Showing 159001 words to 162000 words out of 307403 words
Chapter 54 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
ta watsa mashi tana ƴar dariya tace"wlh ƙarya kake yi mun nafa son shekarunka,Allah kamar ma mun girmeka,don ka ganka dogo shiyasa zaka 6oye mun shekarunka ko'?
Murmushi ya ɗan saki tare da nuna mata sofa ɗin dake a falon yace"Mu zauna mana,nagaji da tsayuwa,baccin ma bai isheni ba Allah,naji daɗin sanyin nan ba kamar gidanmu ba,fankar ɗakina ma,6eraye sun lalata mun ita,"ya ƙarasa maganar tare da samun wuri ya zauna,itama ta zauna suna fuskantar juna,
Sae faman bin falon yakeyi da kallo,ƙasa ƙasa yayi da muryarshi ya ambaci sunanta"rishi,"
"Na'am"ta amsa mashi
"Wai wannan mai mutuncin,mai kama dake ɗinnan Yayanku ne"?
"Me hali dai bazai ta6a canzawa ba,ashe har yanzu kana nan da wannan tsegumin naka kamar mace"?cike da zolaya tayi maganar,harararta yayi tare da cewa"Ae tsegumin nawa ku ma yayi maku amfani!ko kinmanta ni ne ɗan leƙan asirin Mamanmu?ita ke cewa nazo gidanku najiyo mata idan kun ci abinci,idan nayi la6e naji kuna kukan yunwa sai in watsa da gudu inje in sanar mata.... "
Dariya sehrish tayi har haƙoranta suka bayyana,baki asake Sadeeq yace"Wai!madarar kyau!rishi kinga yadda kikayi kyau kuwa da kika washe bakinki Fararen haƙoranki suka fito kamar na Ketrina kef?ba kamar lokacin da ba,Haƙorannan Jawur dasu kona Maclean ma babu,"
ɗaure fuska sehrish tayi kamar ta rufe shi da bugu tace"kai Sadeeq ɗazu fa naji kana cema baban ku,adaina tuna baya,shine nikuma zaka dinga tunamun abunda ya wuce don wulakanci,"
Fashewa yayi da dariya,bin shi tayi da kallo bakowa ya faɗo mata arai ba,fa ce junaid ɗinsu,lokaci guda taji tana kewarshi,
"Sadeeq,mutumin da kake magana akanshi,ba yayana bane,Shi ne mahaifin mu!"tunkan ta taƙarasa maganar ya katseta da cewa"kutmelesi!Amma dai ƙarya kikeyi mun ko?idan shine mahaifinku,Wanccan mai dogon gemun fa?wanene Shi?cike da tuhuma yayi mata tambayar,
Shiru tayi bata bashi amsa ba,tsareta yayi har sai da ta faɗa mashi komai daya faru arayuwarsu,wani Shu'umin murmushi taga yana saki,hakan yasa tace"Wai lafiya"?
"Rishi aike yanzu hajiya ce,Ashe dama ku ƴa'ƴan masu kuɗi ne?Ae wlh bazata sa6u ba,Tunda kunyi arziƙi yanzu sai a ramama kura aniyarta koba haka ba"?yayi maganar yana ɗage mata gira,irin na ƴan duniyar nan,
Dariya sosai tayi,bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"Faɗamun dame dame za'a rama maka"?
Lissafo mata ya shiga yi"Ragowar abinci na da kuka saba cinye mun,tare da ƴan kayan sawa na da maman mu ke kwashewa tana kaima Oummanku don asanya maku kin tuna'?
Shiru sehrish tayi bata bashi amsa ba,bakomai take tunawa ba,fa ce rayuwarsu ta baya,ya tuna mata da lokacin da Maman Sadeeq ke aiko da kayanshi don acanza masu kaya,saboda nasu duk sun yayyage,tun sunayi ma Oummansu kukan bazasu sanya kayan maza ba har suka haƙura ta dinga sanya masu,haka tsoffin takalman sadeeq haka aka dinga kawo masu don su rinka sama kafafunsu,
Ganin hawaye akan fuskarta yasa Sadeeq saurin mikewa ya dawo gefenta ya zauna cikin lallashi yace"rishi nifa wasa nake yi maki,wlh ban faɗi hakan ba,da niyyar in 6ata maki rai ba,kawai inaso in sanyaki nishadi ne,saboda yanzu ta ko'ina Allah ya hore maku,'
Cikin shessheƙar kuka tace"ni baka 6ata mun rai ba sadeeq,na tuna da irin rayuwar da muka yi ne abaya,kaima kasan dole inyi kuka in na tuna,"
"Tunda baki so,mu manta da komai,bazan ƙara tuna maki ba,Yanzu dai faɗamun nawa ne acikin asusun bankin ki?nawa kika tara"?
