Showing 105001 words to 108000 words out of 184118 words
Chapter 36 - Bakar Taada Hausa Novel Complete
sana'a? Ai k'arshen tozarci ke nan. Amma ai na ha'kura kin san ina sonki fiye da komai Asiya. Ban so wani abu a duniyar nan da ya zarta ki ba. Uwa da ubana ne kawai a gaban ki. Dan haka ki daina damun kanki akan wasu matan. Ba sonsu nake yi ba. Da gaske ba wacce nake so a zuciyata sai ke. Amma zan iya ganin wata ta burge ni ko ta bani sha'awa a dalilin Ubangiji ya sanya sha'awar mace sama da d'aya a zuciyar mazaje. Kullum ina ro'kon Ubangiji ya tsare ni da sha'awar wata macen fiye da ke. Duk sadda na ga wata zata burge ni ko ta ba ni sha'awa gida zan garzayo na ga halalina, na yi abin da nake so da ita. Ke dai idan kin gan ni afujajan na dawo miki, to ban da musu da bijire wa da sunan jan aji".
Dan haka ki saki ranki da ni, ke nake so, ke ce halaliya ta, da ke nake fatan na rayu muddin rai".
Na fara k'ananun hawaye na ce "To kuma nufinka korata da ka yi da daddare a ganduna ne? Ya tafi a bilis?"
Ya tarairayo ni cikin rad'a ya ce "Ai ya wuce tunda da kaina na je na dawo da ke".
Na fara turza k'afa ina fa'din "Alkur'an ban yarda ba".
Ya sheke da dariya ya ce "Dole sai kin nuna mini kina da alaka da mutanan Gwaram da Birin kudu domin a bakinsu nake jin wannan rantsuwar".
Na ce "To mahaifiyata ta fito daga yankin ai kuwa kasan jininsu ce".
Ya ce "Haka ne. To yanzu me zan yi ki yarda ki huce".
Na shiru ina tunani sai kawai na ce "Yi mini kukan zakara".
Ya ce "kukan sa wanne a ciki?"
Na ce "oh kukan zakaran kala kala ne?"
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Ya ce "Yana cara idan afijir ya keto, yana yi yayin kiran sallar farillah akwai kuma wanda yake yi idan ya ga kaza yana kyarkyarar ta, yana hilar ta dan ya samu hadin kanta".
Kunya ta kama ni na ce "Yi mini wanda yake yi idan alfijir ya keto kawai".
Ya kuwa ce "Alkur'an ba shi zan yi ba tunda ni ma yanzu kyarkyarar ki nake yi".
Kafin na ce komai ya tak'arkare ya fara wani irin gurnani yan kur kur sai ya kuma ya yi cara tamkar dai zakaran gaske kafin na ankara ya turmushe ni irin yadda zakara yake dank'ar kaza.
Washagari da walwala muka tashi ya dawo Tijjanin da yake kaffa kaffa da ni.
Sai ririta ni yake yi. Komai shi ya yi har abin karyawa.
Na kalle shi cikin nutsuwa bayan ya d'ora ni akan cinya yana shinshinata tamkar maye. Na kama gemunsa na ce "Wannan shine .... d'ina. Amma ba shine na jiya da shekaranjiya ba".
Dariya mai yawa ta k'wace masa ya ce "sabo da Allah little mene ne wani dash dash? Ki ce Tijjanin da kika saba fa'da mana tunda har yau ba ni da k'imar da za'a sakaya mini suna".
Na yi murmushi na ce "Ai tunda na yi al'kawarin sai na haihu da na saka maka suna, to fa sai na haihun. Idan ka matsu kawai nan da sati na fara amai, ka kai ni asibiti ana gwada ni ace ciki ne, tun a ranar zan fara fa'din sunan na ka".
Ya kankame ni sosai yana dariya kwarai da gaske.
Ya ce "Nan da shekaru goma masu zuwa zan tisa ki a gaba ina miki bitar wadannan kalaman a lokacin kin kai ashirin da bakwai.
Na ce "ko zuwa lokacin y'ay'a nawa na haifa?"
Ya zuba mini ido ya ce "Allah yasa sun kai uku"
Na ce "Haba dash dash ina laifin hudu ma. Nifa ina son yara da yawa."
Ya yi kissing din goshina ya ce "Allah ya bamu masu albarka. Nima ina so.
Amma kin san dole control zamu yi bazan yarda ki tara yara da yawa ki man ce da sha'anina ba".
Na yi k'asa da murya na ce "Kai ne fa bebina na farko ta ya ya zan mance ka? To ko y'ay'a dari na haifa kai ne a gabansu. Ni burina na haifo mai kama da kai ma".
Nan da nan kuma sai na rufe fuskata alamun kunya ta rufar mini.
