Showing 189001 words to 192000 words out of 307403 words

Chapter 64 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

agabanta"ina sauraronki Aunty,"
  "Yawwa inaso ki natsu ki saurare ni,nasan kina jin tsoron Sgr sosai,saboda yanayinsa,Yawan ɗaure fuska,rashin fara'a da sauransu,wannan tsoron shi nake so ki cire!
  Ɗan waro ido sehrish tayi hankalinta atashe tace"Aunty,taya zan daina jin shakkarshi"?
  "Na farko dai mutunne kamarki,ba aljani ba,dole sai kin cire kunya idan har kina so kija ra'ayinshi agare ki,har yanzu fa Sgr baisan so ba,sha'awarki kawai yake yi shiyasa ya fara kulaki,koda ace ma yana sonki bazai iya gane hakan ba,har sai kin koyar dashi,"
  "Amma Aunty taya zan iya koyar dashi soyayya"?muryarta sanyaye tayi maganar
  "Yanzu Sgr ya fara sha'awarki,bazaiyi wasa dake ba,zaki ga canji atattare dashi,zai fara baki kulawa ta musamman kuma zai damu dake,ba don komai ba sai don saboda yasan cewa ta wurinki ne kawai zai samu natsuwa aduk lokacin da desire dinshi ta motsa,zai dinga tarairayarki ne yana baki kulawa sosae,ko tari kika yi zai tambayeki lafiya?Sanin cewa in fa baki da ƙoshin lafiya,abun zai shafe shi ne shiyasa zai dinga tambayarki da zarar yaga canji atattare dake,daga yanzu inaso ki lura dakyau ki gano wurin da yafi ra'ayin ta6awa ajikinki,saboda ta hakanne zaki gane lagwansa,sannan a duk lokacin da zaki je part ɗinshi,ki dinga ɗaukar wanka kuma kada ki dinga sanya manyan kaya irin atampa ko shadda wannan sai za'aje unguwa,ko cikin gida,ki dinga sanya kayan da zasu bayyana surar jikinki,Yadda zai dinga ganin komai Zahiran har ya gaza samun kwanciyar hankali,amma fa idan zaki sanya kalar wannan kayan ki tabbatar da kin sanya hijab ajikinki saboda akwai maza agidan,daga baya idan kinje part ɗinshi sai ki cire kina jina ko"?
  "Eh,"ta amsa mata,
"Yawwa,nasan dai basai na ƙara tunasar dake ba,game da tsafta duk kina yin wannan,Amma shagwa6a fa kin ta6a jaraba yi mashi...."tunkan ta ƙarasa maganar,Sehrish ta 6a66ake da dariya,
  Hajiya azeema tace"Allah kuwa,bafa wasa nake yi maki ba,shagwa6a tana ɗaya daga cikin abunda ke jan hankalin ɗa namiji zuwa ga mace,da kuma salon magana,da tafiya,da sauransu,"
  "Aunty azeema shagwa6a fa kika ce,babban yaya zan yiwa shagwa6a aikuwa da rabon insha Mari,"daƙyar ta ƙarasa maganar saboda dariyar data zo mata,
  Itama azeema dariyar take yi,sai da suka tsagaita da yin dariyar tukunna tace"Don kina jin tsoranshi ne shiyasa kike jin wani banbarakwai,ai ba wani abu bane,ko da yake kufa Majority ɗinku kunya ke hanaku nunawa miji soyayya,ba zaku iya sakin jiki ku nuna ma miji Soyayya ba,ga kuma girman kai,duk da nasan ke baki da wannam girman kan,kunyar dai ce kawai da kuma tsoro,'
  Murmushi kawai Sehrish keyi tana sauraronta,aranta kuwa tana aayyana abunda zai faru idan tayi kuskuren yi ma Sgr shagwa6a,
   "Ki ƙaddara cewa,Sgr jinjiri ne aka baki shi don ki kula da rayuwarshi,komai kece zaki koya mashi,kamar soyayya da bai iyaba zaki iya koya Mashi,duk abunda kika saba mashi,to shima ko bai iyaba zai fara kwatanta yi maki ne,"sosai Aunty azeema ta shiga koyar da ita,Yadda zata jawo hankalin Sgr,suna cikin magana ta wurga idonta kan Wall Clock,sam ta manta bata kai mashi breakfast ɗinshi ba,"
  Aruɗe tace"Aunty azeema,na manta ban kai mashi breakfast ɗinshi ba"
  "Okey,ki kwantar da hankalinki pls,Zamuyi Magana anjima,"
. sallama Su kayi da ita,jiki na rawa Sehrish ta koma gaban mirror,janbaki ta ɗauko red colour ta murza ma la66anta suka ciza sosai,turarenta ta ɗauka ta feshe jikinta dashi,
  Komawa tayi gaban wardrobe ta ɗauko babban mayafi ta lullu6e jikinta dashi tun daga saman kanta,