Fashewa tayi da dariya jin abunda yace,
Da hannu ta nuna mashi yatsunta guda biyar,
"ɗari biyar"?yayi guessing yana kallonta,girgiza mashi kai tayi alamar a'a,
"Dubu biyar"?ya sake canka,cike da sa ran ya faɗi dai dai,
Girgiza mashi kai ta kuma yi,
"To dubu ɗari biyar,"nan ma ta girgiza mashi kai Alamar a'a,tur6une fuska ya ɗanyi saboda ya fara tunanin kamar ƙarya takeson ta shirga mashi,
A ƙule yace"Miliyan biyar"murmushi ta sakar mashi tare da jinjina mashi kai alamar ya faɗi dai dai,
wani kallon rainin wayau ya jefa mata tare da cewa"Alkazzubu haramun,"
"Wlh dagaske nake maka,Ina da kuɗi sosai sunma fi miliyan biyar amma basa a hannuna,duk suna a wurin Daddyn...."kasa ƙarasa maganar tayi,ganin Sadeeq ya sauko daga saman kujerar ya dawo ƙasa saman carpet ya zauna agabanta tare da lankwashe ƙafafunshi zaman cin tuwo,
"Lafiya naga ka dawo ƙasa,"?
Hannu yasa tare da ɗan sosa ƙeyarshi yace"Ae matsayinmu ba ɗaya ba,kefa Millionaire ce,ni kuma Faƙiri mamallakin naira ɗari biyar acikin aljihu,bazaiyiwu mu zauna a saman kujera ɗaya ba,abun ma sam babu ladabi acikinsa,
Fashewa Sehrish tayi da dariya,Yau sadeeq ya sanyata nishaɗi sosai,komai yayi yana tuna mata da junaid,
"Aunty sehrish,kinji nace ina da ɗari biyar ko?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh , "Yawwa,wlh itama Wanki da guga nayi a shagon wani abokina aka bani ita,Nifa nan da kike gani na sai inyi fiye da wata ɗaya babu ko sisi a aljihuna,Babanmu kuwa idan kinga ya bani kuɗi to sai dai fa,idan naje islamiyya ne,haka itama maman mu,ataƙaice dai bari in fito maki a mutun,wlh Sehrish ko abun hawa bandashi,tunda keke na ya samu matsala ba'a ƙara gyaramun shi ba,naje wurin mai gyara yace sai ya ci dubu uku,tun daga nan na jingine shi gefe guda,
Zuba mashi ido sehrish tayi tana kallonshi,yadda kasan ɗan Almajiri haka ya zauna yana zayyano mata matsolilin dayake fama dasu na rashin kuɗi,ta kasa kunne tana sauraronshi,
A 6angaren Abusufyan kuwa,lokacin daya shiga yayi arba Da abu a zaune dirshan saman gadon tana faman zazzare idanuwanta,ba ƙaramin daɗi yaji ba,ƙarasa shiga ciki yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna,zuba mashi ido tayi tana kallonshi,
Murmushi ya sakar mata tare da miƙa mata hannunshi,zuba ma tafin hannunshi ido tayi tana kallonshi,ta gane fuskarshi a matsayin wanda ya taimaketa,ta fito daga hannun masu fararen kayan nan,
"Ina ƴa'ƴana suke"?muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,
"Kada ki damu,ƴa'ƴanki suna atare dani zan kaiki wurinsu,kina so ko"?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
"A ƙarshe dai duk yawace yawacen naki,gashi kin dawo wurina abu,saboda ƙaddararki tana atare dani,kamar yadda kika zama ƙaddarata nima,Ashe da rabon zan sake ganin wannan kyakkyawar fuskartaki"?calmly yayi maganar,tsantsar sonta ne da ƙaunarta ke addabarshi,ji yake yi tamkar ya mayar da ita cikin cikinshi,
"Abu na,Faɗamun har yanzu kina sona kamar yadda nima nakeson ki,"
Wuƙi wuƙi tayi mashi da ido tana kallonshi,sam batasan inda zacen nashi ya dosa ba,
"Kaine ka kashe mun babana ko?kuma ka rabani da ƴa'ƴana ko?Zaka kashe munsu ko"?
