Showing 1 words to 3000 words out of 307403 words
Chapter 1 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
[3/19, 2:56 PM] *💋Boss Bature💋*
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
Zagayeta su kayi gaba ɗayansu,su jahad na ambatar sunanta,fawan ne ya ɗauko masu ruwa a fridge ya dawo ya miƙa ma uncle ɗinsu,kar6a yayi tare da buɗe murfin ya ɗebo ruwan hannunshi nata kerma ya watsa mata shi a fuskarta,nan take ta farka tana faman yin atishawa,Alhamdulillah suka shiga faɗi suna kallonta,yunkurawa tayi ta tashi daga zaune tana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ta mayar da idanunta akan Su hosana da jahad da suka zuba mata ido,
Muryarta na rawa tace"jaj..jahad hos...sana...ku ne?ko dae idona ne ke nuna mun ba dai dai ba?
Ba ƙaramin farin ciki ne ya lullu6esu ba sehrish ta dawo cikin hayyacinta ta gane su,atare suka faɗa jikinta suka rungume juna suna kuka,
Murmushi kawai Abusufyan ke saki bashi kaɗae ba ma fuskar kowannansu na ɗauke da murmushi,musamman Abbansu junaid farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,haka hajiya azeemarsu har cewa take yi"yanzu nan waɗannan ƴan ukun duka namu ne?ƴa'ƴan mu ne?Allah abun godiya,yau dole in yi nafilar dare don miƙa godiyata ga Allah S.W.A daya nuna mun ƴa'ƴan abusufyan ɗinmu da ranmu kuma da lafiyarmu,Ashe dae da rabon yara suga danginsu,bayin Allah sun sha wahalar rayuwa,amma bakomai har yanzu lokaci bai ƙure mana ba,zamu nuna maku soyayyar da baku samu ba arayuwarku,Zamu baku duk wani jin daɗi na duniya da kuka rasa,zamu gatanta ku,sai mun cika ku da farin cikin da zaisa ku manta duk wani ƙunci da kuka ta6a fuskanta arayuwarku,waɗanda kuma sukayi silar jefa rayuwarku cikin hatsari tabbas sai sun ɗanɗani kuɗarsu sai sunji dama ba'a halicce su cikin duniyar nan ba,
Abbansu junaid ya kar6e da cewa"Ae daga rana irin ta yau su fara ƙirgen kwanakin mutuwarsu,saboda ƙarshen su yazo,sun tabka babban kuskuren ta6a jinin SALAHUDDEEEN HUSSEIN!Wallahi thumma tallahi ɗaya daga cikinsu bazai sha ba!' ranshi amatuƙar 6ace yayi maganar,
Abbas yace"Abba ina ganin yakamata yaran nan suje su kwanta dare yayi sosai,suna buƙatar hutu,in yaso koma menene gobe zamu ida tattauna akai,'
Jinjina kai Abbansu yayi tare da mayar da idanunshi kansu sehrish dake manne da juna suna kuka,
Gyaran murya ya ɗan yi masu,atare suka ɗago suna kallonshi da idanunsu dake zubar da hawaye,
"Kuyi kuka yara bazan hanaku ba,dole kuyi kuka domin kuwa an cuci rayuwarku,an zalunce ku,an ƙuntata maku,an rabaku da mahaifinku na asali kuma an rabaku da danginku,duk akan laifin da baku kuka aikata ba,saboda son zuciya irin na mutanan nan su rasa akan wa zasu ɗauki fansar su sae akan waɗannan bayin Allahn.... 'Shiru ya ɗanyi yana faman sauke ajiyar zuciya,
abusufyan na zuƙunne akusa dasu ya sunnar da kanshi ƙasa,hakanan ya dinga jin kunyar yaran yana ji aranshi tamkar duk shi ne silar jefa su cikin halin da suka shiga,
Su fawan kuwa dasu twins irfan jabeer da sauransu duk suna atsaye kowannansu jikinshi asanyaye kamar waɗanda aka zare ma lakka,lokaci guda sukaji tsananin Son yaran ya kamasu,
duk wannan abun dake faruwa gwaggon katsina,na zaune saman kujera tana ta faman matsar kwalla,har lokacin bata daina tsinar dangin Sayyadi ba,haris sai faman lallashinta yake yi tana buge mashi hannu tana faɗin"ka rabu dani Harisu!abun da ciwo wlh,Zuciyata tafarfasa takeyi,ƴa'ƴan abusufyan ɗina aka wulaƙanta kamar dabbobi?wlh bazan ta6a daina tsinewa Sayyadi ba,munafuki algungumi ɗan wuta,Ya Allah ka tsine ma sayyadi da duk zuriyarshi harda unguwar zomar da ta yanke mashi cibinshi, Ya Allah kayi mana maganinsu,Sayyadi ko ɗan iska,uwarshi ta haifa mana masifa....munafuki lokacin da yake zuwa wurin abu har ƙasa yake zukunnawa ya gaishe Ni,da wata guntuwar jallabiyarshi ta gado,ƙafafun nan nashi kaman shebur sanye cikin silifar ɗan ta shegiya...Muna yi mashi kallon Biri yana yi mana kallon ayaba.....'
