Showing 60001 words to 63000 words out of 307403 words
Chapter 21 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
iya rama mata ne," dariya Amani tayi tare da cewa"ki barta inga ƙarshen rashin kunya,wlh dai dai nake da kowane shege acikin ku,Bana jin tsoranku a yanzu,tun ranar da Amal ta sanar dani komai game da ukubar da kukeyi mata tun daga ranar na ɗaura ɗamarar yin yaƙi daku,"
Hankali tashe hayaam da aunty babba suka kalli juna jin ta ambaci sunan Amal,
Hafsat ce tace"Amal na wurinki ne"!?
Jinjina kai amani tayi tare da cewa"Amal tana wurina!itace yarinyar dana zo da ita cikin gidan nan,kun so ku kashe mun ƙanwata,Amma Allah bai baku nasara akanta ba,Amal ta tako da ƙafafunta ta kawo kanta har cikin garin nan,"
Shiru duk sukayi suna sauraronta,
"Haƙƙin Amal kaɗai ya isa ya jefa rayuwarku cikin masifa,laifin me Amal tayi maku da har kuka wulaƙantar da rayuwarta?yarinya ƴar ƙanƙanuwa amma kukayi mata taron dangi wurin azabtar da ita,saboda tsabar mugunta irin taku,ƙiri ƙiri kuka hanani ganin Amal,ku ka yi mun ƙaryar cewar Amal ta 6ace ba'a ganta ba,mugaye kawai ashe gidan makwabtanmu kuke kaita kuna rufeta,duk in nazo har in bar garin,tana can arufe kamar akuya,ko abinci ma baku bata,wai ku wasu irin mutanene?wace irin zuciya gare ku...?
Kasa ƙarasa maganar Amani tayi saboda kukan daya ciyota,nan take ta fashe da wani irin matsanancin kuka,ba ita kaɗae bama hatta hafsat sai da ta zubar mata da kwalla,baƙin ciki kamar ta binne kanta,abun kunyar da mommynta ta aikata ba ƙaramin illa yayi ma zuciyarta ba,
Hayaam kuwa sae faman mazurai takeyi ita da aunty babba sunyi wuƙi wuƙi,basu da abun cewa,dama ance rana dubu ta 6arawo,rana ɗaya ta me kaya,
"Wlh kaɗan kuka fara gani!haƙƙin Amal da kuma haƙƙin waɗannan bayin Allahn da kuka cutar bazai ta6a barinku ku zauna lafiya ba,in har ba zaku canza waɗannan munanan ɗabi'un naku ba,mugunta da kwaɗayin abun duniya,dogon buri,rayuwar ƙarya,duk ku kadae gashi har yau Allah bai ta6a baku nasara ba,mutumin da bai ta6a sa Allah alamurransa ba taya zaiga dai dai"?
Tsoki Aunty babba ta buga tare da nuna mata hanyar fita daga ɗakin tace"zo ki fuce ki bamu wuri tun kafin ranki ya 6aci a wurin nan!shashasha kawai kina tunanin cewa kalamanki zasu iya tankwarani ne?duk duniya ba ayi mutumin da zai zauna yanayi mun nasiha ba,wlh ba ayi shi ba,"
Girgiza kai amani tayi tare da juyawa a fusace tabar ɗakin tana faɗin"Jiki magayi,"
Komawa Aunty babba tayi yaraf ta zauna gefen gadon tana faman cizon yatsa,miƙewa hafsat tayi tare da fucewa daga ɗakin,
Fitar ta keda wuya,Hayaam ta dawo gefen aunty babba ta zauna tana faɗin"Yanzu menene mafita"?
..fuskarta a hargitse tace"mafita ta wuce mu gudu salin alin batare da sanin kowa ba,"
"Saboda me zamu gudu?hakan na nufin cewa sun ci nasara akanmu kenan"?
"Hayaam ba zaki gane ba,ina tsoran in sake yin arba da hosana ne,bata da hankali,zata ci gaba da tona mun asirine a bainar jama'a"
"Amma Aunty laila,taya akai yaran suka zauna a wurinki har hakan ya faru?meyasa baki kashesu ba tun lokacin"?