girgiza kai Abusufyan yayi tare da cewa"ni bani bane na kashe maki mahaifinki ba abu,Nifa ne Abusufyan ɗinki,uban ƴa'ƴanki,ba zaki iya tunawa ba ko kaɗan,"
Kallon dayaga tana binshi dashi ne ya tabbatar mashi da cewar a harzuke take,jira take yayi yunƙurin matsawa kusa da ita,Yasha bugu,
Dariya ya ɗan yi tare dacewa"kwantar da hankalinki,
⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫
*_MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI_*
*DOMIN. DAWO DA MARTABAN NONONKI*
Shin ko kinsan nono yanada matukar muhimmanci a wajan mai gida ,? Shin ko kinsan babu abunda namiji yafiso yafi daukar hankalinahi kamar cikar k'irji , ? To nono shine babban Martaban mace a wajan mijinta , don babu namijin da zaiso mace mai yakunannen nono kamar silifas ,wannan yasa Nazo maku da sahihi kuma ingantaccen maganin nono Wanda bashida wata matsala hadin gargajiya ne , acikin lokaci kalilan zakisha mamakin yadda nononki zai ciko sosai Wanda wannan cikowar ita zata bashi damar da zai tashi sosai ta yadda kema zaki Shiga cikin jerin mata masu aji agaban mazajensu ........kedai hanzarta ki nemi mmn Yusuf mai kayan mata yar mutan sokoto zaki samu ingantattun kayan mata masu tafiyar da hankalin maigida.......don neman Karin bayani 07069711327 ......
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Am sorry🙏
Babu abunda zan yi maki,a haka ma daɗi nake ji,kina kallona ina kallonki,"murguɗa mashi baki tayi tare da kawar da idanuwanta gefe guda,
Wuraren ƙarfe 8 na safe,nurse ɗin dake kula da abu ta ƙaraso,taimaka mata tayi wurin yin wanka a toilet ta gyara mata jikinta,da gashin kanta ko'ina ta wanke mata shi,lokaci guda Abu ta fito fess da ita,ƴar doguwar rigar material ta sanya mata,ita kanta abun sai murna takeyi da aka gyara mata gashin kanta da jikinta,taji daɗin jikinta sosai,Sehrish ce ta shirya masu breakfast gaba dayansu suka hallara a falo suka zauna suna ci,banda abu dake zaune a bedroom ɗinta tare da nurse ɗin,saboda ita kaɗai zata iya da ita,dama sune masu kula dasu a gidan mahaukatan,Sun san duk wasu dabaru da zasu bi wurin tafiyar dasu batare da sunsha wahala ba,a baki ta dinga bata abincin kalacinta tana ci,saboda bata iya ci da hannunta ba,Zubarwa takeyi a ƙasa,kamar ƙaramar yarinya haka take yin wasa da abincin,Bayan nurse ɗin ta kammala kimtsata,Dr yazo ya duba ta,bayan tafiyarshi ne ta samu bacci,
*SGR*
Da gudun gaske motarsu ta shararo izuwa cikin gidan yadda kasan zasu tashi sama,gudu bana wasa ba,Sam ya kasa samun natsuwa acikin zuciyarshi,jikinshi sai tsuma yake yi a ƙagare yake dasu ƙarasa cikin gidan,Armstrong nazaune agefenshi sai faman tausarshi yake yi ganin yadda ya tashi hankalinshi,slowly sojan daya ɗaukkosu from Airport ya rage gudun motar lokacin da ya ƙaraso wurin da zai yi parking ɗinta,saboda tsabar sauri,tun kafin a buɗe mashi ƙopa yasa ƙafarshi azafafe ya harba ƙopar,gudu gudu sauri dauri ya nufi cikin main palour ɗinsu,wayaam babu kowa tsit kake ji,A hanzarce ya haura upstairs direct ya wuce bedroom ɗin junaid,a buɗe ya samu ƙopar ɗakin hannu yasa ya tura tare da shigewa ciki,gabanshi ne ya faɗi rasss ganin babu junaid,saboda yasan cewa junaid bai zuwa ko'ina tunda sanyin safiya,adai irin wannan lokacin zaka same shi kwance saman gadonshi rungume da pillow,
Muryarshi tamkar zata fasa maƙoshinshi haka ya shiga ƙwala mashi kira"JUNAID!JUNAID!!JUNAID!!!"a gaggauce ya nufi toilet ɗinshi yasa hannu ya tura,nan ma yaga wayaam babu kowa,jiki asanyaye ya fito daga ɗakin junaid ya wuce bedroom ɗin Marshal Omar,tura ƙopar yayi ya shiga daga ciki,babu kowa a falonsa,bedroom ɗinshi ya nufa nan ma babu kowa,tashin hankali!