Shi kuma da'din kalamaina ya yi matu'kar kama shi. Ya samu nutsuwar da gaske ina sonsa yanzu. Ya rungume ni tsam tsam ya kasa cewa komai.
Ya sakar mini nishin da yake rura mini jiki. Ya ce "Ni kuma na fi son ki haifo mini little girl mai kama da ke. Amma ba mafad'aciya irin Asiya Toro ba".
Na cuna baki na ce "Yo ai ni fa'da na sai an tab'o ni".
Ya ce "Amma Asiya ai ni bana tab'o ki kike rikice mini. Yanzun nan zamu rabu k'alau. Idan na dawo sai na ga kina share ni, ko mu yini lafiya, idan mun kwanta ki hau buge mini hannu kina ture ni. Haka ake yi?"
Na ce "Amma ai sai ka dade baka dawo ba ne, nake share ka. Zuciyata tana harbawa da k'arfi tare da raya mini tadi ka tsaya yi".
Ya dad'a ruk'o ni sosai cikin rarrashi ya ce "Shaid'an ne yake wasa da ke Asiya. Kuma dai ai babu kyau a yanke wa mutum hukunci da zato. Ki dinga sassauta mini, da gaske bana son fishin ki, bana son mu dinga fad'a".
Na dauke kai bayan na tura baki na ce "Ai kai ne, kake murde mini tunda ka fahimci ka fara shiga raina. Idan ba wuta wuta nake yi maka ba, ba k'aramin jana zaka yi a k'asa ba."
Ya kwashe da dariya mai tsananin gaske.
Ya ce "Asiyaty an buga an bar ki. Wato da iron hand zaki yi handling d'ina."
Na ce "Ai dama yaya Ummi ta ce "Nan gaba sai ka mini fiye da abubuwan da na yi maka. Ilai kuwa na fara ga ni.
A buge wa Asiya baki.
A zabge Asiya da mari.
A dinga yiwa Asiya iyakar daki a gidanta.
A rufe wa Asiya gida. Aka fitittke sai ta tafi gida.
An fara jawa Asiya rai. Sai an jagwalgwalata sai a juya baya a ce sai ta bada hak'uri.
An ki yiwa Asiya ciki.
Idan Asiya bata saki lalle ko kitso ta taso ta yi barka da dawowa ba, a yi mata fishi.
Asiya ba son a dinga gatsa sunan ta da na garinta take yi ba. Amma haka za'a daddage ana ce mata Asiya Toro.
Ai Wallahi na yi laushi. Ina matukar hak'uri. Ban ma sake maka fuska gabadaya ba kake yi mini hakan ina kuma a ce lako lako nake?"
Ya jima yana kallona da matsanancin mamaki. Sai kuma dariyar da bai shirya ba ta sake k'wace masa. Ya dinga yi, ni kuwa na ce "Yi dariyar ka son ranka. Allah ne ya ara maka dama. Ka zuba ruwa a k'asa ka sha. Ka same ni da yawa".
Ai kuwa ya jima yana yi, sai ya yi shiru sai ya kalle ni ya ce "Ah aha". Ko ya ce ",Na k'i yi miki ciki ko Asiya?"
Sai ya sake kyalkyale wa da dariya.
Sai da ya nutsu ya ce "Little ki daina yi mini wuta wuta kin ji. Idan kina son ki damke ni, kawai ki kiyaye abin da bana so. Ki kuma dage wajen yin abubuwan da nake so. Ciki kuwa zan miki, ki k'ara hak'uri lokaci ne kin ji".
Na ce "To! Amma kai ma kada ka sake ce wa na tafi gida. Ai kasan Baban Marina ba dad'i zai ji ba. Ni kuma magauta su tisa ni a gaba da habaici da gori."
Ya kankame ni ya ce "Har abada ba zan sake ce wa ki tafi ba Asiya. Duk laifin da zaki yi mini kuwa. Matukar kin yarda na haramta miki zuwa gidajen mutane da sunan sana'a. Bana so, ba kuma zan dauka ba".
Da azama na ce "Bazan sake yi ba har abada".
Dad'i ya kama shi ya dinga kissing d'in kunne na, yana fad'in "I cherish you dear "
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
✍️
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*
*Watanni shida a gaba*.
Zuwa lokacin duk kaucen kaucen Tijjani na kada na shiga harkar ri'ke masa gida ta ci tura. Duk yadda baya son ya karbi ku'dina abin ya faskara domin samun ku'di ba k'aramin wahala yake ga talaka a wannan lokacin da aka janye tallafin mai a Nijeriya ba. Mafi yawa masu kananun sana'u sun shiga halin ni y'asu bare kuma wanda sana'ar sa hab'o ce ma'ana sai an samu za'a yi.
