Showing 156001 words to 159000 words out of 307403 words

Chapter 53 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

a cikin asibitin Sgr,Yana ganin sunan Sgr ya bayyana akan screen ɗin wayarshi,jiki na rawa ya kashe wayar gaba ɗaya,
  Abun ba ƙaramin ɗaurewa Sgr kai yai ba,kowa ya kira ba'a picking,shi Major ma kiran ya shiga,daga baya kuma aka kashe wayar,hakan ya ƙarasa shi zargin cewa wani mummunan abunne ya faru,
  Komawa Upstairs yayi da sauri bedroom ɗin da Sehrish take ciki,tura kopar yayi ya shiga,a kwance ya sameta rungume da pillow,

   "I know u are awake,inaso ki kiramin layin wani daga cikin sisters ɗinki,i wanna talk with them "
  Yunƙurawa sehrish tayi tare da kai hannu ta ɗauki wayarta da ta aje gefenta bayan ta kashe wakar,layin jahad ta lalubo ta danna mata kira,A lokacin wayar na a hannun Major ya kar6eta daga hannun police men ɗin,koda yaga kiran My Own sis ya shigo,ta layin jahad,kin daga kiran yayi har ya yanke,hakan yasa sehrish sake kira,sai ya kashe wayar gaba ɗaya,
  ɗagowa tayi tare da kallon Sgr,tun kafin tayi magana,ya riga ta cewa"Switch off ko"?ɗaga mashi kai tayi alamar eh,tare da cewa"Bari na kira layin Hosana,"
  Numbar hosana ta lalubo,tare da danna mata kira,tana fara ringing hosana ta ɗaga kiran,muryarta da alamun bacci atare da ita,
   "Wai wanene ke kira na"?
Sehrish tace"ke nice,Ina jahad ne na kira layinta a kashe"?
   Hosana tace"tun ɗazu da suka fita da junaid shan ice cream basu dawo ba,inata jiransu har bacci ya ɗauke ni,"kafin Sehrish ta ƙara cewa wani abu,da sauri Sgr ya sanya hannu ya kar6e wayar,
  tare da karata a kunnansa"Ina Omar yake"?rass taji gabanta ya faɗi,daga kwance take,amma jin maganar babban yayansu yasa ta miƙe zaune,anatse tace"Wlh bansan inda yake ba,ko yana gida ko yana waje oho,ni dai ina ɗakinmu,"
   "Go to his bedroom right now,and see if he's around,"
Mikewa hosana tayi tare da saukowa daga saman gadon,gudu gudu sauri sauri ta wuce upstairs bedroom ɗin Omar,a buɗe ta samu ƙopar,turawa tayi ta shiga daga ciki,ko'ina ta duba,hada leƙa toilet ɗinsa,ganin babu kowa yasa ta sanya wayar a kunnanta,
  "Ya Rafayet,na duba ko'ina,amma banga ya Omar ba,"
  "Its okey,ki koma ɗaki,"yana faɗin hakan ya katse kiran,
  ɗagowa yayi da lumsassun idanuwanshi masu ɗauke da bacci ya kalli Sehrish itama kallon nashi takeyi,duk jikinsu yayi sanyi mika mata wayar yayi"take ur phone,"hannu tasa ta kar6a,
  Da sauri ya juya,jikinshi duk babu ƙwari a lokacin idonshi ya sauka kan belt din shi dake akasa,hannu yakai ya dauka ya fara kokarin maida shi jikinsa tare da fucewa ya nufi downstairs,a dai dai lokacin Abusufyan na fitowa daga ɗakin da suka kwantar da Abu,jikinshi sanye da jallabiya,
  Yana jin takun takalmi,yakai idanuwanshi wurin,yana ganin Sgr ya tunkareshi da sauri,
  "Rafayet!wai kunyi waya da Junaid ne?i ave been trying his phone number,Amma akashe!nayi traying har nagaji,since evening ya sanar dani cewa,zasu fita tare da jahad shan ice cream,inaso naji ko sun koma gida,itama kuma phone dinta akashe"
  Ƙarasa saukkowa daga saman benen Sgr yayi tare da kallon Uncle ɗin nasu yace"Uncle nima bansan meke faruwa ba,kowa na kira layinshi switched off,babu mai picking call ɗina,That's why na yanke shawarar zuwa Abuja yanzun nan zan bi jirgi naje can," ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin wucewa ta gefen Abusufyan,da sauri ya ruƙo damtsen hannunshi tare da cewa"A'a Rafayet!ka haƙura sai gobe mana ka wuce can ɗin,"acewar Abusufyan
Girgiza kai ya shiga yi tare da cewa"Bazan iya jurewa ba,inaso nasan meke faruwa ne acan ɗin,na damu akan rashin jin muryar Junaid,daddy ma ya kira ni yanzu,yana cikin damuwa,ko don saboda shi inaso naje can na haɗashi da junaid,if not ko bacci bazai iya yi ba,tunda ya sama ranshi son jin muryar junaid,"
  "Zanyi magana da yaya hossein ɗin,ka ajiye tafiyar nan dare yayi,sai zuwa gobe da asuba,"
  Ba don ya so ba,a dolenshi ya haƙura,komawa sukayi saman sofa suka zauna jigum jigum,Suna jiran tsammani,kowa da abunda yake saƙawa acikin ranshi,
 
