Showing 261001 words to 264000 words out of 307403 words

Chapter 88 - Abban Sojoji Takun Karshe Hausa Novel Complete

"Yana gidan Dr harriet,Nasan kasanta,"
Tunkafin takai ƙarshen Maganar,Omar yayi hanzarin juyawa a gaggauce Ya fuce daga cikin gidan,Mota ya shiga,Major yajasu da gudun gaske zuwa gidan,dan bazai manta kwatancen gidan ba,tunda sun ta6a zuwa a lokacin baya,

Yana yin parking ɗin motar,tunkafin Major ya zagayo ya buɗe mashi ƙopa,Yasa hannu ya ture murfin motar,kaitsaye ya nufi cikin gidan,A buɗe ya samu ƙopar da zata sadaka da palourn gidan,ko sallama baiyi ba ya faɗa cikin gidan,A saman dining ya taras da Harriet tare da twins ɗinta matasan ƴan mata su biyu suna yin breakfast,Tana ganin shi ta soma sakin murmushi,
"Omar yau kaine a gidana,"bai amsa mata tambayarta ba,Sai cewa yayi"Ina Rafayet yake,"?jim ta ɗanyi tana kallonshi Sam babu natsuwa atattare dashi,dama tayi mamakin ganinshi,
Nuna mashi upstairs tayi"Suna acan sama,"ko kwatancen ɗakin bai tsaya tayi mashi ba,Da gudun gaske ya haye stairs ɗin,cikin sa'a ya gano ɗakin,Yana turo ƙopar Ya samu Sehrish zaune ta jingina kanta jikin headboard na gadon,Duk atakure take,

"Sister,"ya ambaci sunanta da wata irin kasalalliyar murya,
Firgigit sehrish ta ware idanuwanta akanshi,tana ganinshi wani irin farin ciki ya lullu6eta,"Ya Omar",Da sauri ya ƙarasa gefen gadon ya zauna,Zuba mata ido yayi yana kallon Canzawar da tayi,Ta rame sosai takuma yi haske,

"Ya jikin naki"?bata amsa mashi ba,saboda kukan daya ciyota,Sosai ta fashe mashi da kuka,ruƙo hannayenshi tayi"Ya Omar dan Allah ka tafi dani gida,Wlh banjin daɗin zama anan,nafison na ganni cikin ƴan uwana"
Tsananin tausayinta ne ya kamashi,tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi,
"Ya Omar wlh ka tafi dani gida tunkafin Ya rafayet Ya fito,don bazai ta6a bari ka tafi dani ba,Ni kuma natsani zama a gidan nan,duk a ƙuntace nake babu daɗi,"
"Yana ina rafayet ɗin"?
"Ya shiga wanka"
Jinjina kanshi ya ɗanyi,kafin yace"Zaki iya tafiya,"
Girgiza kai tayi"a'a bazan iyaba",don tasan in dae da kafafunta zata taka to kuwa har sgr ya fito ya gansu,
Batare da 6ata Lokaci ba Omar ya ɗauketa saman kafadarshi ya sauko downstairs da ita,Dr harriet na ganinshi da ita,Hankalinta ya tashi aruɗe ta tare shi tana faɗin"Omar where are u going with her?Rafayet ne ya baka izni?Ko alex ce tace kazo ka ɗauketa,
Tunkafin Omar yayi magana Sehrish tace"Ya Omar kada ka saurareta,wlh in ka barni acikin gidan nan Poison zansha in mutu,"yana jin haka ya ƙara harzuka,
Ko kallon Harriet baiyi ba Ya fuce daga falon,Major ya bude mashi mota ya shigar da sehrish yana cewa"nasan idan ya fito yaji cewa Mun tafi da ita,dole ya dawo gida,"

Da gudun gaske Motar major ta fuce daga cikin gidan,Sehrish sai faman sauke ajiyar zuciya take yi,baiwar Allah daga ita sai wannan rigar mai kama da uniform,Ƴan ƙafafuwan ko takalma babu,Kanta ko mayafi babu sai dai gashin kanta dake a cukurkuɗe,duk ta ƙosa taga Mahaifiyarta da mahaifinta,da kuma ƴan uwanta,Rafayet ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,ya ƙumsa mata baƙin cikin da bazata ta6a mantawa ba,Ya sanya mata ƙiyayyarsa acikin zuciyarta,