High heels ta sanya a ƙafarta launin rigar jikinta,ƙarasawa tayi tare da buɗe ƙopar ɗakin ta fito,tun kafin ta ƙarasa fitowa daga cikin corridor ɗin ta soma jin sautin ƙarar Cokula,alamar abinci suke ci,

Kamar karta fito haka ta dinga ji,batasan taya zata nufi part ɗinshi ba,ga mutane a dining area kuma dole ne in zata gifta sai sun ganta har ma su nemi jin ba'asin rashin fitowarta cin abincin,

Daƙyar ta ɗaure,ta nufi dining ɗin kaitsaye,tun kafin ta isa sautin takalmanta yaja hankalinsu,gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta
  "Daugher!dama idonki biyu?amma shi ne baki fito kin ci abinci ba"?Abusufyan ne yayi maganar,
  "Ni nayi tunanin ma ko bacci takeyi shiyasa banyi magana ba,"acewar Abba,wanda ya tasa plate ɗin abinci agabanshi sam ya kasa cin abinci,har yanzu kewar junaid ke ɗawainiya dashi,
  "Ina kwananku,"ta gaisar dasu cikin girmamawa atare suka amsa mata,
  Duka matasan gidan nan suka hallara,dogon table ɗin mai mazaunin mutun 12,anan Abbansu yake tare da Mommynsu,Fawan,Irfan, Jabeer,Khaleed,sai kanal Yousouf tare dasu Talal,Najeeb da twins,

Ɗayan table ɗin kuma mai mazaunin mutun 6,Oummansu ce tare da Abusufyan sai su Jahad da Hosana,idan ka kalli fuskokin matasan gidan sai sun baka tausayi,don kuwa kamar anyi masu dole don suci abinci,musamman fawan jujjuya cokalin hannunshi kawai yake yi,har yau ya hana kanshi jin daɗi duk don saboda Junaid,

"Samu wuri ki zauna mana"Mommynsu Junaid ce tayi mata magana ganin ta tsaya atsaye kiƙam,
  Sunkuyar da kanta ƙasa tayi,tana wasa da yatsun hannunta sam taƙi motsawa,
  "Ki zauna mana baki ji ana magana ba"Abusufyan ne ya tunasar da ita,
  Tafiya ta soma yi zata zagaya ta zauna,
  "Ina azmee take ne?naga yau tunda ta jera abinci,bata fito tayi serving ɗinmu ba kamar yadda ta saba,kodai bata lafiya ne"Abba ne yayi maganar cike da son jin ƙarin bayani daga wurinsu
Abusufyan yace"Nima tun ɗazu na lura bata a wurin nan,yakamata a dubo ta aji ko lafiya,"
"Bari naje na kirata,"Ko sauraron amsarsu batayi ba,dama so take ta gudu daga Dining area ɗin,
  Gudu gudu sauri sauri ta nufi corridor ɗin ɗakinsu,a ƙopar ɗakin azmee ta tsaya tare da sanya hannu ta kwankwasa ƙopar,kusan sau uku tana buga ƙopar,ana ƙarshe ne tajiyo muryar azmee daga cikin ɗakin tana tambayar wanene,
  "Sehrish ce Aunty azmee,su daddy ne ke nemanki,Sun ji shiru shi ne suka ce a kirawo ki,"
  "Okey,gani nan zuwa,bana jin daɗi ne,"
  Tsayawa sehrish tayi a bakin ƙopar ɗakin har saida azmee ta fito jikinta sanye da hijabi,
  "Aunty azmee ya jikin naki"?
Daƙyar ta iya buɗe baki"da sauki,ciwon kai ne,kuma nasha magani,"
  "Allah ya ƙaro sauki Aunty azmee,"ta ƙarasa maganar tare da ruko hannun azmee cikin nata,suka kama hanyar zuwa dining ɗin atare,

Lokacin da suka ƙaraso dining area ɗin,hankalin kowa ya dawo kansu,
"Oumma ga Aunty azmee nan,kallatta ki gani,itace muke baki labarinta jiya mai girka mana abinci"a wani slow abu ta wurga eyeballs ɗinta akan fuskar Azmee,karaf idanuwansu suka shiga cikin na juna,Zumbur abu ta miƙe tsaye tana kallonta,kallon kamar nasanki,Itama Azmeen kallon Sani take yi mata,
  Ganin sun ƙurawa juna ido,babu mai magana acikinsu,yasa Abusufyan tanka masu"Ko kunsan juna ne"?
  Girgiza kai abu tayi"a'a gani nake yi kamar na santa ne,tayi mun kama da wata dana ta6a sani arayuwata,Amma bazan iya tunawa ba,
  "Aunty azmee kefa?kinsan Oumma ne"?Sehrish ce tayi mata tambayar,girgiza kai azmeen tayi"A'a nima dai kallon sani nake yi mata,kamar na ta6a sanin wata mai irin fuskarta,amma dai ba ita bace ba,sunyi kama ne"
  Murmushi sehrish ta ɗan saki tare da cewa,"tunda baku san juna ba,bari na gabatar da kowannanku,"
  "Aunty Azmee wannan itace Oummanmu,mahaifiyarmu,"
  Sannan ta nuna Azmee"Oumma ga Aunty azmeen da muke baki labarinta jiya,ba iya girki kaɗai ta iya ba,tana da kyakkyawar zuciya,mutuniyar kirki ce ita,"
  Murmushi abu ta saki tare da miƙa ma azmee hannu suka gaisa da juna,kowa fuskarshi ɗauke da murmushi,

Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke,ganin hankalin kowa ya koma kansu yasa tayi saurin lalla6awa ta wuce kitchen,shaf shaf ta shiga haɗa mashi breakfast ɗinshi,

"Sehrish ta faɗamun irin halarcin da kikayi mata,bansan da wasu kalmomi zanyi amfani dasu ba wurin gode maki,Allah ne kaɗai zai iya saka maki"
  Murmushi Azmee tayi"Ae duk yiwa kaine,na dauki sehrish tamkar ƴar cikina,"dakatawa ta ɗan yi da yin maganar,ta mayar da idonta kan Abusufyan"ina tayaka murna sosai,Allah ya ƙara haɗa kan zuri'arku,"addu'o'i ta shiga yi masu suna amsa mata da Ameen,kafin daga bisani Abba yace"Samu wuri ki zauna,Ke ma Azmee daga yanzu bana so kina wannan tsayuwar,don yanzu kinfi ƙarfin ƴar aiki a wurinmu,pls kada kiyi mun musu kamar yadda kika saba,"
Murmushi Azmee tayi tare da samun wuri a table ɗinsu Abusufyan ta zauna,Abu ma ta zauna,a tsanake kowa yake cin abincinshi,Abunda zai ɗaure maka kai,ya baka mamaki shine duk bayan ƴan mintina sai abu ta saci kallon Azmee,da alama dai tasanta ne,kuma tana ƙoƙarin tuna wurin da suka ta6a haɗuwa,itama Azmeen satar kallon nata take yi,kowa da abunda yake sakawa aranshi,
Fitowa tayi daga cikin kitchen ɗin hannunta ruƙe da ƙayataccen tray,hannu bibbiyu ta ruƙo shi,cikin sanɗa ta wuce upstairs,direct ta nufi part ɗin Sgr,a bakin ƙopar shiga falon ta tsaya sallama tayi jin shiru ba'a amsa mata ba,yasa ta wuce ciki izuwa bedroom ɗinshi,tana ƙoƙarin shiga,tajiyo maganganunsu shi da Omar,kasa kunne tayi tana sauraronsu,
  "Yanzu ya zamuyi?duk mun jefa kanmu cikin haɗari,idan har Abba yasan cewa ƙaryane ba kidnapping ɗin su Junaid akayi ba daga ranar zai ƙullace mu aranshi,kuma girmanmu zai faɗi agaban ƙannenmu ne,nayi regretting wlh,"Omar ne yayi maganar,a yayin da yake zaune gefen gadon,
  "Omar,nima ina danasanin yin hakan,na shiga damuwa sosai,bansan ya zamu yi ba,remain just one week and some days,daddy tare dasu fawan jiranmu kawai suke yi mu kawo masu Junaid"yayi maganar ne yayin da yake tsaye gaban mirror yana gyara jikinshi dake sanye da Bathrobe,ga danshi danshin ruwa da alama bai jima da fitowa wanka ba,
  Kowanne fuskarshi akwai tarin damuwa,abun ya tsaya masu aransu,
  Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,
  "Assalamu alaikum,"jin muryarta yasa suka tsagaita da yin firartasu,
   "Who's there"Sgr ne yayi tambayar
  "Sehrish ce,breakfast ne na kawo maka"
  Murmushi Omar ya fara saki,yana kallonshi,harara Sgr ya ɗan wurga mashi,
  Miƙewa Omar din yayi"kar na takura maka,bari na baka wuri,idan Mun haɗu zamuyi magana,"bai tanka mashi ba,Ya nufi hanyar fita daga ɗakin,
  Sehrish na ganinshi tayi saurin gaisar dashi"Ina kwana ya Omar,"
  Fuskarshi ɗauka da fara'a ya amsa mata"Lafiya lou,ina fata kema haka". 
  "Ina lafiya,"daga haka ya matsa mata hanya ta wuce ciki,Shi kuma ya fuce daga ɗakin,