*HAROON*

Around 12 na dare,Yana zaune gefen gadonshi,message ya shigo wayarshi,da sauri yakai hannunshi ya zarota daga cikin trouser pocket ɗinsa,buɗe message ɗin yayi ya soma karanta shi kamar haka,
   _Oga Aiki ya kammalu fa!ka duba whatsapp ɗinka,mun tura maka video zazzafan gaske,nasan yau zakayi kwanan farin ciki_
  Shu'umin murmushin nan nashi ya saki,jiki na rawa ya shiga whatsapp ɗinshi anan ya samu Video ɗin da suka tura mashi,bayan ya kunna Wi-fi ɗin wayarsa,tunkan video ɗin ya ƙarasa yin loading jikinshi keta tsuma harya ƙagara yaga Videon menene,
  Ƙura ido yayi akan screen ɗin wayar,lokacin da video ɗin ya buɗe,motar Junaid ya gani tana ta ci da wuta,ta lomatse ta rakwakkwa6e,Wani irin ihu ya fasa cike da tsantsar farin ciki ya miƙe tsaye yana faɗin"Yess!Yess!!finally Burina ya cika,ko ayanzu na mutu nasan cewa,na gama dasu,na kashe farin cikin da suke taƙama dashi!"
Ya ƙarasa maganar tare da fashewa da wata irin mahaukaciyar dariya,lokaci guda kuma ya dakata da yin dariyar,jikinshi ya soma kerma sakamakon Muryar junaid da tayi mashi gizau acikin kunnanshi
   _Ya haroon!burinka ya cika ko?ka rabani da rayuwata,laifin me nayi maka?menayi maka dana cancanci wannan ɗanyen hukuncin a wurinka!yanzu shikenan bazan sake ganin ƴan uwana ba?ka rabani da mahaifina kuma kana farin ciki?haƙƙina bazai ta6a barinka ba_
  A tsorace Haroon ya shiga waige waige a cikin ɗakin nashi,ba ƙaramin razana yayi ba,ganin baiga kowa ba,yasa shi sauke ajiyar zuciya,
  ɗago da wayarshi yayi tare da Calling layin waɗanda yasa su kashe mashi junaid,tana fara ringing aka ɗaga kiran,
  Muryarshi asanyaye yace"dagaske ne video ɗin da kuka turomin cewa kun kashe junaid"?
  On the other hand,mutumin yace"ƙwarai kuwa!Yaron nan babu shi yanzu a doron duniyar nan!domin kuwa da truck muka take motarshi,bayan mun tabbatar yana acikin Motar,Amma ita yarinyar bata acikin motar kamar yadda ka bamu umarni,ta tsallaka titi zata siya masu ice cream......"
  Tunkan ya ƙarasa maganar,haroon ya zube saman guiwowinsa,wata irin zufa ce ta shiga tsatstsafo mashi ajikinshi,tuni ta wanke shi sharkaf,
  "Ya Haroon!Kamar baka farin ciki?naji kayi shiru"?
  Kasa buɗe baki haroon yayi,la66ansa sae kerma suke yi,
  "Hello!hello!Oga haroon!kana a kan layi kuwa"?jin shiru bai tanka masu ba yasa suka katse kiran,
  Jikin taƙaura yayi la'asar,gaba ɗaya haroon ya shiga ruɗani,Shin farin ciki yake yi da mutuwar junaid ko kuwa baƙin ciki?Tun yanzu ya fara tsorata da gizan da muryar junaid tayi mashi,
  _Laifin me junaid yayi mun?na kasa yarda cewa ni da kaina na bada umarnin a akashe shi_
  Runtse idanuwanshi yayi sosai,yana tariyo fuskar junaid,mai ɗauke da kyakkyawan murmushi nan nashi,
  Guiwowinsa duk sun sage,ya kasa miƙewa tsaye,yayi fiye da awanni zuƙunne batare daya motsa ba........