A hankali Major Ya shigar da motar ta cikin babban gate ɗin gidan,Bayan yayi parking ɗinta,Ya fito da sauri Ya buɗe mashi Mota,Saukowa marshal yayi tare da zura hannayenshi Ya kinkimo Sehrish asaman kafaɗarshi,
"Thank u Major"Yana ambaton hakan ya wuce da ita cikin gidan,A lokacin babu kowa a palour sai dai mutanan dake kitchen suna shirya breakfast,Yana yin sallama hankalinsu Ya dawo kan Omar dayake suna hangenshi daga inda yake,Koda abu tayi arba da matashiyar dake kwance asaman kafaɗarshi,nan take taji aranta cewa Sehrish ce,Da gudun gaske ta fito daga kitchen ɗin,Hajiya azeema tare da Mommy suka biyo bayanta,Ai koda Mommy taganshi ɗauke da sehrish sai da gabanta Ya faɗi,Har warning tayi mashi akan kar ya sanarwa kowa inda ta suke,Sai gashi ɗungurugum Ya ɗauko ta,

Aruɗe abu take kallonta"Sehrish ce?Meya faru da ita"?tayi tambayar tana ƙare mata kallo,har lokacin bai sauketa daga kan faɗarshi ba,
Hajiya azeema kuwa Alhamdulillah ta soma faɗi,fuskarta ɗauke da murmushi,duk da ta damuwa sosai ganin yadda ta rame,
"Dan Allah ku faɗamun meya faru da ita,Meyasa nake ganinta haka?kamar bata da lafiya,"
Omar na ƙoƙarin Yin Magana,Sehrish Tace"Oumma,Lafiyata qalou,Yaya Omar ka kaini ɗaki inaso inga ƴan uwana,"
Wucewa bedroom ɗinsu yayi,da sauri suka bi bayanshi,jikin abu duk yayi sanyi,koba a fada mata ba tasan cewa babu lafiya atattare da ita,tunda har bazata iya tafiya da ƙafafuwanta ba,Suna ƙarasowa kopar ɗakin,Oumma ta buɗe mashi Ya shiga da ita,A lokacin Jahad na zaune gefen gadon Tana karatun al'qur'ani,Hosana kuma ta kabbara sallah,Don bata samu yin sallar a lokacinta ba,

A firgice Jahad ta miƙe tana kallon Ya Omar dake ɗauke da Sehrish,da ƙarfi ta ambaci sunanta Sehrish!Ae Hosana najin an kira sunan Sehrish Ta katse sallar da take yi dama tunda suka shigo take ƴan waige waige,A hankali Omar ya zaunar da ita samam gadon,Ya sanya mata pillow a bayanta,ɗaya bayan ɗaya take bin fuskokinsu da kallo kamar yadda suma suke binta da kallon ƙurulla,Hosana sai tsalle take yi tana ambaton sunanta saboda murna,

Fashewa Sehrish tayi da matsanancin kuka,Da sauri ta sanya tafin hannunta asaman fuskarta,tsananin tausayinta ne ya kamasu,da sauri Oumma ta zauna gefen gadon"Sehrish meya faru dake ne?na damu sosai akan rashin ganinki,Har Abusufyan na tambaya yake sanar dani cewa kunyi tafiya keda babban yayanku,"kasa buɗe baki sehrish tayi,saboda ƙululun baƙin cikin da ya tokare mata makoshinta,A duk lokacin data tuna abunda Sgr yayi mata,
Zuƙunnowa Hajiya azeema tayi saitin fuskarta"Pls stop crying,Wlh nashiga damuwa sosai akan rashinki,banji daɗin abunda ya faru ba,Amma kiyi haƙuri haka Allah ya ƙaddara maki,Yanzu dai ki sassauta kukan nan naki,kodan saboda mahaifiyarki zata shiga damuwa sosai"tayi maganar ne ta yadda abu bazata iya jiyota ba,
"Koda sun tambayeki meyake damunki,Kice baki da lafiya zazza6ine ya kamaki,"cikin shessheƙar kuka Sehrish ta ɗaga mata kai alamar zatayi yadda tace,Miƙewa Hajiya azeema ta yi,Jahad ta zauna saman side drawer na gadon tana tambayarta Lafiya,
Cikin shessheƙar kuka tace"Bani da lafiya ne,Amma jikin da sauƙi,kawai nayi kewarku ne sosai,"
Kallonta kawai Jahad take yi ba don ta yadda da abunda tace ba,
"Tana buƙatar hutu,Bai kamata mu takura mata da tambayoyi ba,idan ta huta sai muyi magana da ita,"acewar Hajiya Azeema,daga haka babu wanda ya ƙara tambayarta,
Matsawa abu tayi kusa da ita,ta sanya hannunta ta rungumota jikinta,wani irin zafi dama kullum cikin zazza6in take,
"Allah ya baki lafiya Sehrish,"
"Ameen Oumma,"_

Mommy kuwa bayan fitar Omar da sauri tabi bayanshi,
"Why omar meyasa zaka ɗaukota?haka mukayi dakai"?
Juyawo yayi fuskarshi sam babu annuri acikinta,.
"Haba mommy,don me zan barta acan?An ƙuntata rayuwar yarinyar nan sosai,Na farko an cutar da ita,na biyu kuma an kaita wani wuri inda batasan kowa ba,Hakanan ya rabata da kowa nata,lokacin dana je kuka ta dinga yi mun tana ruƙe hannuwana akan in tafi da ita gida kota kashe kanta,Shiyasa na yanke shawarar ɗaukota,Tunda jikin nata da sauƙi,"
"Shikenan Omar,Nima nayi tunanin a dawo da ita gidan,Kawai ina fargabar halin da Zasu shiga ne idan suka ganta,"
"Kada ki damu Mommy,rashin ganinta a kusa dasu shiya fi haɗari,Amma in tana atare dasu,To da sauƙi,ita kanta tafi son cikin ƴan uwanta,"
Jinjina kai Mommy tayi"Wannan haka yake,nagode sosai Omar,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa Ta nufi kitchen,shi kuma Ya wuce ɗakin Abusufyan,Hannu yasa yana kwankwasa kopar,A lokacin Abusufyan yana ta faman zarya cikin ɗakin,Damuwa duk ta isheshi,jin knocking ɗin ƙopar yasa shi yin hanzarin juyawa yaje ya buɗe mashi,
Tunda yaga fuskar Omar awashe ranshi ya bashi cewa Akwai labari me daɗi,.
Muryarshi na kerma yace"Omar,An gano inda suke,".
Fuskar Omar ɗauke da murmushi yace"yanzu haka Sehrish tana aɗakinsu,"tunkan yakai ƙarshen maganar Abusufyan Ya fuce da sauri har yana tuntu6e,

Suna zaune saman gadon sun zagayeta,Sai gashi Ya banko ƙopar dakin Yana ambaton sunanta"Sehrish!"yadda kasan makoshinshi zai 6allo,
"Daddy,"ta amsa mashi fuskarta ɗauke da murmushi,Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarshi,Da sauri ya ƙarasa suka matsa mashi,Ya hau saman gadon Ya rungumota jikinshi,Wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya Ya sauke,Wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke mashi fuskarshi,
"Daughter,Am sorry for everything,i ave regretted already,duk nine silar halin da kika tsinci kanki,"sosai yayi tighting ɗinta ajikinshi,tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi,
tamkar raɗa haka yake yi mata maganar don kar suji abunda yake cewa,tunda bakowa yasan ainihin abunda ya faru da ita ba,
Cikin shessheƙar tace"Daddy kamar Bazan rayu ba,Nasha wahala,Lokacin mutuwa nane kawai baiyi ba,'
"Nasani,wlh naji ajikina Daughter,danasan hakan zata faru da ban tursasa mashi akan ya sakeki ba,da duk hakan bata faru ba,"Sai lokacin Sehrish ta gane dalilin dayasa Sgr yayi mata hakan,
Janyeta yayi daga jikinshi,tare da sanya hannunshi asaman fuskarta yana share mata hawayenta yace"Ina babban yayan naku?nayi tunanin atare dashi zaku dawo,'
Girgiza kai ta ɗan yi"A'a,Sai zuwa anjima zai dawo,Ya Omar ne ya kawo ni,Na matsa mashi ne akan inaso na dawo gida," sunyi pretending ne don kada Oummansu ta gano gaskiyar abunda Ya faru da ita,
"Allah ya baki Lafiya Daughter,"
"Ameen daddy,"
Turo kopar ɗakin akayi,Mommy ce ta shigo hannunta ruke da plate mai ɗauke da farfesun nama,da zafi zafinshi sai ƙamshi yake yi,