Guntun tsoki taja tare da kawar da kanta gefe cike da takaici tace"sai yanzu nake danasanin barinsu araye,meyasa ban kashesu ba tun lokacin da suke a wurina ba?wancan shashashan mutumin dana bama aikin zubar mun dasu a daji bansan ya akai yayi sakacin da har suka ku6uta daga hannunshi ba,kuma tun ranar dana bashi su nake ta jaraba kiran wayarshi akashe kullum har na gaji na daina kira,duk shi ya kwafsamin wlh,yanzu yawo acikin gidan nan ma ya haramta agareni,Allah yaso Hafsat ta siya niqabi a kasuwa,zan kar6e shine in sanya a fuskata saboda gudun kar waccen mai ta6in hankalin cikin sun ta ganni.....'
Shiru suka ɗanyi na wani lokaci,zurfin tunani ta shiga yi kwatsam ta tuna da maganar nan da hajjaju ta ta6a sanar da ita kwanakin baya can da suka wuce lokacin su hosana na a gidan,
"Idan kin toshe waɗannan hanyoyin,ita kuma waccen ɗayar hanyar da ta riga isa inda baki so fa ya zakiyi da ita'
Jinjina kai Aunty babba tayi tare da faɗin"Allah ya isa tsakanina da hajjaju,sarai tasan komai game da rayuwar yaran nan amma taƙi sanar dani,babu yadda banyi da ita ba,amma taƙiya saboda tsabar baƙin hali irin nata,da tun farko ta sanar dani cewa ƴan ukune yaran akwai ɗaya dake aiki a gidan da tuni nasan abunyi,
wannan masifar har ina"?
"Amma kina ganin Ammi zata barsu ne acikin gidan nan?Jiya munyi plan ɗin cewa zaki kirata a waya ki sanar da ita cewa yaran shaggu ne,kin sanar da ita hakan," ta ƙarasa maganar tana kallon fuskar aunty babba wadda ke a hargitse,jin maganar hayaam yasa ta ɗan jinkirta,kamar me nazarin wani abu can ta ɗan washe baki tare da cewa"Hakane!Wannan ita kaɗae ce hanyar da ta rage mun,jiya na kira ammi a waya kuma na sanar da ita cewar Abusufyan ne ya ta6a yi ma wata fyaɗe harta samu ciki ta haifesu,ina da tabbacin cewar AMMI bazata barsu su zauna ba,dole ta koresu ƴan jakar uban,wlh na tsani yaran can,na tsani mahaifinsu duk shine silar komai,ya tashi yayi aure batare da sanin kowa ba,gayanan ya jefa mu acikin masifa,ni duk bama wannan ba,taya akai AMAL ta gudo daga gida tazo Abuja wurin waccen baƙar munafukar?ta ya akai Mammy da Abrah su kayi gangancin da har AMAL ta gudu daga gida ta dawo wurin Amani?
Hayaam tace"Nima abunda nake tunani kenan,don ko aranar da zan bar gidan Amal na ƙunƙume aɗakinmu,zazza6i ya rufeta,Ni babban baƙin cikina ma,muna nan sake da baki,Amal na iya zuwa ta aure wani daga cikin matasan gidan,kinga ae shikenan mukuma tamu ta ƙare,maƙiyanmu za suyi ta cin nasara akan mu,'
"Insha Allah hakan ma bazata faru ba,in har ɗaya daga cikinku ke da abra bai auri ɗaya daga cikin matasan gidan ba,to sai dai ayi Ragas,Uban kowa ya rasa,itama Amal ɗin tarasa,ita kuma waccen ƴar iskar sai nayi silar mutuwan aurenta,tunda har ta iya ɗaga hannu ta kikkifamun mari,wlh saita gane kuranta,kuma wlh billahil azeemu,muddin Ishaq ya sake ni,itama sai Abbas ya sake ta,inyaso sai muyi zawarcin atare,"ta ƙarasa maganar tana faman sakin huci,tayi danasanin zuwanta gidannan!
