Showing 12001 words to 15000 words out of 307403 words
Chapter 5 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete
ba,dama yasan shi firgitacce ne,yaso ace tun farko saida ya fara yi mashi bayani anatse sannan yaje ɗakin nasu,
Ayaan kuwa tun lokacin da yaji junaid ya fasa ƙara,ya ƙumshe dariya abakinsa,saboda yasan tsiyar daya tsula mashi,zaiyi wuya junaid ya yarda cewar Sehrish ƴan uku ne,ba kasafai yake fahimtar irin waɗannan abubuwan ba,sai an zaunar dashi cikin lalama anyi mashi bayani dalla dalla,sannan ake samu ya yadda,
"Junaid ne ko"?abusufyan ne yayi tambayar,yayin da yake daga zaune saman gadon,
Sehrish tace"Shine daddy,ya ruɗe ne saboda ya ganmu mu uku,ya tsorata sosai naso na fahimtar dashi amma sai naga ya watsa aguje,'jin haka yasa abusufyan yin hanzarin saukowa daga saman gadon ya fuce daga ɗakin,
Jikin jahad ba ƙaramin sanyi yayi ba,ganin halin da junaid ya shiga saboda ya gansu su uku,tsoronta kar wani abu ya same shi,ganin yadda ya watsa waje aguje,
"Inaso naje naga halin da yake ciki,bansan meyasa ya firgita ba har haka,"sehrish ce tayi maganar a yayin da take miƙewa daga saman stool,jikinta na sanye da farar riga da dogon wando fari,kanta kuma na sanye da hula fara ta roba,buɗe ƙopar dakin tayi ta fuce tare da nufar inda suke,
Komawa jahad tayi ta zauna saman kujerar gaban mirror,hannu tasa tare da ɗaukar man shafawar sehrish ta buɗe shi tana lakuto shi a hannunta tana shafa ma jikinta,
"Jahad wai meya faru ne?naji sautin ƙara a kunne na," hosana ce tayi maganar,tana zaune tsakiyar gadon sae faman hamma takeyi saboda yunwar da take ji,
"Ƙanin Ya Omar ne,junaid ya shigo ɗakin nan,ina tunanin ya tsorata ne da ganinmu shiyasa ya firgita,saboda yaga fuskokinmu iri ɗaya dana sehrish,"
sauko da ƙafafunta tayi ƙasa tana cewa"bari naje naga meke faruwa a wajen,"
Da sauri jahad tace"Kada ki fita hosana!sehrish ta fita muddin ya ƙara yin arba dake zai zauce ne,ki bari sehrish tadawo sai muji daga bakinta,idan an fahimtar dashi ya fahimta,sai mu fita atare,
Hosana tace"amma fa Yunwa nake ji sosai aciki na,'
"Bari daddy ya dawo zanyi mashi magana,nasan zai sa ashirya mana breakfast ɗinmu,'acewar jahad,
Murmushi hosana tayi tare da cewa"jahad bakiji irin farin cikin da nayi ba jiyan nan!,wlh inason Daddynmu sosai,tun lokacin da gwaggon katsina tace mu ƴa'ƴan abusufyan ɗinta ne,ta kuma kirashi awaya tabamu mu gaisa dashi,tun daga lokacin nake jinshi araina,na dinga addu'ar Allah yasa ya zama mahaifinmun duk da alokacin nasan wanene mahaifin namu......'
"Nikaina hosana a lokacin,da muka fara waya dashi sai da naji jikina yayi sanyi,naji wani irin yanayi atattare dani ashe dae dagaske mahaifin namu ne,gaskiya munyi dacen uba,yana da kirki sosai duk da ban zauna dashi na wani lokaci ba,amma tun daga kan Fuskarshi zakasan cewar mutumin kirki ne,ashe lokacin da muna yara har zuwa ya ta6ayi ya ɗauke mu yakaimu gidansu yayi mana wanka sannan yayi mana kitson kalaba,bawan Allah,Allah kaɗai yasan yadda yaji acikin zuciyarshi lokacin da wannan baƙin mugun ya rabashi damu,'
Hosana ta ƙara da cewa"Mummuna kawai,fuskarshi kamar ɗuwawu saboda rashin kyau,har naqosa naga yadda Ya omar ɗina zai karairaya ƙasusuwan jikinshi,"ta ƙarasa maganar tana yin nuni da hannayenta,yadda takeso Omar yayi ma Ya sayyadi,
Ta cikin mirror jahad ke kallonta tana dariya tace"ae ba ƴa'ƴa Omar kaɗae ba,baki lura da yadda wannan mai blue eyes ɗin nan yayi ba,wani fari kyakkyawa mai ƙirar nan,har ni sai da na tsorata dashi ganin yadda ya zabura yabar wurin yana huci......'