sai faman sambatu takeyi abun ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,can kuma tace"Allah sarki abu,nasan yanzu ta gane cewa Allah ɗaya ne,yarinyar nan akwai taurin kai kamar kwallon goruba ga kafiya,kunnuwan nan nata kamar na Zoman daji falo falo dasu,ba irin jan kunnan da banyi mata ba,amma taƙi ji na,Ae ga irinta nan yanzu majnun ya koya mata hankali yanzu tana can Saman bola tana sambatu baiwar Allah,wama yasan uwa duniyar data shiga.......'
"Sehrish ku tashi ku tafi ɗaki ku kwanta,gobe zamu ƙarasa magana daku," Abbansu ne yayi maganar,
Miƙewa sukayi tsaye tare da yi masu sallama sannan suka wuce ɗakin nata,gaba ɗaya sehrish ta ɗan shiga ruɗu,batasan meya faru ba,amma bakomai yafi ɗaure mata kai ba face ganinsu hosana da jahad,taya akai suka San inda take har suka zo wurinta?abun kamar a mafarki take ganinshi,
Atare suka shiga cikin ɗakin,anan fa suka tsaya suna kallon juna fuskar kowaccen su ɗauke da tsantsar farin ciki mara misaltuwa,
"Sehrish Ashe da rabon zamu sake ganinki a duniyar nan"?jahad ce tayi maganar yayin da hawaye ke sauka a fuskarta,
ta ɗaura da cewa "Sehrish munyi kewarki sosai,munyi kukan rashinki atare damu,munsha wahala sosai,abubuwa marasa daɗi sun faru damu bayan rabuwar mu dake,amma duk wani hali da muka shiga hakan baisa mun manta dake ba sehrish kullum kina aranmu,koda yaushe muna cikin zullumin a wane hali kike?kina raye kuwa?kina jin daɗin rayuwarki?kina da ƙoshin lpy ko akasin hakan ....'
jin wannan maganar ta Jahad yasa ta fashe da kuka mai cin rai,janyota jahad tayi jikinta sosai ta rungumeta,itama hosana ta matsa tare da sanya hannayenta ta bayansu,suka haɗe su ukun,sun jima a wannan yanayin kafin daga bisani suka haye saman gadon su duka ukun suka zagaye junansu suna fuskantar juna a zaune
Sai lokacin sehrish ta buɗe bakinta tare da cewa"inaso ku faɗamun meya faru na daina samun wayar tsohuwa,sannan kuma inason jin yadda akai har ku ka san inda nake,nayi mamakin yadda na manta daku gaba ɗaya acikin rayuwata,nasan ban kyauta maku ba,Amma kuyi haƙuri ku yafe mun........'