Ƙarasowa ciki tayi fuskarta a ɗan sake tace"Ya jikin naki,"
Batare da sehrish ta kalleta ba ta amsata"da sauki Mommy,"
Miƙa ma Abu plate ɗin tayi"Ga wannan nasan zata buƙace shi,Akwai tea dana haɗa mata,bari naje na ɗauko mata shi,"
Hannu bibbiyu Oumma tasa ta kar6i plate ɗin"Mun gode sosai,"
"Kada ki damu,duk yiwa kaine"takai ƙarshen maganar,tare da juyawa a hanzarce tabar bedroom ɗin,Abusufyan ya lura da sehrish,tunda Mommy ta shigo bata kalli fuskarta ba,tayi hakanne saboda ta tsani ganin fuskar Sgr,Ita kuma Mommy dashi take kama shiyasa taƙi kallonta,
Shafa fuskarta yayi"Daughter,"murmushi ta ɗan saki batare data ɗago da idanuwanta ba,Sun cika tab da kwalla,
Juyawa yayi tare da kallon Abu dake tsaye hannunta ruƙe da plate,.
Kar6ar plate ɗin yayi daga hannunta,
Ruƙo hannun Oumma Mommy azeema tayi"mu koma kitchen munbar Aiki acan,In sha Allah zata samu sauƙi,"atare suka fuce daga ɗakin,
Ya rage daga Abusufyan Sai Hosana da Jahad dake kewaye da ita,
jim kaɗan Mommy ta dawo hannunta ɗauke da Cup wanda ta haɗa mata Kakkauran tea acikinsa,
Asaman side drawer ta ajiye mata Cup ɗin,
Kafin ta juya tabar dakin,
"Rishi wai ina kika shiga ne?Kin tafi kin barmu da tunani,"Hosana ce tayi maganar fuskarta a yamutse,
Jahad tace"Dan Allah kibarta ta huta,Ba kiga bata da lafiya ba,Sannu Sehrish Allah ya baki Lafiya,muryarta ƙasa ƙasa ta amsa mata da Ameen,
Abusufyan da kanshi Ya zauna yana bata farfesun abakinta,Cike da kulawa,ba ƙaramin daɗinshi taji ba,sosai tasha,kusan duka ta shanye duk da hosana ta tsoma masu hannu,Ta dinga ɗaukar naman tana turawa abakinta wai ae itama bata ci ba,

Bayan ta kammala Ya ajiye plate ɗin Ya dauki cup of tea ɗin da mommy ta ajiye mata,A baki ya kafa mata shi,Sosai ta shiga kur6arshi abakinta,
"Amma nima ka bani tea ɗin abaki"?
Hosana ce tayi maganar,tana tura mashi bakinta,Hakan ba ƙaramin dariya yaso ya basu ba,murmushi sehrish ta ɗan saki tana kallonta,
"Daddy ka bata tasha,"
Cike da zolaya Abusufyan yace"Na mara lafiya ne,Hosana kiyi hakuri wannan na sehrish ne,bata baki tausayi ba Kalli fa ki gani duk ta rame,"
A shagwa6e Hosana ta langwa6ar da kanta,tasa hannu tana nuna mashi ƙashin wuyanta,
"Daddy ae nima banda Lafiya,Kalli ka gani,"
Kallon wuyanta yayi acike yake babu wani ƙashin daya leƙo,
Harara Jahad ta ɗan watsa mata"Saboda kofin tea zaki jama kanki ciwo,Tirr da wannan halin naki,Shegen Ci kamar gara"
Guntun tsoki Hosana taja"eh ɗin ina ruwanki,Ƴar shigar shugula,ba'a kasa dake ba,kin tsomo mana baki,".
Dariya sosai Abusufyan yayi yana kallonsu,ita kanta Sehrish murmushi ne kwance akan fuskarta,Hankalinta Ya kwanta sosai,gata ga iyayenta ga kuma ƴan uwanta,