Hosana tace"ae nagane shi,Ni wlh tsoran idanunshi nake ji, kaman aljani,wai shima yanzu ɗan uwanmu ne ko?duk ƴan gidansu ya Omar ne ko?
"Yayanmu zaki ce,ae yanzu duk wanda kika gani acikin gidan nan,to yayan mu ne,jiya baki lura da wani matashi acikinsu ba wani fari,mai mutunci wanda yazo ya kira mu,lokacin da alAbbansu ke neman mu"?
Murmushi hosana tayi alamar tagane shi tace"daga gani zaiyi sauƙin kai sosai,kuma da alama ba ƙaramin farin ciki yake damu ba,mun gode ma Allah jahad daya haɗamu da dangin mu,'
Lokacin da sehrish ta shiga main palour din nasu,anan ta samu matasan gidan duk tsaitsaye akan junaid,dake kwance saman doguwar sofa ɗin da Abbansu ya kwantar dashi,a lokacin har sun yayyafa mashi ruwa ya farfaɗo,bakinsa sai faman kerma yake yi kuma har lokacin bai daina faɗin "Rishi guda uku"ba,
Abusufyan yace"bawan Allah,nidai naji an saki ƙara ashe wai junaid ne,bansan time ɗin daya shigo ba,lokacin ina bacci ne,ae da ban bari hakan ya faru ba,da tun lokacin na fahimtar dashi,ashe har yanzu junaid na nan da wannan firgitar tashi,ae nayi tunanin ya daina,'
Shafa gefen fuskarshi abba yayi a yayin da yake zaune daga gefen daman kujerar yace"Ya tsorata ne sosai,ae ni kaina banyi tsammanin zaije ɗakin nata bane,naso ace saida na fara yi mashi albishir sannan yaje wurinsu,'
Jahan dake tsaye yace"Aikin ayaan ne,shine ya tura shi ɗakin nata,'ya ƙarasa maganar yana hararar ayaan dake tsaye yana dariya,
Duk Alexandra na tsaye tana sauraronsu,sam batasan inda zancen nasu ya dosa ba,
Koda sehrish ta ƙaraso,zuba mata ido Alexandra tayi tana kallonta,gaban sehrish ne ya faɗi lokacin da tayi arba da ita,har sai da ta ambaci Innalillahi acikin zuciyarta,ba komae ya firgitar da ita ba face ganin fuskar sgr a fuskar matar,kuma batasan da ita acikin gidan ba, sai dai lokaci guda taji aranta kaman ta ta6a ganin hoton matar,
Cike da mamaki Alexandra tace"wacece wannan kuma"?tayi maganar tare da yin nuni da sehrish wadda tuni ta koma bayan abusufyan ta tsaya,
Jahan ne ya bata amsa da cewa"Ƴan ukun uncle abusufyan ne,'.
"Abusufyan kuma?dama ya ta6a aure ne?
