Showing 228001 words to 231000 words out of 307403 words

Chapter 77 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

Sehrish ɗakin Abusufyan suka wuce,A saman gadonshi suka kwanta tuni bacci ya ɗaukesu,Jahad dae ta kasa runtsawa tunanin Junaid ya hanata sakat,kokwanto take tayi acikin zuciyarta,ita dai a iya saninta in mutun ya mutu bai dawowa,Amma shi Junaid gashi ya dawo,Tabbas Tana ji aranta ba mutun bane fatalwarshi ce tazo a matsayinshi,

Acan ɗakin Abusufyan kuwa,Sehrish da Amrish tuni bacci yayi awon gaba dasu,can cikin dare wuraren ƙarfe ɗaya da rabi,Wayar dake cikin aljihun doguwar rigarta ta fara ringing,Sam ta manta da wayar Sgr da ta ɗauko acikin aljihunta,cikin magagin bacci ta zura hannu tare da curo wayar,picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta,
  "Who's on the line"?Jin Muryarshi yasa Sehrish ta wartsake daga baccin da take yi,miƙewa tayi daga zaune,
  "Ya Rafayet,"da wata irin kasalalliyar murya ta ambaci sunanshi,. 
  "Dama ke kika ɗauki wayar,"?
Jinjina kai tayi kamar tana agabanshi"eh,ni ce,na manta ban baka ita ba a asibiti"
  "Its okey,just keep it for me,"ta amsa mashi da toh,kafin tace"Ya jikin nasu"?
  "Da sauƙi,Zuwa gobe zamu dawo gida,Anan za'a cigaba da treating dinsu"yanayin muryarshi tayi sanyi sosai,
  Shiru suka ɗan yi na wani lokacin,
"Zan maida video call,"Jin yace haka ta janye wayar daga kunnanta,saukowa tayi daga saman gadon ta kunna hasken ɗakin kafin ta koma ta zauna saman gadon,
  Saita fuskarta tayi akan screen ɗin wayar a lokacin Ya canza kiran zuwa video Call,
  Kwance yake saman wani haɗaɗɗen gado kai kace ba cikin asibiti bane,daga shi sai dogon wando ya cire rigar jikinshi,Ya ɗan tada kanshi saman pillow,

Ƙura mashi ido tayi tana kallonshi kamar yarda shima yake kallonta,
  "Me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba"?
  "Kaine ka tashe ni,Har na fara bacci,"
  "Okey,"shiru ya ɗan yi,gashi yana so suyi fira da ita,amma bai iya ba,ita kanta ta lura da hakan,sam bai iya surutu ba,
  "Meya hanaka bacci,"?daƙyar ta iya tambayarshi,. 
   Da buɗar bakinshi sai cewa yayi"not having u by my side" saboda tsabar mamakin maganarshi ta ɗan zaro ido tare da buɗe baki irin mamakin nan ya kamata jin yace wai rashinta a gefenshi,
  "Am so proud of you,"yayi maganar yana nunata da finger ɗinsa,A lokacin ji yake kamar ya janyota ta cikin wayar ya rungumeta,sai dai babu halin yin hakan,
  "When are u going back to U.S"?daƙyar ta iya tambayarshi,
"Kin ƙosa na tafi ne"?
Girgiza kai tayi"a'a,nasan cewa dole zaka tafi,that's why i asked u,'
"Ko zaki bini ne"?
Da sauri tace"A'a,"

"You won't follow me?tell me why"?yayi maganar yayin da idanuwanshi ke lumshewa,

"Bayan rabuwa zamuyi nan da wasu ƴan kwanaki,zaka sake ni,ka koma U.s,"
Lokaci guda taga ya canza fuskarshi alamar baiji daɗin maganarta ba,
"Its okey,take care of ur self,"yana kai ƙarshen maganar yayi rejecting ɗin kiran,Jiki asanyaye Sehrish ta ajiye wayar saman side drawer,

Gyara kwanciyarta tayi zuciyarta cike fal da tunanin maganganunsa,tai mamakin canzawar da yayi jin tace bazata bishi U.S ba,
"I don't know why,but ni bazan bishi ba,koda ace ya buƙaci hakan tunda ba so na yake ba,yar aikinsa ya dauke ni,yanzu bani da burin daya wuce ya bani takardar sakina kawae in san matsayi na,tunda Aikina ya qare,"ta ƙarasa maganar tare da rufe idanuwanta,nan take bacci Yayi awon gaba da ita,


A 6angaren Hajiya sarat kuwa,Lokacin da kiran ƙare kukanka ya shigo wayarta cike da zumuɗi ta ɗaga kiran don taji ko sun samu nasarar kashe su Junaid din don ta gama sama ranta zasu yi nasara,
Lokacin dasuka sanar da ita cewa sun rasa su,Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata makoshinta,Nan take Zuciyarta ta buga ta yanke jiki ta faɗi ƙasa wanwar.........."

