Showing 6001 words to 9000 words out of 184118 words
Chapter 3 - Bakar Taada Hausa Novel Complete
Kudu suka fuskanci wulakanci daga wajen Mama. Shikenan duk haihuwar da take yi basu sake yin gayya sun zo ba.
Sai dai a samu mutum biyu su zo su ganta washagari su juya sassafe.
Wannan matakin da suka dauka shine ya zama laifin da yak'i wuce wa a wajen Dada da take ta musguna mata da gorin ba y'ar babbar haula ba ce, sannan yan'uwanta masu k'ullaci ne, duk kuma cikin matan gidan mahaifiyarmu ce kawai bata da kowa a garin Toro shi yasa ma wani abin ake yi mata da gan gan.
Duk da ba jin dadin zaman take yi ba, ta jure dukkan kalubale dan kawai ta zauna da mu yaranta, amma bata tsira ba tunda Babanmu ma haka siddan sai ya dauke mata wuta na tsawon lokaci mai yawa. Mama kuwa bata fasa yi mata yankan baya a duk inda ta zauna ko ta samu damar yin hakan ba.
Ko yaushe Gwaggo a cikin mutuntunta Dada take hatta wankin kayanta har yau bata daina yi mata ba, amma babu gwaninta bare yabawa.
Nan da nan na tunzura na ce "Da yake shi kina jin tsoron kada ya keta ki shiyasa kike fa'din hakan. Amma ni kin bu'de baki kina niyyar tozarta ni.
Tunda ban gaishe shi ba, ya yi mini magana ban amsa ba, ba sai ya rabu da ni ba?
Bana son harka da shi ne, a duniya na tsani sunan da yake kirana da shi. Sannan idan zai mini magana sai ya lanjare murya, kuma kinsan dai ba sosai nake ji ba, bare na ji shi da kyau".
K'wafa ta yi tare da cewa "Kowa ya yi na gari ai dan kansa Yabi".
Basira ta ce "Yi ha'kuri Dada d'ora mana karatun kawai".
Ta rausayar da kai gwanin tausayi ta ce "Kayya Basira zuciyata ta jagula ainun karatun nan sai gobe kuma".
Firdausi ta ce "Yaya Bulkachuwa saka baki Dada ta d'ora mana karatun, bata ha'kuri mana".
Ya kalle ta ya ce "Dadarmu share kawai, nima na ha'kura ai. Kinsan hankalin Asiyan Toro a k'auri yake".
Na sake hauro wa na ce "Tijjani ka bari, ka ga dai bana shiga harkarka akan me zaka nemi takure ni ne? Gaskiya bana son haka".
Dada ta sake yin k'wafa tare da cewa "Yabi kin janyo muku, domin na lura tashen balaga kike ji, zan kuwa yi maganinki."
Kafin wani ya yi magana sai ga Ikilima k'anwata da a yanzu take shekaru tara.
Ta shigo cikin nutsuwa ta kalle ni ta ce "Adda Yabi ki zo".
Da azama na mike domin nasan Yaya Jabir ne.
Saurayin da yake gigita zuciyata da ruhina.
Ban ce komai ba, na mike ina cewa "Sai da safenku".
Dada ta bimu da ido tana cewa "Jabiru ne ko kuwa wani ne?"
Ban kula ba, ba kuma wacce ta tanka.
Domin dai na fi su farin jinin mane ma duk kuwa da ba finsu kyau na yi ba, asalima wasu sun fini kyau, sun kuma fini cikar mace.
A bakin kofar Shashenmu ya jingina.
Matashin saurayi mai cike da nutsuwa da kamala.
Wankan tarwada ne, siriri mai matsakaicin tsayi, mai sanyi a halayya da kuma dabi'a.
Bashi da kwaramniya tun tashinmu, mai hakuri ne na gaske, da wahalar gaske ka ga fa'dan Yaya Jabir.
Sosai muke shiri da shi, duk kuwa da ni din mai tsiwa ce, mai kuma hayaniya ce.
Amma jininmu ya ha'du sosai.
Kusan tun soyayyar kuruciya ce ta rikide ta zama ta gaske.
Dalibi ne a jami'ar tarayya ta Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Ajinsa uku sawess yake yi a cikin Jos.
Sannan ya yi sa'a ma'aikaci ne a karamar hukuma da aka dauke shi aiki da sakandire a lokacin kawunsa kanin mahaifiyarsa kansila ne a yankin gundumar Toro.