*Boss Bature*
❤🤍❤
turo ƙofar ɗakin da ammi ta sauka akayi,Azmee ce ta shigo hannunta ɗauke da kakkauran tea ɗin data haɗa mata,a zaune ta same ta saman darduma jikinta sanye da hijabi,yayin da hannunta ke ruƙe da cazbaha,da alama sallah ta kammala yi,
Cike da girmamawa azmee ta ƙarasa tare da zuƙunnawa ta gaishe ta,"Ina yini Ammi,ya gajiyar tafiya,"
da buɗar bakinta sae cewa tayi"Ina Abusufyan yake"?
Azmee tace"sun fita sallar magrib,amma nasan yanzu suna kan hanyar dawowa gida,nan bada jimawa ba nasan zasu shigo ciki,"
Jinjina kai tayi tare da kai hannu ta ɗauki cup ɗin da azmee ta miƙa mata,abaki takai cup din ta kur6e sa kusan sau uku sannan tace"Idan sun dawo,kice su jira ni a palour gaba ɗayansu,inason ganinsu,"
Tuni Azmee tasha jinin jikinta,aranta tace"tashin hankali,'a fili kuma tayi saurin cewa"Za'a sanar masu,"sannan ta mike ta kama hanyar fita daga ɗakin,har azmee ta ruƙe handle din ƙopar zata fita,muryar Ammi ta katse mata hanzarinta da cewa"Next time idan zaki haɗamun tea,bana son sugar yayi yawa,sannan madarar tafi bornvitan yawa,da fatan za'a kiyaye,'
"insha Allah za'a kiyaye,ko akwai wani abu da kike buƙata"?
"Idan ina buƙata zan sanar dake ne,basai kin tambaye ni ba,zaki iya tafiya,"
jinjina kai azmee tayi kafin ta buɗe kopar ɗakin ta fuce,babban falo ta nufa tana tafiya tana jinjina wa izza irin ta Ammi,saboda tsabar masifa,ko bornvita azmee bata zuba a tea din ba,madara kawai ta sanya mata amma saboda hali irin na ammi,da ba'a iya yi mata gwaninta,ta buga warning akan madara tafi bornvita yawa,ko ta ina taga bornvitan"?akan tea ma tayi ƙorafin anyi ba dai dai ba,inaga In taji abunda Abusufyan ya aikata batare da saninta ba,tabbas akwai matsala,rayuwarsu sehrish tana cikin garari,don wannan guyababbiyar matar bazata barsu su zauna lafiya ba,acikin gidan nan,
Jin sautin muryoyinsu,yasa Azmee dawowa daga zurfin tunanin da ta shiga,dawowarsu kenan daga masallaci kowa bakin shi ɗauke da sallama suka shigo cikin Main palour din,Abba ne tare da Abusufyan sae junaid atare,bayansu kuma su Abbas ne da ishaq,Mg Osman da kuma Captain Adam,sai kanal yousouf da kuma Marshal wanda ke tare da Dr harris,a bayansu kuma akwai Fawan,twins,jabeer,irfan,khaleed dukansu dai suka shigo ciki,
ƙarasawa Azmee tayi wurinsu tanayi masu sannu da dawowa,daga bisani ta isar masu da saƙon ammi,nan fa kowa ya shiga fargabar dalilin tarasu da Ammi tace ayi,musamman Abusufyan yafi kowa shiga damuwa,tsayawa su kayi a tsaye kowa yana ta zullumin fitowarta,Abba dae sai ƙarfafa ma abusufyan gwiwa yake,akan ya jure,kada tsoro ya hanashi yi ma Ammi bayanin komai yadda zata fahimta,
Jin takun takalminta kwas kwas!yasa su yin saurin kai idanunsu akanta,fuskarta na manne da farin glass,kwata kwata babu annuri a fuskarta,yayin da hannunta ke ruƙe da sandar nan ta alfarma,Ƙarasowa tayi tare da samun wuri ta zauna saman 3 seater,sannan ta aza ƙafarta ɗaya bisa ɗaya,tare da kallonsu tace"Ku zauna,"
A ƙasa su fawan suka zauna,yayin da Abbansu junaid,da abusufyan suka zauna asaman ɗayar 3 seater ɗin,ishaq da abbas suka zauna asaman 2 seater,Dr harris da Omar suka zauna a ɗayar 2 seater,dama 2 set ne na sofa a babban falon,manyan ne suka zauna saman kujerun,yayin da ƙananan daga kan Kanal yousouf suka zauna aƙasa,
Tsit falon yayi na wani lokaci,kai kace mutuwa ce ta gifta,ko motsin mutun bakaji a wurin,kowa ya kame kanshi,
ɗaya bayan ɗaya Ammi ta dinga binsu da kallo,kowa sae faman noƙe kai yake,shi dai abusufyan ya gaza sakewa,don ko idonshi bai ɗago ya kalle taba,
ɗaga sandar hannunta tayi tare da nuna Ayan tace"wannan dogon gashin fa?sai kace wani ɗan daudu meyasa baka aske shi ba?