ta ƙarasa maganar tare da kai hannunta ta shafo gefen fuskar hosana tana kallonta da idanunta waɗanda suka canza launi sosai,sai lokacin ta gane cewa ashe sune yaran da Marshal Omar ke ruƙo a wurinshi,rashin sani yafi dare duhu,har waya suka yi dasu jahad amma bata ganesu ba,saboda bata acikin hayyacinta,
Jahad ce ta kwashe dukkan abunda ya faru tun daga kan Jefa wayar tsohuwa da hosana tayi acikin Masai da kuma mutuwar tsohuwa,da kuma zamansu acikin cell,haɗuwarsu da Marshal Omar,zamansu a wurin gwaggon katsina da kuma rayuwarsu agidan Aunty babba,komai ta sanar mata,
Sosai sehrish tayi kuka tamkar ranta zai fita,har zazza6i saida ya lullu6eta nan take,bakomai yafi girgiza ta ba face mutuwar tsohuwa,da kuma zamansu hosana a gidan Aunty babba,abun ba ƙaramin ta6a zuciyarta yayi ba,wani irin ciwon kai ne ya rufar mata mai raɗaɗin gaske,rarrafawa tayi ta koma gefe guda saman bed mattress ɗin ta kwanta tare da janyo pillow ta rufe fuskarta dashi,Wurinta su jahad suka koma tare da kwantawa kusa da ita,kowanannsu na acikin yanayi,tabbas sunga rayuwa......
Daƙyar bacci 6arawo ya sace su,amma fa dukkansu babu wanda babu zazza6i ajikinshi,
Kowa fa ya manta da cikinshi saboda lamarin su hosana,a gidan babu wanda yaci abincin daren shi,saboda ƙunci da takaicin yadda rayuwar ƴa'ƴan uncle ɗinsu ta kasance,
Lokacin da Azmee ta turo ƙopar ɗakin nasu samun su tayi kwance suna bacci kowacce fuskarta ɗauke da hawaye,bacci sukeyi amma hawayen basu daina zuba daga idanunsu ba,ba ƙaramin tausayinsu taji ba,ta jima tana kallonsu kafin ta rufe masu ƙopar ta koma bedroom ɗinta,
Kwance yake asaman katafaren gadonshi,tunda ya dawo bedroom ɗinshi,ya shiga toilet yayi wanka,ya dawo ya kwanta yana tunanin duniya,juyi kawai yake yi asaman gadon bacci yaƙi ɗaukarshi,har lokacin zuciyarshi bata sauka ba,abun ya dame shi sosae,ya tsani zalunci arayuwarshi,ya tsani mugun mutun mai hali irin na dabbobi,tabbas idan har sayyadi ya bari ya shigo hannunshi sai ya ɗanɗani kuɗarshi,daga baya kuma ya dawo yana tunanin wai yanzu ƴar yarinyar nan da take yi mashi aiki,ashe ƴar uwarshi ce?jinin shi?ɗiyar Uncle ɗinsu?hakan na nufin cewa ita ƙanwarshi ce...?
"Wonders shall neva end'ya furta hakan tare da lumshe idanunshi,nan take kuma ya tuna da hoton da Uncle abusufyan ya basu lokacin da suke a U.s,hakan na nufin cewa Hoton yaran ne ya basu lokacin da suke ƙanana,zan tambayi uncle hoton wacece nai selecting acikinsu,as I promised then zan taimaketa da kuɗi ta sayi duk abunda takeso bazan fasa ba...... '
Wasu dae sunyi bacci a wannan daren yayin da wasu kuma Baccin ya ƙaurace ma idanunsu,a tsaye Abusufyan ya kwana idanunshi sun ƙanƙance saboda raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi,bawan Allah,wlh abunda ciwo,taya ma zai iya bacci?yasha kuka dae,ga wani irin Matsanancin ciwon kai da yake fama dashi,yawo yake ta yi acikin dakin yama rasa tunanin da zai yi yayin da tafin hannunshi na dama ke dafe da saitin zuciyarshi,wani irin bugawa takeyi mashi mara daɗi,
Yana cikin tsayuwar ne har aka kira sallar asuba bai ankare ba,sae da Yaji ana mashi knocking ƙopa,muryarshi ashaƙe yace"Wanene,"
"Ni ne"muryar Abban su junaid ce,
Hakan yasa shi cewa"ƙopar abuɗe take yaya ka shigo daga ciki,".
