Showing 246001 words to 249000 words out of 307403 words
Chapter 83 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
dasu jiya
"Ae daga ɗakinsu nake,Na same su suna shiryawa,"
Jinjina kai tayi"Masha Allah,zaki iya tafiya,"
Buɗe kopar tayi ta fuce izuwa ɗaki na gaba,
Jahad na kwance,since yesterday night bata runtsa ba,tashiga damuwa sosai akan junaid,hankalinta yaƙi kwanciya,tunda ya nuna baisanta ba,duk ta rasa natsuwarta,ita kaɗai Ce kwance saman gadon,Hosana na acikin toilet,
Kwankwasa ƙopar ɗakin akayi,Muryarta adisashe tace"Wanene"?
Muryar Hafsat ta juyo daga waje,
"Nice,"
saukowa tayi daga saman gadon taƙarasa tare da buɗe mata ƙopar,
"Aunty hafsat"Tsaye take jikinta sanye da riga da wando,ta yafa mayafi akanta,
"Jahad ce ko sehrish,"tayi tambayar ne don bata ganeta ba,
"Jahad ce,Kin tashi lafiya?Ya gajiyar tafiya"?
"Lafiyalou Alhamdullih"ta amsa mata tare da shugowa daga cikin ɗakin,
Gefen gadonsu ta zauna,kafin tace"Jahad inason magana dake,"jin haka yasa jahad ta koma gefenta ta zauna,ina sauraronki Aunty hafsat,
Calmy ta soma magana"Game da abunda Mommyna tayi maku,Ina nema mata yafiya a wurinku,dan Nasan haƙƙinku ne ke bibiyarta,Jahad tana cikin mawuyacin hali,Yanzu haka maganar da nake yi maki,ƙafarta ta ru6e ta lalace,A sakamakon wani mai mota daya bugeta A enugu,Ni bansan ma meya kaita can ba"idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,
Hankali tashe jahad Tasoma ambaton'Innalallahi wa'inna ilaihirra'jin!"
"Wlh jahad,ta zama abun tausayi,A gefen bishiya take kwana,dare da rana tana zaune a wurin,Kona abinci bata dashi sai in ansamu na Allah ya bata sadaqa,tukunna take samun abunda zata sama cikinta,"
Jahad sarkin tausayi tuni hawaye sun wanke mata fuskarta,
Hosana dake a la6e cikin toilet tana sauraronsu,Sai 6a66aka dariya takeyi hada dafe cikinta,Don bala'e ko kuskure bakinta batayi ba,yayi dama dama da kumfa,Hannunta ruƙe da brush,
"Allah sarki aunty hafsat,wlh na tausaya mata baiwar Allah,Ni indan tani ce,Tuntuni na yafe mata,Amma meyasa ba ataimaka mata ba"?
"Jahad bamusan komai game da tafiyarta enugu ba,wayarta ma ba'a samu,Ashe tun lokacin da mai motar ya bugeta,Anan ta rasa wayarta,Shiyasa bamusan halin da take ciki ba,Amma yanzu nayiwa daddy magana,Yanzu haka tana kwance gadon asibiti acan enugun,saboda lalacewar da ƙafar tayi baza a iya ɗaukota kaitsaye ba zuwa abuja,Dole acan za'a fara yi mata aiki,Za'a cire ƙafarne....."
Tunkan hafsat takai ƙarshen maganarta,Hosana dake ƙumshe dariya acikin toilet,ta tuntsire da wata irin mahaukaciyar dariya,
"Waye acikin toilet?Naji kamar sautin dariya"
Da sauri jahad tace"Bakowa aunty hafsat,Allah Ya bata lafiya,in sha Allah zata ji sauƙi,zamu tayata da addu'a,"
Hannu tasa tana share hawayen fuskarta,Kalaman jahad sun sanyaya mata zuciyarta,
'Nagode sosai jahad,Yanzu saura hosana inaso na nema mata yafiyarta,"
Jahad na ƙoƙarin buɗe baki tayi magana,hosana dake acikin toilet ta ɗaga murya tare da cewa"Wlh na yafe mata,tunda an gutsire kafar,Allah ya kyauta gaba,"
Da sauri jahad ta daka mata tsawa"Hosana ya ishe ki haka,Wai meyasa baki iya magana ba,"
Hafsat kuwa murya asanyaye tace"Nagode hosana,Ni banga laifinta ba,Ai ita taja ma kanta,"tana kai ƙarshen maganar,ta nufi hanyar fita daga dakin,bayan fitarta,hosana ta futo daga cikin toilet,bakinta washe,
Harara Jahad ta jefe mata"Wawuya kawai sullu6iya,Yanzu abunda kika faɗa ma Aunty hafsat ya dace"?