A hankali take tafiya ta cikin mirror yake ƙare mata kallo,A saman table ta ajiye mashi tray ɗin,sannan ta ɗan juya tare da kallon bayanshi,gaisar dashi tayi"Gm ya Rafayet,ka tashi lafiya,"shiru bai amsa mata ba,kamar bashi bane ya gama magana yanzu tare da Omar,

Juyawa tayi saɗaf saɗaf zata bar bedroom ɗin nashi,
  "Where are u going?kin kammala aikin ki ne?"
   "A'a,naga kamar kana shiri ne,Zan jira a falo,idan ka kammala zan shigo daga ciki in yi aikin,"
  A wani slow ya juyo tare da kallonta,adai dai lokacin itama ta waiwayo shi,
   Har sai da gabanta ya faɗi lokacin da idanuwansu suka haɗu cikin na juna,
  Da hannu yayi mata alamar ta dawo,kamar wadda aka zarewa laka,haka ta dawo daga ciki duk tasha jinin jikinta,ƙoƙarin gyara Mashi bedroom ɗin ta shiga yi,kamar daga sama taji ya cire mata mayafin jikinta,da sauri ta juya tana kallonshi
   "Taya zaki ji daɗin yi mun aiki da wannan abun a jikinki"?
  Shiru tayi batace komai ba,Sae ƴan kame kame takeyi,
   Jefa mata shi yayi asaman bayanta,"ki san inda zaki ajiye shi,"
  Ruƙo mayafin tayi tare da ɗaure ɗamararta dashi kamar yadda ta saba yi,mayar da hankalinta tayi wurin gyara mashi gadon,
  Cike da tsantsan sha'awarta yake bin jikinta da kallo,bai ta6a sanin kyawun launin ja ba sai da yayi arba da rigar jikin Sehrish wadda ta kasance Red colour,ga shi hannu ɗaya gareta,Soft skin ɗin bayanta mai matukar jan hankali sai fisgarshi takeyi izuwa gare ta,