Tura ƙopar Abba yayi ya shiga ciki yana ganin Abusufyan atsaye yace"dama saida rai na ya bani cewar baka yi bacci ba abusufyan,'
Yayi maganar tare da ƙarasawa ya dafa kafaɗarshi yana kallon fuskarshi da hawaye suka wanke ta sharkaf,
Cikin sanyin murya yace"duk wanda yace maka kayi haƙuri tamkar ya cuce kane!amma ya zakayi abusufyan?dole haƙurin nan shi zakayi,nasan abun da ciwo,raɗaɗinshi na iya zarce na ƙunar wuta,abusufyan bazan ce kayi laifi ba,amma kasan cewa dole ne dama kaga badai dai ba!kayi aure batare da sanin mahaifiyarka ba,baka sanar mata ba balle tasanya albarka acikin auren naku,kunyi komai a6oye kai da gwaggon katsina,sai gashi yau Allah ya bayyana mana komai,nasan kai kanka kayi mamakin ganin Ƴa'ƴanka su duka ukun a ƙarƙashin kulawar gidan mu,kaɗan daga cikin Ikon Allah kenan!kwata kwata yaran basu san suna da dangi ba,garari kawai sukeyi a wulaƙance cikin gari,mu ma haka bamu son cewa akwai wasu ƴa'ƴa waɗanda suka kasance jinin mu ne su ba,babu wanda yasan haka,amma cikin ikon Allah da yake shi hakimun ne,sai gashi silar aikatau ɗaya ta faɗo hannunmu,yayin da silar ciwon ɗaya daga cikinsu da aka kai asibiti Allah ya ƙaddara haɗuwarsu da Omar yayin da shi kuma yaje wurin ɗan uwanshi Dr haris,lamarin ubangiji girma gare shi!gaba ɗaya Allah ya haɗa yaran a wurinmu ta hanyar da bamu ta6a tsammani ba,kamar yadda kai da gwaggon katsina baku yi tsammanin abunda kuka aikata asirrance zai tonu ba,tunda baku sanar mana ba sae gashi Allah ya sanar damu,su kansu yaran basu yi tsammanin zasu haɗu da dangin ubansu na asali ba,su dama basu da masaniya akan wanine ubansu......'
Dakatawa abba yayi da maganar yana kallon abusufyan dake ta faman shessheƙar kuka muryarshi na kerma ya shiga cewa"Ya Allah ka yafe mun kuskuren dana aikata na auren abu batare da sanin mahaifiyata ba da kuma dangina ba......tun farko nine silar jefa rayuwarsu Cikin halin da suka tsinci kansu,da ace ban 6oye ma kowa ba,duk da ammi bazata barni in auri abu ba amma ina da tabbacin cewar Abbanmu salahuddeen zai aura mun ita inna nasanar mashi,iyakaci dae Ammi zata zangwameta ne daga baya kuma nasan zata fara sonta,wlh ni sam tunanin hakan baizo mani ba a wannan lokacin,idona ya makance,kuma ba laifin gwaggon katsina bane,Son da takeyi mun ne yasa ta aikata hakan don ta faranta mun ganin halin da na shiga a lokacin jin cewar Mommynmu ba zata bari in auri abu ba,gashi na mutu akan sonta
kaicona.......'fashewa yayi da wani sabon kukan,dana sani kenan irin wadda ba'ason yinta,abun yayi ta maka ciwo azuciyarka,shiyasa kullum muke cewa Allah ya tsare mu daga aikata aikin danasani,saboda bai da daɗi,ɗaci gare shi,
Ba ƙaramin tausayi yaba Abba ba,tuni shima hawaye suka fara sauka akan fuskarshi,janyo abusufyan yayi ajikinshi sosai ya rungume shi yana lallashinshi,
A ƙarshe yace"Abusufyan ka manta da duk wani abu daya faru dazun,yanzu lokacin farin cikine,yakamata ka nuna godiyarka ga Allah subhanahu wata ala daya nuna maka wannan ranar da ya haɗaka da triplet ɗinka dukkansu da ransu kuma da lafiyarsu!wlh abusufyan dana ga yaran nan amatsayin ƴa'ƴanka kaɗan ya hana in buga tsalle saboda murna.....'yayi maganar yayin da suka raba jikinsu dana juna,
tallabo fuskarshi abba yayi cike da zolaya yace"Kasan me?
Abusufyan ya girgiza mashi kai alamar a'a,
Abba yace"nifa ɗazu dana ga ka firgita da ganin yarinyar nan nayi tunanin cewa ko ka ƙyasa ne,har ina cewa shikenan lokacin barin gwaurantakar abusufyan yayi aduniya ashe ashe uban ne gaba ɗaya........'