Duk da k'arancin shekaruna na fahimci matu'kar Tijjani zai fita ya dawo gida ba tare da ya ru'ko wani abu komai kankantar sa ba, to kuwa a wannan ranar ba zan gane kansa ba. Duk yadda zan yi masa rawar jiki da haba haba dan na samar masa da nutsuwlar bai gaza ba, ba kuma laifi ba ne dan ya fita ya dawo bai samo wani abu ya kawo mini ba. Kullum sai na fa'da masa cinikin da nake yi da nake samun makudan k'udade na yi imani mafita Ubangiji ya kawo mana, domin ba ni ka'dai ba ce wacce ta iya lallai a garin Toro. Amma duk macen da ta tunbatsa, duk macen da ta isa ko ta kai ta kawo to kuwa wajena take yin k'unshi da kitso. Sannan mafi yawa basa ba ni adadin ku'dina sai sun yi mini k'ari.
Idan ya bu'de baki sai ya ce "Ko ke ce Zainab Shamsuna ai ba'a ce na zauna na nad'e k'afar wando ki yi mini komai ba. Ubangiji ya ce na ciyar da ke, na tufatar da ke gwargwadon k'arfina."
Na nisa na ce "Haka ne! To a maimakon ka dinga tayar da hankalinka, nima kana tayar mini da nawa. Mu yi wata ka'ida mana".
Ya zuba mini ido yana saurarona. Na ce "Ka dinga siyar da lalle da mahallabiya da salatip. Ni kuma sai na dinga siya a wajen ka. Pure water ma da nake siyar wa sai ya koma naka ne zan dinga siyar maka".
Ya ce na yarda zan siyar da lalle amma ba zan siyar da ruwa ba tunda ai fridge din ba nawa ba ne".
Na ri'ke hannunsa na ce "Ashe kayana ba naka ba ne? Rannan a kunne na wata cikin y'anuwana take ta fa'din matu'kar mace da namiji igiyar aure ta zarge su ai komai da suke da shi ya zama mallakin junansu. Ta kalli idona ta ce mussaman idan ta haifa masa y'ay'a to ba wani sauran iyaka a tsakanin abubuwan da suka mallaka."
Na nisa na ce "Kana nufin wannan yarfen da aka yi mini, ni da kai ba kamar sauran ma'aurata ba ne? Abuna ba naka ba ne. Kai ma abin ka ba nawa ba ne saboda ni ban haihu ba?"
Na fa'da da rawar murya.
Jikinsa ya yi sanyi ya janyo ni jikinsa ya ce "Kina dai son ki yi mini rikici ne little ban da haka menene abin kuka? Duka ma shekarar ki nawa ne? Ni fa a halin da nake ciki ma ban shirya karban bebi ba. Hidimar ki ka'dai tana gagarata ina kuma da jariririn da bai san babu ba. Amma idan haihuwar ta zo ina so, kawai dai zan so ace bebinmu sun zo a lokacin da komai ya dai-daita mini ta yadda zan musu hidima sosai".
Na yi shiru na ce "Ka sare da yawa ne. Amma da sannu Allah zai kawo mafita."
Ya saki gauron numfashi ya ce "Ai al'amuran k'asar ne ya lalace komai sai da hanya, hanyar ma sai ka biya makudan k'udade kafin ka samu aikin gwamnati."
Na ce "Idan Allah ya k'addara abu rabon bawa ne komin tsanani sai ya same shi".
Da haka na lallaba shi na samu kwanciyar hankali, domin ni rashin ku'dinsa baya damuna irin idan ya takure ya k'i sukuni. Nafi son soyayya, nafi son walwala. Bana kuma samun hakan sai idan yana kawo wani abu, domin ya riga ya k'yamaci ace ni ce nake ciyar da mu.
Washagari da wuri ya fita.
Bai dawo ba sai yamma lis. Wani abun mamaki da buhun sabon lalle irin mai L din nan ya dawo har buhu uku amma d'anye ne.
Na kalle shi na ga ya yi laga laga.
Tabbacin da kansa ya shiga jeji ya samo.
Tausayinsa ya yi matu'kar kama ni.
Hawaye ya cika mini ido, a zuciyata sai addu'a nake yi masa akan Ubangiji ya hore masa hanyar da zai ri'ke gidansa cikin sau'ki.
Da k'yar na ha'diye kukan nawa na dinga yi masa sannu. Ya zauna akan baranda ya ce "Asiya na gaji sosai ga k'aya ta yi ta suka na."
Da tausayi na ce "Sannu, Ubangiji
ya baka lada, ya kuma sanya wa neman ka albarka."
Na dauko masa ruwa ya sha. Na kalle shi ya yi kaca kaca da shi. Har kan gashinsa k'ura ne.
Na ce "Bari na juyo maka ruwa wanka ga shi akan gawayi.
Da kai ya amsa mini.
Na sirka ruwan na kai masa bandaki.
Ya shiga ya yi. Ya fito ya jika kayan da ya cire. Sannan ya shiga daki dan ya shirya.
Kafin nan kuwa na Kai masa abinci falo.
Na zuba omo na sab'e masa kayan na shanya masa.
Ya fito ya ga ina shanya. Ya murmusa ya ce "Ni ina ce Asiya Toro ce ta ce Aji dawun ta yiwa k'ato wanki?"
Kunya ta kama ni domin na sani tsokana ta ya yi, tare da tuna mini sababin da nake yiwa Nasiba idan tana yi masa wanki.
Na dara na ce "Ai har yanzu ma ba zan yi ba, kawai na yi maka ne a matsayinka na mijina kuma bebina".
Ya shiga falon yana ce wa "zo mu yi maganar a zaune".
Yana cin abinci ina masa fifita. Ya ce "Da wayo da wayo dai so kike ki dinga ce mini Bebi ko?"
Na yi gajeriyar dariya na ce "A a ai sunan ka yana zuciyata lokacin kawai nake jira. Amma kai kanka ai kasan bebi ne. Domin abin da kake yi mini ai bebis ne suke yin hakan. Ba dama ka kwanta sai ina kusa da kai. Ko juyi zan yi sai dai mu juya kwanciyar gaba'daya, saboda kana.." sai na kasa fa'da.
Ya zuba mini ido ya ce "Fadi mana marar kunya. Me nake yi? Na daure na ce zuke wa bebis din da zan haifa mana abinsu."
Ya murmusa ya ce "Ai ba nasu ba ne, nawa ne, idan sun zo dai zan dinga sammu su, idan lokacin shansu ya k'are za'a cire su, su bar mini kayana. Ni ai ba zaki taba yaye ni ba".
Na yi dariya na kawar da maganar da ce wa "Wai da kanka ka je yago lallen ne?"
Ya ce "Eh. Baban Marina na tambaya ko ina zan dinga samun lalle ina sara. Sai ya kwatanta mini yankin da Ubangiji ya azurta da lalle. D'an na goro ake bawa digacin yankin sai ka je ka yi ta yanka.
Shine ma ya bani dubu guda duk da shima fama yake da kansa. Da naki karba kin ga b'acin ran da ya yi?
Wai raina shi na yi, shi yasa nake ganin ba zai iya bani abu na kar'ba ba.
Nasa hannu biyu na kar'ba ina ba shi ha'kuri, shi kuma yana ta yi mini fararen addu'oin da suka k'arfafa mini guiwa.".
Na rausayar da kai na ce "Allah ya bada sa'a, yasa a fara a sa'a".
Ya amsa da "Ameen Little".
Kwanaki ka'dan lallensa ya bushe. Da kansa ya zauna ya gyara abinsa tsab. Ya ha'de su a buhu biyu.
Ya fita da su, ni dai bansan inda ya kai ba sai gani na yi ya dawo da shi ya zama gari mai laushi ainun, kuma ya yi auki domin ba k'aramin yawa ne da shi ba. Ya kusa yin buhu guda.
Ganin hakan sai na auni kwano biyu na zauna na k'ulle shi tas. D'aurin hamsin, da d'ari. Duk wanda suka zo k'unshi sai na yi musu tallan ina sayar da lalle, ina k'wabawa mutum yasa a gidansa.
Nan ma sai Ubangiji ya sanya albarka domin duk sati sai na k'ulla kwano biyu, nima kuma a satin ina k'arar da fin kwano uku ma.
Kafin ka ce miye wannan sai jarin Tijjani ya kafu ya samu na siyo mahallabiya da kwalin salatip.
Duk sati kuwa zai je ya yago domin ya gamsu ba k'aramin rufin asiri hakan ya yi masa ba.
Tunda duk sati zan ha'da masa ku'dinsa a kalla dubu goma. Idan ya kar'ba kuwa zai siyo kayan abinci da k'ananun abubuwa. Maganar ku'din cefane kuwa da ku'din pure water muke yi. Duk da hakan nawa yana shiga amma ba mai yawa ba ne. A hakan kuma bai fasa fita ya yi sana'a ba idan ya samu.
Hankalinmu a kwance yake, mun samu rufin asiri. Tunda ya samu ya biya ku'din gidan amma na watanni shida, rabin shekara. Duk nacin ya kar'ba ya biya na shekarar sai ya biya ni a hankali bai yarda ba.
Da na matsa ma sai ce mini ya yi "Allah ya karbi ransa kafin ya ga ranar da zan biya masa ku'din hayar gidan da zai kwana."
Daga haka na ja bakina na tsuke.
Muna cikin wannan rayuwar mai da'di domin dukkanmu mun gamsu da kokarin junanmu. Na