Wani irin wahallallan yawu ya haɗiya,fitowa yayi daga part ɗin Omar ya nufo downstairs,gudu gudu sauri sauri haka yake taka staircases ɗin,yana a second to the last step,yaji shigowar message a wayarshi,dakatawa yayi tare da sanya hannu cikin trouser pocket ɗinsa,duba screen ɗin wayar yayi,bayan ya sanya finger ɗinsa ya buɗe saƙon,a tsanake ya soma karantawa
_Gm Sir,ina fata ban takura maka ba,Marshal yana kwance a gadon asibitin mu yanzu haka_
Message from doctor Emran,Hankalinshi yayi mugun tashi,a ruɗe ya furta"Omar?kwance a gadon asibiti?
Da sauri ya nufi hanyar fita daga falon,fitarshi keda wuya,Hosana ta fito daga bedroom ɗinsu,tasha kuka kamar ranta zai fita,saboda an barta ita kaɗai,babu Jahad babu Sehrish babu Junaid,bugu da ƙari kuma babu Ya Omar,tun ɗazu take ta zaryar zuwa ɗakin shi,don taga ko ya dawo amma babu shi,palour ta dawo ta zauna saman sofa,hawaye wasu na bin wasu,fuskar ta jiƙe sharkaf,
"Hosana"!jin muryar Azmee yasa ta miƙe tare da juyowa tana kallonta,sanye take cikin doguwar jallabiya,tayi rolling mayafi akanta,
Tunkararta hosana tayi cikin shessheƙar kuka tace"A...aunty azmee har yanzu basu dawo ba,ni kaɗai aka bari,gidan duk babu daɗi,"
Janyota Azmee tayi tare da rungumeta ajikinta,tana ɗan lallashinta,
"Don't worry ur self,wipe ur tears,in sha Allah nasan nan bada jimawa ba,Ya Omar ɗinki zai dawo cikin gidan nan,Just calm down ur mind,"ta ƙarasa maganar tare da ɗago hosana daga jikinta,
"Aunty azmee,shiru fa since yesterday night,kuma har kiran layinshi nayi wayarshi a kashe,Ni shikenan kowa ya tafi ya barni,dama ba so na akeyi ba,"tana magana hawaye na sharara akan fuskarta,ɗan murmushi Azmee tayi tare da kai hannunta saman fuskar hosana,taja kumatunta tare da cewa"Haba Babyn Omar,shalelen Abusufyan,kinfi kowa sanin yadda ya Omar ɗinki ke tsananin sonki,Ina da tabbacin cewa duk inda yake a yanzu,tunaninki yake yi,ya hosanata ta ke?me take yi a yanzu?tana kewata kuwa?
Murmushi hosana ta saki har hankalinta ya ɗan kwanta jin abunda Azmee tace,
"Aunty azmee kin tabbata cewa ya Omar yana tunani na yanzu haka"?
