan na yi masa ba zata. Ta ce zan tattara abin da nake da shi a yi tafiyar nan da shi".
Idon ta ya ciko da k'walla tana ayyana yadda Baban 2 yake fatan ya kai ta Makkah. Ashe abin na ransa, ashe itace zata riga shi zuwa Sau'udiyya?
Hawaye ya tsinke mata. Babah ma ta shiga taya ta. Aliyu ya ce "Maimakon ku yi masa addu'a sai kuma ku yi masa tukuicin kuka?".
Cikin kuka sosai Dada ta ce "Kai ku yi kukanku da kyau kun ji ai! Ali ai dole mu yi kuka. Yau sama da shekara Shehu na garkame a haka aka samu rabon Asma'u. Kai rabon haihuwa zazzafa ne".
Aliyu ya ce "Kai Dada da fitina kike. Me ya kawo wannan maganar a yanzu kuma? Sannan kuma Yaya Tijjani ne ya koma shehun ko kuwa?"
Ta ce "Eh shi fa. Tunda ga y'aya'nsa na girma ai gara na tsayar masa da suna d'aya. To na zabi Alhaji Shehu kawai domin sha Allahu wataran zai zama Alhaji da ikon Ubangiji kuwa".
Ya gintse dariyasa ya ce "Ni na tafi, tunda Yabi ta had'a ni da aikin dauko Baban Marina gobe".
Sai lokacin na ce "Tare zamu je, zan duba yaron Adda Nazira da ya yi targade."
Ya ce "Tom in sha Allah".
Babah ta ce "To kuma ya zaka yi da wannan kilifar ne tunda bata isa yaye ba. Watanta uku kacal" Ya ce da ita zaku tafi mana".
Dada ta ce "Allahu akabar! Yabi ta haifo Yabi."
Ya kwashe da dariya ya ce "A a Dada. Ai Yabi wadda aka haifa a hanyar sau'udiyya dan aikin Hajj ne ko aka je da cikinta. Ita kuwa wannan ai an riga an haife ta, sannan Umrah zaku je ba tawwali ba".
Ta ce Hakane, sai ace mata Ummara Husna. Domin na tabbatar sai ta yi jidalin Asiya idan ba'a ce mata Ummarah ba. Oh ashe dai da rabon burin Yabi na zama Hajiya a kusa zai tabbata. Nasan Shehu ya biya mini ne dan na kula da ita, na jagorance ta a wajen sa'ayi da safa da Marwa".
Ta bawa Aliyu dariya ainun ya ce "A Ina zaki jagorance ta din? Ai ko ke yanzu kika je d'aya zaku zama, ko wanda ya je bara idan ya koma bana sai ya ga abubuwan da bai san da su ba. Saboda yadda gwamnatin Sau'udiyya ta mayar da hankalinta akan Makkah da Madina gabad'aya. Bare ke mai shekaru ashirin da biyar da zuwa, ina ce da kika je ma ba'a haifi Anas ba?"
Ta rausayar da kai ta ce"Ko Yabi yayarsa ma ba'a haife ta ba. Kasan ana daf da aihuwata ta Alhaji ya hadu da sharrin masu zamba cikin aminci, aihuwarta ta zo cikin wani irin yanayi mai tsananin gaske ".
Na hauro na ce "Dada kina son fad'an wannan labarin. Nasan idan tafiya ta mika zaki k'arasa abin da kuke fad'a cewar ni na kore masa arzikinsa".
Ta kama baki da azama ta ce "Yabi ki yiwa darajar Alhaji da Asma'u kada ki birkice mini. Ko mahaukaci ya ji labarin ki da irin bajintar da kike yiwa uwa da uba ai yasan ke din arzika ce ba wai Yabi ba. Yo duk gidan Marina akwai wanda bai ci arzikinki ba ne? Babu shi Wallahi. Allahu ya huci zuciyar ki. Bazan sake ba. Kai Ali tashi ka yi tafiyar ka, nima alwallah zan yi na yi munajiti da Ubangiji. Kai ma ka yawaita zikirrn ambaton Ubangiji ko na istigifari, ko da kuwa tukin mota kake yi ".
Ya yi dariya ya ce "Wato da Yaya Tijjani da Nasiba da Yabi sune maganin Dada."
Na dauke kai na ce "Kada ka sani Yaya Aliyu! Baban 2 da Nasiba dai. Tun fil-azal sune zasu yi sa insa da ita ta yi mukus. Amma ni kam menene bata yi mini ba?"
Ta yi shiru ya kasa ce wa komai. Sai Babah ce ta fanshe ta da ce wa "To marasa kunya ta yi din. Suma wadancan din waye su da zasu yi maganin uwarmu? Ai tunda aka yi sa'a tana tsananta ibada komai zai daidaita mata."
Da haka aka bar maganar domin jikin Dada ya yi sanyi.
*INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA ABUBAKAR ZARIA*
*ZAKU SAME SU SOFT COPIES A HANNUNA*
*HAKA NAN AKWAI WASU DAGA CIKIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA HAFSAT C SODANGI, SUMA SOFT COPIES*
*HAJIYA HANNE ADO ABDULLAHI?*
*MARUBUCIYAR WANKA DA GARI DA KUMA WACECE UWA?*
*TO ITA MA TAKANAS NA SAMO MUKU LITTAFANTA DOMIN KUN SANI TA YI RUBUTUN MASU MA'ANA*.
*LITTAFAN DA YAWA, AMMA AKWAI DISCOUNT DOMIN SO NAKE KU YI TA SIYAWA Y'AYA'NKU DA KANNENKU LITTAFAI MASU DARASI DA MA'ANA*.
*BA DA JIMAWA BA ZAN ZO MUKU DA SU*.
*0803277333*.
Da kaina na je Toro na sanar da Baban Marina cewar Tijjani ya biya mana Umrah ni da Dada Aliyu kuwa ya biyawa Babah. Ni kuma na biya masa.
Ya yi k'asa kansa tsawon lokaci bai yi ko da motsi ba bare ya yi magana. Ya jima kafin ya d'ago. Na ga hawaye jagejage a fuskar sa.
Nima nawa hawayen ya kwace mini amma ni kam na farincikin yadda Ubangiji ya yiwa fafutukar sana'ata albarka nake yi. Domin bani da burin da ya wuce na sanya Baban Marina farinciki tun ina mitsitsiya ta. Gorin da ake mini, haihuwa ta ce ta tsiyata shi. Da kuma bak'in cikin yadda ya zama koma baya a cikin gidanmu na matuka mintsinin zuciyata.
Da k'yar ya yi jarumtar ce wa "Na sha fad'a miki ke kad'ai gayya ce Asiya. Na fad'a miki zaki yi albarka. Na dad'e ina fad'a miki akwai lokacin da zai zo da kowa sai ya so ki har makiyan na ki. Ga shi na fara ganin sakamakon alherin da Ubangiji zai yiwa hak'uri da juriyar da kika yi a rayuwar ki. Allah ya yi miki albarka. Daga nan har kasa ta rufe mini ido na yafe miki, kina cikin farar addu'a ta. Allah yasa y'aya'n ki su yi fiye da ke. Allah ya miki tukuici da alheri. Kin yi hak'urin aure, kin yi juriya. Da ikon Allah ba zaki sake fuskantar tsanani a gaba ba."
Ina kuka na ce "Allah ya amsa Babanmu! Na gode Allah ya k'ara lafiya.
Ya ce "Ku tafi da gyatumar ki Yabi. Kin ga dukkanku mata ne. Da ikon Allah zaki kai ni."
Na girgiza kai na ce "Zata je Baba! Amma wannan kudin na tara kaso uku cikin hudu da sana'ar da na rayu ina yin ta. Kai nake son ka je, dan ka ji dad'i ka kuma godewa Ubangiji da ya jarrabe ka da fitinar yan'uwa. Sai kuma ya baka y'aya'n da zasu sadaukar da komai dan ka yi murmushi. Ka je ka yi mana addu'a. Ka kuma tayamu addu'ar Ubangiji ya kubuto mana da Tijjani ".
Sai kuka na sosai ya k'wace mini. Abin mamaki sai shima ya taya ni kukan muka dinga yinsa a hankali.
Da yake a dakin Gwaggo yake. Ta shigo da Husna a hannunta da ta fara kukan neman nono. Ta tsaya cak bata miko mini ita ba. Ta sassauta murya ta ce "Ayyah Yabi baki ga kullum girma sake kama shi yake ba? Me yasa kike kasa hak'uri a idan kina gabansa? Kin san yadda kukan ki yake rikita shi kuwa? Kalli irin kukan da yake yi mana. Me yasa kike rasa dukkan jarumtar ki a gabansa?"
Na kasa magana. Sai shine ya ce "Ni ne nake rasa dukkan jarumtata akan lamarin Yabi. Tana matukar bani tausayi, kuma dama ita ce raunina a cikin dukkan y'aya'na. Shiyasa Ubangiji yake ta jarabtata akan sha'anin ta. Tafi kowa shiga garari da kalubalen rayuwa. Asma'u ki ji tausayin ta?. Ki sake ninka addu'ar da kike yi mata. Zauna a zaune ki ji al'amarin da ta zo da shi."
Yana hawaye ya fad'a mata zuwn nawa albishir na yi masa zai tafi gabas. Yana rufe baki itama ta fara hawaye tana fad'in Allah mun gode. Ina taya Yabi godiyar yadda ka cika mata burin ta, na mayar da Alhaji dakin ka. Allah ka k'ara yaukaka mata arziki, ka shirya mata zuria. Ka mata tsari da dukkan abin da zai cutar da ita ko iyalinta".
Ya k'ira Mama da Inna ya fad'a musu alherin da ya same