Tana cikin gyaran taji motsinshi a bayanta,A firgice ta juya karaf suka haɗa idanu,Zazzare mashi kyawawan idanuwanta ta shiga yi,farare ƙyal dasu masu ɗauke da kwayar ido brown colour,ja da bayan da take ƙoƙarin yi ne yasa ta kusa faɗawa saman gadonshi saboda ta ƙure mashi,da sauri ya cafko Waist ɗinta da hannu ɗaya ya janyota izuwa jikinshi,gaba ɗaya yayi hugging ɗinta so tightly,ta ko'ina ƙamshin turarenta neman yi mashi illa yake yi yana ƙoƙarin Zautar dashi,natsuwa Sehrish tayi yayin da kanta ke kwance luff asaman faffaɗan ƙirjinshi,wannan daddaɗan ƙamshin turaren nashi ne ke dakar hancinta,Gaba ɗaya jikinta ya mace,
  Moving hands ɗinshi yayi tun daga kan Ass ɗinta ya tarboshi,ya jinjina girman hips ɗinta,slowly yayi sama da hannun zuwa cikin sumar kanta,sosai ya shiga murza gashin da yatsun hannunshi,tamkar yana yi mata susa haka ta dinga ji,ga wani irin daɗi mara misaltuwa,almost 5 mins ya rabata da jikinshi,Yayin da idanuwansu ke kallon cikin na juna kamar masu jin bacci,dawo da hannun nashi yayi saman Hips ɗinta tare da pulling ɗinta ya haɗe gabansu sosai,Ji yake tamkar kawai ya aiwatar da abunda zuciyarshi ke raya mashi,but this is not the right time da yake son wannan abun ya kasance,
"Meyasa baki gaishe ni ba"?da wata irin kasalalliyar murya yayi maganar,
   Muryarta na kerma tace"wlh na gaishe da kai,tunda na shigo,"
   "Haka ake gaisuwa?"?
  Abun nashi ya fara ɗaure mata kai,
   Cigaba da magana yayi"Ni ba haka nake son ana gaishe dani ba,a kowani lokaci idan kika zo part ɗina,lemme teach u.."moving face ɗinshi yayi izuwa gefen fuskarta,Ya manna mata kiss,side by side na fuskarta,slowly ya dawo da sweet lips ɗinshi saman nata soft lips ɗin ya haɗesu wuri guda,kissing ɗinta ya fara yi,da niyyar ya koyar da ita yadda yake son ta dinga gaisar dashi,Boss man ɗin sai gashi ya fara Hawa kan Network,sosai ya matseta ajikinshi,A susuce ya shiga sucking lips ɗinta,Mayar mashi da martani ta shiga yi hakan yasa shi ƙara zaucewa,gaba daya ya sabeta izuwa saman gadonshi ya kwantar da ita,yabi kayansa ya turmushe,Zage zip ɗin rigarta ya fara yi,ƙankame hannunshi tayi saboda bata kaiga fita hayyacinta ba,kuma ta jiyo motsin mutun a falo,a rude yake faɗin"feed me pls,i really need it,"hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,ya zauce gashi wani yana tunkaro ɗakin,
   Girgiza mashi kai ta shiga yi tana faɗin"Akwai mutun a falo,bazan iya ba,"
   "I don't care,just feed me,ƙoƙarin sabule mata rigar jikinta yake yi,don ya samu yasha ko ya kore kishin ruwan da yake ji,don maƙoshin shi a bushe yake,
   "Rafayet"!muryar Abbansu ce ta karaɗe kunnuwansu,jiki na rawa Sehrish ta janye jikinta daga nashi,A hanzarce ta diro daga saman gadon ta faɗa bayan labule ta 6oye,tana faman sauke ajiyar zuciya,
  Kasa amsa mashi kiran nashi yayi numfashin shi na fita da wani irin huci huci,yayi Uban goho asaman gadon,Sumar kanshi duk ta rufe mashi fuskarshi,
  Shigowa cikin bedroom ɗin Abba yayi,yana kallonshi cike da mamaki yace"Rafayet baka da lafiya ne"?
  Daƙyar ya iya motsa lips ɗinshi"Am ok,"
  Ƙarasa shiga cikin ɗakin Abbansu yayi tare da samun wuri ya zauna daga gefen gadon yana ƙare mashi kallo,Yaƙi yadda ya ɗago da kanshi,gudun kada Abbansu ya gano shi,Don kallo guda zai yi mashi ya shaida cewa wani abu ke faruwa,ga janbakin sehrish daya 6ata mashi chest ɗinshi,
   "Rafayet,inason magana da kai game da Junaid,na kasa cin abinci ko isasshen bacci bana samu,Raina yana bani cewa kamar bazai dawo ba,idan har akwai abunda kuke 6oye mun kaida Omar dan Allah ku sanar dani,Don in fidda rai da dawowarshi,"
  Gyara bathrobe ɗin jikinshi yayi,ya ɗaure igiyoyin jikinta,sai da ya fara daidaita natsuwarshi sannan ya miƙe daga zaune ya zuro da ƙafafunshi ƙasa,kallon juna su kayi shi da Abbansu,hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba,Ganin hawaye asaman fuskar Abbansu,
  "Daddy,don Allah kadaina zubar da hawayenka,before end of this month,in sha Allah daddy,zan sanar dakai komai,"
  "Har yaushe ne zaku cigaba da samun ran dawowarshi?Idan mutuwa yayi ku sanar dani mana,na fara zargin hakan acikin raina,da ace kidnapping ɗin Junaid akayi dagaske,Even one day bazaku bari yayi ba,batare da kun dawo dashi cikin gidan nan ba,Amma almost 3 Weeks Junaid baya a gidan nan?kullum ƙara samana ran dawowarshi kuke yi"miƙewa yayi daga tsaye jikinshi na kerma ya soma tafiya daƙyar yake iya tafiya,har sai da yakai bakin ƙopar sannan ya dakata da yin maganar ya juyo tare da kallonshi har lokacin bai motsa ba daga zaunen da yake,
   Cikin sanyin murya ya Ambaci sunanshi"RAFAYET"
"Na'am Abba,"ya furta hakan yayin da yake kallonshi,jikinshi ya gama yin sanyi,
  "In cigaba da sa ran dawowarshi ne?ko in fidda rai,"shiru Sgr yayi batare daya tanka mashi ba,Nazarin maganar shi ya shiga yi,muddin yace mashi ya fidda rai,to tabbas zai fahimci cewa Junaid ya mutu ne,
  Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yace"Am really sorry Abba,dan Allah ka bani time,zan baka amsar tambayarka,Amma ba yanzu ba,akwai wani investigation da nakeyi,Zan sanar dakai komai,"
  Gyaɗa kanshi yayi tare da kama hanya ya fita daga cikin ɗakin,Yana juyo muryarshi yana fadin"Zan cigaba dasa rai,"
  Sun jefa kansu cikin tsaka mai wuya,kifa kanshi yayi A saman mattress ɗin,
  Sehrish dake la6e abayan curtains ɗin sai faman shessheƙar kuka takeyi,tausayinsu ne ya kamata,ta jima tana kuka abayan labulen kafin ta fito tana tafiya izuwa gefen da Sgr yake a kwance,
  Tsayawa tayi tana kallonshi,yatsun hannunshi sae kerma sukeyi kamar wanda sanyi ya kama,
  A hankali ta furta sunanshi"Ya Rafayet,"
  "Pls,Just Leave am not in the mood,"da gudun gaske Sehrish ta kama hanyar fita ɗakin tana kuka,bata ji zafin maganarshi ba,

Yinin ranar ko abinci Sgr baici ba,Yadda takai mashi kayan abinci haka ta kwaso su,bai ta6a koda Coffee ba,

After 5 days,bayan kwana biyar,wanda yayi dai dai da sati uku da kwana Biyu da rasuwar baby Junaid!!!!!saura kwana 5 ya rage masu su bayyanar da Junaid,komai ya gama hargitse masu babu wani sauran kwanciyar hankali da suke dashi,

Wuraren ƙarfe 9 na dare,Suna kwance a ɗakinsu,har lokacin Atare suke kwana da Oummansu,Har ɗaki aka ware mata haɗaɗɗen bedroom amma tace ita tafi son ta kwana tare da ƴa'ƴanta,Su uku ne saman gadon suna bacci,Oummansu tare dasu Hosana da Jahad,Sae faman sharar bacci suke yi,
  Sehrish kuwa sam ta gaza runtsawa,ta sanya damuwa sosai aranta,ta ɗaurawa kanta nauyin alhakin Ƙaryar dasu Ya Omar su kayi ma Abbansu,
  Tana zaune saman sallaya bata jima da kammala yin nafilfilin dare ba,hannayenta ta ɗaga saman tana addu'a,yayin da hawaye ke shararowa akan fuskarta,kusan minti 30 Sehrish bata dakata da yin addu'ar ba,sai da tayi mai isarta aƙarshe ta fashe da matsanancin kuka,da sauri ta sanya tafin hannayenta saman fuskarta ta toshe bakinta gudun kada sautin kukanta ya tashi su Oummansu,
A saman dardumar ta kwanta,tana ci gaba da yin kukan,taso ace zata iya taimaka masu sai dai babu halin yin hakan,tafi damuwa da Sgr don tun ranar da Abbansu ya ƙara tunasar dashi akan Junaid,ita shaidace bai ƙara cin abinci ba,Sai dai lemu da yake sha,babu bacci a idanuwanshi,kullum babu lafiya ajikinshi,duk yabi ya hargitse,

A cikin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login