Washe Garin ranar,Wuraren ƙarfe 7 na safe,Slowly motocinsu suka shararo da matsakaicin gudu izuwa cikin gidan,A jere motocin suka biyo layi,Bayan sunyi parking ɗinsu,Motar farko ta Sgr ce,a hanzarce Armstrong ya fito tare da zagayawa ya buɗe masu ƙopa,Fitowa Sgr yayi tare da zura hannuwanshi Ya ɗauko Junaid irin ɗaukar da akeyi jariri,

Motar bayansu ta marshal Omar ce,Major ne ya buɗe mashi ƙopar ya fito tare da zagayawa ya taimaka ma Abbansu wurin fitowa daga ciki,har yanzu da sauran jikinshi,Amma ya samu sauki dama ciwon na rashin Baby Junaid ne yanzu gashi Ya dawo,hankali ya kwanta No more tension,

Daga Motar Omar,Sae motar Kanal Yousouf,shi ya ɗauko Baba mai gadi na gidansu Amrish,

Motar fawan kuwa,Mommynsu ce aciki,Daga motarshi sai Motar Ya Mu'allim,Haka suka dinga fitowa daga cikin Motocin,gaba ɗaya suka ɗunguma izuwa cikin gidan,kaitsaye Sgr ya wuce da Junaid izuwa bedroom ɗin Abbansu,Omar na biye dashi Ya tallabo Abbansu saboda rashin ƙwarin jikinshi,

Asaman gadon Abbansu Sgr Ya kwantar da Junaid,Sannan Ya taimaka ma Abbansu Ya kwanta shima,Akwai Medicines dinsu da suka taho masu dashi,hada na asthma din Junaid tare da injections ɗin da za'a cigaba dayi mashi kafin Allah yasa ya dawo cikin Hayyacinshi,

"Yanzu duk wahalar da muke sha ashe Yaron nan yana araye"?Omar ne yayi maganar yana kallon Sgr,
Kafin yaci gaba da cewa"Gaskiya duk wanda yayi silar jefa mu cikin wannan matsanancin tashin hankalin Sae ya ɗanɗani kudarshi,sai ya yi danasanin haihuwarshi da uwarshi tayi acikin duniyar nan,zanso nasan wanene wannan MASTER PLANNER ɗin"




   *Masu cewa Basu son littafin abban sojoji na kuɗi bane,Littafina na kuɗi ne,Book one ne kawai nayi shi kyauta,Amma 2 da 3 Na kuɗi ne,Dukansu 300 ne duk maiso yayi mun magana kaitsaye Amma message ta whatsapp 08103884440*
 
 
 

 
 

 




 
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋





𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠

*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*





Kafin yaci gaba da cewa"Gaskiya duk wanda yayi silar jefa mu cikin wannan matsanancin tashin hankalin,Sae ya ɗanɗani kudarshi,sai yayi danasanin haihuwarshi da uwarshi tayi acikin duniyar nan,zanso nasan wanene wannan MASTER PLANNER ɗin"

Sannu da jiki suka ƙara Yi ma Abbansu kafin suka juya atare suka bar bedroom ɗin nashi,Matsawa Abba Yayi kusa da Junaid,Zuba mashi ido Yayi yana kallonshi cike da tsantsar so da ƙauna,Ji yake tamkar ya mayar dashi cikin cikinshi,tsananin tausayinshi ne ya kamashi,Rungumeshi yayi ajikinshi kamar jinjiri haka Ya koma,shafa sumar kanshi Abba Ya Soma yi a hankali har zuwa bayanshi,sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi,Jiya haka suka kwana a Asibiti manne da juna saboda firgitar da yake yi,kuma da zarar Abba ya janye jikinshi daga nashi sai ya dinga kiran sunanshi,har sai ya ji shi ajikinsa sannan yake rufe bakinshi,