Murguɗa mata baki Hosana tayi"Anje an faɗa,Allah shi ƙara in ma da ƙarin Ya ƙara,Uban dayasa ta kulle mu acikin store kamar wasu dabbobi,Wlh ni daɗi naji,wai agefen bishiya take kwana,har na hango ƙoƙwan bararta....."fashewa ta kuma yi da dariya hada dafe ciki,jahad dai bata tanka mata ba,ido kawai tabi ta dashi,cike da takaici,
Guntun tsoki taja"Ya omar dai baiyi dacen mata ba,"
Harara hosana ta watsa mata kafin tace"eh ɗin ina ruwanki?A haka ya gani yana so,ɗan baƙin ciki sai dai ya mutu,Ni da ya Omar mutu ka raba takalmin kaza,"
Girgiza kai kawai Tayi batare da ta kuma tanka mata ba,Komawa tayi gefen gadon ta zauna,
*Junaid Romeo*
Har cikin ɗaki,Mommy ta shigo mashi da breakfast ɗinshi,Jiya atare dashi suka kwana,dama tunda ya fara jinya a tsakiyarsu suke sanyashi,Yanzu kuma ya fara jin sauki,Ya fara tunanin komawa bedroom ɗinshi,
A kwance ta same shi idanuwanshi na fuskantar ceilling,yayin da hawaye yake gangarowa kan fuskarsa,hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,
"Junaid meke damunka ne"?tayi maganar a yayin da take ƙoƙarin zama gefenshi bayan ta ajiye mashi tray din kayan abinci saman table,
Dakyar ya iya mikewa daga kwanciyar da yayi ya zaune,hannu tasa tana goge mashi hawayen dake akan fuskarshi
"Pls tell me meyasa kake zubar da hawayenka"?ta tambaya cikin damuwa sosai,.
"Mommy,ina aunty azmee take"?
Ɗaure fuska Alex tayi"Junaid kar na sake ji,kayi mun zancenta,Yanzu azmee bata atare damu tana a prison,"
Cikin shessheƙar kuka yace"Mommy aunty azmee tana a prison why?Meyasa za'a kaita can?nifa bata cutar dani ba....."rufe mashi baki mommy tayi da tafin hannunta"Shut up!ashe baka da hankali!duk irin cin zalun da tayi maka,amma kake faɗin bata cutar dakai ba?itace silar ciwon asthma ɗinka,sannan itace Ta mayar dakai soko ta hanaka ɗaukar karatu acikin brain ɗinka,A haka har kake cewa bata Cutar dakai ba"?shiru yayi baice komai ba,still hawaye basu daina zuba akan fuskarshi ba,
'Why junaid?just because of azmee kake zubar da expensive tears ɗinka?kana so ka 6ata mun rai ko"?
Girgiza kai yayi"Am sorry mommy,Bazan ƙara magana akanta ba,"cikin sanyin murya yayi maganar,
Hugging ɗinshi tayi ajikinta"yawwa my baby boy,mu manta da abunda ya faru,Yakama ka mayar da hankalinka akan future ɗinka,yanzu dai bari na fara zuba maka abinci kaci ka koshi sai muyi magana mai mahimmanci akan rayuwarka,"
Janye shi tayi daga jikinta,sannan ta soma yin serving dinshi,Ta tasa shi gaba Sai da yaci ya ƙoshi tukunna suka soma magana dashi,Akan karatunshi,
*Boss Bature*
Wuraren ƙarfe 12 na rana,Gaba ɗaya matasan gidan suka shirya cikin kakinsu na sojoji,A jere motocinsu suka fita daga cikin gidan,babban taro su kayi a headquater ɗinsu,domin ƙarrama matasan gidan tare da ƙara masu Matsayin aikinsu,Farin ciki a wurin abbansu kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,bakinshi Yaƙi rufuwa,ganin yadda ake ta yabon ƴa'ƴanshi,Manya manyan shuwagabanni na Armed forces suka halarci taron,na ƙasashe daban daban,
*SEHRISH*
Bata jima da fitowa daga wanka ba,Jikinta sanye da bathrobe,ta yarfo da gashin kanta ta gefen wuyanta,a takure ta samu amrish saman gadon,still taƙi sakin jikinta tayi rayuwarta kamar kowa,
"Wai meke damunki ne"?