*AUNTY BABBA*

Tun bayan da Abra ta gudu daga hotel ɗinnan,Tana fitowa daga wanka,jikinta ɗaure da towel,sam bata kawoma ranta komai ba,duk da tayi mamakin ganin babu kowa,Jinjina kai ta shiga yi tana faɗin"Ko gidan ubanwa taje?bayan na sanar da ita cewa Yanzu zamu tafi,zata dawo ta same ni,"ta ambaci hakan tare da samun wuri gefen gadon ta zauna,tun tana sa ran dawowar abra har ta fara fidda rai,tunawa da abunda ya faru da hayaam a hotel yasa hankalinta ya tashi,tsoranta kar ace itama abra,an samu wani ya ƙurmushe ta ne,hakan yasa tayi firgit ta miƙe tsaye,tare da kai hannu saman bedside drawer ta ɗauki wayarta dake ajiye a samanta,
  Yanke shawarar kiran Abra tayi,tun kafin ta shiga Contacts ɗinta,saƙon abra ya shigo cikin wayar,on the top of screen ɗin wayar,
  Janyo saƙon tayi ta buɗeshi,a tsanake ta soma karanta saƙon
  _Aunty laila sai dai kiyi haƙuri,wlh bazan iya zuwa wurin bokan nan ba!saboda ƙaryar da kika yi mun dangane da hayaam,ashe Aunty hayaam tana kwance rai hannun Allan agadon asibiti,amma kika gudu kika barta saboda kawai tsautsayi ya same ta?ashe dama amfani kike yi damu don ki cimma burinki!baki damu da rayuwarmu ba,Naji tsoro ne saboda nasan cewa nima wata rana in irin hakan ta faru dani zaki gujeni ne,ina mai baki haƙuri Aunty laila,bansan ya rayuwarki zata ƙare ba a Enugu,domin kuwa na kwashe duk wasu kuɗi da muka zo dasu,Na tafi da handbag ɗinki gaba ɗayama,kada ki sha wahalar nemanta Aunty hayaam da aunty Amani ne suka sa nayi hakan a ƙarshe ina maki fatan sa'a_
  Saboda tsabar kiɗima a hautsine ta jefar da wayar ƙasa,Dafe ƙirjinta tayi hankalinta a matuƙar tashe,ta furta"kutumar Uba!Ni Abra zata yiwa iya shege!Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Ya Allah ka rabani da mugun ji da mugun gani!Ya Allah kasa mafarki ne ba gaske ba,Abra ta yashe ni!ta gama dani!na shiga uku na ni yau! Na gama yawo!
  Tuni Ido ya raina fata,cizon yatsanta ta shiga yi,tana faman yarfa hannunta,Duk tabi ta ruɗe ta rasa inda zata tsoma ranta,
  Zuƙunnawa tayi ta ɗauki wayar da tayi wurgi da ita ƙasa,layin Abra ta kira,unfortunately ta samu wayar akashe!
  "Allahumma Ajirni fil musibati wa'aklifni khairan Minha,Meyasa Abra zatayi mun haka!Nashiga uku ni yau,Wannan wata irin Musiba ce!daga wannan sai wannan?"
  Hawaye ne suka soma saukowa daga saman fuskarta,a susuce ta shiga faɗin"Wlh baku isa ba!baku isa ku hanani zuwa wurin bokan nan ba!Wlh sai naje,Allah ya isa tsakanina Da Amani!Munafuka duk ita ta shirya mun wannan,Ita kuma waccen kingin gardawan bamma san ya akai ta farfaɗo ba,don nasan itace ta sanarwa Amani har suka shiryamin wannan tuggun,Wlh bazan ƙyalesu ba....."Aunty babba fa ta zare sai faman sakin sambatu takeyi,da alama ta fara zarewa,zagaye ɗakin tashiga yi tana safa da marwa,hannunta asaman kanta,
   Yanke shawarar bin bayan Abra tayi,a gaggauce ta buɗe trolley ɗin kayansu,ta ɗauko doguwar riga ta zura ajikinta,Ta yafa mayafi buɗe ƙopar tayi,jiki na rawa,haka ta shiga zagaye hotel ɗin tana neman Abra,har wurin receptionists taje,ta tambayesu ita,hada yi masu kwatancenta anan suka sanar da ita cewa,sunga gifcinta a lokacin da take ƙoƙarin barin reception ɗin,Jin haka yasa Aunty babba ta zabura da gudu ta fuce daga reception ɗin ta miƙi hanyar fita daga hotel ɗin,gudu gudu sauri sauri haka ta fita waje gefen titi tana Neman Abra,
  Hanya ta miƙa tana tafiya tana sambatu,tana ƙoƙarin ta tsallaka titi wata jibgegiyar Mota ƙirar Range rover tayi Awon gaba da ita,Koda mai motar nan yaga aika aikar da yayi jini har asaman glass ɗin motarshi,aikuwa a hanzarce yaja motarshi da gudun gaske ya bata wuta kamar zai tashi sama yabar Wurin!!!
  Aunty babba kuwa sai kwala ihu takeyi tana shure shuren ƙafa asaman titi,
   "Wayyo Allah!nashiga uku!na bani Na lalace!Ya kashe ni!Ya gama dani!"
  Dandazon mutane ne suka taru a kewaye da ita,sun zuba mata ido suna ta kallonta an ransa wanda zai iya taimaka mata,kowa tsoro yake ji kada ace shine yayi silar mutuwarta,Wannan dalilinne yasa aka rasa wanda zai ta6ata,kuma babu wanda yayi tunanin kiran ƴan sanda don yayi reporting akan Incident ɗin,
  Tun tana shure shuren kafarta jini na tsargowa ajikinta,har jikinta ya soma saki alamar rai zai yi Halinsa........