cikin sauri Ayan yace"ƙuraje ne ke fitomun akaina duk in nayi yunƙurin aske gashin"
Ta6e la66anta tayi,kafin ta janye idonta daga kan Ayaan ta mayar dasu kan fawan,sunnar da kai ƙasa yayi yana ƴan kame kame,
"Ƴa'ƴan fatima kenan,ba zaku ta6a canzawa ba,yadda kasan sun haɗa jinsi da ibliss,ji bi ɗan iskan askin dake akanshi,hada kala ma ka canza mashi kaiga ƙeƙasasshe ko"?
Fawan akeyi ma faɗan Amma Abbansu ne ke jin maganar har cikin zuciyarshi,bakomai ya ɗan 6ata mashi rai ba,sai kalmar data faɗi na cewar kamar sun haɗa jinsi da iblis,abun ya tsaya mashi arai,jurewa kawai yakeyi,
ɗaya bayan ɗaya haka ta dinga sharrance su,har sai da tazo kan junaid wanda keta faman sakin murmushi kamar wani zautacce,
"Iko sai Allah!kai zonan,"da sandar hannunta tayi mashi nuni da yazo,miƙewa junaid yayi ya koma ƙasan kujerar da take ya zauna,hannu tasa tare da jan kunnanshi tace"Bakasan nazo bane?kowa na zuwa ya gaishe ni,amma banda kai,Abbanku ya sangarta ka ko?shiyasa ka fara jin kanka wani shege,"dafe hannunta yayi yana dariya yace"Ammi dan Allah ki sakarmin kunne na,Da zafi fa,Abba kana gani ko,"?
"Me Abban naku zai iya yimun bakasan cewa ni na tsugunna na haifesa ba,"
Zumbura mata baki junaid yayi tare da murguɗa mata baki,
"Fiye da haka ma zaka iya yimun tunda ubanka ya ɗaure maka mazauni,dole ka murguɗamun baki,ae bazan bar gidan nan ba,sae nasa an tura ka aikin soja,sannan hankalina zai kwanta,"
Bubbuga ƙafa junaid ya shigayi yana yi mata ƙunƙuni,hakan ba ƙaramin dariya yaso ya bata ba,amma bata bayyana hakan akan fuskarta ba,"
Shiru ta ɗanyi na wani lokacin kafin tace"kai irfan,tashi ka kiramun gwaggonku,tare da Auntynku Azeema inason ganinsu,"cikin sauri irfan ya miƙe tare da barin wurin ya wuce ɗakinsu gwaggo,
Bada jimawa ba,sae gashi ya dawo tare da gwaggo da hajiya azeema abayan shi,duk wannan surutun na gwaggon katsina,yau tsit kake jin bakinta,sae faman wurga ido take,wuri suka samu suka zauna,a saman sofas ɗin dake cin mutun ɗaya,
Bayan kowannansu ya natsu,Ammi ta tsayar da idanunta akan Abusufyan,wanda tunda suka zauna a falon,bai ɗago ya kalleta ba,
gyaran murya ta ɗan yi tare da ambaton sunanshi"Abusufyan"a firgice ya ɗago yana kallonta,bawan Allah harya fara haɗa gumi,ga yatsun hannunshi dake ta kerma,duk wasu alamu na rashin gaskiya sun bayyana a tattare dashi,Abba sai tausarshi yakeyi yana faɗin"ka kwantar da hankalinka,ka natsu dan Allah,duk kabi ka firgice,hakan ma zaisa taƙi yadda da hujjojin da zamu bata,"ƙasa ƙasa yake yi mashi maganar don karta ji shi,
ɗakyar Abusufyan ya iya amsa kiran da tayi mashi"Na'am Mommy,"
"Meyasa kabar ƙasar nan,batare da ka sanar mun ba?laifin me na aikata maka da har kake gudu na?sai kace bani na haifeka ba?bansan me ka ɗaukeni ba,'
muryarshi na rawa yace"Kiyi haƙuri Ammi,Nima bada son raina na tafi na bar ƙasar nan ba,nasan ni mai laifine a wurinki,ki yafe mun....'saukowa yayi daga saman sofa ɗin ya dawo ƙasa ya zuƙunna yana bata haƙuri,
"idan har dagaske kasan cewar kai mai laifine,meyasa da ka dawo Nigeria bakazo gida ka same ni ba,don ka nemi yafiyata ba"?
Shiru yayi yayin da idanunshi ke cike tab da kwalla,gaba ɗaya ya rasa inda zai tsoma ranshi,babbar damuwarshi shine,yadda zai fara yi mata zancensu sehrish,
..hmmmm ta furta sautin tare da mayar da idanunta kan gwaggon katsina tace"Saboda yardar da nayi dake ne yasa na ɗamƙa maki Amanarshi,don ki ladabtar mun dashi,a tunanina zaki canzamin shi,ashe bansan nayi aikin banza ba,"
ɗaure fuska gwaggon katsina tayi,alamar ranta ya 6aci,
"Ammi dan Allah komai ya wuce,just forget about the past,haba dan Allah,komai ya wuce mana,taya za'a zauna ana ta faman nanata abunda ya riga ya faru.,.,.."
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,jin abunda Jahan ke cewa,yadda kasan wanda yasha giya haka ya shiga sambatu yana faman jan guntun tsoki ƙasa kasa,yunƙurawa Marshal yayi da nufin ya buge masa baki,Ammi ta dakatar dashi"basshi ya ƙarasa,ba laifinsa bane,gado yayi wurin Uwarsa,ae ni bansan yaushe ne ƴa'ƴan fatima zasu fara girmamani ba,amatsayina na wadda ta haifi ubansu,"
Rai a6ace jahan ya miƙe zai bar wurin Abbansu ya daka mashi tsawa tare da korosa yace"Koma ka zauna,Allah yasa inga ka ƙara cewa uffan a wurin nan,"
Komawa yayi gefen ayaan ya zauna yana faman hura hanci,
Jinjina kai Ammi tayi tana kallonshi tace"Nan gaba fa,in ban bi asannu ba,bugu yaran nan zasu fara kaimun,To Allah ya kyauta gaba,"
Abba yace'Insha Allah hakan ma bazata ta6a faruwa ba"
Shidai abusufyan har lokacin yana zuƙunne asaman guiwowinsa,cike da zullumin me zai biyo baya,
"Uncle ka tashi ka koma ka zauna,jikinka sai kerma yakeyi,Ammi fa ba abunda zata iyayi maka,"Sakin baki abbansu yayi yana kallon junaid dake magana,yana ƙoƙarin kashe wutar da jahan ke ƙoƙarin kunnawa shi kuma zai hura wata wutar,
Girgiza kai Ammi tayi tare da wurga ma Abbansu harara tace"Bazan iya zama agidan nan ba,yaranka sunfi ƙarfina,"sunnar da kai ƙasa abba yayi kafin ya ɗago yana kallon junaid da yayi maganar ya ɗan jefa mashi harara,
Suna cikin wannan Zaman sai ga hosana ta shigo cikin falon,tana neman warin ɗan kunnanta daya faɗi,'tashin hankali,gaba ɗaya hankalin kowa ya koma kanta,abusufyan kuwa arazane ya ɗago yana kallonta,ammi duk bata lura da ita ba har sai da Hosana ta buɗe baki tayi magana"Daddy ɗan kunnena ya faɗi a falon nan ban ganshi ba,'juyawa ammi tayi tare da kai idanunta kan hosana dake tsaye tana magana,a wani slow ta sanya hannu ta zame glass ɗin dake a fuskarta,tashiga ƙare ma hosana kallo,cike da mamaki tace"Ina kuka samu matashiyar yarinya acikin gidan nan"?sunnar da kai ƙasa Abusufyan yayi yana faman zare ido zuciyarshi tamkar zata faso kirjinshi ta fito saboda razana,
Shiru kowa yayi mata aka rasa wanda zai buɗe baki ya bata amsa,
Jin sunyi banza da ita yasa ta kira hosana da hannunta"Zo nan,"
Shiga ciki hosana tayi tare da tsayawa agaban Ammi tace"Gani,"
"Wanene mahaifinki a wurin nan"tayi maganar tana nunasu da sandar hannunta,
...murmushi hosana ta saki tare da ɗaga yatsan hannunta ta nuna abusufyan sannan tace"Gashi nan,shine daddynmu,ni dasu Sehrish da Jahad,"
..a wayance Ammi tace"Oh harku nawa ne a wurinshi"?