Ya ƙarasa maganar yana dariya,murmushi abusufyan ya ɗanyi,
Abba ya kuma cewa"Wai yanzu nan duk aikinka ne waɗannan abusufyan?ashe dae ƙanin nawa bana wasa bane...'
fashewa da dariya abusufyan yayi tare da sunnar da kanshi ƙasa,
Hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Abba ba,dama so yake ya sanyashi farin ciki don ya gusar mashi da damuwar da yake ciki,
dafa kaɗarshi abba ya kuma yi tare da cewa"duk haihuwata ya'ya goma sha takwas akan su jahan ne kawai na samu ƴan biyu,amma kai da yake mai sa'a ne,na ku ba irin namu bane sai gashi ka haifa mana ƴan uku reras!ko Ya ammi zata ji in taga ƴa'ƴan mara jin maganar nan nata abusufyan....nasan zata ce shegen bisa zai aika ae,
Wannan karan atare suka fashe da dariya,
Daga bisani Abusufyan yace"yaya hussein inaso naga yaran nan sosai,na damu dasu wlh....'
Wani irin kallon rainin wayau Abba yayi mashi kafin yace"yau naga ikon Allah!ni kake fadama kana son ganin ƴa'ƴanka?Yaran nan fa naka ne halak malak,ae ni nama yi tunanin a wurinsu zaka kwana,saboda suna buƙatarka sosai atare dasu,yanzu basu da burin daya wuce suga mahaifinsu atare dasu,"
Wani irin daɗi ne ya lullu6e abusufyan yace
"Zan iya zuwa wurinsu yanzu"?
Abba yace"Ka bari mu dawo daga masallaci inyaso kai tsaye kawai sai ka wuce wurinsu,"
Fuskar shi ɗauke da farin ciki yace"okey,bari naje nayi alwala,"
Abba yace"muna jiranka a main palour in ka kammala,ka same mu acan,"
Yana ƙarasa maganar tashi ya juya tare da nufar ƙopar ɗakin nashi ya fuce tare da tura masa ƙopar,
Toilet abusufyan ya shiga batare da 6ata lokaci ba,ya ɗauro alwalar,
Lokacin daya fito babban falon anan ya same su kowannansu ka kalla zakaga alamun damuwa a fuskokinsu,wasu ma da alama basuyi bacci ba,musamman Marshal Omar babu alamar yayi bacci adaren jiya,hatta Sgr ma akwai alamun rashin isasshen bacci atattare dashi,taya zaiyi bacci sayyadi na yawo acikin gari,shi fa in ya ƙullaci mutun irin haka har sai yaga bayanshi sannan yake samun kwanciyar hankali,su twins kuwa fuskokinsu sunyi jawur su da fawan,kowa dae da damuwa aranshi,
Bayan sun kammala haɗuwa suka wuce masallaci atare,
Tura ƙopar ɗakin nasu azmee tayi don ta tashe su sallar asuba,ba ƙaramin mamaki tayi ba,ganinsu ajere suna sallah,kowaccensu na sanye da dogon hijabi a jikinta hijjaban sehrish ne hosana da jahad suka sanya,abun ba ƙaramin burgeta yayi ba,dama indae suna tare su ukun,musamman in akace maka akwai jahad atare dasu tofa basa wasa da ibada,duk da itama Sehrish ɗin ba daga baya ba,amma jahad ɗin itace kan gaba,saboda ita ba'a tashinta sallar asuba da zarar anfara kiran sallar asuba duk nisan baccin da tayi zata farka ne da kanta,abun sama rai ne da kuma sabo da yi,da kuma imanin mutun,
*Murmushi kawai azmee ke saki tana kallonsu gwanin ban sha'awa,ƴa'ƴan abusufyan,jikokin Ammi da salahuddeeen,ƴa'ƴan ƙanin Abban sojoji Abusufyan,ƙanne ga Marshal Da Sgr duk su kaɗae,abun farin ciki abun murna!yanzu su sun zama abunso wlh,yayyansu gaba ɗaya sojoji har goma sha takwas,ko sauro ne yayi gigin Cixon fatar jikinsu sae yaji saukar alburushin bindiga asaman goshin shi* 🤣