Kwankwasa ƙopar ɗakin akayi,Abusufyan yace"Wanene"?
"Nice Amrish,"
"Okey shigo daga ciki,"turo ƙopar ɗakin tayi,jikinta sanye da hijabi dai dai guiwa,Waro ido waje tayi ganin Sehrish
Da ƙarfi ta ambaci sunanta"SEHRISH"
Wani irin farin ciki ne ya lullu6ete,har ta manta da abusufyan dake zaune,Da gudu ta ƙarasa gefen gadon,Ta haura sama ta rungumota ajikinta,
"Sehrish ina kika shiga ne?ina ta nemanki?Oumma tace mun kunyi tafiya keda Babban yayanku,"
Fuskar Sehrish ɗauke da murmushi tace"Am sorry Amrish,Nayi laifi ban sanar dake ba,Tafiyarce ban shirya mata ba,ni kaina bansan da ita ba,"
ɗagowa amrish tayi daga jikinta ta sanya tafin hannayenta ta tallabo fuskar Sehrish"Duk kin rame,Baki lafiya ne "
"Zazza6i nake yi,"
Gyaran murya Abusufyan yayi mata,Da sauri Amrish ta sauko daga saman gadon ta zuƙunna tana gaishe shi"Ina kwana daddy,An tashi lafiya,Ya mai jiki,"
Murmushi Abusufyan ya sakar mata tare da cewa"Lafiya Lou,yaushe rabon dana sanyaki acikin idanuwana,bakyason zuwa kina gaishe ni ko"?
Sunnar dakai ƙasa tayi cike da jin kunyarshi tace"A'a,inason zuwa,"
"Baki ɗaukeni a matsayin mahaifinki bane"?
Da sauri tace"Na ɗauke ka,"
"To meyasa bakya sakin jiki dani ne"?
Shiru tayi batace Komai ba,
"Daga yanzu inaso ki saki jikinki dani,Dake dasu Sehrish duk ɗaya kuke a wurina,duk wani abu da kike buƙata na rayuwa,ki sanar dani ni kuma zanyi maki shi,"
"Nagode sosai Daddy,"ta ambaci hakan tare da miƙewa,
"Sehrish wayarki na ɗaki,bari na ɗauko maki ita,"
Da sauri ta juya ta fuce daga ɗakin,Kallonta Abusufyan yayi,
"U need a rest,ki kwanta ki huta,Zuwa anjima zan sake zuwa dubaki,Yanzu hankalina ya kwanta,ashe da rabon yau inyi bacci hada minshari don tunda kuka tafi wlh ban runtsawa sai dae bacci 6arawo ya dan dauke ni Daughter,"
Murmushi ta ɗan saki,mikewa yayi tare da kallonsu Jahad yace"Ku kulamun da ita pls,"
Atare suka amsa mashi da toh,kafin ya bude kopar ɗakin ya fuce,

Baijima da fita ba,Amrish ta shigo ɗakin hannunta ruƙe da wayar Sehrish,zama gefen gadon tayi tare da miƙa mata wayar,hannu tasa ta kar6i wayar,
"Ya jikin naki"?
"Am feeling better now,nayi missing dinku sosai,"
Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Nima nayi missing ɗinki sosai,Kullum saina tambayi Oumma yaushe zaki dawo,"
"Allah sarki,nagode sosai da nuna damuwarku akaina,"

Bayan fitar Abusufyan kaitsaye ya nufi ɗakin Ammi,A lokacin khadija da nafeesat suna acikin ɗakinta,Suna tattaunawa game da bikin da za'ayi,

Da sallama ya shiga ɗakin,atare suka amsa mashi,da sauri suka soma gaisar dashi,fuskarshi asake ya amsa masu,Suna zaune ƙasa sun lankwashe kafafunsu,Ammi kuma na zaune gefen gadonta,
Agabanta ya zuƙunna"Ina kwana Ammi,kun tashi lafiya,"
"Lafiya lou,Autana,Ina fata kaima haka,"
"Alhamdulillah"ya amsa mata,
"Da alama yau akwai labari me daɗi akan fuskarka,murmushi ya saki tare dacewa"Ammi Sehrish ta dawo,Yanzu haka daga ɗakinsu nake,"
"Masha Allah,Kai amma naji daɗi sosai wlh,Amma waye ya kawota?
"Omar ne ya ɗaukota,"
"Amma ya lafiyar jikin nata"
"Da sauki ammi,"
Miƙewa tayi hannunta ruƙe da sandarta,kallonsu Nafisat tayi"yanzu zan dawo,Zanje na duba jikin jikata ne,"
Mikewa sukayi atare"Muma zamu je ammi,"
Murmushi tasaki"shikenan bismilla,"Abusufyan Ya shiga gaba suka bi bayanshi,har zuwa ɗakin Su Sehrish,
Ba ƙaramin farin ciki ammi tayi ba,Ganin yadda sehrish take ta faman sakin murmushi,tashi Amrish tayi daga gefen gadon,Ammi ta sauna suna fuskantar juna ita da sehrish,
Atare suka haɗa baki suna gaishe da ita,Bayan ta amsa masu tace"Ya jikin naki"?
"Naji sauki,"
Jinjina kai ammi tayi"Alhamdulillah mun godewa Allah,Haka mukeso,"Takai ƙarshen maganar tare da kallonsu Khadija dake atsaye,Ga ƴar uwarku nan,ɗaya daga cikin ƴan ukun Abusufyan ne,Bata da lafiya ne,"