"Babu komai"ta bata amsa a taƙaice,
"Idan kina jin kaɗaici ki fita waje mana,Ga ƴan uwa can suna ta fira a palour,"
"Bazan iya zuwa wurinsu ba,"
Tsananin tausayinta ya kamata,baiwar Allah duk ta tsani rayuwarta,ta takure kanta,
"Zanyi magana da daddy,May be idan shi yayi maki magana zaki faɗa mashi damuwarki,"
Da sauri tace"dan Allah kada kiyi mashi magana,wlh babu abunda ke damuna,rashin sabo ne nan da ɗan wani lokaci zan saba da kowa,"
Gyaɗa kai sehrish tayi tare da samun wuri gaban mirror ta zauna,
Zamanta keda wuya wayarta dake ajiye saman side drawer ta soma ringing,hannu amrish tasa ta ɗauki wayar,kafin ta sauko daga saman gadon ta miƙa mata,
Kar6ar wayar Sehrish tayi tare da kallon screen ɗin,My Boss Man ne ke kiranta,
Tayi mamakin ganin kiran Sgr,a wannan lokacin,picking call ɗin tayi tare da manna wayar a kunnanta,
"Assalamu alaikum,"
Bai amsa mata sallamarta ba,Sai cewa yayi"what are u doing now"?
"Yanzu na fito daga wanka,ina shiryawa"cikin sanyin murya ta bashi amsa,
"Its okey,before na dawo,ki shirya mun kanki,"
cike da mamaki ta amsa mashi da"Toh "
Daga haka bai ƙara cewa komai ba,yayi rejecting kiran,tana ƙoƙarin ajiye wayar kiran Aunty azeema ya shigo wayar,murmushi ta saki dama tun jiya take ta son suyi magana da ita,
Ɗaga kiran tayi tare da manna wayar akan kunnanta,tunkafin tayi sallama hajiya azeema tace"Daughter,ki sameni a ɗakina,inason magana dake,"
Cike da zumuɗi Sehrish ta amsa mata da toh auntyna Am on my way,
Bayan ta katse wayar ta miƙe,ta nufi wardrobe,dogon hijabi ta ɗauko ta zumbulashi ajikinta,ɗaukar wayarta dake ajiye saman mirror tayi,Amrish ta mika ma wayar"Ki yi amfani da ita,Zata ɗebe maki kewa kafin na dawo,zanje wurin auntyna ne,"
Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Nagode,Saikin dawo,"
Da sauri ta fuce daga ɗakin,gyara kwanciya amrish tayi saman gadon,Hannunta ruƙe da wayar Sehrish,comedy din cikin wayar ta fara kallo,tun tana murmushi har ta fara tiƙar dariya,tana cikin kallon videos din Kiran ya shigo wayar,Duba sunan Mai kiran wayar tayi,
*Yaya Yusif*
A fili tace"yayanta ne ke kira,i won't pick it,idan ta dawo zan faɗa mata,"har kiran ya katse bata ɗaga ba,after one minute,wani kiran nashi ya sake shigowa wayar,
Yanke shawarar ɗaga kiran tayi,A kunne ta manna wayar,Shiru tayi bata ce mashi komai ba,
"Assalamu Alaikum,Sister ya kike"?
Murmushi tasaki da yake ta ƙware wurin iya kwaikwayon muryar mutane sai cewa tayi"Lafiya lou yaya yusif,Ya kake"?
"Ina lafiya,kinyi mamakin kira na ko"?
"Eh,"ta amsa mashi,
"Na kira ne don na tambayeki,Yarinyar nan ƙawarki,i forgot her name,me irin sunanki,"
"Amrish"?tayi tambayar tana jiran jin amsarshi,
"Yeah,ita nake Nufi,naga ban cika ganinta ba,ina fata dai babu abunda ke damunta ko"?
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e amrish,ashe akwai wanda suka damu da ita acikin gidan,
"Kinyi shiru baki ce komai ba"?
Da sauri tace"Lafiyarta qalou,Yanzu haka nabarta ɗaki tana bacci,"
"Its okey,ki shafa mun kanta,idan ta tashi ki sanar da ita cewa,ina gaishe da ita,"
"Zanyi yadda kace in sha Allah,"
"Good"Yana katse kiran,ta fashe da wata irin dariya,saboda tsabar farin ciki hada yin ƙundunbale ta wutsila gefe ɗaya,Kamar anyi mata Albishir da gidan Aljanna,
A 6angaren Sehrish kuwa,Lokacin da ta shiga ɗakin hajiya Azeema a zaune ta sameta gefen gadonta,bubu gown ce ajikinta ta material,ba ƙaramin kyau yayi mata ba,
"My daughter,Zo ki zauna kusa dani,long time bamu haɗu ba,"
"Aunty ai jiya saida nazo ɗakinki,Na sameki kina bacci,sai dai na haƙura na koma,"ta ƙarasa maganar tare da samun wuri ta zauna daga gefenta,Suna fuskantar juna,
"Kinsan jiya mun kwaso gajiya,shiyasa ban samu na kiraki mun yi magana ba,Amma yanzu Alhamdullilah"
Murmushi sehrish ta saki tare da sunnar da kanta kasa tana kallon yatsun hannunta,
"Naga canji sosai attare dake,Kinyi haske kin ƙara kyau,ta ko'ina dai masha Allah,har na ƙosa naji labari me daɗi daga gare ki,"
Kunyace ta rufe sehrish da sauri ta sanya tafin hannunta asaman fuskarta ta rufe,"
dariya hajiya azeema tayi"kinfa san tsakanina dake babu kunya,Ba nace maki ki ɗauke ni tamkar ƙawarki ba"?tayi maganar tana kallonta fuskarta
Daƙyar sehrish ta iya cewa"Eh,"
"Yawwa,to cire hannunki yanzu,inaso ki faɗamun wani cigaba aka samu"?
Daƙyar ta daure ta cije cike da jin kunya ta soma bayyana mata,duk wani abu dake a tsakaninta da SGR,
Dariya sosai hajiya azeema tayi,bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"Wonderful!My daughter u did a good job,you're so special tunda gashi kin fara Canza mana Sgr,Naji daɗin jin hakan sosai,"ajiyar zuciya ta ɗan sauke kafin ta cigaba da cewa"Yanzu ya ake ciki game da tafiyarshi U.S?Yace zai tafi dake ko kuwa baiyi maki magana akan hakan ba"?
"Bani da masaniya akan wannan,bansani ba ko yana so ya tafi dani ko bayaso ya tafi dani,tunda baiyi mun magana akan hakan ba,Amma gaskiya aunty ko yace zai tafi dani ni bazan bishi ba,Saboda ba sona yake yi ba,bai ta6a furta mun kalmar so ba,"jiki asanyaye tayi maganar,
"Kin faɗi gaskiya,Amma inaso ki sani,Shi so ba dole sai ta kalamin baki ake furta shi ba,kowa da kalar nashi salon Soyayyar,Rafayet Baison so ba,Idan har ya kasance akanki yafara jin shi,zaiyi matuƙar wuya ya iya gane hakan,bazance ki bi shi ba,kuma bazance kada ki bi shi ba,tunda Wuƙa da nama suna a hannun abusufyan,Dole sai idan Sgr Ya soke wannan yarjejeniyar dake a tsakaninku,Ya miƙa wuya,Ya kuma amince zai rayu dake a matsayin matarshi,Uwar ƴa'ƴanshi,Idan ba haka ba,Bana tunanin Abusufyan zai bari ya tafi dake,zai nemi ya sake ki ne,"
Hankalin Sehrish ya ɗan tashi,don tasan halin Sgr,zai iya sakinta,tunda tasan ba sonta yake yi ba,A tunaninta kenan,.
"Yanzu mommy,Shikenan"
Jinjina kai hajiya azeema tayi,ƙwarai kuwa,bani da sauran shawarar da zan baki,Illa kawai mu zuba ido,muji me Abusufyan zaice,"
Sun jima suna tattaunawa kafin daga bisani,Sehrish ta baro bedroom ɗin,har wani jiri take gani acikin idanuwanta,daƙyar ta lalla6a ta koma ɗakinsu,Lokacin Amrish ta shiga toilet,saman gado ta haye tare da jan bargo ta lullu6e kanta ciki,
Fitowa amrish tayi daga cikin toilet din,tayi ɗaurin gaba da towel,ganin sehrish cikin bargo yasa ta ɗanyi mata gyaran murya tare da cewa"kin dawo kenan"?
"Eh"ta bata amsa atakaice,
"Okey,"ta ambaci hakan tare da wucewa gaban wardrobe ta buɗe ta dauko kayan da zata sanya,
Lokacin sallar magrib dakyar ta samu tayi sallah,ita kaɗai ta rage a ɗakin,Amrish ta ɗan fita waje,wurinsu Jahad,
Basu tashi dawowa cikin gidan ba,Sai wuraren ƙarfe 8 na dare,Gidan ya cika fam da manya manyan baƙi,ta ko'ina ka waiga Sojoji ne sanye cikin kakinsu,Wasu kuma Suna acikin shigarmu ta hausawa,Abun ya ƙayatar sosai,kowa na farin ciki banda mutun ɗaya SGR,domin kuwa yau ta kasance ranar baƙin ciki awurinshi,Fuskarshi kwata kwata babu annuri tunda suka fita har aka kammala taron,An karramashi shida Omar,Ga wani ƙarin matsayin da za'a yi masu a U.S yana jiransu,Sauran matasan gidan kowanne da muƙamin da aka bashi,basu samun lokacin hutu ba,sai wuraren ƙarfe 10 lokacin Manyan bakin da suka zo,Duk sun tafi,Gidan ya rage sai mutanan cikinsu,Kowa Ya wuce bedroom ɗinshi domin hutawa,
*SGR*
Tun da ya shiga bedroom ɗinshi sai zarya yake yi,ya kasa samun natsuwa ko uniform ɗin jikinshi bai cire ba,Abbansu kawai yake jira Ya shigo cikin gidan suyi magana dashi,Sai kiran wayarshi yake yi,Amma bai ɗaga ba,atare dashi suka dawo,Amma bai shigo gidan ba,Yana a wurin abokinshi tafeeda a waje,komawa yayi gefen gadon ya zauna,kamar ance ya duba screen ɗin wayarshi,Sai ga text message na abusufyan,ƙin buɗe saƙon yayi don yasan cewa akan maganar sakin Sehrish ne,duk yabi ya tayar mashi da hankalinshi,duk yinin yau baisanya abinci acikinshi ba,Kamar me azumi,saboda tsabar tashin hankali,Zuciyarshi tare da agogo suke bugawa, awanni kaɗan suka rage mashi,shikaɗai yasan yadda yake ji acikin zuciyarshi,Yau da ƙishir ruwanta ya yini,yayi maraicin ganinta,duk a tunaninshi Uncle ne Ya dakatar da ita,
Yana cikin wannan mawuyacin halin,Omar Ya faɗo bedroom ɗin nashi jikinshi sanye da kaki,Yana ta faman ƙwala mashi kira"Rafayet!Rafayet"!
Daƙyar ya iya amsa mashi"Na'am,"
Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kafin yace"Wai meke damunka ne?tunda muka fita na lura dakai,fuskarka a ɗaure tamau,babu annuri,In wani abu ne ka faɗamun mana,May be i ave the solution of it,"
Har lokacin bai motsa daga zaunan da yake ba,Gefen shi omar ya zauna tare da dafa kafaɗarsa,cikin lallami yake yi mashi magana"Pls my own bro,ka faɗamun mana,wlh duk na damu da halin da kake ciki,"
Daƙyar ya samu Sgr Ya faɗa mashi abunda ya faru tsakaninshi da Abusufyan Da asuba,"
Cike da takaici Omar yace"Ya salaam!Rafayet meke damunka ne wai?Wai meyasa komai saika nuna fin ƙarfi akanshi ne!don me zaka ce mashi haka?kana so ka tafi da ƴarshi ba don kana sonta a matsayin matarka ba,Sai don kanaso taci gaba da yi maka aiki kamar wata baiwa!?
Runtse ido sgr yayi tare da cizon pink lips ɗinsa,
"Its okey Omar,Stop shouting at me,kana cika mun kunne na,"
Rai a6ace Omar ya miƙe tare da acewa "Oh haka ma zakace!Good,wlh baka ji jiki ba,Uncle yayi mun dai dai,"juyawa yayi a fusace har yakai baƙin ƙopar ya kuma juyowa tare da kallonshi,
"Dole na fada maka gaskiya koda kuwa bakasan jinta,Rafayet ka kamu da Son Yarinyar nan!Kana tsananin sonta am advising u,tunkafin lokaci ya ƙure maka,Kayi hanzarin miƙa wuya,Idan kuma kace zaka sanya girman kai aciki,Wlh u will regret it,"yana kai ƙarshen maganarshi,ya fuce daga cikin ɗakin,bawan allah saboda yadda ya damu da sgr,a ƙopar falonshi ya tsaya sam ya kasa tafiya,tsananin tausayinshi ne ya kamashi,Sam baisan menene so ba,gashi yanzu zai fara shan wahalarshi,
Ya jima a haka kafin ya fito daga part ɗinsa,yana ƙoƙarin saukowa downstairs su kayi kici6us da Abbansu,da alama bene zai hau,shigowarshi kenan ko kakin jikinshi bai cire ba,
"Yawwa abba,Inason magana dakai,"
"Meya faru omar?Allah yasa dai Lafiya,Naga missed calls ɗin rafayet yana ta kirana,bansani ba saboda na sanya wayar silent"
Ruƙo hannunshi Omar yayi,Suka koma upstairs din,a tsaye suka soma magana,
"Abba,na samu rafayet cikin mawuyacin hali,dama duk yinin yau na lura dashi,ko abinci baici ba,Yanzu naje bedroom ɗinshi na tambayeshi meke damunshi,Shine yake sanar dani cewa Uncle abusufyan Ya nemi ya sakar mashi ƴarsa,"
Murmushin takaici Abba yayi kafin yace"Wata amsa ya bashi"?