Azmee na tsaye tana kallonsu taji alamun motsin mutun a bayanta,jin an dafa ta yasa tayi firgit ta ɗan juya,Hajiya azeema ce jikinta sanye da hijabi blue,hannunta ruƙe da carbi,fuskar nan ɗauke da murmushi tace"Nazo ganin ƴa'ƴanmu ne,idan ba damuwa ki bani hanya in wuce ciki,"
Murmushi azmee tayi tare da matsa mata hanya ta wuce ciki,sai da ta shiga ciki sannan azmee tabi bayanta tana cewa"sallah nazo in tashe su suyi,shi ne na same su ashe har sun tashi ma,abun ba ƙaramin burgeni yayi ba dana gansu ajere su ukun suna sallah,'
Murmushi hajiya azeema tayi ayayin da take zama daga gefen gadon su tace"Albishirinki,"tayi maganar tana kallon azmee,
Azmee tace"Goro,"
"Fari ko ja,"cike da zolaya tayi maganar,
"Fari dae,shi ne ke tare da alkhairi,wannan launin jan alamace ta hatsari,"
Dariya hajiya azeema tayi kafin tace"Tab jiya anyi babu ke!Labari da ɗumi ɗuminsa!zazzafan gaske....'
A ƙagare azmee tace"Meya faru"!
A lokacin su jahad sun sallame sallah,suna zaune saman dardumar suna sauraransu,
Nuna su hajiya azeema tayi tare da cewa"Ke wai ashe yaran nan ƴa'ƴan abusufyan ne!!!"
Gaban azmee ne ya faɗi Rasss!saboda yadda maganar ta dirar mata kai tsaye acikin kunnuwanta,
"Wai dagaske"?tayi tambayar cike da mamaki,
Hajiya azeema tace"hmmmm ke dae bari,wani iko sai ubangiji,dagaske fa nake,babu wanda baiyi mamakin wannan abun al'ajabin ba,yara dae ƴa'ƴan ƙaninmu ne sufyan,'
Juyawa azmee tayi tana kallonsu sehrish da sukayi zuru suna kallonsu musamman Sehrish da batasan kan zancen ba,saboda bata a hayyacinta lokacin da akayi maganar,amma lokacin da jahad ke bada labarin rayuwarsu taji komai a kunnanta kuma daga nan ne Sihirin jikinta ya lalace saboda tunaninta daya rinjayi kwalwarta harta tariyo dukkan abunda ya faru arayuwarsu ga kuma addu'ar da Sgr keta yi mata acikin kunne,
Cike da mamaki azmee tace"taya akai hakan ya faru?dama abusufyan ya ta6a aure ne kenan?
Ataƙaice azeema ta bata labarin yadda abusufyan ya auri abu batare da saninsu ba,har suka samu ƙaruwar ƴan uku,'
Wani irin farin cikine ya lullu6e azmee saboda tsabar farin ciki bakinta yaƙi rufuwa,
"Jahad!dagaske ne abunda kunne na ke jiyo mun"?sehrish ce tayi maganar tana kallon jahad da tsananin mamaki,
Murmushi jahad tayi ta jinjina mata kai alamar eh,ta ƙara da cewar"jiya duk baki a hayyacinki,abun farin cikin nan ya faru,Mun jima muna wahalar rayuwa ashe muna da dangi mai girma irin wannan bamu sani ba,cikin ikon Allah kuma sai gashi Allah ya haɗa mu dasu ta hanyar da bamuyi tsammani ba,ina tunanin addu'ar da muka jima munayi ne Allah ya kar6a mana,Ashe oumman mu sai da ta fara auren uncle ɗin su abusufyan sannan ta auri wannan fasiƙin mutumin sayyadi,da cikinmu ta shiga gidan shi........'
Aruɗe sehrish tace"taya hakan zai yiwu?
Hajiya azeema ce ta katse ta da cewar tabbas zancenta gaskiya ne sehrish!ku ƴa'ƴan ƙaninmu ne Abusufyan,sai da ya fara auren mahaifiyarku sannan Mugun mutumin nan daya ƙuntata rayuwarku ya aureta.......'gaba ɗaya hajiya azeema ta kwashe labarin rayuwar mahaifiyarsu