Bayan fitarsu Sgr daga bedroom ɗin,direct suka wuce Babban Falon gidan Inda kowa Ya hallara Kamar yarda Ya Mu'allim Ya nemi alfarmar Yin magana dasu,A saman Sofa mai mazaunin mutun uku,Sgr tare da Marshal da kanal Yusuf,ɗayar Sofa ɗin itama mai 3 seat,dama 2 sofa sets ne a babban palourn,Ayyan da Jahan ne tare da Irfan suka zauna asamanta,Jabeer da khaleed suna a zaune saman sofa mai mazaunin mutun biyu,Alexandra tare da Fawan suna zaune a saman same Sofa,Abusufyan na tare da Ya' Mu'allim,gaba ɗayansu ne banda wanda suka kwana gidan,
  Gyaran Murya Ya Mu'allim yayi tare da cewa"Idan ba damuwa,ina buƙatar ganin sauran da basu hallara ba,"
Miƙewa Fawan yayi dama shine messenger,Duk in wani aike ya tashi jiki na rawa zaka ga Ya miƙe,

Bedroom ɗinsu Sehrish Ya nufa,A ƙopar ɗakin ya tsaya tare da kwankwasa ƙopar,Almost 3 times Yana buga ƙopar,Sae sharar bacci suke yi sun baje saman gado,da yake sun tara gajiya kuma basuyi bacci da wuri ba,
  Yana ƙoƙarin sake buga ƙopar yaji an buɗe ta,Tsayawa tayi ruƙe da qugu,fuskar nan a kumbure idanuwan sun ƙankance,Tunkafin yayi magana tace"Ya fawan wai lafiya irin wannan bugun ƙopar ɗakin haka,Sai kace zaka 6alle ƙopar,"
Sai da takai ƙarshen maganar,Ya wurga mata harara,don ya gane wacece acikinsu
"Rasa kunya 6eran tanka,aiko ni akayi,Ki shiga ciki ki sanar dasu cewa ana son ganin kowa a main palour,"
Murguɗa mashi baki tayi,har ya ɗaga hannu zai make bakin,Sae ga Abu na ƙoƙarin fitowa Jikinta sanye da hijabi,da sauri Ya kawar da hannun,
  "Ina kwana Aunty,"abu ta amsa mashi"Lafiya lou,fawan Ashe kun dawo,"
  "Eh,bamu jima da dawowa ba,dama An aiko ni ne don in kira ku,Ana son ganin kowa da kowa ne a babban falo,"
  "Allah yasa Lafiya,Bari na shiga ciki na tashi jahad,Yanzu zamu fito,"
  Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta koma ciki,a lokacin Hosana ma ta shige ciki,
Ɗakin Azmee Ya nufa,Hannu yasa ya kwankwasa mata ƙopar ɗakin,bugun farko yajiyo muryarta tana magana daga cikin ɗakin
  "Wanene"?
"Fawan ne Aunty azmee,"
Jim kaɗan ta buɗe mashi ƙopar ɗakin,Jallabiya ce ajikinta ta yafa babban mayafi,Hannunta na ruƙe da Cazbaha,
  "Kun dawo kenan Ya jikin Abban naku,"
  "Jikinshi da sauƙi Alhamdulliah,"
"Allah Ya tashi kafaɗunshi"
"Ameen,Dama Akwai baƙi a palour,naga baki fito ba,Ko abunsha ne ataimaka a haɗo masu",
Jinjina kai tayi"badamuwa,gani nan zuwa,"tayi maganar tare da komawa cikin ɗakin,juyawa Fawan yayi a hanzarce Ya koma palourn,tare da samun wuri ya zauna,Shigarshi da minti Biyar,Abu ta fito tare da Jahad suka nufi palourn,Hosana kuma Oummansu ta aiketa Bedroom ɗin Abusufyan don ta kira su Sehrish,