Hosana tace"Ƴan ukune mu,ko in kira maki su jahad ki gansu?"
Cike da mamaki Ammi tace"kira mun su in gansu,"da gudu hosana ta nufi ɗakinsu don ta kira su jahad,
Tashin hankali,
Wani irin gumi ne ya shiga fesowa daga jikin abusufyan,gaba ɗaya duk yabi ya kama kansa,jikinshi sae faman kerma yakeyi,bashi kaɗae ba hatta sauran dake a wurin zaune,kowa saida yasha jinin jikinsa,musamman Kallon da Ammi ta dinga binsu dashi ɗaya bayan ɗaya,kallon tuhuma,
Lokacin da hosana ta faɗa corridor ɗin ɗakunansu,hayaam na tsaye a wurin,tana ganinta tasha gabanta tare da cewa"daga ina kike"?
Murguɗa mata baki hosana tayi kafin tace"Ni bansan wacece keba,ki bani hanya in wuce,su jahad zan kira,wata tsohuwa ce fara tass take son ganinsu,"
Jin haka yasa hayaam ta gane cewa cewa AMMI ce ke son ganinsu,shu'umin murmushin nan nata tasaki,kafin ta matsa ma hosana hanya ta wuce,jinjina kai hayaam tayi tana faɗin"hada wani zumuɗin Ammi ta kirasu,basu son cewa watan korarsu daga gidan yayi ba,"tana ƙarasa maganar ta nufi ɗakin da Aunty babba take,tana shiga ta sanar da ita cewar ga Ammi can tasa a kira mata ƴa'ƴan Abusufyan,jiki na rawa Aunty babba ta taso,suka fito daga ɗakin domin suje yin la6e,don su ga irin korar karen da ammi zatasa ayi ma su Sehrish,
Bada jimawa ba,Hosana ta fito hannunta ruƙe dana sehrish,ɗayan hannun kuma ruƙe da hannun Jahad,jikinsu na sanye da hijab don tunda su kayi sallar Magrib basu ciresu ba,hosana ce kawai ta cire hijabin jikinta,ta yafa mayafi akanta,
da sallama a bakunansu suka shigo cikin falon,ya salam ae tuni Abusufyan ya zauna ƙasa dirshan yana lazimi,Abba kuwa sae faman jinjina kai yakeyi,gwaggon katsina kuwa tana ganinsu jahad ta shiga zare na mazurai don tasan cewa ƙarshe abun kanta zai ƙare ita da ta sanya mashi hannu ta ɗaure mashi mazaunai wurin yin auren batare da sanin Ammi ba,kowa dai yashiga zullumin abunda zai biyo baya,
Aunty babba kuwa suna la6e ita da hayaam sun kasa kunne suna jiran jin mai zai biyo baya,jikinsu sae faman tsuma yakeyi,
Zuba masu ido Ammi tayi tana kallonsu,one by one,ganin yadda matar ta ƙura masu ido yasa duk suka sha jinin jikinsu,daƙyar suka iya haɗa baki wurin gaishe da ita"Ina yini,"
Bata amsa masu gaisuwar tasu ba,sae nuni da tayi masu da sandar hannunta alamar su zauna,wuri suka samu agaban kujerar da su Omar ke zaune,suka zauna daga ƙasa tare da lankwashe ƙafafunsu,zaman cin tuwo,
Nuna Sehrish tayi da sandar hannunta