Na isa gare shi, yana sanye cikin farin yadi fari k'al.
Wato duk samarin gidanmu babu mai tsabtar Yaya J.
Ina jin da'din k'iransa da Yaya J. Na lura shima ba karamin son sunan yake yi ba. Ni ka'dai ce nake fa'da masa hakan kuma.
Kusan halayyarmu daya ni da shi, domin nima tsabta ce da ni, har fa'di ake yi aljanun tsabta ne da ni. Baya ga haka muna da son y'anuwanmu, bama jin k'yashi wajen salwantar da duk abi da yake namu ne akan d'an-uwanmu, har rashin girman jikinmu iri d'aya ne.
Shine d'a na farko a bangaren Baban Tsakiya.
Mutane da yawa suna fa'din kama muke yi ni da shi, ni kuma bana ganin kamar kawia dai yanayinmu ne daya tunda shi din ba wani girma ne da shi ba, haka yake dan madaidaici avarage height ne.
Haka nima duk cikin y'anmatan da muka taso ko wacce ta fini tsayi, bani da tsayi, nafi kusa da gajerta.
Ina da gashi sosai, sannan ina da manyan idanuwa baya ga hakan fara ce sosai.
Yadda nake yar cif cif sai nake matu'kar daukar hankalin mutane.
Kullum idan zan fita sai Gwaggo ta ce ban da wulakanci Yabi, domin al'adar gidanmu ne yarinya bata kammala karatun sakandire.
Shekaru sha biyar ake aurar wa, amma mu da alamu za'a bari mu kammala duk da dai Dada ta fara fa'din mu shirya dama kuma ita ce take matsa lambar sai an yi aure.
Ya zuba mini ido babu walwala jikina ya yi sanyi na yi kasa da kaina ina fa'din "wannan kallon tuhumar fa Yaya J?"
Ya saki gauron numfashi ya ce "kin kama kanki da kanki Yabi. Jiya ma fa sai da kuka tsaya da yaron nan dan gidan Sarkin k'ofa ko?".
Na yi murmushi na ce "Ai dai baka ji me na ce masa ba".
Na fa'da cikin shagwaba shagwaba.
Ya sake yin kasa da murya ya ce "Ban ji ba, amma yanzu fa'da mini na ji".
Na yi k'asa da kaina na ce "Na fa'da masa cewar ni bana sonsa akwai wani bawan Allan da ya riga shi yin wuf da zuciyar Yabin Marina".
Ina kallonsa ya dan murmusa ya ce "Waye wannan bawan Allan?"
Na dago amma ban kalle shi ba a dalilin hasken kwai na kanmu.
Na juyar da fuska na ce "Yaya J mana".
A wannan karon murmushi mai sauti ya yi.
Ya nisa ya ce "Yauwa Yabin J, kin biya ni.
Amma idan kina son ki burge ni, ki daina ma sauraronsa ba shi kawai ba, kowanne namiji ma.
Sannan ki daina fa'da dazu ma sai da kika yi dambe da Saratu.
Kin ta'ba gani na ina dambe?"
Na girgiza kai tare da cewa "Ha'kuri ne ya yi maka yawa, ni kuwa bani da shi, domin duk wacce ta ta'ba ni ba zan k'yale ba"
Ya girgiza kai ya ce "Ha'kuri fa falala ne da shi Yabi".
Na girgiza kai na ce "To ka dinga yi mini addu'a na shiga sahun masu ha'kurin domin kuwa ni duk wanda ya ta'ba ni idan ban rama ba sai nake ganin na zama sullutu".
Ya murmusa sosai domin ba mai dabi'ar k'yal-k'yala dariya ba ne.
Ya zuba mini ido ya ce "Wai Goggo ce ta haife ki, al'amarin Ubangiji da girma yake.
Waton idan kika rama baki zama sullutu ba?".
Da hanzari na ce "Ras Yaya J domin dai kai din shaida ne na yadda ake kaffa kaffa da ni, da duk kayana".
Ya zuba mini ido ya ce "Allah ka sanyawa Yabi ha'kuri da juriya, a mayar mini ita ta zama mai shanye dukkan kalubale da ha'kuri da kuma kawaici".