"Eh,ya ta6a aure batare da sanin kowa ba,sai daga baya abun ya bayyana cewar ƴa'ƴansa ne,kuma ƴan ukune kamanninsu iri ɗaya sak,abunda yasa kika ga junaid ya ruɗe kenan,baisan cewa su uku bane,ɗaya ya sani acikinsu,muma sai jiya Allah yasa mukasan da zamansu muka san cewa ƴa'ƴanshi ne,Nasan abba zai sanar dake komai,'
Jinjina kai Alexandra tayi tare da ɗan ta6e bakinta,yayin da ta janye idanunta daga kan sehrish ta mayar dasu kan junaid dake ta faman sambatu,
"Abba pls ku fahimtar dani mana!meyasa nake ganin Sehrish guda uku?ko na samu ta6in hankali ne,'
"Junaid u should calm down ur mind,in baka natsu ba taya zamu fahimtar dakai,"acewar abbansu,
Jin hannun mutun acikin nata yasata yin saurin juyawa,sai lokacin ta lura dashi sam bata ga fitowarshi ba,
"Mommy,"ya ambaci sunanta cikin sanyin murya,cike da farin ciki tace"Fawan!ka farka daga baccin kenan"?tayi maganar ayayin da take janyo shi jikinta,sosai ta rungume shi,
"Mommy tun yaushe kika zo ba'a sanar mun ba?sae dai na fito na ganki unexpected"
"Tun jiya nazo fawan,muna tare da junaid acan gidana muka kwana tare dashi sai yau da safe muka dawo atare,da fatan na sameka cikin ƙoshin lapiya,'
"Alhamdulillah mommy munyi missing ɗinki sosai da sosai,'
"Nima nayi missing ɗinku fawan,'magana suka cigaba dayi atsakaninsu,
Duk wannan abun dake faruwa alexandra bata tanka ma abusufyan ba,shima kuma bai tanka mata ba,tun lokacin daya shigo falon yayi arba da ita,yaga ta kawar da kanta gefe tun daga lokacin shima ya share ta,dama bata shiri dashi,tun lokacin da Abba ya aurota,ya ta6a zama agidan,yanayin yadda take wahalar da yayanshi ne yasa yayi mata rashin kunyar da ta haddasa gaba atsakaninsu,saboda shi bakinshi bai rufuwa muddin yaga tana gaya ma Yayanshi hossein magana saiya mayar mata da martani mai zafi,wannan dalilin ne yasa Abba yace ya tattara ya koma wurin ammi don bazai iya jurar zama dashi ba,kullum haɗa mashi Bomb yakeyi acikin gida,shiyasa abusufyan bai zauna agidan yayan nashi ba,kuma ammi bata kawo shi gidan ba lokacin daya addabeta da rashin jin maganarshi,kawai ta yanke shawarar kai shi gidan hajiya Ameenatu,
Kowa daya fito tun daga kan su irfan jabeer,khaleed da kanal yousouf babu wanda baiyi farin cikin zuwan mommynsu junaid ba,daya bayan ɗaya saida tayi hugging ɗinsu ajikinta,kanal yousouf ne kawai ta manna ma kiss a gefen fuskarshi,ji suke tamkar mahaifiyarsu ce Maryam ta dawo gidan,Allah sarki Allah ya jiƙan rai,tun daga yanayin yadda alexandra ta kar6esu hannu bibbiyu tana rungumarsu ransu ya basu cewar ta shiryu yanzu,da alama babu wannan girman kan nata da kuma Zafin ran nan,
Sehrish dae duk jikinta yayi sanyi tun daga kan irin kallon da taga Mommynsu junaid nayi mata,ranta ya bata cewar akwai matsala,sam fuskarta babu yabo babu fallasa lokacin da Jahan ke sanar da ita cewar ɗiyar uncle ɗinsu ce,
Abbansu na ƙoƙarin fahimtar da junaid,suka jiyo muryar sgr yana tambayar"Meya faru ne!"yayi maganar ne ayayin da yake saukowa daga saman stairs ɗin,jikinshi na sanye da shirt fara ta ɗame jikinshi sai kuma dogon wando jeans,ba ƙaramin kyau yayi ba,
Gaba daya suka juyo suna kallonshi,Marshal Omar na biye dashi abayanshi,atare suka sauko,
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e alexandra lokacin da tayi arba da first born dinta wato Surgeon General Rafayet,gaba ɗaya tagaza rufe bakinta saboda ba ƙaramin so take mashi ba,tana matuƙar alfahari dashi,
Sehrish kuwa tunda taji muryarshi taji gabanta ya faɗi rass,tabbas tayi kewarshi sosai,jiya abubuwan da suka faru ne suka hana takai mashi dinner ɗinshi,tasan cewa daƙyar ne idan yaci wani abu ajiyan nan,
Aranta tace"bansani ba ko yana farin ciki da kasancewata ƴar uwarshi,ɗiyar ƙanin Mahaifinshi,ko yaya yaji aranshi"?