Har suna hada baki wurin yi mata Ya jiki,fuskarta asake ta amsa masu,kafin ta soma gabatar masu dasu,
"Jikokin modibbo ne,Ƴa'ƴan ƙanwar Mahaifiyarsu Omar,sannan kuma nan bada jimawa ba,Zasu zama surukan Abba,ta 6angaren Adam Da Osman"

Farin ciki ne ya lullu6esu,Ammi taci gaba da cewa"su kuma waɗannan zasu bi sahunku suma,Wato zasu Zama surukan Abba,Ga Sehrish nan Amaryar Babban Yayansu,ɗan wurin Fatima," tunda ammi ta ambaci hakan ran Sehrish ya 6aci sosai,tuni ta ɗaure fuskarta,Sam babu wanda ya lura da ita,
"Bayan ita kuma Sai Jahad,Amaryar shalelen Abba wato Junaid,"da sauri jahad Ta kife kanta saman katifar saboda kunya,
"Ita kuma wannan,Mai hankalin cikinsu,Amaryar Omar ce in sha Allah,"
Fashewa Hosana tayi da dariya,kowa najin kunya banda ita,
"Inason nayi magana da ita, ku ɗan bamu wuri,"

Amsa mata suka yi da toh,Gaba ɗaya suka fuce daga dakin,A waje suka tsaya suna fira atsakaninsu,Amrish dai tayi shiru saboda ita batasan matsayarta ba,Amma taso ace hada ita za'a ɗaurama aure,Itama ta zama ɗaya daga cikin amaren gidan,

Bayan fitarsu Ammi ta zauna tayi mata nasiha sosai,ta kuma nuna mata 6acin ranta akan abunda Sgr yayi mata,A ƙarshe ta ruƙe hannayenta"Bazanso abunda zai cutar dake ba,Dama jiran dawowarki nake yi,Saboda inaso inji ra'ayinki game dashi,Kina son Cigaba da rayuwa dashi,Ko kuwa A'a,"
kamar jira takeyi da sauri tace"Banaso ammi,dan Allah ku rabani dashi,wlh bazan iya rayuwa dashi ba,Ni dai kawai asanyashi Ya sake ni,"hada hawayenta,
Shiru ammi ta ɗan yi tana kallonta,Kafin tace"Amma fa yana sonki sosai,Wanda silar hakan ne yajawo har ya aikata maki hakan,Saboda anyi ƙoƙarin rabashi dake,"
Cikin shessheƙar tace"Nidai bana sonshi ammi,wlh yafita araina,"
Ajiyar zuciya ammi ta sauke,
"Shikenan,In sha Allah zan shiga tsakaninki dashi"

WANNAN KENAN!

*masu yi mun ya jiki nagode sosai da irin kulawarku,kuma in sha Allah kamar yadda nace very soon zan kammala maku littafi in Allah ya yarda,koda ba lafiya indai yatsun hannuna na motsi zan daure inyi ne,Don in gama akan lokaci,kafin watan ramadan,*Ga mai buƙatar karanta Littafin Abban Sojoji from Book one to 3,Yayi mun magana ta whatsapp 08103884440*
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*


*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*




Story And written By

*Hafsat Bature*




Not edited



Ammi ta jima zaune a wurinta,kafin daga bisani tayi mata sallama ta fita,A hankali ta gyara kwanciyarta samam gadon,lumshe idanuwanta tayi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata abunda ya faru lokacin Da Sgr Ya farmaketa,wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta,a irin kallon da take yi mashi yanzu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login