Na ce "Gaskiya Yaya J kada mu yi haka da kai, roka mini na zama yar gwagwarmaya mana, sai kawai ka roka mini na zama mai ha'kuri komai aka yi mini sai dai na yi kuka, ko ya yi ta cina a zuciyata, watarana sai dai kawai a budi ido aga Yabi ta ha'du da jinya ko ta mace ma gaba'daya. To ni ba zan zama hakan ba".
Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Kinsan darajar ha'kuri kuwa Asiya?"
Na kalle shi domin bai cika fa'din zahirin sunana ba, tunda ya fahimci ina son inkiyata ta Yabi shi kenan ya wajabta ma kansa fa'da mini duk da dai yafi son Asiya.
Domin an sha dakuwa da ni akan ce mini Asiya, ina ganin duk wanda ba zai ce mini Yabi ba, to hassada yake yi mini, tunda an yi dawafi da ni a ciki, an yi tsayuwar arfa da ni, an yi jifan shaidan da ni, an yi sa'ayi da ni to mene ne na tauye mini Hajjin?"
Ban bashi amsa ba ya ce "W
anda Ubangiji ya masa baiwar ha'kuri to ina tabbatar miki an ba shi arzikin duniya da lahira, ba kuma abin da ba zai cimma ba a rayuwarsa, daure ki zama jaruma amma ba jarumtar rashin ha'kuri ba".
Na girgiza kai ina murmushi domin dai ban gamsu ba.
Har yau da na fara mallakar hankalina ban ga ribar ha'kurin da mahaifiyata take yi ba.
Ban ga ribar kawaici da ha'kurin da mahaifinmu yake yiwa zumunci ba.
Ban ga ribar ha'kurin da Yaya Ummi take da mijinta da uwargidanta ba.
Tunda har yau ita ce a wahale, kuskure ka'dan zata yi ya mata tijara a tsakar gida a gaban kowa tamkar ba ita ce mai k'uruciya ba.
Dan haka na k'udire a raina ba wanda zai nemi ta'ba ni, na k'yale shi, zan yi komai dan na tabbatar ban bari na zama gajeriyar katanga mai da'din k'etara ba.
Yanayina ya tabbatar masa ban yarda zan iya yin hakan ba.
Ya girgiza kai ya ce "Ai shikenan sai dai zan cigaba da yi miki addu'ar dace wa da babban arzikin duniya wato Ha'kuri".
Na yi dariya na ce "Dama addu'ar na zama hamshakiyar y'ar kasuwa kake yi mini, ta yadda kasuwacina zai d'auke mini hankali daga dukkan wani rashin ha'kurina da kake ga ni".
Da sauri ya ce "Ina yi miki Yabina! Da ikon Ubangiji komai kika kasa sai kin sayar, kullum sai na roka miki Ubangiji ya baki dauwamammiyar sana'a da zaki tsufa kina cin gajiyarta".
Da'di ya kama ni, domin Yaya J ne kawai ya fahimci irin yadda nake son na zama shahararrriyar y'ar kasuwa.
Ya miko mini tsarabar Jos leda biyu da ya ajiye a bayan k'yauren shiga shashinmu.
Na karb'a ina godiya sosai.
Na tabbatar Atile ce da kuma turare, tunda sune abu mafi soyuwa a mini kyautarsu.
Fahimtar hakan da ya yi, sai ya dimanci yi mini tsarabarsu.
Shine ya fara koya mini amfani da turaren Far-away.
Daga haka muka yi sallamah.
Kai tsaye dakin uwata na nufa ban koma wajen Dada ba.
*Akwai kayayyakin gyara mace sosai irin na kasar Chad.*
*Akwai maganin sanyi sadidan*
*Ku tuntube ni a wannan lambar*
*08032773332.*
✍️
*BAK'AR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*.