A gefen Mommy,Oumma ta zauna,Jahad kuma A ƙasa ta zauna saman carpet,musayar gaisuwa suka shiga yi atsakaninsu,Bayan sun kammala gaisawa kowa Ya shiga natsuwarshi,
"Sun gama hallara ko akwai sauran wanda baya nan ne"?Ya Mu'allim Ya tambaya,don bayason wani yayi missing discussion ɗin da zasuyi,
"Akwai saura,Amma na aiki Hosana taje ta kirasu,"Abuce ta
bashi amsa,Lokacin da Hosana ta kutsa kai ɗakin,A baje ta samu Sehrish da Amrish suna bacci,saman gadon ta hau tare da sanya hannunta tana bubbuga ƙafafunsu"Wai bazaku tashi ba!"shiru ba wadda ta motsa acikinsu,
  Bubbuga ƙafafun nasu ta kuma yi"wlh ko ku tashi,Ko in ɗebo ruwan sanyi in watsa maku,"jin wannan maganar yasa Sehrish ta buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci,koda tayi arba da fuskar hosana nan take ta ɗaure fuskarta,A ƙule tace"Lafiya'?
"Nima bansani ba,Oumma ne tace na kira mata ku,Ana son ganinku a palour,"
Takai ƙarshen maganar tare da saukowa daga saman gadon ta fice daga ɗakin tana ƙara jaddada masu akan su fito,

Atare da Amrish suka fito daga ɗakin hannunsu ruƙe dana juna,tunkan su ƙaraso Sehrish ta hango Sgr dake gefen Kanal Yusuf ya lumshe idanuwanshi,kamar mai jin bacci,da alama Jiyan nan baiyi bacci ba,ko bai samu isasshen bacci ba,

Ƙarasawa Cikin palourn su kayi,A nan saman Carpet gefen Jahad suka zauna suma tare da lankwashe ƙafafuwansu,

Ɗagowa Ya Mu'allim yayi tare da binsu da kallo,kafin yace"Akwai saura ko su kenan"?
"na kira Aunty Azmee,Yanzu zata zo itama,"Fawan ne ya bashi amsa,Duk sun ƙagara suji abunda Ya Mu'allim ke son sanar dasu,

Saukowa Azmee tayi daga 3 steps na fitowa daga Corridor ɗin ɗakunansu,bata nufi falon kaitsaye ba,kitchen ta nufa,after few minutes ta fito hannunta ruƙe da faffaɗan tray saman shi glass cups ne,Wanda ta shirya masu abunsha ciki,

Jin takun takalmanta ne Ya jawo hankalinsu,tana ƙarasowa wurin sofas ɗin da suke zaune,Kamar ance ta ɗago karaf Suka haɗa ido da Ya Mu'allim,A gigice Azmee ta saki tray ɗin hannunta Wani irin sauti suka bada ji kake fass fass tatass Glass Cups ɗin suka faffashe,ganin haka yasa kowa Ya shiga tambayarta Lafiya,kasa buɗe baki tayi don tayi magana,gaba ɗaya duk tabi ta firgice ta rasa natsuwarta,Da gudu ta juya zata bar wurin Ya Mu'allim Ya daka mata tsawa"Karki kuskura kice zaki bar wurin nan,idan har kika ƙara ɗaga ƙafarki a wurin nan,Saina sa6a maki,"Cak ta tsaya lokaci guda wata irin Zufa ta shiga wanke mata fuskarta,
Abun ya ɗaure masu kai,har suna haɗa baki wurin tambayarshi A ina yasan Azmee?,
  Miƙewa tsaye Ya mu'allim yayi tare da nuna ta da yatsan hannunshi"Wannan itace Silar duk wani hali da kuka shiga acikin gidan nan!"
Saboda tsabar firgitar da su kayi gaba ɗaya suka miƙe suna kallonshi,
"Anya kasan me kake faɗa kuwa?Wannan fa Azmee ce,me aikin gidanmu,kusan Shekara Ashirin tana Yi mana aiki,"kanal Yusuf ne yayi maganar,

"Kodai tayi maka kama da wadda ka sani ne"?acewar Irfan,
A tsanake Ya mu'allim ya soma magana"Niko nasan Azmee farin sani!Ku ne baku santa ba,Wannan matar da kuke Gani,Mushirika ce ƴar qungiyar asiri",
Hankali A matuƙar tashe Suke kallonshi,Duk basu kaiga yarda da maganarshi ba,
Azmee kuwa tuni ta ɗaura hannu asaman kanta,Tunda Ya Mu'allim Ya fallasa cewa ƴar gungiyar asiri ce ita,tasan cewa Alƙadarinta ya karye!A ƙa'idar ƙungiyarsu daga inda wani Yasan sirrinka shikenan ƙarfin sihirinka zai naƙasa............"