Jahan ne ya sanar dasu abunda ya faru da junaid,
ƙarasawa Sgr yayi wurin Mommyn tasu,ita tafara manna mashi kiss a gefe da gefen fuskarshi sannan shima yayi mata kamar yadda tayi mashi,daga bisani kuma suka rungume junansu,
Abun ba ƙaramin burge sehrish yayi ba,har sai da ta ɗan saki murmushi kaɗan a fuskarta,
"Am really glad to see u mom,"ya furta hakan ayayin da suka raba jikinsu daga na juna,
Shafa gefen fuskarshi tayi tare da cewa"Yanzu ka kyauta mun?tun yaushe rabon dana sanya ka a idanuna Alex?ka daina zuwa wurina,kusan 1 year kenan baka tako ƙafarka kazo ba,'
Ganin hawaye sun cicciko a idanunta yasashi yin saurin ruko hannayenta tare da cewa"pls mom just forget about the past,nasan ban kyauta ba,amma kullum kina araina,kuma ina kiranki awaya muna gaisawa....'
Abbansu ne ya katse firar tasu da cewa"Ashe ba daɗi,Rama mun yayi Nima,ƙiri ƙiri kin rabani da aurena kinsa anata yi mun kallon Tazuru,'
Dariya sukayi gaba ɗayansu,banda sehrish dake tsaye jugum tana sauraronsu,
Matsawa Omar yayi cike da zolaya yace"Oh Mommy abun ƴar wariyar launin fata ce ko?atare da bro ɗina muka fito,amma ko kulani bakiyi ba...'yayi maganar yana ɗan ɗaure fuskarshi,
murmushi alexandra tayi tare da komawa wurin marshal,ta manna mashi kiss agefen fuskarshi sannan ta dafa shoulders ɗinshi tare da cewa"Omar ni bazan iya cewa komai ba,so nake nafara huce haushina akanshi kafin nadawo kanka,dama kaine mai ɗan son zumuncin,duk lokacin da kuka samu hutun aiki kana janyo shi kuzo wurina,amma yanzu duk kun juya mun baya,ni nasan duk shirin Abbanku ne yasan cewa dole nayi kewarku....'
Omar yace"no ba haka bane mommy,rayuwarce sai a slow,bamu manta dake ba,kuma kamar yadda rafayet ya fadi,muna kiran ki fa awaya kullum mu tambayi lpyrki,da ace kin ƙara 1 week baki zo nigeria ba,da kin ganmu munzo,ba don ma aiyuka da sukayi mana yawa ba,ae da mun rigaki zuwa....'
Ba ƙaramin daɗin kalaman Omar taji ba,yasan duk wata hanya da zaibi don ya kare kansu a wurinta,ba kamar SGR ba,shi kai tsaye kawai yake maganarshi ba wata kwana kwana,'
Sai da suka samu natsuwa sosai,sannan suka tattara hankalinsu kan junaid,
"Ina sehrish take ne"?Abbansu ne ya ambaci sunanta,saboda yaga gifcinta a wurin,
Da sauri ta amsa mashi da cewa"Gani nan Abba,"tayi maganar tare da fitowa daga tsayen da take abayan daddynsu,
Haɗa ido sukayi da Sgr,da sauri ta kawar da idonta,zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi,daƙyar ta iya ƙarasawa wurin abban nasu ta gaishe shi,
Bayan ya amsa mata yace"ki fahimtar da junaid,ina tunanin in yaji daga bakinki zaifi yadda cewa ku ƴan uku ne,'
Murmushi sehrish ta ɗan yi tana kallon fuskar junaid wanda ke kwance saman kujerar duk yabi ya rikita kanshi,tunda tayi magana yasan cewa itace saboda yaji muryarta,
Cikin sanyin murya ta soma magana,
"Junaid ka manta kwanaki na ta6a sanar dakai cewa Ina da ƴan uwa?waɗanda nake kira da wayarka?