"Yace shi bazai saketa ba,Ya soke yarjejeniyar auren,Maimakon yabi ta lalama,Sai cewa yayi wai zai tafi da ita U.s don taci gaba da yi mashi aiki,"
Cike da takaici,Abba ya dafe goshinshi"Ni dama nasani wlh,shiyasa tunfarko nayi ƙoƙarin in karkato hankalinshi don ya soke yarjejeniyar,Amma ya nuna mun cewa baya buƙatarta,Da zarar wata uku sun cika zai sakar mashi ƴarshi,Yanzu gashi lokaci ya cika,Ni ba abunda zan iya yi mashi Omar,nasan na isa da abusufyan amma ban isa na hana shi yin iko da ƴarshi ba,"
"Yanzu abba,Babu wani solution?Ni so nake A soke wannan auren yarjejeniyar,A barshi yayi rayuwa da matarshi,"
"Kasan Allah,in har rafayet bai miƙa wuya ba,Ni bazan ta6a tursasa ma abusufyan ba,Dole ya sauke jiji da kannan nashi,in har yana son yaci gaba da rayuwa da ita,Shi Yafi ƙarfin yayi biyayya ya samu abunda yakeso,Komai sai yace a dole saiya same shi,Ai bakomai ne ƙarfi da dukiya suke iya siya ma mutun ba,babban abun takaicin ma,Ya maida abusufyan tamkar tsaranshi,ko ba komai ,Shifa uncle dinsa ne,baya respecting dinshi yadda ya dace,"
jinjina kai omar yayi'Shikenan Abba,Zanyi ƙoƙari wurin ganin na fahimtar dashi,wlh banaso a wahalar mun da ɗan uwana,irin rayuwar da aka saba mashi da itane,Shiyasa ya kasance haka,"
Suna cikin maganar nan,suka jiyo takun takalmi,Alamar wani na tunkaraso,da sauri suka kai idanuwansu wurin,Bakowa bane face Abusufyan,Jikinshi na sanye da Jallabiya brown colour,ƙarasawa yayi tare da miƙa ma abba hannu suka gaisa,
Fuskarshi asake yace"Sannu da dawowa Yayana nakaina,Yanzun nan Ayaan ke sanar dani cewa ka dawo gida,"
"Eh wlh,ban jima da shigowa ba,Na nufo nan,wurin mutumin naka,"ya ƙarasa maganar da zolaya,
ta6e baki Abusufyan yayi batare da yace komai ba,
"Yanzu omar ke sanar dani abunda Ya faru atsakaninka da Sgr,Gaskiya banji daɗi ba,Rafayet bai kyauta ba,"
Sai lokacin abusufyan ya soma magana"Allah yaya rafayet saiya gane kuskurenshi,A ƙule nake dashi,Wai har ni zai kalli tsabar idona yace wai Ya soke yarjejeniyar aurenshi da ita,Kuma zai tafi da ita u.s,don taci gaba dayi mashi aiki?wato shi yafi ƙarfin yace yana sonta a matsayin matarshi......."daƙyar yakai karshen maganar saboda ranshi yayi mugun 6aci,
"Dan Allah uncle kayi haƙuri,Amma ......"tunkan Omar yakai ƙarshen maganar ya dakatar dashi"kada kace komai Omar,Ka barni da rafayet kawai,Ya raina ni,Har ni zan kai mashi paper don ya rubuta mata sakinta,Yasa hannu ya ɗauki paper ya kekketata akan idona,Baiso xaman lafiya ba Allah,"
Tunda ya soma magana Abba ke