ɗaga mata kai azmee tayi alamar eh,kafin tace"Kina aransa mana,yanzu abunda za'ayi,me zai hana mu shiga kitchen atare mu haɗa mashi lafiyayyen breakfast,da zarar ya dawo gida kinga sai ki kai mashi,Zaiji daɗi sosai,"
Cike da zumuɗi hosana tace"Mu tafi kitchen ɗin,Hada chocolate zamu haɗa mashi,nasan zaiji daɗinshi sosai"
Ruƙo hannunta Azmee tayi atare suka wuce cikin kitchen,Suna aiki suna fira,gwanin ban sha'awa,
*SGR HOSPITAL*
Slowly Motarsu ta shiga cikin katafaren asibitin,bayan Armstrong yayi parking ɗin Motar,buɗewa Sgr yayi a hanzarce ya wuce cikin asibitin da saurin gaske,Armstrong na biye dashi,Tashin hankali,Soldiers ɗin da suka kawo Marshal Omar,Suna yin arba da fuskar Sgr nan fa kowa yasha jinin jikinshi,Hankalinshi a matuƙar tashe yake kallonsu one by one,Sara mashi suka shiga yi,batare da ya tanka masu ba,jiki a sanyaye yake tafiya kamar wanda aka zarewa Lakar jikinshi,tuni ya soma karaya,Zuciyarshi sai tsinkewa take yi,
Lokacin da ya ƙaraso wurin da Major ke tsaye,Suna haɗa ido major ya saddar da kanshi ƙasa,yayin da zuciyarshi ke bugawa,Don yasan cewa dole ya tuhume shi game da kashe mashi waya da yayi,
"Major"da wata irin raunanniyar Murya Sgr ya ambaci sunanshi,
Batare da ya ɗago sun haɗa ido ba yace"Na'am yalla6ai,"
"Where's Omar"?
Da hannu major ya nuna mashi medical room ɗin da aka kwantar dashi,batare da ya kuma tambayarshi wani abu ba,Ya wuce cikin ɗakin har izuwa gaban gadon da Marshal ke kwance,babu alamun sauƙi a jikinshi,
biyo bayanshi Major yayi tare da Armstrong suka tsaya agefe,
Juyowa yayi tare da wurga eyeballs ɗinshi kan fuskar Major,tun kafin yayi magana a ruɗe Major ya dakatar dashi"Am sorry sir,don Allah don sonka da manzon Allah (SAW)kada ka tambayeni komai,saboda bazan iya amsa maka ba,"
gyaɗa kai kawai yayi tare da juyawa daƙyar ya iya ɗaga kafarshi har izuwa gefen gadon ya zauna,yana kallon Omar,ya jima yana mamakin menene silar kwantar dashi gadon asibiti?A iya sanin shi ba ƙaramin abune zaisa a kwantar da Omar gadon asibiti ba,
Turo ƙopa Dr Emran yayi ganin su Armstrong sunyi cirko cirko yasa shima yaja gefe ɗaya ya tsaya,To fa kowa tunani ya shiga yi taya zasu fahimtar da Sgr batare da ya haukace masu ba,
"Major!"ya ambaci sunanshi,
Hankali atashe major yace"Na'am Yalla6ai,"
"Meya faru da ɗan uwana ne?"ƴan kame kame major ya shiga yi duk yabi ya susuce ya rasa ta ina zai fara kora mashi bayani,
"Emran!meya faru da Omar ne"?ya sake tambayar Dr emran,Shiru Emran yayi shima ya rasa ta ina zai fara,Jin sunyi mashi shiru yasa zuciyarshi ta hasala,jikinshi na kerma ya miƙe tare da kallonsu,ranshi a matuƙar 6ace yake magana!
"Bazaku amsa mun ba!Kun wani zuba min ido kuna kallona,kun mayar dani tamkar wani shashasha,"hankalinsu ya tashi matuƙa,kowa sai motsa la66ansa yake yi,suna so suyi magana amma fargaba ta hanasu,
Hannu yasa ya daki ƙirjinshi da ƙarfi,lokaci guda idanuwanshi suka juye tamkar ba mutun ba,rarumar plastic chair ɗin dake agaban gadon Marshal yayi azafafe yayi wurgi da ita,nan take kujerar ta yi gefe guda ta daki ƙasan tiles,
A razane suke kallonshi,wata irin zufa ce ta soma gangarowa ta gefen fuskarshi,ɗaya bayan ɗaya yake binsu da kallo,jikinsu sai kerma yake yi,Dr Emran ma ƙoƙarin guduwa yake yi,Armstrong kuwa sai lalla6ashi yake yi akan su sanar dashi abunda ke faruwa tun kafin ya birkice masu,
"Rafayet"!muryar Marshal Omar ce ta dawo dashi cikin hayyacinshi,jiki na rawa ya juya yana kallonshi,a hankali Omar ke buɗe idanuwanshi waɗanda sukayi jawur dasu,zufa ta ko'ina ajikinshi duk da sanyin A.c ɗin dake akwai,da sauri Sgr ya koma gefen gadon ya zauna tare da ruƙo hannunshi,
"Omar pls tell me,what's happening wit u?meyasa na ganka a asibiti?Are u not feeling well"?daƙyar Marshal ya samu ya yunƙura tare da mikewa ya zauna,numfashinshi da huci yake fita,bawan Allah yaji jiki sosai,wasu zafafan hawaye ne suka wanke mashi fuskarshi,
Muryarshi na rawa yace"Bro,Yaushe ka dawo Abuja?
Muryar Sgr tamkar zai yi kuka yace"Omar duk ba wannan ba,Where's Junaid?nadamu akan son ganinshi,Daddy ma yana ta kira na saboda rashin samun Junaid a waya..."ya ƙarasa maganar yana faman haɗiyar yawu,
Marshal na ƙoƙarin buɗe baki yayi mashi magana,Karaf idanuwanshi suka sauka akan Major dake girgiza mashi kai alamar karya kuskura ya faɗa mashi,kasa magana Omar yayi,sai ma zuba mashi ido da yayi yana kallonshi,
"Wai menene haka?kowa na tambaya sai yayi mun shiru babu magana?meke faruwa ne!in wani abu ne ya faru ba zaku sanar mun ba ne?Ni fa Musulmi ne!nayi imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau,ku faɗa mun mana......"ya ƙarasa maganar fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa,
Daƙyar Omar ya iya buɗe baki yace"Babu abunda ya faru,Junaid yana lafiya...."tunkan ya ƙarasa maganar Sgr yace"That's impossible!Taya zaka ce mun junaid yana lafiya kuma in yarda?To idan yana nan a nuna mun shi inaso in ganshi!Meyasa layinshi a kashe?meyasa nake ganin hawaye akan fuskarka?
Daurewa kawai Omar keyi,saboda kukan dake cinshi,So yake ya fashe da kuka ko ya samu ya rage raɗaɗin dake acikin zuciyarshi,
Tausasa murya Sgr yayi"pls Omar,ka sanar dani!ina ƙanina yake?wani abu ya faru dashi ne?saboda shi jiya ko bacci ban samu ba,
Da sauri Omar ya sanya tafin hannunshi tare da share hawayenshi,
"Rafayet!I won't hide it for u,Junaid was kidnapped...."daƙyar ya ƙarasa maganar ganin irin kallon da Sgr ke jefa mashi,kallon tuhuma,
"Omar,ni kake faɗama cewa Anyi kidnapping ɗin junaid"?shiru Omar yayi batare da yace mashi komai ba,
"Omar,If it is true,Junaid was kidnapped,as a Senior Soldier with the rank of Marshal,you will be brave enough to rescue him,bawai na ganka kwance a gadon asibiti ba kana zubar da hawaye,"tausasa muryarshi yayi"don Allah Omar ka faɗa mun gaskiyar abunda ya faru,kada kasa zuciyata ta buga,Ina junaid ɗina yake?meya faru dashi?yanayin yadda yayi maganar ne yasa jikinsu kara yin sanyi lakwas,
Daƙyar Major ya daure ya cije,ya yi karfin halin bude baki yace"Sir,Junaid ya riga mu gidan gaskiya!junaid ya koma ga mahalicci....."bai ƙarasa maganar ba sakamakon Zaburar da yaga Sgr yayi gadan gadan ya tunkareshi,yana faɗin",repeat what u just said Major!"yana magana yana naɗe hannun rigarshi alamar zaiyi dambe,da sauri Omar ya ambaci sunanshi Rafayet,wanda hakan ya dakatar dashi tare da juyawa yana kallon Omar,
Cikin shesshekar kuka Marshal yace"Junaid has