"Amma ai kince mun baki da wasu ƴan uwa lokacin da muka yi maki magana akansu ni da aunty azmee,"yayi maganar yana faman hura hanci,
"Junaid a lokacin bana cikin hayyacina bansan ya akai na manta dasu ba,amma yanzu nadawo hayyacina kuma Zan iya tuna komai a game dasu,idan baka yadda dani ba,bari na tuna maka,ko ka tuna Yarinyar daka ɗauko a school cikin motarka?tun lokacin saida nayi ƙoƙarin fahimtar dakai cewar bani bace,ni ina a makaranta ka barni,shine dalilin da yasa nasha wahala aranar,'
Jin wannan maganar ta sehrish yasa junaid miƙewa daga zaune,bakomai ne ya faɗo mashi aranshi ba face,yadda jahad ta kasa sakewa dashi,kuma launin gashin kanta baƙi ne ba irin na sehrish ba,hatta muryarsu ma akwai ɗan bambanci,haba no wonder shi dae ya jima yana tunanin cewa al'jana ya ɗauko a motarshi ashe ashe mutunce,indae dagaske ne xancen sehrish hakan na nufin cewa ƴar uwartace ya ɗauko a motarshi?to kodai sune yaran da Ya Omar ɗinsu yasa su gyarama gidan uncle ɗinsu zai kawosu suyi rayuwa aciki......'bai ƙarasa zancen zucin nashi ba,Muryar Omar ta katse Hanzarin shi"Junaid!maganar da take faɗa maka dagaske ne!they're triplet,kuma ƴa'ƴan uncle abusufyan ne,dukanmu bamu son da haka ba sai jiya Allah ya bayyana mana komai,'
Yana kai ƙarshen maganar tashi ya juya tare da kallon fawan yace"Kaje ka kira mun su hosana da jahad suzo ya gansu da idanunshi don ya shaida cewar mutane ne ba aljanu ba,'
Cike da zumuɗi fawan ya wuce bedroom ɗin sehrish a lokacin har jahad ta kammala shirya kanta cikin riga da skirt na sehrish,ba ƙaramin kyau tayi ba,
Kwankwasa ƙopar fawan yayi kafin ya turo tare da cewa"Ya omar nason ganinku yanzu,'jin haka yasa sukayi saurin kimtsawa,duk suka yafa gyala a kansu,
Atare da fawan suka shigo cikin main palour ɗin,
Jerawa sukayi kusa da sehrish duk sun sha jinin jikinsu tsoransu kar ace wani abun ne kuma ya taso,
zuba masu ido junaid yayi yana kallonsu,idan ya kalli jahad sai ya kalli hosana,
A ƙarshe ya tsaida idanunshi kan jahad,ta hanyar gashin girarta ya gane cewa itace ya ɗauko a motarshi,har suka sha Love,
Dafe kanshi yayi tare da cewa"OMG!Abba kenan reesh ƴar uwata ce,jini na,ɗiyar uncle ɗinmu abusufyan!taya hakan ya faru?kuma dama rishi ƴan uku ne su ba ita kaɗae bace!idan har dagaske ne meyasa basu taso atare damu ba!!!!!!!_
Karaf maganganun da junaid ke faɗi suka dira a kunnan Hayaam,wadda fitowarta kenan,yunwa ta korota daga bedroom ɗinta ta gaza jurewa shine ta lalla6a ta fito don ta shiga kitchen,
Gabanta ne yayi wani irin bugu ji kake rasss!rarasss!hankali amatuƙar tashe ta ɗago da idanunta ta sauke su akan Mutanen dake tsaitsaye acikin falon,waro ido waje tayi ganin Sehrish dasu jahad,anan ta tuna abunda azmee ta faɗa mata jiya na cewa ƴan uku ne su,kuma kamanninsu iri ɗaya sak,a fili ta ambaci"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!Ya Allah ka rabani da mugun Ji da kuma mugun gani!nashiga uku Ni yau Hayaam,bari dae na ƙara kasa kunne naji uban da suke tattaunawa,ya Allah kasa korar shaggun za'ayi daga gidan,