*Marubuciyar*
*Halin Yau*
*Sabo da kaza*
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYERS*
https://www.wattpad.com/1381521145?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=SurayyaIbrahim1&wp_originator=2c15XL0D2bIzHhiZQM1Ufz9MWPlKieRkWxJuGH2P9gX0b9XHQk5Jym8fxiz%2BPI0TAhOUhwh2GWl2lunKDNI2ObmS%2B%2FfL1BUVY3%2Ft%2BNKg%2B0D0iEZNLOPdWH9AZxOaGd51
https://arewabooks.com/book?id=64e93a53984f91b3605ae432
*Ina makaranta labaran Books ɗin Ayshat Ɗansabo lemu, marubuciyar TAIMIYYAH DA NUFIN ALLAH kai har ma da sauran daɗaɗan littafanta? Marubuciyar na muku albishir da cewa sabon littafinta mai suna ƘADDARAR ZOYA ya fara sauka da zafinsa,labarin ƘADDARAR ZOYA labari ne da ya faru a gaske ba ƙageggen labari bane.Don haka kar ku bari ayi wannan tafiyar babu ku a cikinta,labarin zai zo muku akan 500 Whatsapp group sai VIP group on Telegram 1k.Ku tuntuɓi marubuciyar akan lambarta 08167768704 domin samun free pages na labarin kai tsaye, kafin ku kai ga yin payment.Kar ku manta it's a true life story,don haka ku hanzarta shiga cikin tafiyar da babu danasanin bin alƙaminsa....✍🏻*
5&6.
A zaune na tarar da ita tana kullin siga, da yake tana auno rabin kwano tana k'ullawa, idan an zo siyan koko ana siya.
Ikilima tana gefenta tana faman barci.
Na ajiye ledar a gabanta.
Ta kalle ni ta ce "Yabi na sha fa'da miki, jikina na bani sha'aninku da Jabiru ba mai yiwuwa ba ne, ba sa'an auren ki ba ne, gara ki tsaya akan Abdulrashid zai fi mana sau'ki da kwanciyar hankali".
Na yi shiru, amma zuciyata sai tsalle take yi.
Babban tashin hankalina a duniya shine Gwaggo ta ce mini aurena da Yaya J ba zai yiwu ba.
Na yi k'asa da kaina a hankali na ce "Gwaggo fa'da mini dame ya fini da kike ganin yafi k'arfina?"
Ta murmusa ka'dan ta ce "Saboda Babanki ba shi da arziki, sun tsere mana, sannan uwarsa tana da buri a kansa, bayan haka ga Mama k'ut take da uwarsa, dan haka zata yi dukkan mai yiwuwa ta sake b'ata lamarin tunda akwai haske a tare da shi, ba zata so wannan hasken a tare da ke ba.
Sanin kanki ne kuma mutanen gidan nan baza su dauke ki su ba shi ba, tunda kuna da yawa, zasu yi kwarya tabi kwarya ne a tsakani.
Da ace ke din diyar Baban kasuwa ce to, da ba fargabar da zan yi".
Na numfasa k'irjina ya daure ainun.
Na dinga tambayar kaina shin zan iya rabuwa da Yaya J?
Da gaske har lalacewar zumunci ya kai za a iya hanamu aure ba tare da wani dalili gamshasshe ba?
Ashe har za'a iya ture karfin jini saboda kawai dan-uwanka ba shi da wadatar abin duniya?
Na sauke nannauyan numfashi na ce "Ki daina damuwa Gwaggo! Ban tsananta ba, ban kuma dage sai shi ba.
Ki cigaba da yi mini addu'a".
Ta sake kafe ni da ido ta ce " Ina yi miki addu'a sosai Yabi, amma zata yi tasiri ka'dai idan kin barwa Allah ya yi miki zabi, kin kuma yak'i zuciyarki akan Jabiru. Ina nufin ki rage zurfafa a al'amariinsa."
A sanyaye na ce "To Gwaggo".
Sai kuma na zauna ina taya ta k'ulla sigan ina bata labarin yadda ta kaya a tsakanina da Dada.
Ta nisa ta ce "Ba kya jin magana ne, ban da hakan mene ne zaki dinga janyo wa tana yi miki mugun fata?
Kinsan kuwa bakinta zai kama ki domin ita ma uwa ce a wajen ki".
Jikina ya sake yin sanyi, na dinga yin addu'ar Allah yasa na daina tanka mata akan Shehu tunda mafi yawa saboda hakan take fusata.
Ta ke tsanata mini, har take yi mini
mummunar addu'a.
Washagari takwas saura muka d'unguma zuwa makarantarmu ta jeka ka dawo ta gwamnatin jahar Bauchi.
Ajin mu hudu wato ss1.
Ko wacce tana cikin tsafta, duk inda muka wuce sai an kallemu wataran akan kunnenmu mu ke jiyo yadda ake fadin "y'an Marina ne, kasan yawa ne dasu tamkar tsaki."
Ko muji an ce "kai wato gidan Marina akwai zuka zukan zaratan y'anmata fa."
Muna tafe ina tambayar Basira da Nazira jiya Dada ta d'ora musu karatun kuwa bayan na tafi?.
Nasiba ta ce "Bayan kin bata mata rai yaushe zata iya yin karatu? Kin san kullum sai ta ce haramun ne yin karatun addini a cikin fishi ko a cikin rashin tsarki".
Muka k'yal-k'yalale da dariya gaba'daya.
Muka isa makaranta hatta Malamai kwarjini muke yi musu saboda yawanmu da kuma yadda muke kama da juna baya ga hakan tare ake ganinmu tamkar kashin awaki alhalin a gidajenmu babu wannan soyayyar da jin kai da ake gani a tare da mu.
Lokacin tashi yayi muka dawo a jiga ce a dalilin rana ake yi duk da zafin ranarmu da sau'ki akan ta Bauchi da Jigawa.
Wajibi ne idan zamu tafi sai mun shiga mun gaida Dada, haka nan idan mun dawo.
Tsabar saka ido da kwakkafin baiwar Allan nan duk wacce bata je ba sai ta ga ne, hakan kuma na iya zama sanadin rikici a gidan, domin bai zame mata komai ba, ta kira uwar yarinya ta yi mata tass, ta ce da sa hannunta y'arta ta raina ta.
Kuma abin mamakin idan baka kama sunanta ba, to da kai da wacce bata je ba daidai kuke.
Ina tsaye suka dinga shiga suna fitobwa ba abin da ake ji sai "Dada mun dawo, sannu da gida" .
Yayin da ita kuma take kama sunan kowa tana cewa "Sannunku da dawowa, lale da y'anmata Dada".
Sanin da na yi garina da tsakuwa da ita, ya sanya nake jingirta wa sai na je gabanta sosai ta yadda zata shaida ni da kyau.
Tunda kullum sai na je, amma idan ta so ci mana mutunci ni da Gwaggo sai ta ce ban je ba, ko kuma na yi mata gaisuwar gadara da wulakanci daga bakin k'ofa
Dan haka da na k'ara wayo sai nake isa gabanta mu hada ido sosai sannan na yi gaisuwar.
A gajiye na k'arisa k'ofarmu na tarar da bacin rai domin tsagwaya na tarar an yi a matsayin abincin rana, wani irin nau'in abinci ne da ake sirfa dawa sai a dafa a ci da manja.
Na tsani abincin ba dan babu da'di ba, sai dan kawai bana so.
Na zauna a tsakar d'akin Gwaggo ina kunci sosai.
Ta shigo ta kalle ni ta ce "ban ga kin cire inifom din naki, kin yi sallah kin zuba abinci ba?"
Na tumbatsa da fishi ban tanka ba.
Ta kafe ni da ido ta ce "Yabi kullum aka yi tsagwaya sai kin tayar mini da hankali? Sanin kan ki ne mahaifinku ya saka takunkunmin siyo abinci a waje ko a ro'ko a wani waje. Me yasa ba zaki rufe ido ki ci dan ta yi miki maganin yunwa ba?
Idan kin yi ha'kuri ai wataran barin gidan zaki yi, ranar da Allah ya kai ki dakinki komai kike so sai ki yi wanda bai wuce wadatar mijinki ba".
Cikin bacin rai na ce "Ki taimake ni ki bar ni na jika gari na sha, Allah ya sani yunwa nake ji kamar na mutu".
A sanyaye ta ce "To ki jika amma nafi son ki dinga ci tunda idan kin ci din ba illah take miki ba."
Haka na jika gari na bu'de jakar makaranta na dauko gyada maro na bushe na zuba, ina sha, ina fa'din "ba dan na k'osa ba, da Iklima ta siyo mini madara, to aikenta bana me sauri bane ko wanda yake a matse irina, domin shad'arta ta yi yawa".
Gwaggo ta girgiza kai ta ce "Ke dai duk salon k'wadayi kin san shi, ki dinga bin duniya a sannu sannu Yabi".
Na yi dariya na ce "Gwaggo tuni aka daina bin duniya a sannu. Saboda gaggawar mutanen cikinta ba zasu bar mai binta a sannu ya kai ga gaci ba, yanzu da nake yin kitso na ha'da da lalle ba gashi muna d'an samun taro