"Kinji haushin rayuwarki!Muguwa azzaluma,dama Alƙawarine na ɗaukarwa kaina saina Tona maki asiri,koda kuwa zakiyi silar mutuwata ne,balle kuma ke baki isa ki kawar dani ba,"

Kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu,Kowa yasha jinin Jikinshi,
Hankali atashe Mommy tace"Don Allah ka fahimtar damu,"

Cigaba da magana yayi"nasan ba lalle ne wasun ku su gane ni ba,Amma mahaifinku zai iya tuna fuskata,Ni ina ɗaya daga cikin malaman da aka ɗauko don su koyama Junaid karatu lokacin yana yaro,A lokacin Mahaifinku Ya faɗamun cewa duk malamin daya ɗauko don ya koya mashi karatu,tun arana ta farko idan Yazo bai ƙara dawowa,Abun Ya ɗaure mun kai,farkon haɗuwata dashi A masallaci ne,Ta dalilin  yabona da mutane keyi ne ya jawo hankalinshi akaina,harya jani gefe yake sanar dani game da ɗanshi da yake son indinga zuwa ina koya mashi karatu,

A ranar dana fara zuwa gidan nan koya ma junaid karatu,A garden muka zauna dashi in ban manta ba,Saman darduma ne muke zaune dashi,Idan inayi mashi karatu sai ya ƙura mun ido yana kallon bakina kamar yana fahimtar abunda nake cewa,Ashe kwata kwata bai ganewa ne,Abun ba ƙaramin ƙona mashi rai yake yi ba,a ƙarshe sai ya fashe mun da kuka yana cewa shi baiso ana zuwa yi mashi karatu tunda ba ganewa yake yi ba,Wahalar dashi muke Yi,naji tausayinshi sosai a wannan lokacin,Na kuma Yi mamakin yarda bai gane karatun al'qur'ani,sanin cewa Ƙaramin yaro yafi ɗaukar karatu a lokacin ƙuruciyarshi,Amma shi ko Bismillah wuyar faɗi take yi mashi,Idan na matsa mashi akan yayi karatu da zarar ya buɗe baki zai amsa karatun da nake biya mashi,kwatsam sai inga ya sanya hannu ya toshe kunnuwanshi,La66anshi na kerma,wani lokacin kuma sai inga yana ruƙe maƙoshinshi,tundaga nan na sanya ayar tambaya akanshi,bayan na koma gida,Yini nayi da tunanin Junaid,Saboda Yaron akwai shiga rai,Ya kwantamin araina sosai,a daren ranar,wuraren ƙarfe 1 na dare aka kira wayata Ana yi mun barazana akan karna kuskura na ƙara zuwa koya ma junaid karatu idan ba haka ba zan rasa raina ne,duk da haka ban daddara ba,A washe garin ranar na kuma dawowa koya mashi karatu hada ruwan Zam Zam na addu'a nazo mashi dashi don yasha,ruwan Addu'ar yana karya sihiri duk mun ƙarfinshi in akayi ma mutun in ba wani iko na Allah ba,Aranar nayi ƙoƙarin na bashi yasha ruwan addu'ar nan amma wani abun mamaki daga nayi yunƙurin kafa mashi ruwan a bakinshi don yasha Sai kawai inji an buge mun hannuna,tun daga nan na ƙara yarda cewa akwai sihirin ajikinshi,Sae na fara tunanin yin bincike akan Wanda ke  sarrafa kwakwalwarshi,domin in taimakeshi,Akwai wata rana Da Azmee ta kawoshi da hannunta,A ranar na gane cewa itace ke sarrafa shi,Allah yayi mun baiwar gane mutun mai sihiri da zarar mun hada ido,ta kalle ni na kalleta,Bayan tafiyarta nake tambayarshi Wacece ita,ko mahaifiyarshi ce?Sai ce mun yayi Eh,Mamansu ce,banyarda da maganarshi ba a lokacin saboda sam babu kamanceceniya a tsakaninsu,Hasken yaron ba irin nata bane,ko irin kama ta jini babu atsakaninsu,da na tsare shi da tambaya sai yake cemun mamanshi bata nan,kuma bata sonshi ta tafi tabarshi,Sai tausayinshi ya kamani,Bayan na koma gida na shiga zurfin tunani akanshi,Abunda ya tsayamun araina shine meyasa mahaifiyarshi ta tafi tabarshi?Wacece wannan matar dake sarrafa kwakwalwarshi,Meyasa take son juye mashi tunani don karya gane karatu,Na nace akan son sanin dalilinta na yin hakan,Gashi bansan wa zan tambaya ya bani amsa ba,matasan gidan kuma ba gwanayen son magana bane,Gasu sojoji in nace zan tambayesu ba dole su fahimce ni ba,Zasu yi mun wata mummunar fahimtar ne,akwai wata rana da muka haɗu da mahaifinku a lokacin na kammala Koya mashi karatun ranar,Shi kuma ya dawo daga wurin aiki,Na ƙarasa muka shiga gaisawa dashi har yake ce mun in shigo daga cikin gidan muci abinci atare,Dayake mutun ne shi mai son jama'a,baida girman kai ko kaɗan,Yana da kyakkyawar zuciya,Banyi niyyar shiga cikin gidan cin abinci ba,Amma tunawa da binciken da nakeso nayi saina Yanke shawarar binshi,

Lafiyayyen Abinci Azmee ta shirya mana tare dashi,a lokacin in ban manta ba,Hada waɗannan tagwayen guda biyu,ko gaishe ni basuyi ba lokacin,Dama tunda na kallesu nagane cewa suna da girman kai,wani kallon ƙaskanci suke yi mun,Amma wani abu dana hasko shine,Hasken fatarsu irin na Junaid ne,Sai na fara tunanin kodai cikin Iyayensu akwai jinsin turawa ne?Saboda ƙwayar idon ɗaya daga cikinsu,muna cikin cin abincin Sai naji ɗaya na tambayar Abbansu,na kasa kunne ina sauraronshi,
"Abba,har yanzu Mommy bazata dawo ba"?Sai Abbanku Yace"bana tunanin zata dawo da zama Nigeria,
Sai naji yaja dogon tsoki yana cewa"Gaskiya batayi mana adalci ba,kodan saboda Junaid yakamata ta dawo taci gaba da kula dashi,Ni bana so Azmee taci gaba da rainonshi....."bai kai ƙarshen maganarshi ba sai Abbanku yayi mashi tsawa,nan take yaja bakinshi yayi shiru,bayan mun kammala cin abincin,Na shirya tafiya mahaifinku yayi mun jagora a lokacin ko abun hawan kaina ban mallaka ba,A ƙafafuna nake yawo,ko in hau abun hawa,to a lokacin shima yana da wani uziri a waje,Sae yace mun in shiga motarshi su rage mun hanya,

Muka shiga motar atare,Driver ɗinshi Yaja motar muka fita,A cikin motar ne,na soma ƙoƙarin bugun cikinshi,
"Na lura kamar akwai damuwa akan fuskarka,"sai yayi ƙoƙarin 6oye damuwarshi yace mun bakomai,
Sai na canza maganar nace"Maganar Junaid Alhaji,Yau mahaifiyarshi data kawo mun shi daƙyar ya tsaya,Yana ta kuka sai ya bita,"Nayi mashi zancen junaid ne don na lura ba ƙaramin son Yaron yake yi ba,indai kanason kaga fara'arshi toh kayi mashi maganar Junaid,
  Nan yake ce mun ae ba mahaifiyarshi bace,Mommynshi bata a ƙasar tun lokacin da ta haifeshi tabar ƙasar,Wannan matar dana gani mai aikin gidan ce,Itace ta shayar dashi,sun shaƙu sosai,Ya saba da ita baison rabuwa da ita,iya haka ya tsaya mun da bayani,Bai faɗamun dalilin dayasa Mahaifiyarshi tabar ƙasar nan ba,batare data ƙarasa shayar dashi ba,Ni kuma a wannan lokacin na samu abunda nakeso,bayan sun sauke ni a gida,Yinin ranar da tunanin maganganun mahaifinku na kwana,Saboda yarda nasa ma raina junaid har mafarkinshi nake yi,Dana zauna nayi nazari sosai,Sai na hasasho wani abu game da Azmee,tabbas akwai wata mummunar manufa dayasa take zaune a gidan,In ba haka ba meyasa zata Juye mashi kwakwalwarshi?Saboda yaron yana da kaifin basira!he's genius,irin yaron nan ne masu wayon tsiya,Gifted Ne shi,ita kuma Azmee ita ke rainonshi dole zai iya kasancewa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login