"Junaid sehrish ɗin daka sani da kuma waɗannan biyun masu kama da ita sak,ƴa'ƴana ne,ni ne mahaifinsu,Na auri mahaifiyarsu ne ba tare da sanin kowa ba........'ataƙaice Abusufyan ya fayyace ma Junaid komai,
Saboda tsabar kiɗima hayaam ƙiris ya rage ta fasa ƙara a wurin,ta matukar firgita da jin abunda abusufyan ya sanar ma jahad,tashin hankalin da ba'a sama shi date,gudu gudu,sauri sauri hada tuntube wurin komawarta cikin bedroom ɗinta,jikinta sae faman kerma yake yi kamar wadda sanyi ya kama,hannu ta aza asaman kanta tana faɗin"nashiga uku!na bani na lalace!ƙarshe na yazo acikin gidan nan!taya akai haka ya faru duk ina nan sake da baki bansani ba,wai yanzu dagaske yarinyar nan mai aikin gidan dana raina,nake ganinta ƙaskantacciya yar wurin uncle ɗinsu ce Abusufyan,Tabɗijancan,Kallo ya koma sama!kai anya kuwa banyi kuskure wurin sauraran maganar shi ba?
Turo ƙopar da akayi ne yasa ta yin firgit ta juya,
Tana ganin azmee hannunta ɗauke da plate na breakfast ɗin da ta kawo mata,
Jiki na rawa hayaam ta ƙarasa wurinta tare da cewa"Aunty Azmee wai dagaske ne Seh...seh..rish ɗiyar uncle ɗinsu ce abusufyan!"
Ƙayataccen murmushi azmee ta saki tare da cewa"Dagaske ne mana!Nima sai da asuba nakejin wannan labarin a wurin Hajiya azeemarsu....'tunda azmee ta soma magana hayaam ta fita hayyacinta,
Har sai da azmee ta ambaci sunanta"Hayaam!naga kamar kin tafi duniyar tunani ne?lafiyarki kuwa?
Murmushin yaƙe ta saki tana ƙoƙarin danne damuwarta tace"Azmee bana jin daɗi ne,zuciyata tafarfasa takeyi ne,"
.azmee tace"Allah sarki,dama saida raina ya bani cewa baki lafiya,To Allah ya sawake,yanzu dae ga wannan ki fara karyawa nasan kina jin yunwa.....'
Wani irin bugu Hayaam takai ma plate ɗin dake hannun azmee nan take yayi gefe guda ya tarwatse ƙasa,snacks ɗin dake aciki suka 6are,
Ita kanta hayaam sai da ta firgita saboda ba'a cikin hayyacinta tayi hakan ba,tsananin 6acin rai ne da ƙiɗimar da tayi,
Hankali tashe azmee tace"Hayaam!!'
Tunkan ta karasa maganar hayamm ta zukunna jiki na rawa tashiga kwashe snacks ɗin dake zube aƙasa tana mayarwa cikin plate din,
Muryarta na rawa tace"dan Allah aunty azmee ki tafi kawai,nagode sosai zanci....'
Ƙiris ya rage azmee ta fashe da dariya,ganin yadda la66an hayaam ke kerma kamar gandar nama,tasan cewa duk akansu sehrish ne,
"Allah ya baki lafiya,"ta ambaci hakan tare da juyawa tabar mata ɗakin,
Azmee na fita hayaam ta jefar da plate ɗin,
. miƙewa tsaye tayi nan fa tashiga safa da marwa tana zagaye ɗakin,bakowa ne ya faɗo mata aranta ba face Aunty laila,tabbas ya kamata tayi gaggawar sanar da ita halin da ake ciki,
Jiki na rawa ta ɗauko wayarta dake ajiye saman mirror,tana danna wayar yatsun hannunta na kakarwa,daƙyar ta tsaida hankalinta wuri guda ta danna ma Aunty Babba kira.
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga