Showing 18001 words to 21000 words out of 184118 words

Chapter 7 - Bakar Taada Hausa Novel Complete

ba.
Wannan rikicin yana cikin al'amura masu tsananin gaske da ya faru.
Domin da daddare babu kunya bare kawaici Baban kasuwa ya gurfanar da mahaifina a gaban Dada yana ta sababin ya gaji da yadda na takura wa ya'yansa amma ubana ya kasa tsawatarwa.
Da yake Dada bata iya tsallake umarninsa sai kuwa tabi bayansa.
Ta dinga fa'din ai tsoron zuciyata yake yi.
Cikin rishin kuka Baban kasuwa ya ce "Ki gafarce ni Dada! Wani satin zan koma gidana dana kammala gina wa tun bara, amma na kasa tashi saboda ke, to yanzu kam zan tashi na gaji da wannan masifar Wallahi".
Dada ta ce "Wallahi ko ubanta ba zai tashe ka ba tunda matsayinku guda a cikin gidan bare kuma ita.
Share hawayenka ita ce zata bar mini gidan".
Na sake kasa kunne domin tunda aka aiko cewar Babanmu ya zo in ji Dada nasan karata za'a kai sai na bi bayansa ba tare da yasan ina binsa ba.
Na makale a soron Dada ina addu'ar kada Allah ya kawo Bulkachuwa tunda dakinsa a cikin soron yake.
Ta ce "ka fa'dawa Yabi ta tsayar da miji da dukkan yaran ma.
Na umarce ku, ku aurar da su nan da watanni biyu".
Baban kasuwa ya ce "Shi kenan"
Ya fice ya barta da Babanmu."
Ganin zai fito ya gan ni sai na yi maza na fice daga soron na tsaya a bakin k'ofar shashinmu.
Ya zo wuce wa ya dallaro mini ido da sabuwar tocilayit dinsa da alamu suka nuna yau ya zuba mata sabbin batira saboda tsananin hasken ta.
Na dauke kai tare da saka hannunwana na rufe fuskata dan rage wa kaina kaifin hasken da ya dauke mini ido.
Takaicin rashin gaishe shi ya sanya ya ce "Asiya ce?"
Na dauke kai a shak'e na ce "Yabi ce?"
Ya kuwa bu'de murya ya ce "Ja'irar yarinya mai mugun y'anci dama nasan ke ce zaki gan ni ki mini irin wannan iyashegen. Na ce ba, zaki yiwa ubanki Sani hakan?"
Na dauke kai ina kunkunin fa'din "Ai kai ma ba zaka yiwa su Maijidda irin hakan ba".
"Me kika ce? Bude Baki sosai ki fa'di abin da kike ce wa shedaniya."
Ganin Baban Tsakiya dawo ya nufo mu dan ya shiga wajensa ya sanya Baban kasuwa ya d'auki k'arfaffan salati.
Ganinmu hakan ya sanya Baban Tsakiya ya dakata ya ce "ya ya ne Iliya?"
Ai kuwa ya hau rattab'a masa bayanin da aka yi masa na karya akan fad'anmu da Maijidda.
Wani abin mamaki a gabana ya lauya zance yana fa'din a gabansa ma, na zage shi yanzu nan. Da kunnensa ya ji ina zaginsa.
Baban Tsakiya yana bu'de baki sai ce wa ya yi "Tuni fa na d'iga alamar tambaya akan yarinyar nan domin wacce ta saba cudanya da maza ne take irin wannan dibar albarka."
Gabana ya yanke ya fa'di wacce irin magana ce mai muni ta fito a bakin kanin mahaifina kuma uban wanda nake burin aure?"
Na yunkura da nufin mayar masa da zazzafar magana sai kuma na tuna girman aika aikar da zan janyo wa kaina da uwata.
Na sani mahaifina ba zai d'auki al'amarin da sauki ba, domin kuwa zai ce tunda na iya zagin dan-uwansa shima zan zage shi, hukuncin da zai biyo baya kuwa na tabbatar zai zama mai tsananin gaske.
Na ha'diye maganar na juya na tafi na barsu dan kada na yi subutul kalam.
Sai na sake juyo muryar Baban kasuwa yana sake cewa "Na kagu a samu mai tsautsayin daukar kara da kiyashi ya zo ya kwashe ta, ko zamu sarara da musibarta domin ta riga ta zame mana tamkar annoba" .
Baban Tsakiya ya ce "Lallai kuwa kara da kiyashi daukar marar sani, na tausaya wa ahalin gidan Sarkin gida q tunda ina ganin d'ansu a wajenta"
"To namu d'an fa? In ji Baban kasuwa.
Baban Tsakiya ya yi wata irin dariya ya ce "Ta yaro ai kyau take yi bata k'arko, yaushe kana ganin kashi a jikin mutum, za kuma ka yi kuskuren bari naka ya dauki abin nan?"
Kai-tsaye dakin Gwaggo na fa'da na zauna akan tabarmar da take shinfide, yayin da take zaune gefe daya, yanayinta ya nuna a takure take ma'ana tana cikin zullumin kiran da aka yiwa Babanmu me zai haifar mata.
Na sassauta murya na ce "Gwaggo ki yi ha'kuri dan Allah"
Ta muskuta ta ce "Idan ban yi ha'kuri ba ya ya zan yi ne Yabi?
Ai a gabanki aka tabbatar mini ni agwagwa ce akan ki.
Kinsan me hakan yake nufi kuwa?"
Manufa kina gaba ina bin ki a baya, saboda gudun zuciyarki da nake yi.
Ace yanzu kullum a cikin d'aukar wa kanki baki kike, sai ka ce ke kad'ai ce a gidan?
Ga yar'uwarki nan ban ta'ba jin an kawo togaciyar Nazira ba.
Amma ke idan ba'a kawo k'ararki ba, sai idan baki fita ba, ko kuma kin ha'du da masu alkunya, anya Yabi kina ganin kin hau turba mai b'ille wa?
Jikina ya yi sanyi sosai na ce "Duk fa'dan da nake yi kowanne takala ta ake yi, ba wanda nake yin sa na rashin gaskiya, amma ki yi ha'kuri zan yi kokarin koyo ha'kuri idan an nemi ganin rikicina".
Ta kafe ni da ido tana cewa "koya ma zaki yi Yabi?
To fa'da mini zuwa yaushe zaki fara bita?"
Na yi kasa da kaina na ce "Addu'a zaki tsananta yi mini a sanya ni cikin bayi masu ha'kuri da kawaicin cutarwar mutane. Amma a zahiri saboda ke zan yarda na zama mai kawaicin tunda abin da kike so ke nan.
Domin ni dai har yau ban ga ranar da ha'kurinki ya miki ba, ban ga kuma ranar da kawaicin Babanmu yayi masa ba, tunda yau an kai dan-uwansa ne mai kirana da lalatacciya mai bin maza".
Na fa'da hawaye na kwace mini ba tare da na shirya zubarsu ba.

*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


*VIP 1k, regular 500.*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*Shaidar biya ta*
*08032773332.*
*BAK'AR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*.

*Marubuciyar*
*Halin Yau*
*Sabo da kaza*.


*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


11&12.

A ki'dime Gwaggo ta ce "Baban Kasuwa ne ya fada miki hakan Yabi?".
Na girgiza kai na ce " A a Baban Tsakiya ne".
"Tirk'ashi"
Gwaggo ta fa'da a hautsine.
Na sunkuyar da kaina k'asa ina jin wani irin al'amarin tashin hankali na ratsa ni. Da kaina nake jin shekaruna sun yi k'aranci na dinga fuskantar irin wannan rikita rikitar.
Na rasa dalilin da ya sanya nake da ba'kin jini a cikin gidanmu.
Hatta a k'ofarmu mak'iyan da nake da su sun wuce misali.
Domin kafatalin y'an d'akin Mama Nazira ce take sona fisabidillahi, sai ko Yaya Salamatu ita ma kuma ba yadda za'a yi alheri ya samu ta doshe ni da shi, sai dai Nazira, tana dai bani kuncen kayanta da suka sha ruwa ainun.
Ni kuma murna nake yi domin tafi sauran yi mini adalci da sassauci.
Mama kuwa da tana da ikon da zata kore ni a gidan da tuni ta yi hakan tsabar yadda ta washi ta bude ido ta gan ni, mussaman yanzu da sana'ata take sake kafuwa.
Y'an dakinmu ne bana fuskantar adawarsu sai dai muna yawan haura wa sama da su a dalilinsu na ce wa ina daga wa Gwaggo hankali tunda kusan kullum sai na janyo mata bacin rai.
Inna kuwa tare wa yaranta fa'da da nake yi ne ya sanya na kubuta daga nata kaidin.
A hankali ta ce "Ai kuwa ribar ha'kurina gashi nan a bayyane tunda ban yarda na tafi na barku kun yi rayuwar ni y'asu a dalilin rashin uwa ba.
Kina gani ina nan din ma ya ya kuka kare ne, bare kuma na zubar da ku na tafi?
Ashe yanzu yadda yayunki suke dawainyar rike gidan nan bai isa abin alfaharina ba?
A bayyane yake kafatalin ya'yan gidan nan ba wanda Babanku yake mora irin yaran dakin nan. Ai kuwa ko iya hakan na ga ni ba abin da zan ce da Allah sai godiya. Domin wasu da yawa yaran nasu basu amfani kansu ba bare waninsu ya amfanesu.
Ubangiji ba abin da bai yi mini ba, na gode masa, kema na hore ki ri'ke ha'kuri ba abin da hakuri ba zai baki ba.
Ta ri'ke kaina ta ce "Àllah ya miki albarka, ya sassauta miki al'amuranki.
Ina fatan Ubangijin da yake sarrafa zuciya, ya sarrafa taki ta zama mai sassauci da afuwa".
Kuka ya k'wace mini sosai ina cewa "Ameen Gwaggo".
Ba komai yake sanya ni d'imuwa ba irin maganar Baban Tsakiya.
Maganarsa ishara ce akan aurena da Yaya J ba zai yiwu ba.
Zuciyata ta yi nauyi ainun. Na shiga rud'ani mai yawa, na sani idan har zan yi aiki da lura kamata ya yi na nisanci d'ansa tunda har yake neman maraba da ni a cikin gidanmu, ina kuma ace na zama cikin ahalinsa?
Mutumin da bakinsa yake ambaton jaje da alhini ga ahalin wanda d'ansu zai kwashe ni.
Bansan yadda aka yi ba na tsinci kaina da fashe wa da matsanancin kuka.
Saboda fishin Baban kasuwa ya sanya Baban Tsakiya tsayawa ya mini irin wannan tozarcin da zai yi wahalar gaske na sake ganin girmansa.
Na samu kaina da tambayar anya kuwa Babanmu ba dan uba ba ne a tsakaninsu?
Sai nake ayyana ai ko y'ay'an Baffanni suke (cousins) bai kamata su dinga yi masa irin wannan kaskancin ba, dan kawai sun fishi wadatar abin duniya. Balle kuma girman nasaba irin ta uba guda, sai dai kuma babu haufi cikinsu daya ma'ana Dada ce ta yi nakudarsa tun gabbannin a yi tasu.
Babban farin cikina d'aya, bai rasa wadatar zuciya ba, tunda duk tsananin wahala ba zai bu'de baki ya ce su taimake shi ba.
Idan sun yi niyya akan kansu sun yi masa kyauta to zai kar'ba, amma idan zamu kwana mu yini bamu ci ba, ba dai ya ce wane ga halin da nake ciki ba, sai dai idan ya'yan cikinsa ne.
Har ya k'wammace ya fa'da wa aminisa Alhaji Tanimu tsananin da yake ciki, ya tsananta.
Matu'kar kuma zai fa'da masa to kuwa zai sauke masa buhun masara, dawa, dana gero.
Sau tari kallon wadatar da ake yiwa su Baban Kasuwa yake hana masu k'arfi tallafa wa Babanmu.
Sannan mutanan yau suna da dabi'ar k'in taimaka wa matu'kar ba ro'konsu ka yi ba, yayin da mafi yawa aka fi taimako da azumi, shima fake wa ake yi da sunan neman lada alhali a ku'din zakkar da Allah ya wajaba a fitar ne suke siyan kayan abinci suna rarraba wa.
Oh mutanan yau mun rungumi *Bakaken Ta'adodi* daban daban.
Allah ya shirye mu kawai.
Muryar Inna na ji cikin sigar umarni ta ce "Ki cire Jabiru a ranki, nasan zai yi matu'kar wahalar gaske wannan al'amarin bai zama sanadin yin shamaki a tsakaninki da shi ba.
Ina son ki ninka jarumtar ki, tun kafin su miki 'kwalele da shi."
Kafin na bu'de baki sai ganin Baban Marina muka yi ya shigo a fusace yana fa'din "Ina Asiya?"
Da rawar murya na ce "Ga ni Babanmu".
Ya ce "zo ki fice ki bar mini gida tunda har zaki iya tsaya wa gar da gar ki zagi Badamasi da Iliya akan idonsu.
Ai bansan zaki iya irin wannan dib'ar albarkar ba. Na dauka abin naki akwai lissafi a ciki amma tunda kina ganin idan kin yi karo tsakanin kwai da dutse zai miki daidai sai ki je ki yi a wani gidan, amma ba a nan ba.
Ban haifi d'an da zai zagi dan-uwana akan idonsa na bar shi ba.
Na sha fa'da miki babu ruwan ki da shiga tsakanina da y'anuwana.
Amma sam kin k'i ji"
Cikin kuka na ce "Ka yi ha'kuri Babanmu!
Ba yadda aka fa'da maka al'amarin ya kasance ba. Ban zage su ba, har abada kuma ba zan zage su ba, kada ka kore ni a gidanka, zai iya zama sanadin tabarbare war al'amura masu yawa, ka mini dukkan hukuncin da zaka gamsu. Ka taimaki kanka, ka kuma tserar da ni fa'da wa halaka akan wad'anda basa nufin ka da alheri".
Ya jijjiga kai ya ce "Yabi ki yawaita hamdala da baki zo a cikin mutanan farko ba, lah shakka da irinku ne masu kafiya akan ra'ayinku ko da ya ci karo da gaskiya.
Na ji ba zan kore ki ba, amma dole ki yi nisa da gidan nan tun ban fusata na miki baki ba, tunda ba'kin cikin da kika cusa mini a sanadin musayar yawun da kika yi da iyayenki ba mai sau'ki ba ne, akan kannena mahaifiyata take mini mugun baki. Yabi kibi a sannu fa."
Na sake tsorata na ce "Àllah ya huci zuciyarka Baba, Allah ya shiga cikin al'muranka, ya iya maka da iyawarsa".
Nan da nan ya sauka ya hau fa'din "ameen".
Gobe ki shirya ki tafi gidan Salisu har sai na nemi ki, saura can din ma ki nemi gigita masa zaman lafiya a gidansa, dan nasan zaki gano masa laifukan da iyalinsa take yi wanda shi yake yin uzziri a cikinsu".
Na yi kasa da kaina na kasa cewa komai.
Washagari kuwa Gwaggo da kanta ta shirya mini kayana a ledar biba tana ta jaddada mini idan na kuskura na yi rikici da matarsa to ba tantama da ita na yi.
A sanyaye na ce "Komai zan ga ni zan runtse idona babu ruwana, ko da kuwa zata tsokane ni."
Wani irin salama ya shiga Gwaggo ta dinga fa'din "Yauwa Yabina Allah ya sassauta miki".
Anas ne ya fara yi mini gaba da kayana.
Yayin da zamu tafi da Nazira da Iki idan anjima.
Nazira sai kuka take akan tafiyar da zan yi na barta.
Na yi shirin zuwa gaida Dada wanda rashin zuwa wannan gaisuwar ba k'aramin abu take mayar da shi ba.
Babu kuzari na ce "Nazira mu je mu gaida Dada".
Ta girgiza kai tare da cewa "je ki kawai, bana jin dadi anjima na leka".
Na ce "Tom na tafi, ina jin da'di tare da k'arfafa wa kaina guiwar ko na rasa soyayyar kowa a fuskar zumunci ina da yakinin ba zan rasa soyayyar Nazira ba.
Tana sona fiye da zatona, haka nima nake sonta tamkar yadda nake son shakikiyata Yaya Ummi.
Tun daga bayan katangar Dada nake jin tashin muryoyinta da na Ya'yanta
Na karasa har cikin soron sosai na dinga jin kumfar bakin da Baba Maryo uwar Nasiba take yi akan ba zata ta'ba yarda a dauki Nasiba a bawa Tijjani ba.
Kuka take yi wiwi. Tana cewa "sai dai a ga laifina a banza, amma wannan ha'din ba mai yiwu wa ba ne."
Yayin da Babah ta Bulkachuwa take fa'din "Ai ban ga laifinki ba, gaskiyar magana kika fa'da.
Kuma dama mutum shi yake mutunta kansa, da ya nutsu ya zama mutumin kirki ina ce a ko ina zai nemi aure a ba shi?.
Yanzu kuwa da ya zama abin da ya zama a cikin danginsa ma gudunsa za'a yi bare a waje".
Dada ta ce "Ya isa haka, ba cece-kuce zaku yi mini ba.
Na rufe wannan maganar, na yi zaton auren nasa da ita zai kawo masa dai-daito tunda tana sonsa, idan aka yi sa'a sai ya shiryu, ruwan wankan aure ka'dai maganin wanda ko wacce suka fand'are ne. Amma tunda abin zai zama tashin hankali a bar maganar haka nan
Nasiba ba matarsa ba ce."
Kafin na yi wani motsi sai jin muryar Baban Tsakiya ya yi yana fa'din "Kazalika wannan yar iskar yarinyar ba matar Jabir ba ce, ko bayan raina idan aka bari ya aure ta Wallahi Allah ya isa, na fa'da a gabanku, kuma yanzu ma idan na tashi zan je na sami Yaya Sani na tabbatar masa babu maganar aure, mun gama magana da Iliya, Maijidda zai aura.
Domin ba zan yadda ya dauko mini majuniniyar yarinyar nan ta zo ta tarwatsa mini zuri'a ba".
Daidai lokacin na yi sallama na gaida Dada sannan na gaishe su a jamma'u.
Babar Bulkachuwa ce ta amsa cikin karfin hali tana danne bacin ran da ya ke kutso mata.
Nima na yi jarumtar cewa "Ashe kin zo Babah?"
Ta ce " Na zo dazun nan kin san sammakon zuwa nake yi saboda motar Jos muke shigowa.
Na yi yake na ce "Sannu da zuwa".
Na mike da nufin tafiya sai kuwa Baban Tsakiya ya ce "Dawo ki zauna.
Na zauna ina kallonsa k'ir domin ya riga ya wanke mini a zuciyata.
Ya kausasa murya ya ce "ki hanzarta turo wanda kuka shirya domin kuwa watan jibi da saba'a zaku bar gidan nan".
Cikin son nuna masa iyaka na ce "To ai Jabir naka muka daidaita da shi, wannan satin zai iso garin, wajenka zan turo shi, ko wajen Baban Kasuwa?"
Ya zabura ya mini dakuwa ya ce "Marar kunya, marar mutunci ki zagi dan-uwana, ki mini tsaki a gabana ki yi zaton kuma zaki zama surukuta, ko dai bayan sharholiyar da kike yi har shayeshaye kike had'a wa da shi?
To saurara ki ji! Jabir ba zai auri wanda zata zagi ubansa ba."
Babu fargaba na ce "Na karbi wannan hukuncin da hannu biyu Baba, ban kuma saka ka cikin masu son rai ba, domin na yi laifin da na cancancin hakan.
Alfarma d'aya nake ro'ko a wajenku tunda ni ce bani da tarbiya, to ku musanya wa Yaya Jabir ni da Nazira domin dukkanku nan ba wanda zai zargeta da rashin tarbiya ko sharholiyar da ni nake yi".
Nan da nan Baban kasuwa ya ce "Anki a bashi ita din dan uwarki, makira, algunguma, Maijidda ce matarsa har a kiyama kuwa".
Ga mamakina sai na mike na tsinci kaina da cewa "Gaskiya Baban Marina ne ba a so, shi kuma har yana kora ta saboda ku.
Ba komai Ubangiji ya sanya alheri".
Har na fice ba wanda ya iya bu'de baki ya ce mini kala tsabar kad'uwar da suka yi da furucina.
Baban Tsakiya ne cikin fishi ya ce "Ba shakka dangin uwar yarinyar nan akwai majununai".
Na so na tsaya na ce "ko wanne d'a yafi gadon dangin ubansa, dan ya gane sune majununai ba mutanan Kangire ba. Sai dai kuma duk iyashegena ai wata fuskar tafi gaban mari, kannen ubana ne,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login