DAMATURU,

Wuraren karfe 1 na dare,Abba na zaune zugudum tsakiyar gadonsu ya zabga uban tagumi,zuciyarshi sai bugawa take yi,kwakkwaran juyi Alexandra tayi karaf idanuwanta suka sauka akan shi,da ya ke akwai hasken bedside lamp dake a kunne,muryarta adisashe tace"Abban Junaid!lafiya har yanzu bakayi bacci ba,"?
Hankalinshi atashe yace"taya zan iya runtsawa?kullum junaid ya saba kirana a waya da daddare kafin ya kwanta yayi bacci,Amma yau shiru wayarshi a kashe,wayar Omar a kashe,na rasa wanda zan samu a gidan in kira shi don ya sanar dani halin da junaid ke ciki,"
Jin wannan maganar yasa hankalin Alexandra ya tashi haiƙam,mikewa zaune tayi cike da mamaki tace"nikaina nayi mamakin rashin kirana da junaid,baiyi ba amma ban kawo komai araina ba har bacci ya dauke ni"
Abba na ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,suka ji an ƙwanƙwasa ƙopar ɗakin nasu,
Atare suka haɗa baki wurin cewa"Wanene"?
Muryar Twins ce ta amsa masu"Mommy mune,"
Kallon juna sukayi at same time,kafin Abba yace"Ku shigo ciki,"
Tura ƙopar sukayi atare suka shiga kowannansu sai faman hammar bacci yake yi idanuwansu a lumshe saboda baccin da suke ji,
Aruɗe Alexandra tace"is everything alright twins?me kuke yi har yanzu bakuyi bacci ba"?
Ayaan yace"mommy wlh ba lafiya,mun kasa runtsawa saboda yau junaid kwata kwata bai kira wayarmu ba,Ko text message ɗin da ya saba tura mana yau bamu gani ba,kuma mun bibiyi layinshi a kashe,har ya Omar mun kira muji ko lapia shima a kashe,taya hankalinmu zai kwanta,"yana kai ƙarshen maganarshi jahan ya ɗaura da cewa"Mommy,Daddy Ni da Ayaan mun yanke shawarar komawa gida gobe,dan Bazamu juri rashin junaid a kusa damu ba,"
Tashin hankali,zuba masu ido Sukayi suna kallonsu,kowanne yasha sleeping dress ajikinshi,
"Ku zauna"Abbansu ne yayi maganar tare da nuna masu doguwar sofa ɗin dake acikin bedroom ɗin,Zama su kayi kowa fuskarshi ɗauke da damuwa,
"Mommy!"gabanta ne ya faɗi jin Muryar fawan,da sauri takai idanuwanta bakin ƙopar ɗakin,shigowarshi kenan,idanuwanshi sunyi luhu luhu dasu,ƙarasa shiga ciki yayi daƙyar yake iya ɗaga ƙafarshi saboda bacci,
"Fawan!kaima baka yi bacci ba"?Abbansu ne yayi tambayar,
ɗaga mashi kai yayi alamar eh,tare da cewa"Abba,junaid fa?ko wani yayi waya dashi acikin ku?duk yau bai kira ni ba,kamar yadda ya saba,har text yana turamun kullum amma yau shiru,ko ta whatsapp bai turo man ba,da abun na kwanta yanzu na farka still banga sakon shi ba, layinshi ma a switched off,duk na damu wlh,'
Tashin hankali,abun fa ya fara basu tsoro,wasa wasa one by one su Irfan kowa ya shiga shigowa ɗakin yana tambayar junaid,dayake family house ne,duka danginsu na 6angaren Mahaifinsu,suna acikin katafaren gidan,wanda ya kasance mallakin kakansu,mijin Ammi,
Aranar dukkansu babu wanda ya runtsa,mafi yawancinsu a zaune suka kwana,don sunci alwashin dawowa gida,tun da asussuba,Abbansu yafi kowa ƙagara daya dawo yaga meke faru ne,Ya ƙwallafa rai akan son ganin junaid,don da ace yana da fiffike da ba abunda zai hanashi tashi sama atsakar daren nan yadawo gida! *Allah sarki*

Kamar yarda su Abba suka kwana a zaune,haka Sgr da Abusufyan suka kwana a zaune,cikin falon gidan,babu wanda ya runtsa acikinsu,haƙika ba ƙaramin so sukeyi wa junaid ba,Rashin kiran da baiyi masu ba a waya yasa duk sun tashi hankalinsu,inaga sunji mutuwarshi?mezai faru?kowa fa yasha jinin jikinshi,

Tunda asussuba Jirginsu Sgr da Armstrong ya ɗaga izuwa Abuja,

*Sehrish*

Bayan sallar asuba,Sehrish ta koma ɗakin Oummansu,har lokacin bata farka ba,Wuri ta samu saman gadon daga gefenta,ta kwanta abubuwa da yawa suna zuwa mata aranta,ita kanta tasan cewa tayi kewar wasu daga cikin mutanen gidan,musamman Su Hosana da Junaid,da Aunty azmee,kowa missing ɗinshi take yi,gashi batasan ranar da zasu koma gida ba,tana cikin wannan zancen zucin nata,tajiyo muryar Oummansu tana sambatu,tana faɗin"kada a ta6a mun ƴa'ƴana,dan Allah abarmun su,su kaɗai nake dasu,sune dangina,sune komai nawa,'
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e Sehrish,miƙewa tayi zaune tana kallonta,a hankali ta furta"Oumma" slowly abu ta buɗe idanuwanta,tare da wurgasu kan fuskar sehrish,wani irin kallo take bin ta dashi,kallon tuhuma,
Murmushi sehrish ta sakar mata tare da ƙoƙarin miƙa hannu zata shafa gefen fuskarta,aikuwa a tsorace Abu ta miƙe zumbur tana ja da baya,girgiza mata kai ta shiga yi tare da zare mata manyan idanuwanta,wai don kada ta ta6ata,.
Jikin sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba,
"Oumma baki gane ni ba?Ni ce fa sehrish!Rishi ɗinki'
A ruɗe ta shirga girgiza kanta tana cewa"a'a a'a Ni bansan wacece ke ba,bake bace rishi ɗina ba,Rishi ɗina ƙarama ce,"
Cikin sanyin murya Sehrish tace"Oumma kallanni dakyau ki gani,nifa ce rishi ɗinki,nasan bazaki manta da kamannin fuskata ba,na ƙara girma ne kaɗan,"
Harara abu ta watsa mata,dama tun fil azal abu mace ce mai taurin kan tsiya ga kafiya,tun tana da hankalinta balle kuma yanzu da babu hankalin atare da ita,
Zubama juna ido sukayi kowa na kallon kowa,taƙi yarda sehrish ta kusantota,da zarar sehrish ta matsa,itama da sauri zata matsa,ganin ta kusa ƙurewa gadon gudun kada ta faɗa ƙasa,yasa Sehrish ta ƙyaleta,
Cikin lallashi tace"Oumma!kin tuna da Hosana?da jahad?
Girgiza mata kai tayi alamar a'a,"Ni bansan su ba,Ni ki ƙyaleni bansan kowa ba,ƴa'ƴana na sani Nemansu nake yi,yace zai kashe munsu,dan Allah akawo mun ƴa'ƴana kusa dani,"
Murmushi sehrish ta saki tana kallonta,tsantsar son mahaifiyarsu take ji kamar kamar me,gashi taƙi bari ko rungumarta tayi,
"Kiyi haƙuri kinji,Babu wanda zai ta6a maki ƴa'ƴanki,idan har kika bani dama,Ni dakaina zan kawo maki ƴa'ƴanki,"
Shiru tayi bata tanka mata ba,Sai ma wani kallo da take bin ta dashi,kallon ban yarda dake ba,wayau zakiyi mun,
Jin sallamarsu Abusufyan yasa tayi saurin amsa masu tare da saukowa daga saman gadon,ta fito daga ƙopar dakin,Su uku ne suka shigo,Baban sadeeq tare da Abusufyan sai Sadeeq ɗansu da suka ɗauko jiya,Anan ya kwana gidan,
Fuskarta ɗauke da fara'a ta gaisar dasu"ina kwananku?Kun tashi lafiya,"
Atare suka amsa mata"lafiyalou,Alhamdulillah,"
"Sadeeq ka ganeta kuwa,"?Baban sadeeq ne yayi maganar yana kallon sadeeq ɗin dake tsaye agefenshi,murmushi ya ɗan saki tare da girgiza kai alamar a'a,yace"fuskarta kamar na santa,amma bazan iya tunawa ba,'
Abusufyan yace"Ae zaiyi wuya ya ganeta saboda canzawar da tayi,ba kamar daba da yasanta,yanzu ta ɗan ƙara girma,"
Baban sadeeq yace"Allah sarki,Sadeeq wannan fa ba kowa bace face daya daga cikin waɗannan ƴan ukun na Wurin abu,waɗanda suke yawan zuwa gidanmu su yini wani sa'in ma harsu kwana,"
Cike da mamaki Sadeeq yace"Wai su rishi,hosana,da jahad"?sae lokacin ya ganeta,baki asake yake kallonta,don bazai manta lokacin da suke yawon zarya acikin gidansu ba,musamman in yunwa ta addabesu,wani sa'in ma shi Mamansu ke aikawa gidansu ya kai masu abinci idan tajiyo kukansu,da zarar ya kai masu abincin,Jiki na rawa suke kar6a su zauna suna ci,'
"Rayuwa kenan,banta6a tsammnin rana irin ta yau ba,gani ga rishi,"tuni idonshi sun ɗan cicciko da ƙwalla,haka itama sehrish ɗin
Baban sadeeq yace"ka tuna lokacin da kake kuka saboda mamanka taba su rishi abincinka'?
Fashewa sukayi da dariya gaba ɗayansu,
Kunya duk ta rufeshi daƙyar ya iya buɗe baki yace"Dan Allah Abba,adaina tuna abunda ya wuce,'
"Shikenan tunda haka kake so andaina,"
Wuce wa Abusufyan yayi cikin ɗakin abu,Baban sadeeq ma ya wuce ɗakin da suka sauka,ya rage daga ita sai Sadeeq atsaye,suna fira,
"Yanzu shekarunki nawa'?ya tambaya yana kallonta,
Wurga ido ta ɗan yi kamar mai tunanin wani abu,kafin tace"sha takwas kaifa"?
Hannu yasa tare da ɗan sosa keyarsa yace"Sha tara," harara


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login